Showing 225001 words to 228000 words out of 231198 words

Chapter 76 - TAKARI Book Complete by Zainab Makawa .txt

muna na zuwan su, Sudan kai amarya,
A cikin gatse na ce masu saura mukai wa yan Niger tasu amarya su kuma muga yadda za suyi muna ko,,
Har suna saurin hada baki suna fadin cewa wace ce za,a kai Niger kuma,
Ce masu nayi watace nan makwabciyar mu ce ,
Maman Umar ta kalleni tana dariya tace min ai ina ga kamar bukin suna za mu fara sha kafin na makwabtar ko,
Dan murmushi na yi na ce mata har da ke cikin yi min sheri ko,
Washegari duk yadda naso Abba yai sakko hakan bai yu,yuba saboda kofar dakin su yana a rufe alamar basu tashi ba ke nan gashi rana, har ya soma fitowa a lokacin,
Sau biyu sheriff yana bugo min waya don yaji ko an tafi asibitin,
Saida taga dama don kanta ta bude side din, kafin su fito sai da aka dauki wani dan lokaci,
A raina nace lalai wanan matar takai muguwar gaske, dan ciwon ba a jikin ta yake ba, shi yasa tai haka ko,
Tana fitowa tazauna cin abinci Abba yana zaune cikin jallabiyar shi fara,
Na,zo har inda yake na gaishe shi da kwana tare da sheda, mai cewa driver yana jiran shi tun dazu doctor kamal ya kira waya, tundazu,,
Bayan fitan su na bi bayan su dakallo cikin tausayin Abba wanda sai yadda hjy mama tayi da shi saboda hakkurin shi,
Babu abinda ke damun Abba sai hawan jinin da yai mai kamun kwarai ,,,
Gashi kuma ba wani kulawa yake samu a gurin hjy mama ba
Wace ita ta kanta takeyi yanzu duk karfin haline kawai ya rage mata,
Tare suka dawo da doctor kamal , yazo dauke da maganin da yake son adora Abba akai
Mariya ce yakira yace itace yake son ta dinga ba Abba maganin har kwana uku,
Kafin akara yi mai wani awon, fuskan hjy mama na kalla dan ganin ko zata yarda da abin da doctor yace ,
Ya tsunar fuskan take yi kamar mai jin kashi ko warin mutane,
Wasu takardu doctor ya miko min ina dibawa nai dariya a lokacin ina biye a bayan doctor nace mai,African people's
Takardun shedar haihuwan su twins ne akayi da sunar a saudiya aka haife su,
Da yamman ranan su sheriff suka dawo daga US
Direct gurin Abba ya nufa dan gane ma idon shi halin da Abban yake ciki,
Sai da yagama tambayar Abba lafiyan jikin shi tukun sannan ta juyo ya gaida hjy mama,
Ta ansa mai cike da basarwa, da kuma takaici a zuciyar ta dan ganin yadda Sheriff yakoma cikakken mutun mai fada aji,
Yana shiga side din shi ya samu har na hada mai ruwan wanka ko,
Saida yadan rungumay ni na dan wani lokaci tukun sanan ya sake ni ya fada bayi,
Abinci yaci daidai lokacin da yake gamawa doctor yakira shi dan jin ko ya iso lafiya,
Saida na kwashe duk kayan da yaci abinci na gyara gurin
Lokacin yana yar dakilar system din shi, saidai duk rabin hankalin shi na akaina,
Yana ganin na gama muka wuce bedroom lokaci guda,
Saida na koma side dina na gyara jikina da kyau,
Sannan na isa gurin maigidan ,
Duk da bawani dadewa yayi ba acan din duk da haka duk kan mu kowa na kokarin nunawa dan uwansa yadda yai missing din sa,
Bakaramin soyayya sheriff ya nuna min ba aranan kamar wanda yai shekara baya tare da ni,
Saida koma ya kamamala a tsakanin mu yadan jawo ni zuwa jikin shi kamar mai min awo, yace,
Kin ko tafi awo, fatima, saida naji wani dam don sam ni ban son harkar awon nan ,
Kaina nadan kwantar a saman kirjin shi sannan nace mai a,a banjeba gaskiya,
Saboda may tafadi cikin karaji,
Nace kai nake jira kadawo mutafi tare, hanci na ya ja min yace ban san may yasa bakya son zuwa asibiti ba fadima,
Gaskiya gaskiya hakan zai iya kawo muna matsala tunda naga ke baki damu da lafiyan ku ba ke da baby,
Dan haka gobe indan Allah ya kaimu ki shirya tunda safe, mutafi ki ga likita,,
Hakan akayi dan wanan karon har E,D,D an rubutamin ko,
Don yanzu watana bakwai ke nan nake ciki, ina kallon yadda sheriff ke jin dadi a ranshi, har saida ya baiyyana afili,
A hankali nadan sasauta murya na na ce sai a rage bani wahala pls,
Yar dariya yayi yakamo hannu na ya matse acikin nashi gam,
Ce ai likita bai ce haka ba kin ga kenan likita ma kila so yake in kara kaimi fiye da da,
,,,,,,,,,,,,,,,,,,,




🐎ZEEE. MAKAWA🐎
[12/15, 9:59 PM] ‪+234 808 968 1079‬: .✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
9⃣9⃣
BY


🐎ZAINAB IDRIS MAKAW🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎


Almost True Life Story,,,,,


Allah yadawo da su Amal saudiya lafiya daga hutun da Almustapha yatafi na aure a garin sudan
Tana sanye cikin lafaya duk ta rufe jikin ta lif da shi,
Dama sa lafaya ba bakon abu bane agurin ta don su ma garin su shi suke sawa saidai ace ba dukka ba,
Kallon ta nayi sai na tuntsire da dariya duka takai mun a baya Sheriff dake kawo wa ya ce cikin daga murya Ke kina da hankali kuwa,
Tace yayan mu baka ganin itace ke min dariya dariyar naci gaba dayi nace ashe ba dadi ko,
Kin manta a madina lokacin ,,,,,
Bankarasa ba tace min ai wancan ya wuce kamata yayi ki tausaya min fadima,
Ina can kasan mutane ina ta kewan ku, ashe ke ba ki ma damu dani ba,
Nace mata ni na isa acan ban kewar yar uwata
Auren ne kawai naga yai maki kyau shi yasa nake dariya kai,
Bayan mundan zauna na gabatar mata da abin rabawa a baki, ne sai fira yaushe rabo ya fara a tsakanin mu,
Take sheda min cewa tawuce da mutuwar hjy tsohuwa a cikin zuciyar ta fam,,
Nace to ya za,a yi sai hakkuri dan hanyar kowa ne mutuwa,
Sai zuwa rana kadan lokacin da zan kaiwa Abba abinci Amal tabini zuwa gaida su,
Kamar yadda hjy mama tasaba yi wa duk wani wanda ya shafi fanin Sheriff ko Abba wulakanci,
Yanzuma da Amal tashigo hakan ne yafaru da ita,
Don ko kallon inda Amal din take hjy batayi ba ,
Abba ke yar hira da Amal din yana tambayar ta labarin mutanen saudiya,
Cikin takaici Amal ta kali gefen inda hjy take zaune tana faman wayar karya tace,
Tace Allah dai ya kyauta Abba Allah yakare muna kai daga sherin masheranta har kullun,
Hjy ta dago idon ta jajaye ta kalli Amal dasu wace a lokacin take shirin tashi,
Dakina muka koma muka kara bajewa saman gado muka hau sabon fira,
Acikin firar tane na fahinci cewa Almustaph mutum ne wanda bai dagawa mace kafa ko kadan
Ita kuma Amal din wanan abin yana damun ta so sai alokacin,
Saida nadan nisa nace mata cikin nuna maganar da zanyi mai ma,anace
Amal yanzu duk yadda kika samu Almustapha dole ne ki daure da halinsa
Saboda rashin sabo ne ke damun ki ke kin a sannu idan har kin saba bazakiyi wanan korafin ba, ai,
Shiru tayi tana nazarin zance na can ta nisa tace amma gaskiya duk yadda naso in daure na kasa daurewa fadima,
Tunda har ki kaji nai maki complaint kin,san abin nadamu na,
Tausayi tabani a cikin zuciya ta, dan nasan cewa ta hadu da wani sabon yanayi ke nan,
Zuciya tace to amma ko ai mustapha bai yi kama da masiffafun maza ba,
Nace ma kaina kajini da wani zance taya dama ake gane namiji mai wanan irin rayuwar,
Hakana dai nai ta bata hakkuri da yan shawar,wari yadda za,tayi,
Nakara mata da nuni da yarda da kaddara komai kan,kantar shi ko girma,
Addu,a tana rage girman mumunar kaddara ga bawa, akoyau she kamar yadda sadaka yake riga kafi ga mumuni,
Abinda duk kagani arayuwar ka mukaddarine ka dogara ga ubanginin ka kar kayarda zuciyar ka ta, raya maka abin da ba daidai ba,
Wata nacan tana neman kwatan kwancin wanan rayuwar bata sanu ba,
Hakan da ubangiji yai maki shine mafi alherin da koyau she iyayyen mu ke rokar muna ga uban gijin mu,
Ranan mun kai wani lokaci munata hiran duniya ,
Har zuwa lokacin da Almustapha yazo daukan ta don su tafi,
Bawani nisa bane sosai a tsakanin mu da su,don kusan unguwa guda muke,
Har kusan fita gida na raka ta nida mariya da Aisha,
Ina dawo,wa na shige wanka dan ko zanji dan dama ajikina,
Tare da alwala nadauro nazo nagabatar da sallah,
Ina idar wa marita tashi dakin dauke da Abba zannah a hannu ta
Gefen gado ta samu ta zauna sai faman murmushi take min
Ina kokarin gyara pillow na ne nake ce mata, wai may ye naga kamar bakin ki akwai zance ,
Yar dariya tai min tace may kikagani halan? nace sanin halin ki mana,
Tace Anty ke nan sai ina da magana zan yi irin haka ,
Daidai lokacin nakai bayana saman gado ina mai kiran sunan Allah tare da neman tsari ga shedan,
Nace mata to nikan sai kuban guri indan rintsa ko kadan ne pls,
Wani kallo taimin cikin shagwaba tace zuwa na fa biyu da niyar in fada maki sai na iske ki kuna magana da anty Amal, in koma,
Nadan kalle ta nace mata, ainace kina da magana kince min tak,
Tayi ma,za tadan gyara zaman ta kamar mai rada tace dama nazo in fada maki ,,
Yau kwana biyu ke nan doctor kamal ya na bugo min waya ,,
Ido nazaro nace waya fa,? mariya ina dai lafiya ko,
Tace a,a fa anty dama wai ya na son zaizo gurinane,
Kallon tanayi cikin tuhuma sai tai saurin cewa ,aa fa bani nace yazo ba,
Shiru nayi kamar may nazari nace mata toke may kikace sai tace min, ce mai nayi sai na fada maki tukun,
Nace o kika daure ni ko mariya,
Tana yar dariyar kunya tace a,a wallahi nace ne kawai sai in anyardar min ,
Na nisa a hankali daidai lokacin nagyara hular kaina nace mata, sai ki bari har in fadawa yayan ki ko,
Tai maza tamike tsaye tana daukar yaron tace shike nan zan fada mai idan ya bugo,
Bayan ta nabi da kallo ina mamakin karfin hali irin na mariya kamar ta har zata tsaya kula kamar doctor kamal wanda kilama ya kusa haihuwan ta in har za,a bibiya,
Amma wai shine har take tsayawa dashi hirar soyayya ,
Naiwa sheriff bayanin duk yadda mukayi da doctor kamal tun farko ,
Da kuma yadda muka yi da ita mariyan yau,
Batare da ya kalleni ba yai yar murmushi kawai yace Allah sa alheri a ciki na kuma yiwa mariya murnan dace da mutun nagari kamar kamal,,,
Mariya wace ke Allah Allah taji ko sheriff ya amince saidai bata da yadda zatayi ne tai shiru,
A daki nasamay ta nai mata bayanin abinda yace kasa boye murnan ta tayi a gabana,
Tun wanan lokacin doctor kamal ya fara zuwa zance gurin mariya,
Don haka duk wani plan na sheriff akan karatun mariya ya tsaya,
Cikina yanzu ya shiga wata na takwas kenan, saboda haka yai min dan tsawo a gaba duk wanda ya ganni sai ya tausaya min,
Sheriff zaune akan saman wata yar kujer office irin mai juyawan nan, , hankalinshi na gurin system din shi
Da alamar duk abin da yakeyi mai muhin manci ne so sai don harda Ummibanan taso yadauke ta amma yadan lalashe ta tai barci,
Doguwar rigace fara,kal,ajikina mai shara,shara mara nauyi, sai hular da nasa akaina ,
Duk jikina kamshin turaren alrahab ke tashi, sai yar lipstick dana dan zizara a bakina,
Fresh milk na dauko mai sanyi kasancewar zafin da akeyi a yau din,
Komai sanyin A,C sai kaji dan dum kadan zaune yake na nufi gefe nadan aje mai milk din duk cikin rashin sanin na iso gurin,
Kamshin turare na ya shaka hakan ya nu a mai cewa ina kusa da shi,
Daidai lokacin da zai dan juyo a lokacin na kwanto mai a bayan shi,
Wani irin sanyayyan ajiyar zuciya yayi har sai da na dan daga mai ajikin shi,
Aje aikin yayi ya juyo inda nake muna fuskantar juna nida shi,
Hannu na namika najawo mai cup din milk din na nufi bakin shi dashi,
Babu musu ya bude bakin nafara bashi yana kurba a hankali yana mai lunshe idon shi,
Saida ya kusa shanye cup din milk din yai min alama da kai ,ya ishe shi hakana,
Namaida cup din sama dan stol din na aje,
Zama nayi wanan karon a saman ciyar shi ina mai wasa da sumar kan shi,
Hannun shi yadauka yasa daidai saitin cikina kamar mai son jin motsin baby alokacin,
Aiko bai kai ga cire hannun shiba yaji wani bul,bul alamar motsi a cikin,
Cikin razana yai saurin ya cire hannun shi kamar wanda za,a rike,
A hankali yadan dago kai yakalle lokacin ina mai dariyar irin reaction din da yayi,
Na kalle shi cikin natsuwa, nace mai nifa wanan karon jinake kamar ma banda ciki pa,
Da sauri yace min a hakan na dan rausaya kaina nace mai kwarai ma, kuwa,
Kowancan ma nasu twins sai da na kusa haihuwa ne kafin intafi Nigeria yafara dan damuna,
Yadan sasauta murya kamar mai rada yace min ashe sai in ci gaba da,,,,,,,
Cikin sauri na rufe mai baki yadan kai min cizo kadan a hannu, cikin sauri na cire,
Namike da kyat ina fadin barin barka ka karass aikin ka kada in damay ka da surutu,
Yace kamar kin san bincike nakeyi akan wasu kaya na Abba wa yanda suka bace ,
Ashe su, Suraj ne suka saidasu ba tare da sanin Abba ba,
Har da wasu daga cikin filayen shi da gidan jeshi,
Suna sayarwa suka gudu suka koma inda suka fito batare da sanin Abban ba,
Hankalina na mayar dan jin wanan labarin mai cike da tashin hankali,
Batare da natashiba saman jikin shi yaci gabada fada min cewa,
Ai,yau babu komai don duk sun kashe kudin har sun fada cikin rikici,
Yace yanzu haka shi babba an harbe shi a kafa agidan rawa yana jinyar kafar ne,
Shiyasa uwar tace ma Abba yazo nan don kada su tagi can yagani hat yaji ba,asin hakan,
Shiko suraj ya auri wata baturi wace suka dade tare har sun ma haifi diya buyu kafin ai auren,
Ido na waro waje kamar mai shirin ihu,
Yace yes, yanzu nasa aimin bincike akai in har yayi auren ta yadda yadace zan yi kokari in tallafa mai,
Nace mai to shi gudan fa,ya ce min yana can wata kasa suna waka a Jamaica,
Innalillahi kawai na kama maimaitawa ina cewa subbahanallah Allah ubangiji ya shirya muna su,
Yace min Ameen Fatima, nace ya Allah ka shirya muna zuriar mu ta hanyar alheri,
Duk sai naji banji dadiba wallahi jiki ba kwari natashi daga jikin shi ina mai yin addu,a abakina,
Duk sai naji tausayin Abba ya kamani ace yara uku sun zama bala,i alokaci guda,
Allah ka shirya muna kai muna jagora mafi alheri,
Daki na nakoma nasamu guri na kwanta jiki ba kwari,
Har sheriff ya shigo dakin yasamay ni a kwance haka,nan cikin damuwa,
Hannu shi yasa saitin fuskana yana dan waven kamar mai maganar kuramay,
Yana shirin zamane yake ce min yana son muje shopping a kasar Turkish,
Banko bari yakarasa zancen shi ba nace mai gaskiya ba,zan je ba ,
Cikin mamaki yake kallona nace mai gaskiya duk abinda zamu bukata za,a samay shi a nan saudiya insha Allah,
Nakarasa da fadin kaga sauran kudin sai kakara ma masu zuwa sauke farali a wanan shekarar ko,
Yaji dadin wanan maganar tawa so sai don ido kawai ya zura min yana min kallo cikin sha,awa,
Bayan kwana biyu sai ga masu dicoretion din gida sun zo a wanan lokacin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login