Showing 174001 words to 177000 words out of 231198 words

Chapter 59 - TAKARI Book Complete by Zainab Makawa .txt

tai ta sintiri a kofar fadima a ganta,
Harda yunkuri zuba Meagan da zai zubar da cikin fadima datayi,.
Cikin sanyi murya tace wallahi ba ita ce ta sace fadima ba san da tayi cewa gurin hukuma za a kaita kara
Indan kuma anyi karanta kasar Dubai zasu dawo da ita kasan haihuwar ta ne ba zasu kara barin ta shiga masu kasa ba,
Tai wani yunkuri don ta mike shiya sanya shi dan ne mata kafa da tasa
Yar kara ta saki ta ta dibe shi da sauri, sai taga ya canza mata ba Ahmad din da tasani bane yau,
Muryanta na rawa tace wallahi bani na sa aka sace taba,
Ni yunkurin zubar da cikin da ta yaudare ni ne kawai nayi,
Wani irin mugun shaka ya kara kai mata ya saida idon ta yafito waje don azaba,
Tunda take ba,a taba gwada mata azaba irin wanan ba,
Duk yadda taso ta motsa ko ta kwace kanta ta kasa
Wani zogi da radadi ya ratsata,
Kallon ta yakeyi yana nazarin irin rudewar da yagani a idon ta,
Can tace wallahi Ahmad ka yarda da ni ban san komai a gamay da batar fadima,
Cikin wani irin zafin rai ya sake ta yana huci yace barin fada maki aziza muddin bincike ya nuna cewa da hannu ki a cikin wanan zancen wallahi bazan raga maki ba ko kadan,
Bai kara koda second ba ya juya yabar gidan cikin fushi,
Nan Aziza ta rushe da kuka mai tsuma zuciya tayi da tasani ga shirin da tayi niyar ai,watar wa a kan fadima,
Wani abokin su ne ya basu shawaran su koma saudiya su kara bincike duk yadda akayi zaau gane inda fadima take,
Su Amal sun rasa gane kan dan uwan su tun da wanan abin yafaru,
Ya koma masu kamar wani mahaukacin zaki, sai jami,an tsaro ke masu sintiri a gida,
Wanan lokacin duk wqni wanda ke tare da shi yasan irin kaunar da son da yakewa fadima,
A nacikin wanan halin aka bugo mai waya daga Nigeria cewa jikin hjy tsohuwa ya tashi,
Gabadayan su suka zo Nigeria dan diba jikin nata,
Kwanan biyu ya koma saudiya don ci gaba da bincike,
Nasir abokin doctor kamal ma aikacin yan sandan ciki ya basu shawaran zuwa ma aikatar tafiye tafiye don adiba masu,
Sheriff yace yasan cewa fadima bazata iya kai kanta gida ba saboda tun tana yar karama akabar Nigeria da ita,
Don haka da wuya ta iya komawa garin su,
Ganin cewa Nasir din ya nace ne yasa su zuwa maaikatar tafiye tafiye na kasar saudiya,
Sunayen wa,yanda sukayi tafiya a wanan date din zuwa yanzu aka fitar da photos din su ,
A madina suka fara bincike basuyi nasara ba sai suka tafi jidda,
Ganin ko a jidda ba suyi nasara ba yasa yace masu su bari kawai don shi dama ya san ceqa ba zan iya komawa gida ba,
Doctor kamal yace sam sai sun tafi Riyadh sun karasa bincikawa,
Binciken farko ya nuna masu photo nadana Aisha a ranan da mukabar gida ranan nabar kasar saudiya zuwa kasata ta haihuwa Nigerian,


🐎ZEEE MAKAWA🐎
✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
8⃣1⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎


Almost true life story,,,,,,




Tunda nazo dogon daji ban fita ko ina ba ina cikin gidan mu,
Don ko yaushe, ina tare da innar mu muna hira,, tana bani labarin bayan tafiya ta,
Duk ,zaman hiran da mukeyi da inna bata taba tambayana komai ba gamay da cikin da ke jikina ba
Don haka nima ban san taya zan yi rashin kunyar fada mata wani zancen ciki can
Shiru nima nayi kamar yadda tasa min ido, ba wanan zancan a tsakanin mu,
Yar uwata mariya ta na matukar, kokarin ta wajen ganin farin cikina don kusan duk wani dawai niyar mu itace mai yi batare da gaza wa ba,
Hafsi ce ke ban mamaki idan natuna yadda ta ke nuna min kyama karara,
Mariya kan ce min in fita batun ta ba laifinta ba ne ,
Ra,ayin mutanen gidan su ne take bi, shiyasa don tasan halin su sarai da iya kulla sheri,
Ina kwance cikin yar rufar karan dake kofar dakin Innar mu, muna shan iska .
Saboda rana yai zafi sosai daki bai zaunuwa a lokacin don haka nan muke dan zama musha iska ,
Abdull kani na yashigo gida da yar ledar shi a hannu dawowar shi kenan da ga makarantar bokon da yake zuwa shida mariya,
Ledar dake hannu shi ya miko min daidai lokacin da nake mai sannu da zuwa,
Nakarbi ledar cikin mutunci da girmana alheri,
Yace min umhumm, kwaida kwaina nis sayo maki
Yanzu niggani shi hanya a na suya nai dama jiya nai alkawarin zan sayo ma wagga diya wani abu da kuddin tarana,
Tausayin yaron yakamani har cikin rai na saboda ni da Aisha ya tauye kan shi yau bai kashe yar ashirin din shi ba, da ake basu,
Ganin da yayi ina tuna ne ban bude ledar ba yasa shi matsowa kusa dani yace ko baki cina naga baki bude ba,
Dan murmushi nayi na bude ledar da sauri,
Sai kamshin awara ya bugi hanci na da sauri cikin irin yanayin kwadai na mai ciki na dauki guda nakai a bakina,
Aisha na mikawa guda biyu saura kwara uku sai na bashi guda, na mikawa inna guda biyun da suka rage,
Inna ta ce aiko yau kaji kumya kaida kasawo kuma harda kai za,aci,
Duk muka sa dariya a lokaci guda,
Muna cikin dariyar mariya ta shigo itama a gajiye saboda dan karen tafiyan da suke sha kafin sukawo gida don makarantar nada dan nisa da cikin gari,
Tashi nayi na kara shimfida masu tabarma nadauko masu abincin su naje masu,
Daidai lokacin mariya tafito daga daki tace kai anty fadima mi da ki ka wahalal da kanki , dauri ki barshi kawai,
Ganin da nayi Aisha ta cinye kwai da kwai har tana yar lasar hannu ta yasa ta bani tausayi so sai,
Saboda nasan yariyar a tauye take ba wai ta saba da irin wanan rayuwar ba ne,
Sai a lokacin natuna da canjin kudin Nigeria da salimat tabani da zamu wanda tace min in rika don zai min rana so sai, idan na isa,
Ta shi nayi na shiga daki na jawo jakata da inna ta tura can kar kashin dan gadon karfen ta,
Gurin dauko kudin ne idona yakai ga wayana dake kashe tun lokacin da na zo Nigeria,
Sai kuma lambar su safiya da nagani a cikin yar pepper da na rubuta ta, tare data hjy umma,
Jakar nadauko gabadayan ta don daukar
Kudin da wayar, nafito waje da shi
Kudin dake acikin jakar gaskiya zasu kai kimanin dubu dari biyu, na Nigeria,
Yan dubu guda guda ne cur din su,
Bayan na zauna na zaro dubu guda duk da ba sanin kan kudin nayi ba,
Na mikawa Abdull nace yaje ya sayowa Aiaha takara ci,
Ido suka fitar waje duk kansu suna hada baki lokaci guda
Dubu daya za,a tai zuwa sayen kwai da kwai da shiya,
Mariya tace wanga kwai dakwai da ko dadi ba shi da,
Galala nayi tsaye ina kallon su da kudin a hannu na,
Mariya tace bari yanzu in tashi in soya maki in so nai kikai yahi atai zuwa sanyen wanda bashi da dadi,
Abdull amshi kudin katai ka sayo wake da mai ,
Tunda na zauna bayan fitar Abdull sai hankalina ya koma ga wata,
Nasan cewa caji ya kare, tunda tunda nazo ban kunnata ba,
Mariya ce ta karba ta dan diba tace wai wai wagga waya aita manyata,
Bari in kai maki ita nan gurin isah yasa maki caji don walleh ba mu da gurin sa caji gidan ga,
Murmushi nayi araina kawai don ba wurin sa caji ba duk gidan ma ai na son gyara,
Naso in dan bada kudi a fara gyara amma sai naji irin maganar da ke ta bin gari cewa yawon karuwanci naje yi a saudiya,
Hakan ne ya hanani yin komai tun da nazo,
Ga kudi nazo da su a jakkata amma ina jin tsoron ba inna su don kar tace aida gaskiyar mutane,
Don zatayi mamakin ina na samu wanan kudin haka,
Duk da nasan cewa tarana gaskiya zatai halinta,

Kafin wani lokaci har mariya ta soya muna kwai da kwai muka zauna mukai mai cin gaskiya ni da Aisha,
Sai dai na lura da inna ko kwara daya bataci ba raina yadan sosu kadan don nasan hakan nada nasaba ga kudin da na ba yar a sawo kayan suyar,
Amma daga baya sai naga ai tana da gaskiyar ta tunda bata san komai ba a gamay da ni,,
Na, inna jin lokacin da mariya kewa innar mu maganar rashin cin wara da batayi ba da aka bata,
Inna tace ma mariya wallahi kawai bata ci ne ba wai taki bane,
Mariya duk yar karamar yariyance amma tasan ya,kamata,
Gashi Allah ya sa mata taisayi na a ranta tanada son yan uwa sosai,
Shi ko Abdull kusan ko yaushe sai ya sayo min kwaida kwai tunda yaga ina so,
Hakan yasa nakara son yan uwa na sosai kuma ina ji da su,
Rashin zuwan hafsi gidan mu da batayi yasani cikin damuwa ina kewar yar uwata so sai,
Yau ba makarantar boko don haka muka shirya fita zuwa unguwa nida mariya da Aisha,
Cikin shiga irin ta mu na can saudiya nake don bazaka iya ganin komai nawa ba,
Gidan kawu salihu muka fara zuwa nai sa,a nasamay shi a gida tare da yaran shi suna gyaran darnin gidan su,
Kawu yayi murna kware da zuwan da nayi ziyaran shi,
Cikin fara,a yake ce min fadima ta yau agidan namu,
A gaishe ki ke ji,,,,, ,a,a gajiyan tahiya
Nace lafiya kalau kawu mun samay ku lafiya,
Sauran yaran kawu suka zo muka fara gaisawa da su,, cikin wasa irin na barkwaci,
Matsala guda shine irin kallon wulakancin da matar kawu tai min uwar gidan,
Amma ita amaryan far far muka gaisa da ita,
Na lura da ita sarai amma sai na share kamar ban fahince ta ba, sam,
Har gabanta naje na tsuguna nace gwago mun samay ku lafiya, kamar ba,zata amsa ba sai dai ta ansa min a dakile,
Har natashi zan wuce sai tace amma dai albasa batai halin ruwa ba,
Kamar diyar yar kulu za ace ta tafi yawon duniya ba kunya kuma har ta tako kafarta har gida da tsarabar yawon duniya,
Jiki a sanyaye na dago daga gurin ta nadawo inda kawu, yake zaune ,
Na zauna gefen kawu kadan Aisha ta dawo kusa da ni ta zauna,
Kawu yace min kuna can kasa mai tsarki abin ku fadima
Nai murmushi kawai batare da yin magana ba,
Gwago da ga inda take zaune ta jefo bakinta cikin zancen tace
Aida wanan gara mutum ya zauna a kauye yafi mai,
Duk muka kalleta lokaci guda batare da mun mata magana ba,
Sai jin muryan mariya nayi tana cewa a, a ha gwago zato zunubi ce
Shedar zina abuce mai girma ga addini,
Kawu yace saratu ina rabaki da wanan mugun hali naki na hassada,
Wanakewa hassada yace aikin fini sani,
Idan ma har diyar yar kulu tayi wani abin kunya nadauka ke ma abin,ya shafe ki ai, diyan yar kulu,
Jinin diyanki ne ko kin ki ko kinso tunda dai jini ya gauraya, ko,
Amma babu komai duk abin da kikayi bazaki rabani da yar uwar haihuwata ba,
Don da dadi da daci ni ina tare da su, idan kinga dama ki fadi alheri ,
Shiru kawai nayi a zuciyata ina wa Allah godiya da ya nuna min zuciyar kowa a gamay da ni,
Nakali kawu a hankali yadda naga ranshi ya yi mugun baci,
Cikin natsuwa nace kawu kayi hakkuri dan Allah
Yadda suke tsan mani abin ba hakana yake ba, da sannu kowa zai gane gaskiya ,
Mundan yi hirar bayan rabuwa da kawu tare da wasu daga cikin yaran shi,
Cikin hirar mu ne kawu ke, fadawa min yadda yayi da innar mu lokacin da Rugaiyya ta kawo mata kudi ,
Yaso ace inna tayi amfani da kudin ta gyara gidan ta da shi amma sai taki karba kudin dukka,
Yace yanzu yasan cewa a matse muke a gidan don rashi wadataccen wuri,
Ya ci gaba da fadin kowa da irin hanyar da Allah ke azurta shi ,
Mu namu hanyar arzikin ke nan da Allah ya tsago muna
Yai min nasiha so sai akan cewa kada indamu da zancen mutanen gari
In barwa Allah al,amurorina kawai shi zai min mafita insha Allah,
Naji dadin wanan nasihar ta kawu so sai wallahi, har cikin rai na,
Bayan dan wani lokaci mukayi sallama da kawu da yaran shi da niyar zamu tafi gidan hafsi a lokacin,
Kudi na debo masu yawa naba kawu na ba sauran yaran nashi nace suma su raba,
Kallon kudin kawu yayi yai shiru,
Can yakira suna na a hankali yace min fadima da kin bar kudin nan don nan gaba za suyi maki amfani so sai,
Don ko banza kin ga gaki da ciki kesan lalurar haihuwa yawa gare shi,
Cikin nuna rashin jin dadi nace wa kawu, na Kawu ko kaima kana kyaimar cin kudi na ne,
Ya ce ko daya fadima saboda na san cewa zargin da akw maki ba gaskiya bane ,
Gani nayi cewa dai kuna bukatar kudi don gina rayuwan ku da ke da maihaifiyar ki,,
Dan murmushi nayi kadan nace kawu ka karba kawai ina da kudin da zamu amfana da shi dagani har yan uwa na, nan gaba,
Ya karba tare da samin albarka yana min fatan alheri,
Jibrin yaron kawu yace hjy fadima ashe zamu zo karban jari a gurinki ke nan ko,
Mariya ce ta bashi ansa da fadin sai kazo baka jin ba bu ai in har zaka amince da tazama shugaban ka,
Dariya muka sa gaba dayan mu
Mukayi wa gwago sallama wace na hada da nata kudin ,
A kofar gidan su hafsi a kwai yar karamar kasuwa a gurin inda mutane ke taruwa manya da yara suna saida yan abubuwan tabawa,
Tundaga nesa naga duk sun zu,bo muna ido caaaaa suna kallon mu irin kallon kauyawa,
A hankali nake takawa har muka dan gwauta inda mutanen suke
Muryan wata yarinya ce mai tallar fura take fadin wallahi nidai wanan matar tabani shawa so sai ta kusa da ita tace ke dallah gafara can itace fa wace tafito yawon duniya kasa mai tsarki,
Dayar tace ke waya fada maki wallahi naji an ce ka,zafi ne akai mata,
Ni ce na hana mariya ta kula su, har muka shige cikin gidan abin mu,
Hafsi tana kofar dakin ta tsaye tana gyara tsabar farar shinkafa ta tuwo ,
Sarakanta da sauran matan yan uwar mijinta suna tsakar gida zaune gidin wani katon iccen lim,
Sallamar mu yasa duk suka juyo gaba dayan su suna kallon mu,
Direct inda suke zaune na nufa na gaishe su cikin girmamawa,
Suka ansa muna ciki ciki, mariya ko kallo basu isheta, ba don har tayi gaba abinta,
Ina bada baya naji muryan wata daga cikin su tana fadin kai wanan wa zaice haihuwar dogon daji ce
Duk ta kwade tayi wani fari kamar balarabiyar gaskiya aida gani kasan larabawa sun more a nan,
Wani irin miyau mai daci ne naji a baki na haka na hade su cikin bacin rai,
Maimakon hafsi ta yi farin ciki da zuwa na sai ce min muna tayi wai lafiya muka zo
Bamu jirata tazo gida

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login