Showing 129001 words to 132000 words out of 231198 words

Chapter 44 - TAKARI Book Complete by Zainab Makawa .txt

kalla lokacin kuma hararan da Amal take min yabani dariya,
Sai yayi sa,a ina dariya a lokacin, Abinda yadade baigani ba ke nan tun ina yar karama a Riyadh lokacin da nake shiga cikin ruwa ina wasa agidan shi,
Murmushi ne ya subce mai ba shiri saboda tunawa da yayi da wanan lokacin
Saboda yaga yadda nake wasa daruwa har dawo yakeyi ya tsaya ta glass din falon shi yana kallo na ,,
Saboda haka kawai yaji in burge shi dan banda tsoro ko fargaba kai tsaye nake abina,,,
Aziza ce tace min inzo in kwashi kayans intafi dasu,
Tazabe duk wanin abinda take bukata daga ciki tabar min sauran tarkacen da rigunonin,
Da alama sheriff yaji dadin hakan da tayi har cikin rashi yace mata
Kai amma dai wanan fitar dama na tane ko ,
Tadan rausaya kanta tace aikasan dole in saya mata tunda har ta bata lokacinta ta rakani batare da nuna gazawanta ,,,
Ina kwasan kayan gurin Amal na nufa direct dasu nara dai dai nace mata ta zabi duk wanda take so tabar min kashi guda,.
Dariyan yake tayi ko shi don yayanta ya gurin ne don kada yace wani abu da bata karbi kayan ba,
Amal tace a,a ki bari kawai in dauki wanan,
Wani dan rigar barci kawai ta dauka,
Tundaga wanan ranan wani irin shakuwa da amin taka ya shiga tsakani na da Aziza ,,
Amal tai min fada taimin nasiha tace inyi hankali da ita don yar duniya ce,
Badan Allah take so na ba ita tana ga da wani manufa take jana ,a jikin ta,
Sai naga cewa kawai, kamar dai don basu ra,ayinta ne kawai,


Yau shiru tunda safe banga Aziza ba a waje ganin da nayi cewa anytime tafito sai ta nemay inda nake ,
Yasa da banganta a waje ba na hausama zuwa dakin su,
Kwance take rub da ciki nai sallama a hankali ta ansa min ,
Tajuyo daga rub da cikin da tayi kwancen, sai naga fuskan ta ya kunbura idon ta da almar tayi kuka ma,i,shin ta,
Subbahanallah nace da sauri na isa gurinta ina mai kokarin dafa ta,
Nace cikin rawar murya hjy mai yasa may ki ,ko baki da lafiya ne,
Duk lokaci guda na sako mata wanan tambayar a jere da juna
Girgiza min kai tayi kamar karamar yarinya,
Ta, bude baki da kyat tace min babu ko daya
Fadima
Matsalata tafi karfin fahintar ki kona fada maki bazaki gane ba saboda,
Ke yarinyace, shiru nayi kamar ina na,zari, can nace to amma anty aiko banza gane ba ai zan yi kila taimaka maki ta wani hanya ko,
Saida tadan shere wani hawaye dake shirin fito mata daga cikin idonta, ta hade miyau da karfi sanan ta mike da ga zauna
Hannaye na takama duka biyu ta hada wuri guda tace Fadima inda zaki fahince ni da kin san cewa muna cikin tashin hankali dagani har Ahmad saboda matsalar da ta samay mu,
Sai duk naji na matsu da insan kowata irin matsala ce haka wadda har yasa wanan jarumar matar kuka haka ,
Dan Allah hjy ki daure ki fada min koma maye ko zan san abin yi pls,
Fadima muna cikin matsala rashin haihuwa nida Ahmad munje asibiti likita yace bazan iya daukan ciki ba,
Sai kuma tasa kuka wi,wi,
Sai naji duk hankalina yatashi,, saboda wanan maganar ba karama bace ga duk wani mahulukin da yasan ciwon kanshi,
Tana shere hawaye taci gaba da fadin ,sai wanan test din da mukayi na karshe likita yace muna inda zan samo wata wacce zata taimaka min asa mata cikin ma,ana ai mata dashen cikin
Idan ya fara girma sai amayar min da abina yace yana ganin haka zai sa in samu baby,
Kinga kuma shi Ahmad baya ganin laifin kanshi sai nawa kinji halinda naje ciki fadima, tanayi tana kallon fuskana don taga irin re,action din da zan nuna,
Fuskana fal da tausayin su ban san lokacin da nafara kuka ba ,wi,wi, nima don ba karamar magana bace wanan,
Mutun kamar sheriff ace ba zai haihu ba, treble,,
Muryanta naji tana cewa amma fa kada ki fada ma kowa wanan sirinane da mijina na fada maki,
Saboda yarda da nai miki yasa har na fada maki sirina,
Hmmm hmmm
Wani sabon kuka nasa mai tsuma rai an muka rugumay juna mukai ta kuka har saida muka gaji,
Nakoma dakina fam da tunane da tausayin su,,,,


🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
6⃣7⃣
BY
🐎 ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎


Almost true life story,,,,,


Cikin dare na kasa yin barci mai nauyi saboda yawan tunanen da ke ta addabata,
Juyi kawai nake yi ina faman ajiyan zuciya da dan guntun tsaki,
A, gaskiya na tausaya ma sheriff din mu so sai yanzu ace duk tausayin shi da mutuncin shi bazai haihu ba,
Ashe haka wasu Allah ke halittan su, batare da haihuwa both miji da mata,,
Saboda ni nadauka cewa mutun guda akan ce baya haihuwa mijin ko matar,
Amma su sai,gashi wai duk kan su case din su gudane,
Babu mai karfin haihu daga cikin su,
Dan sanyin da naji shine cewar da tayi idan an yi dashen cikin za su iya haihuwa insha Allah,
Kwancin bai min hakan yaban damar mike na shiga bathroom na dauro alwala na fara nafila ina fadin bukata na, a wurin Allah,
Nafilan nan da nadan samu na gabatar yasani jin sanyi a zuciyana ,
Har na dan samu barci maidan nauyi yadauke ni zuwa asuba ,
Hakan ne ma yasani makara da sallah asuba,
Saida gari yadan yi haske nafar ka zubur da salatina a baki,
Saidai duk jikina ba karfi hakana naje nadauro alwala,
Ina zaune inda na sallamay sallah asuba ina ta kwarara ma sheriff da iyalin shi addu,a,
Shawar da na yanke tun cikin dare shi na yi niyar aiwatar wa,
Amal na dakinta kwance nafito nace mata zan je masjidul nana Aisha ,,
Da mamaki ta kalleni daga kwancen da take tace min tunda safe haka,
Murmushi nadan yi mata, nasamu gefen gadon ta, na zauna ina gyara belt din takalma na,.
Ido takura min har na kare daura belt din sai tace min may ke damun ki fadima,
Cikin dan basarwa nace mata kamar ya fa,
Hmmm kawai tace min,
Sai kuma tace bana son ki sa kanki acikin fitinar da ba zai amfane kiba, wlh
Saida na mike tsaye da kyau nace mata ba wani fitinar da nasa kaina, aciki Amal kece dai ke hasashen hakan,
Amma for me ba komai ina fadin haka na sa kai nabar dakin
Zuwa masjidul bai dauki wani lokaci saboda sanin hanyoyin da na yi acikin sauki,
Ina isa nai addu,a na dauro niyar umrah nadinga addu,a da larabci, da hausa kai har mada turanci duk na hada ,
Saida na gama dawa,fi, nadawo daidai saitin indararon nan naita zuba addu,a
Saikuma na koma daidai kofar dakin naba mukamin ibrahim baya, nadinga kwararo addu,a agurin,
Dalilin dayasa nai haka gurin hjy Laila nataba ji suna hira da hajiyar mu cewa indan mutum yana neman haihuwa koda dan uwan shi ne keson haihuwa,
Sai yaje yayi dawafi, ga bakwan karshe saika dada addu,a agurin indararo saboda anasa rai cewa guri ne da duk abinda ka roki ubangiji agurin zai ansa ma insha Allah,
Indan ka gama sai ka dawo daidai saitin kofar shiga shi ai,nihin dakin ka,aban ka tsaya tsakiya, inda hali ka dauki ruwan zam,zam kayi wanan dawafin da shi,
Karoki Ubangiji Allah bukatar ka insha Allah Allah zai karba ma mutun,
Wanan ruwan zam,zam din sai kaba wa wace ko wanda ke da lalurar haihuwa ko wani ciwo yasha ya shafa tare da bissimillaj,
Sanin danayi cewa Aziza bazata sha ruwan ba kila ko nakai mata yasa ban dauki ruwan nayi mata dawafin da shi ba,
Saidai addu,an da na tsaya tsakanin mukamin Ibrahima da kofar dakin ka,aba nayi na Allah yataimaka ya bawa sheriff din mu haihuwa mai albarka a rayuwan shi,
Tare da kwararo wa sauran al,umman musulumi a ddu,a,
Daga karshe na tsaya daga can gefen yamma kadan nadibi ruwan zam,zam nasha sai nayi nafila raka,a biyu
Nagode ma ubangijina subbahanahu wata ,ala,
Dana gama nadade gurin zaune na zubawa dakin ido sai naji wasu hawaye masu dumi suna zubowa daga ido na,
Nadade a hakan sannan natashi nasamu guri na zauna a gefe guda,
Ranan anan nai sallolina har i,sha,i ina gurin,
Sai da dare na zo hanya don in tare taxi zuwa gida sai na dinga jin hayaniya,
Ko ban waiga ba nasan cewa yan bagaladine ke kokarin kama wasu daga cikin yan yawon takari,
Hakane ne kuwa don dai daga inda nake inajin muryan su sunacewa Nigeria,
Duk da hayaniyar da akeyi agurin bai hanai jin kuru,ruwar matar da aka kama ba
Azuciya na ,na,ce ya Allah yasa mutanen mu su daina wanan kazamin da bi,ar , tazuwa yawon takaru ba lasisi shiga kasar,
Idan ma mutum na so za,s iya bashi, lasisi idan har yabi ta hanyar daya dace,
Saida na ji cewa ni a halin yanzu zan iya zuwa ko ina saboda ina da kardan zama akasar ,,
Wanda bakowa ne yai min wanan hanyar ba sai sheriff Ahmad Lawal Zanna,
Zuciyata jinta nakeyi tai min shakat kamar an cire min wani nauyi acikin ta,
Haka na dunfari gida cikin wal,wala da sakin fuska ba wani damuwa atataredani,

Har kusan karfe shida sheriff baigan ni ba kuma baiga, na fito waje ba koda ko falon gidan ne,
Duk iya kannewar da zaiyi yayi har dai yakai ga tambayar Amal cewa yau bai gana fito ba koda sau dayane waje, ko lafiya nake,
Sai wannan lokacin Amal ke mai bayanin cewa tunda safe natafi masjidul
Kuma dama nace zan dan dade yau ban dawo ba,
Don haka lokacin da na iso gida suna zaune shida Aziza saman dinning table suna cin abin dinner,
A hankali nayi sallama cikin katafaren falon gidan namu wanda ba lalai bane wanda ke ciki yaji muryan mutun da ga kofar shiga,
Ganin da nayi masu zaune su biyu suna cin abinci yasa nayi niyar wucewa batare da na gaishe suba,
Aziza ce tafara gani ,wanda a zahiri ba haka abin yake ba, sheriff yarigata gani na sai yai wani irin sanyayan ajiyar zuciya,,,
yadai daure ne yai kamar bai gan ni ba , don alokacin inda ban dawo ba da saura kiris yaja almustapha suje bida na,
Aziza ce ke min fadima yau ina kika shigane haka tunda safe naje dakinki yafi sau biyu ban ganki ba,
Naso mudan fita zuwa cikin gari kadan,
Saina dan yi mata murmushi yake kawai badon komai ba sai wanda ke gefenta dake min wani kallo
Da ban iya cewa ga irin shi ko ma,anar shi,
Bangaren da nake tsaye yadan kalla yace min ina tafi ,
A marairaice kamar mai shirin kuka nace mai masjid natafi,
Yar karaman harara yasakar min yana kada spoon a plate yace,
Oho ashe yanzu duk inda kiga dama saiki sa kai kawai ki tafi batare da sanin kowa ba,
Nankan shiru nayi masa don banda ansan da zance duk da dai na fada ma Amal cewa zan fita,
Yace je ki duk abin da kiga yafi maki je ki yi tunda ba ki under control din kowa,
Jiki ba kwari batare da kuma na iya cewa yayi hakkuri ba na shige ciki, abina,
Tunda dai nasan cewa ba wani mugu wuri naje ba,
Ina shiga daki,na Ko Nanfal dina ban cire ba,Amal tashigo dakin tana cewa
Gaskiya yau fadima baki kyauta tun safe fa kika fita duk da nasan cewa ga inda kika tafi ai bai kamata ki kai har dare haka ba,
Don nagajarce zancen ko zan samu saukin bacin ran da naji nace,
Amma dai Amal na fada maki ai kafin in fita ko,
Kafin Amal tace wani abu sai naji murywn sheriff yana cewa
Don kin fada ma Amal ni kin fada min ne ko,ko zaman Amal ki keyi a nan,
Kaina yana kasa don ganin da nai wa sheriff tsaye a tsakiyar dakina
Yacigaba da fadin idan wani abin yaje yasa may ki can fa ya kike son muyi
Ace tun safe mutum yabar gida sai yanzu yana mai diban agogon hannun shi,
Acikin sanyin murya nace mai dan Allah kayi hakkuri bazan sake irin haka ba insha Allah,
Ido yadan kura min nadan wani lokaci kamar mai nazari na tukun sai kuma ya juya yabar dakin batare da yakara magana ba,
Dagani har Amal wani irin ajiyan zuciya mukayi na fargaba,
Amal takai zaune saman gadona tace min gaskiya Fadima yau kin batawa yayan mu rai sosai wlh,
Yayi fadan fitar ki ke kadai batare da kowa ba yace wai laifina ne da nabari kika fita kedaya ban hanaki ba,
Murmushi nayi nakai zaune ina cewa haba dai sakace wata bakuwar gari ,
Bace wa zan yi halan,
Kada dai ki kara irin wanan halin pls,
Kofar dakin aka turo maman Umar ne dauke da abinci kala kala cikin wani dan keken tura abinci zuwa dakuna,
Cikin mamaki naje cewa may yasa takawo min abinci har daki aida tabari infita waje in diba ko,
Dukawa tayi tafara zuba abincin tace min sheriff yace mata ta tabbatar da naci abinci kafin in kwanta,
Amal dake zaune gefe na tadan tabe baki tace kaji yar gatan yaya ko har da abincin ma sai yasa a,yi gadinki har ki ci ko,
Maman Umar tace ai hakan yana da kyau don kinsan cewa fadima ai zaman amana take gare shi kin ga ai dole ya kulata,
Taciki abinci kala kala aplate tamiko min daga inda nake zaune a bakin gado na,
Kawai don tace min ance mata sai naci shiyasa nadan tsakuri abincin kadan,
Nace mata na koshi saidai fruit salad din duk munsha har Amal din,

Nasan cewa yanzu sheriff yana falon shi yana tura sakonne a system din shi,
Duk dare sai yayi wanan aiki in da duk yake
Hakan yabani damar fitowa don in kara bashi hakkuri kamar yadda Amal da maman Umar suka ce min
Dogon rigace ajiki tunda nafito wanka na sauya ta,
Sai plat shoe's ne akafa na shi ma baki mai photo yar kwakwa karama kamar buzubuzu haka,
Ganawa wautar na manta cewa da ba yanzu bane don haka ko mayafi ban dauka ba , tunda naga cewa ai a cikin gida ne kuma sheriff ne fa wanda yasan ni tun ina yar karamana,
A hankali na tako har inda yake zaune saidai ba sakon yake turawa ba shiru yayi yarike gefen habar shi da hannu guda da alamar tunane yake yi,
Jin motsin da yayi a bayan shi yasa yadago a hankali yadubi gurin da yaji motsin,
Sai mukayi idi biyu dashi, amma sai naga kwayar idon shi ya kada yayi ja sosa,
Da sauri batare da tunanen komai ba nace subbahanallah ,
Barci kakeji ne, nasa mu kaina da tambaryan shi,
Shiru nadan wani lokaci bai ansa min ba,
Saidai yadan girgiza min kai kawai,
Ikon Allah saikuma nakara cewa kana ciwon kai naga idon ka ja,
Murmushi yau sherie din yai min da alamar tambayar nawa ya bashi dariya
Yana mai kura min ido shi ja da suka rine yace, min,
Bawa ni ciwon kai illa keda keson ki tarwatsa min kwakawalwata, fadima har ke zaki fita kibar gida tun safe har dare baki dawo ba,
Cikin sauri nakai durkushe a kasa nace mai kayafe min dan Allah insha Allah bazan sake ba,
Da wata dakusarshiyar murya ya ansa min yace gaskiya baki kyauta min ba fadima,
Kaman zan yi kuka nakara cewa ya yi hakuri pls,
Kafin yai wani mafana sai mukaji muryan Aziza abayan mu tana cewa haba dai habibi,
Ai tunda har ta bada hakkuri takamata ka yafe mata hakana pls,
Tazo inda nake tsugune tadan dagoni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login