Showing 210001 words to 213000 words out of 231198 words

Chapter 71 - TAKARI Book Complete by Zainab Makawa .txt

gaida ita ba duk wulgawan da takeyi agaban mu,
Sai alokacin ta dawo tadan zauna tana ce min, duk wa yan nan tare kukazo da sune ? ko kuwa, ?
Duk da tambayar nata yai min zafi amma sai nadake kawai, araina nace mata eh,
Wanan gwago tace wanan kuma matar babana ne,
Abbane ya karba da fadin masha Allah haka yati kyau mungode kwarai da kulawar ku,
Allah ya raya muna yaran yasa masu albarka, kowa dake wajen akace amin, bandani da na karba a cikin zuciyana, ba,a fili ba,
Ba muwani dade ba muka taso zuwa falon hjy tsohuwa don muyi mata saida safe, saboda gaskiya a gajiye muke,
Wai ashe duk zaman da nayi falon hjy bata gane ni ba saida Sheriff yai mata bayanin, ko wace ce ni,,
Ina shigowa naji tace min U,ro, Uro,
Tana min alama da hannu inzo gurinta tanace min ashe abokiyar zuwa dawafi na ne ban gane ,
Kece haka kika girma masha Allah , sai kuma tasa kuka kamar yadda tsofafi keyi indan sunji dadin abu,
Nace mata ta daina kuka dan Allah ai yanzu mun zama daya ba inda zani, kuma muna tate muyi ta zuwa dawafin mu atare,,,
Koda muka koma shiyan da aka ba mu mun samu wayan nan yan matan sun gyara muna shiyan da aka sauke mu sai kamshi yake yi,
Aiko su gwago sukace indai harda sheriff a shiyan zai sauka sam su baza su zauna ba saidai su koma gurin hjya,
Sai ko ga wayan shi yana sheda muna cewa shi ya wuce gurin da zai kwana gidan Baban, Bashir, acan wqni unguwar Bulama,
Jin haka muka sake jikin mu mu kadai saidai duk daki guda muka kwana saboda sam gwago tace ita bata yarda da hjy mama ba,
Hakana muka kwana acikin daki guda, gabadayan mu,
Washegari gashi dai munyi wanka mun shirya tsab, amma har zuwa goma da rabi na safe ba akawo muna abin karin kumallo ba,
Gashi cikin jegone mun tun ina daure wa gwago nata masifar fada tana cewa gaskiya wanan abi da niyya akai haka,
Mai aikin hjy mamace tashigo da sallamar ta dauke wani dan kula abinci wanda, ko mariya da Aisha ba zai kosar ba ,
Kwaine soyyaye da dankalin tura har yayi sanyi, wai hjy ce tace akawo muna ,
Har takai kofa sai gwago tace mata, tazo ta dauka tamayar tace ai mun koshi,
Naso in magana tai cikina da fada so sai tace da wanan cikin jegon naki za,a kawo muna wanan dan abincin haka,
Ganin munkai har rana yasa kawai naiwa sheriff text nace muna jiran abin breakfast,
Cikin mamaki yakirana yana tambayana nan na sheda mai duk yadda akayi kuma na fada mai gwago ta ce amayar mata dashi,
Ba afi minti ashirin ba sai ga take away na wani restaurant ankawo muna gudan mai yawa mukaci har muka koshi,
Sheriff yazo yabawa su gwago hakkuri, tace ita abinda yasa tace amayar saboda idan mun karba ko gobe haka za,a kawo muna kuma ba mai sani ,,
Naji yace masu saboda zuwan mu komai yasa ankawo don bukatar mu
Gwago tace barta kawai munsan irin wanan
Muda muka fito hausa muza,agwadawa barkado,
Kuma muna nan bamu wucewa sai mungama abinda yakawo mu,
Sheriff yaji nauyi sosai amma dayaga su gwago madu yi ne sai yaji dadin hakan don yasan zasu iya maganin mama,,,,




🐎ZEEE MAKAWA🐎


✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
9⃣3⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎


Almost True Life Story,,,




Kafin karfe biyu duk wani simple stock an tanadar muna shi a side din da muke zaune a cikin gidan Abba,
Sau biyu ina zuwa side din hjy mama dan mu,gaida ita amma gurin yana a kulle,
Saida mariya tagama gyara muna ko ina san nan muka kwasa muka koma side din da hjy tsohuwa take ciki,
Mariya da yan manta sukayi muna abincin da zamuci ,
Sai bayan sun kam,mala komai ne suka zubowa kowa a inda yakamay,
Falon hjy tsobuwa muk banje muka fara cin abin cin mu hankali kwance,
Hakan bakaramin dadi yai min ba dan dama duk a tsorace nake da hjy mama,
Dan kada tabar mu da yun wa, gashi tare da su gwago muje bamu kadai bane, duk da sun san halin irin wasu matan a gurin kishi,
Banyan mun gama cin abinci mu kazauna nan falon hjy tsohuwa zaman hira,
Sai a lokacin Ummibanan ta farka daga barci tana ta tsala ihu,
Ruwa maidan dumi nasa mariya tadan zubo min a cup in bata tasha ,ihun da takeyi yasa gwago ce min kada in koya wa yaran fitina man,
Yaron da baya kuka indan aka kyaleshi yana kuka har zuwa wani lokaci zai koyi kukan banza daga wanan lokacin,
Har uwa tarasa gane kan yaro saboda yawan kukan da yaro zai dinga yi,
Hjy tsohuwa dake gefe guda tana jin abinda gwago ke fada tace min,
Dan Allah Fatima ki kula da wa yan nan yaran kinji, kinga uban su abin tausayi ni a duniya
Saboda shi shikadai ya tashi batare da sanin dadin yan uwa ba ,
Tanuna kofar side din hjy mama tace kin gata can bata da halin kirki ko daya,
Tunda kurciyar ta, har yanzu da girma ya kamata mugun haline tatare a zuciyar ta
Hassada da bakin ciki shike cin rayuwar ta akan wanan yaro,
Gashi diyan nata da ta nuwa wa so kamar ta mutu duk ba nagari daga cikin su,
Tun ban san ko wace ce Alhaji karami ya aura ba nake farin ciki da jin cewa wanan karon yar mutunci ce ya aura kuma yar yarinya kamila,
Nai farin ciki kwarai dajin hakan daga bakin Bashir
Saboda duk matan shi na farko sai ina ganin kamar daga, sherin hjy ce yake samun su don babu wace ta dace dashi daga cikin su,
Kawai sai labari naji cewa wai ai matar Amadu na ta haihu, bakaramin farin ciki nayi ba dajin wanan labarin gaskiya,
Tana nuna min yaran da hannu tace wa yan nan yaran da Allah yabaku kawai sun ishe ku a bin tin kaho a duniya,
Kwana nawa ne ,in ubangiji Allah yaraya, maku su za su girma
Kin ga daga wanan lokacin shi kan shi duk wani kwakwan da yakewa yan uwan shi don su shirya dashi zai ragu yadawo ga nashi iyalin,
Zuri, ar Amina ba zuri ar arzikiba ce wlh, tun farko ban so auren yaron nan da ita ba fin karfina ne kawai akayi da kuma rabon iyali atsakanin su,
Don haka ki zama mai hakkuri da mijin ki, kibawa diyan ku tarbiya nagari tayadda za su zamo abin alfahari a cikin duniya baki daya,
Shi kanshi maigidan naki na bukatar kulawar ki sosai don zan iya ce maki duk halaiyar shi guda da mahaifin shi,
Amma kinga shi mahaifin nashi rashin samun mace ra gari wace zata dinga karamai karfin gwiwa wajen kara habbaka rayuwan sa , bai sa,a da hakan ba,
Gaba daya ita gurinta shine tamallake komai nasa ita kadai sai iyalin ta,
Shine yasa kike ganin tana mugun bakin ciki da mijin ki,
Don ita aganin ta ba,aiwa diyanta , yan uba,
Wanan son kan nata yasa har ta cuci kanta da kanta diyanta suka lalace,
Ta girgiza kanta tace Allah ya shirya wa yan nan yaran,
Kamar yaron nan mai mutunci da sanin ciwon kanshi ace diyan shi sun shigo wanan garin da kitso akan su,
Tace fafir Amina ta hana akai Amadu karatu kasan turawa saboda hassada wai zai je inda diyanta suka tafi,
Sai gashi ashe alheri ke kiran shi kasa mai tsarki, don zuwan nashu yanzu yazama duk wani dan uwan mu alheri,
Don kin ga kusan duk yan uwa yai masu sanadin samun wuri madogara,
Wanan hassadan na Amina yanzu haka sai kara ruruwa yake yi akan shi,
Ganin cewa duk diyan ta ba wanda ya kama kafan sa,
Kwanaki har da sherri ta hada wai aje abincike shi yana saida haranttatun kaya akasar saudiya,
Salati su gwago suka sa dan jin abinda hjy tace tace kwarai da gaske sai daga baya ne asirinta ya tonu gurin dan karamin dan ta ,
Yai mata fallasa so sai agaban mutane saboda taki yarda ya auri baturiya ran shi ya baci yai mata tas,
Tai yar murmushin tsofafi tace ki kula da kyau da duk wani abinda Amina zatai maku keda yaran ki don sherinta yawa gare shi,
Nima kin ganni nan to zamana duk yakai mata ko ina wurin nan,
Ni kaina zaman dole ne nakeyi anan dan can kauyen mu yafi mun nan sosai,
Tace dazun da mijin ki yashigo gaida ni saida nai mai korafi akan yabarni in koma dakina koda ma mutuwa zanyi in mutu a dakina,
Jin dogon jawabin hjy tsohuwa akan mama yasa duk jikina yakara mutuwa sai tausayin sheriff ya mamaye min zucita a lokaci guda,
Nace Allah sarki ashe shiyasa yake ta damuwa akan su mama da yaranta watau shi ke son su , su basu kaunar shu sam,
Inko haka dole in kara jawo mijina ajiki dan in kawar mai da damuwar da yake ciki,
Washe gari gidan anty Falmata mukaje yini, gabadayan mu harda hjy tsohuwa tun a mota tasa sheriff agaba akan sai ya maida ita gida kafin ya wuce,
Anty falmata taimin wani irin hadaden miya nadabab tace min wai shi sukewa masu jego kafin suyi arba,in,
Kazace aka dafa taci kayan hadi da kayan kamshi, sai sauran sake saki da aka dafa su tare, da ruwan rubutu,
Tace min ko wanan nasamu naci kawai kafin in yi arba,in yawadatar amma in son samu ne sau uku yakamata inci kafin inyi arba in,
Jin haka yasa na dan faki idon su gwago nace mata tayi kokarin dafa min sauran kafin mu tashi,
Tai yar dariya tace ai zan dafa maki fadima , yadda kika nuna kina kauna na kuma kina kaunar dan uwan na ai dole ni ma in soki fiye da tsanmanin ki,
Sha kurumin ki ai kafin kubar nan zan sa aimaki komai daya kamata,aiwa mace mai haihuwar farko kamar yadda muke yi anan kasar,
Naimata godiya sosai danjin wanan harar cin nata,
Ashe gwago taji tace ke kisha kurumin ki mu kan ai indai kayan hadine gida kikazo nida kaina zan hada maki walle sai kin bide ni kinmin godiya,
Duk muka sa dariya a cikin lokaci guda, anty falmata tace ai ki kwantar da hankaliki fadima duk abinda zan yi wa kaunata ta ciki guda inshaAllah zan maki ke ma,
Saboda naga kishiyoyin ki duk yan bariki ne,
Ni tausayi Ahmad ma nake ji har ina mamakin ko ina ya gangamo da ire,iren su haka,
Dan kin ga shi mutum ne salihi wanda bai magana,
Karar kiran wayana ne ya katse muna hiran, nobar Sheriff ne nagani a wayar
Nakai wayar a kun,ne na, daidai lokacin da yake sallama a cikin natsuwa da tausa murya,
Nima dai tausa muryan nayi na ansa mai yace min yana fatan ba matsala dai ko in harda matsala yazo ya kwashe mu zuwa gida,
Cikin sauri nace mai ba komai gamunan muna ta hira har su gwago sai nani yai yar ajiyar zuciya,
Alamar yaji dadin jin duk mun sake jikin mu da yan uwan shi,
Sai kuma yace min zai zo zuwa hudu yatafi damu mu gaida mahaifin Bashir ,
Dan yana ganin gobe zamu wuce gurin su ummi dan zai koma Saudiya very soon insha Allah,
Gabana yai matukar faduwa dajin cewa zamu koma saudiya tun yanzu,
Don dai gaskiya ni nafi son in zauna nan Nigeria abina,
Duk da bai anbaci cewa dani zai tafi ba nasan cewa mawuyacin abune yabar ni nan,
Shirun da yaji nayi yasa shi cewa hello, na ansa da naam,
Ya, Ce ina fatan kin fahince ni ai ko nace mai eh kawai, yace min ok take care,
Duk hankalin su yana agurina dan ganin cikin dan lokaci kadan na canza fuskana,
Anty falmata ce may tambayar komay ke faruwa,
Ban boye mataba na fada mata cewa wai gobe zamu tafi,
Kuma soon zamu koma saudiya,gaba daya, kuma ni gaskiya bana son komawa can wallahi,
Tace cikin sauri kada ki fara kice bazaki koma ba, fadima , kituna cewa bake kadai bace fa matar shi,
Idan har baki je ba sai wata ta tafi, nadan turo baki nace su tafi mana,
Gwago dake jin mu tun fara zancen tace ke arrr, da wanga hali naki,
Wasu nason atai da su ke ko wai son zama kikai, inkin zauna zaman mi zakiyi, ke dai,anan,
Shiru nayi ina jin maganar gwago da anty falmata
Sai jikina yai sanyi da nasihar nasu don ba yadda na iya dole in bi mijina in koma saudiya kenan,
Wasu hawaye suka dan silalo min natuna cewa ko hjy maisharwali da takai ni saudiya ta dawo Nigeria abinta, da duk wasu wa yanda mukaje tare, alokacin ,
Ni kadai kawai Allah yai zamana acan ke nan, cikin dabara nagoge hawayen ahankali,
Ashe anty falmata ta kuladani, a cikin dabara tajani har zuwa cikin bedroom din ta,
Tace min fadima may kikewa kuka akan komawar ki saudiya ne ko,
Ido ta kura min taa jiran ansa na ganin da tayi banda alamar bata ansa yasa tacigaba da maganar ta,
Tace fadima ki godewa Allah da yabaki Ahmad a matsayin miji, aure, yau kuma gsshi har da zuria a tsakanin ku,
Sam kada ki dauke ni a amatsayi yar uwar mijin ki,
Kisan wasu dangin miji suna zama ma mutum abokan gaba da zaran sunga dan uwan su na son ka, sosai,
Ni tun banganki ba naji kin min kawai don gurin Bashir nake jin labarin ki wanda shima ina ganin gurin Ahmad yake dan samun labarin ki,
Nai maza nadan dago kai ina mamakin maganar ta ,
Tadaga min kai tace kwarai da gaske hakane ko ki na ganin baki isa yai maganar ki a gyefe bane,
Ta ce har in ki na shakku ki daina don ni gaunau ce ba jiyau ba don a gaba yake fadawa Abba da hjy tsohuwa irin halaiyar ki, da abinda yasa har ya aure ki,
Dan haka ki shirya kawai duk lokacin da ya bukaci ku koma ki bishi kawai batare da nuna bacin rain ki ba,
Shin idan kin tsaya nan may zaki tsinta mijin anan din idan har kin tsaya,
Daga kai nayi ina mamakin ta, kodai don bata san ko shekara nawa nayi can batare da iyayyena ba,
Sai naji ansar kuma a bakinta, tana cewa kina yar karama ma ,kin inyi zama batare da iyayyenki ba balle yanzu da kike da aure a kanki,
Kenan tasan koni waye tun farko wasu hawaye naji sun sulalo min a fuska na,
Dafa ni tayi a kafada tace ki zama ma jajircewa akoda yaushe don ki lashe duk wani lanbar yabo daga mijinki ,
Ki zama mai mallake mijin ki ,koya mai yin adalci acikin ku, duk da nasan yana kwatantawa, saboda shi haka ya tashi mutum mai tsoron Allah,
Kiyi kokari ki tarbiyartan da ya'yan ki cikin hikima da dabara ki hane su ga duk wani abinda zai kaisu ga koyon lalacewa,
Hakan bazai kai ga samun nasaran ki ba sai kina kusa da mijin ki uban diyan ki,
Dan haka kada ki kara bata ranki ga wanan tafiyan ki je ki zama mai yi nayi bari na bari kamar yadda aka san ki,
Daga haka bata kara ce min komai ba sai shirun da yabiyo dakin, ido kawai ta zuba min,
Sai can nadan yi ajiyar zuciya, na nisa, nadago kai na kalle ta na ce cikin siririyar murya na gode kwarai anty kuma zan yi kokari in koyi da duk abin da kikace,
Kafin mu fito falo nai ma anty falmata godiya sosai acikin ziciya na kuma ina mai gode ma Allah da ya hada ni da ita ,
Hudu daidai sheriff ya iso inda suka kwashe mu zuwa gidan su Bashir
An muna taro na arziki so sai an kuma nuna muna so da kauna na gaskiya,
Ba mu wani dade ba saboda dare yayi mukayi sallama da su muka dawo gidan Abba,
Washe gari har hjy tsohuwa muka dunguma zuwa garin su can wani local government ne,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login