Showing 150001 words to 153000 words out of 231198 words
Chapter 51 - TAKARI Book Complete by Zainab Makawa .txt
da kaina don a gaskiya ban iya mata rashin mutunci ko kadan,
Sheriff yace min inzo in zauna gefen su sai nadan marairaice murya na nace mai gurin UMMI zan zauna nagode,
Sautin murmushin shi na ji itama azizan shi tawaiga don ganun abinda yakewa murmushin,
Nice yabi da ido har na zauna, kusa da inda ummi ta mayar kamar dakinta gefe guda daga cikin falon,
Wai don ta jaye mai hankali shi daga gare ni sai ta dauko jam tana shafa mai a bread din shi tana wani , kokarin matse jikin ta da nshi,
Tamiko mai yace a,a barshi kawai na koshi zan je in sha fruit, da mai cikin can,,,
Itama yunkuri tayi ta mike tsaye tana fadin barin riga ka kagin ka isa, nima in taya ku,,
A hankali ya lunshe idon shi yai dan takaittacen murmushi,
saboda yasan cewa Aziza nada wani manufa azuciyar ta gamay da ni,
wanda ba zai taba yarda hakan ya faru da, ita insha Allah,
Dar dar nake da ita ta zauna tana wani nan ,nan da ni,
Sai kawai naji fruit din sun fita min a rai sam,
Ganin da yayi ta takura min har ban iya shan fruit din yasa ,
Shi mikewa yana cewa zai je ya dawo, yanzun nan,
Yana fita tabini da wani mugun kallo wanda bani ba har ummi saida ta tsargu da ita,
Suka tashi suka bar falin zuwa cikin dakin su da suka sauka,
Suna shiga Hindu tayi shewa tace mutumiyar kin yi wlh kinga gun ma da kika daure kika nuna afili cewa ba komai,
Kinga yanzu sai mu fara shirin yadda za mu bullo wa lamarin,
Tun bayan faruwan wan rikicin sai yau na kira sheriff a wayana wayanda bansan inda ma na jefata ba, da,,,,
Kiran farko yadauka yana mai cewa Assalamu aikum,
Cikin siri,riyar murya na ansa mai sai kuma na kasa mai magana
Nai shiru kawai ina kalon kasan daki,
Muryan shi naji yana cewa fatima kiyi magana mana,
A hankali na ke ce mai zamu tafi Rauda ni da salimat , anjima kadan,
Shiru yayi can yace aida ni yakamata mu tafi bada salimat ba don muje mu gaida fiyayyen halitta tare da Sahabban shi, ko,
Amma tunda da salimat zaku tafi sai kun dawo saboda ni har na riga kuzuwa don yan zun haka daga can nake dawo,
Dàn Allah ku kula da kan ku saboda irin yawan da akeyi wurin ,
A hankali na ce mai to,
Tare muke da Salimat harda Ummi da falmata duk sun biyo mu,
Bayan munyi sallah muka isa cikin rauda don ziyara,
Nidake kokarin wajen tare wa, mutane fili don suyi nafila, raka,a biyu,,
Sai gashi yau na kasa dole nice aka tarewa gaba da baya har na samu na,idar da sallah na dade zaune gurin ina rokon Allah mafita akan lalura, ta tare da naiman kariya, daga duk wani sheri,
Ummi da falmata suna kallon yadda nake komai nawa acikin tsanaki da kwanciyar hankali,
Hakan yasa su kara godewa Allah da ya Ahmad irin matar da suka dade suna mai sha,awan yi,,,
Muryan falmata ne yakatse ni lokacin da nake tsaye ina ma manzo na salati,
Tana fadin kiyi adduan Allah bayas da masu albarka, dayawa,
Maganarta yasa ni dan yin murmushi kadan, kunya yakamani na dan dukar da kaina kawai,,,
Motar salim ce muka shiga, ina baya tare da anty Falmat da Salimat ummi ce gaba tare da Salim
Munje har bakiya aranan,
Muna kan hanyar mutadawo wane Sheriff yakira layi na,
Yace min ina fatan kun kama hanyar dawo wa yanzu saboda baby na kada ya wahala,
Kin san Allah ya sauwakawa mace mai ciki kaifin ibada,
Cikin jin kunya don banson zance yai nisa don gani nakeyi su falmata da salimat na jin mu ,
Na ansa mai a hankali da fadin eh,,
Mundawo gida lafiya bawa ni damu atare dani ko kasala kamar yadda nasaba ji ajikina duk kwanan kin nan,
Duk wanda yagan,ni yasan cewa ina cikin walwala yau din,
Abin mamaki yau harda dan abinci da ummi tasani gaba saina ci nadan tsankwara kadan,
Batare da nayi amai ba,,ni kaina nayi murnan hakan
Don har nake cewa salimat yau banyi amai ba,
Haka mukai ta zama gidan mu tab da baki kala kala,
Kowa ta shi irin lalurar da ya kawo shi
Irin Aziza da zaman hada plan kawai sukeyi a madina,
Saidai tayi rashin sa,a saboda ta manta cewa a babban birnin da isalama take ne duk cikin duniya,
Annabi yace idan duniya ta kusa kare har addini zai kasu kashi kashi, kuma duk islam ne
To idan har ana son a gane alkibila ta gaskiya aje garin Madina,
Har duniya ta tashi garin Madina suna akan sunna ce ta gaskiya,
Baza su taba canza alkibil da manzo ya dora su akai ba,,,,
Don haka addini ce sahihiya a madinan kusan duk bukata ta alheri ta wanzuwa ga bawa, amma banda na sheri,,,
Duk yadda taso ta fara aiwatar da niyar ta takasa dole suka shirya tafiya komawa Dubai har suje su kara hada sabon plan in yaso sai su dawo da shirin su,,,
Washe gari tunda safe suka shirya da niyar bin nirgi daga madina,zuwa Dubai,
Ina tsaye a dakina ina shirin fita zuwa school yau,
Aziza ta turomin kofar daki ,
Jin yadda aka turo kofan yasa na kalli hanyar shigowa da sauri, don inga kowani mara hankali zai min haka,
Ganin yanayin da takene ba cikin kwanciyar hankalin ta take ba yasa ni nadaure na gaishe ta, acikin sakin fuska,
Hannu ta daga min alamar inyi shiru,
Tadanzo gabana tazagaya harta bayana ta na kare min kallo
Ina tsaye cikin doguwar riga mai yar guntunwar hannu, baka tadan matse ta tsakiya, sakuma kasar rigar tadan bude kamar rigar indaya
Flower farin zare ne akai yi mata a tsatsaye nikaina nasan cewa rigar tai min kyau so sai,
Saida takare min kalli da kyau tadawo ta gabana ta tsaya gab da ni har muna iya jin nunfashin junar mu,
Ta nunani da dan yatsan ta tace fadima ina mai tausaya ki da kika yaudari Aziza a rayuwan ki,
Aziza ba a cutar ta a kwashe lafiya, kisani cewa
Ahmad nawa ne kaida bada kowace mace ba haka kuma wanan dan dake a cikin cikin ki nawane har abada ,,
Wani karfin hali naji yazo min da tace hakana,
Nadan kali inda take tsaye tana wani dan buga kafa nai dan murmushi irin mai ba mutun haushi
Nace mata, tunda har Ahmad din da kike gadaran cewa naki ne ke kadai bada kowace mace,ba
Gashi yau yadawo ga yar karamar yarinya har yakai ga mata abin dake kikadade kina bida da kudin ki da ilimin ki,
Taiwani kukan kura kamar zata shake ni, ashe Hindu nata wajen kofa tana kallon masu shigowa da fice agidan,
Ta rike mata hannu ta baya tana fadin ki,kan mantacewa agarin da shariar musulunci tafi karfi muke aziza,
Takai kusan minti biyu tsaye tana min wani irin mugun kallo na tsana
Ina tsaye kyam ina kallonta babu kowani tsoro,
Ganin kallon bai da alamar karewa yasa nadan geza da gefenta nayi tafiyana zuwa wurin mirroww na din in daura dan kwalina,
Saboda time na kure min na zuwa school,
Tai wani irin kutawa Hindu najan ta suka fita dakin suna fadin cewa zamu hade dake yarinya very soon,
Saida suka fita nabi suda kallo kuma ina mamakin kaina wai yau nice na iya tsayawa gaba da gaba ina bawa aziza ansa
Duk da nasan cewa bata da gaskiya amma nasan cewa hakan bsidace ba tunda ita ba warin yina bace,.
Kafin indaura Naifal dina Yashigo dakin rike da yar briefcase din shi, da alamar cikin sairi yake,,
Saida yai min wani kallo na sha,awa tukun sanan yace min ya muka kwana,
Ina tsaye nadan jingina da mirirrow kaina yana kasa,
Nace mai Alhamdullah,
Masha Allah yace, yakaraso ya man namin kiss a tsakitar goshina,
Kunyan haka da yake min nake ji sosai
Muryan shi naji yana cewa ina son in je in sauke su Aziza airport yanzu,
Yana fadi yana kallon agogon hannunshi,
Yadan kallo ni yace min kada ki damu kanki da duk wani barazanan da aziza zataimaki
Ashirye nake da daukar mataki a kanta,
Har zai fita sai na tsinci kaina ina may mai fatan alheri da adawo lafiya,
Saida yadan waigoni don mamaki,,,,,,,,
🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
7⃣4⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
Almost true life Story,,,
Tun tafiyar su Aziza sai gidan namu yakoma normal kamar yadda muke ada can babu wani haya niya,
Daga can sheriff ya bugo muna waya cewa yatafi Riyadh ba zai samu dawo wa ba.
Hakan yakara dan sani na sake jikina kadan don in samu time din yin karatuna,
saidai kusan ko yaushe ina daki na kwance ko ina karatu,
A yau mun tashi da wuri saboda zamu dan yi test,
Saboda haka a tsatsaye muka shirya don saurin da mukeyi,,
Muna shirin fitane Ummi ta tsaida ni akan cewa bazan fita gida batare da na yi break fast ba,,,
Gudun kar wani abu yaje yasa may ni acan daga salim har Amal dariya suka kamayi,
Ummi ta ce ai bani kadai ba waidon ina da ciki tace, a,a duk musulumi ba,a so yabar gidan shi batare da yasamu dan wani abu yasa a baki ba koda one spoon na koko kona tea, ne
Saboda yin hakan ya a tare wa bawa, kaddara, so sai,
Tace amma ku yanzu saboda ilimin zamani duk kun can za akidar alherin da aka dora mu akai
A hankali na koma na dan hada ruwan coffee kawai batare da nazuba wani abu ba na
Nasamu guri nadan zauna nasha,
Ina tunanen irin alherin da Ummi da yaranta ke min akoda yaushe, abin baiko lissafuwa,
Muryan Salim ce ta katse, min yar tuna nen da nashiga,
Yana cemin idan nagama inyi sauri mutafi in ko zan zauna ne inkara narkewa
Shikan zai tafi ne,
Murmushi na saki gami da mikewa tsaye ina ma su Ummi sallama,
Allah sarki rayuwa haka abubuwa sukai ta dan faru acikin yan kwanakin nan ,
Wuni mukeyi yanzu zungur a makaranta saboda muna gab da fara exam
Hakalina a kwance yake don har naka dan manta da lalurar dake tare da ni,
Abinda ke a gabana kawai shine exam da nasawa rai kamar may
Burina kawai inga na gama wanan karatun,da nakeyi ko zan san ida na dosa da tushi,
Yau ni kadai ce na na dawo, gida , saboda na rigasu fitowa
Sai kawai naji bazan iya tsayawa in jira su ba, natari taxi yakawo ni har kofar gida,,
A kusa da kofar gidan mu kadan naga wasu matasa biyu suna gyaran motar su,
Da alamar lalace masu tayi kila,
A hankali na wuce su zuwa ciji batare da na kula su ba,
Ina shiga ciki naji cikin,
Gidan namu shiru kamar ba kowa aciki, nadiba inda ummi ke yawan zama a falo, bata gurin itama,
Ina mamakin ko ina suka tafine sai na ji muryan su ta bayan gida don haka sai ban tsaya bin ta nasu ba,
Daki na nufa nasamu guri na kwanta, don indan, hutu ,Agajiye nake so sosai,,
Barci mai nauyi yai a,won gaba da ni, so sai,
A, cikin barcin nake jin kamar ina shakewa numfashina yana dan sizing a hankali,
Allah yatai makeni nadan bude idona, a hankali,
Wani dan kya mushashen bakin balarabe nagani rike da wata farar takarda a hanni shi,,,
Ganin da yaimin na farka yasa shi kokarin jada baya a hankali,
Ina son in yi ihu amma nakasa ko da dan motsawa, daga kwancen da nake,
Allah yaban iko nadan yi ihu da karfi har mama Umar dake kitchen saida tajini tare da su ummi mama umar na kawowa suna cin karo da wanan mutumin
Ya,bita tagar dake facing din baya yadira waje,,
I,hun danayi yasa kowa saurin zowa inda nake, a lokacin ne kuma idona yake rufewa a hankali,
Cikin rudani da tashin hakali kowa dake gidan yake
Shigowar Salim yasa su dan natsuwa nan maman umar tai mai bayani ihu na kawai sukaji,
Saidai lokacin da zata shigo ta hadu wani dan saurayin bakin balarabe yana kokarin fita ta window tagar dake kusa da dakina,
Salim bai jira komai ba yakira yayansu ya fada mai abinda ke faruwa a hankali,
Alokacin yana can U S A suna kokakarin kara hafbaka company nonin su ,
Asibiti aka kaini direct har lokacin ban ko da iya dan motsawa ,
Likitoci sunyi iya kokarin su don gane may ke faruwa da ni,
Tun karfe ukun rana da abin yafaru ba agane komai basai kusan shabiyu dare aka gane cewa a shaka min wani powder wanda zai gusar min da hankali har na kwana kusan uku ko biyu,
Daga U,S,A ,sheriff yataso ranan duk da uban aikin dake gaban shi,
Sai asuba ya iso garin madina, ,a masallacin dake kusa da asibiti yai sallah asuba sanan yakaraso cikin asibitin,
Kwance na ke sharkaf dani sai ta nunfashin da nakeyi ta na,urar taimakawa mutun ne za,a gane cewa ina da sauran rayuwa ajikina,
Duk wanda ke gurin a cikin tashin hankali yake, saboda irin yanayin da nake a ciki,
Sheriff kawai akayarda ma yashiga inda nake saboda tsaron guri ba,a yarda kowa ya shiga sai wanda ya ke,zama dolen ka, miji ko mata sai kuma mahifan mutun,
Yana shiga yadan ja ya tsa daga kofa yana min wani irin kallon tausayi,
A, hankali yatako jiki ba kwari har zuwa bakin gadon da nake kwance,
Durkusawa yayi gab dani yana kare min kallo, sai kace bani bace fadimar da yasa ni cikin dan lokaci guda duk na zabge
Hannu na yarike a hankali ya dan duka agefen gado yana min kallo acikin tausayi,
Zuciyar shi duk ta cunkushe da bakin ciki da bacin rai ga wani radadi da zogi da yake masa yawo a zuciyar shi,
Yadan daga kai ya kalli gefen da nake kwance tausayi na yakara kamashi sosai,
Da sauri ya mike daga bakin gadon kamar wanda aka mintsira, yasoma zagayen dakin yakasa zaune ya kasa tsaye,
Duk da sanyin A, C dake dakin bai hana shi karyo da wani irin zufa ba, alokacin,
Wanene wanan mutumin da ake tunanen cewa ya shiga mai gida,
May yake bida a gurina, ko kuma waya turo shi, yazo yai min hakan
Juyawa yayi a hankali yana kallon yadda nake fitar da numfashi a hankali,
Sai kara jin tausayi na yana shigar shi,
Yadan lunshe ido yana tuna yanayin da yasan ni da shi tunfarko, ganin da yai min,
Son wasa da ruwa, murmushi dayawan yin kwazon aiki, sai yar tsiwa ,ga hangen nesa, surutu idan tasan mutum, saikuma iya yin fushi, uwa uba kykkyawan zuciyar da Allah yabata saboda bata rikon mutum duk laifin da ka iya yi mata,
Ya furta a hankali fatima ke ba kowa ce amma kuma kina da komai da kowa ke so,a tare da ke,
Halaiyarki kadai ya ishi ni abin alfahari,
Zama dake yasa ina iya zama da yan uwa na akoda yaushe,
Fatima bazan iya jure rashin mace irinki ba, aduk lokacin da na kalleki, yana wanke min duk wani damuwa da maraicin rashin saboda iyayyena da ban yi ba abaya,
Saboda ita gata mace kuma yar karama amma ta dangana ta jure da rashin ganin yan uwanta da batayi ba,,,
Cikin ikon Allah da tai makon Likitoci suka samu da kyat Allah ya basu sa,a nadan farfado,
Daga dogon sumar dole da ,aka sani,
Sheriff ne tsaye yana fuskantar inda nake kwance sai likitocin da suka dan zagaye ni ,,,
Abuna farko da akafara yi shi ne diba, lafiyan baby da ke a jikina,
Sun tabbatar da lafiya kalau baby yake saidai weak