Showing 105001 words to 108000 words out of 231198 words

Chapter 36 - TAKARI Book Complete by Zainab Makawa .txt

tana fada min mijin ta ya iso ko
Bansan lokacin da nadayi dan ihu murna ba nace mata tai mashi sannu da zuwa ,
Nan nake fada mata nace mata ai yayan mu yazo da amaryan shi mai kyau da ita,
Wanan magana yaiwa Aziza da sherrif dadi don na fahinci cewa yana son aziza sosai,
Nikuma duk abinda yake so ina son shi don yawan kaunar da ya nuna min tun farko,
Da murna nake fada ma Amal sakon salimat Amal din tayi dan dariya tace ashe yau anty amarya ce,
Basu wani dadewa ba sukai muna sallama zuwa masaukin su,

Acikin barci naji tsuwar waya na kamar kada in tashi sai dai nadaure na ansa kiran ,
Amma abin mamaki mai kiran ya boye nobar shi,
A cikin harshen turanci mai shi ke min magana,
Dafarko yace min sorry da damuna da yayi ina barci na,,
Sai na ce ba komai amma dan Allah dawa nake magana ne,
Shiru ne yadan biyo baya, jin danayi ba ansa yasa nace ma maikiran kada ya kara kirana ni matar aure ce ,
Idan yakara zan fada ma mijina,
Dan murmushi yayi yace good ina iya infada ma mijin nawa,
Ganin da nayi zai jani da dogon zance yasani kashe wayar gami da tsaki, nagyara kwancina,

Anashi bangaren jinda yayi nace zan fada ma mijina yasa shi dagaba yace kai wanan yarinyar,
Tashi yayi tsab yakoma cikin bedroom inda Aziza ke kwance tana jiran shigowar shi,
Ce mata yayi baki yi barci bane, saitace mai a,a,
Yana shirin kwancine ta jeho mai tambaya ,, dayasa shi yin tsit,
Tace mai wai Ahmad ya kuke da wanan yariyar fadima ne,
Batare da shakkunta ba ko jin wani dar yace mata yar uwatace itama,
Tace mai maman ku guda ne da ita din ma,
Atakaice yace mata aa, yar uwata ce kawai,
Saida tanisa sai ta dan juyo setin shi tace mai ke nan akwai aure a tsakanin ko ko,
Cikin firgita da jin kalminta yasa shi saurin waigo ta da karfi yace baki da hankali, aziza,
Sister dinace fa sai tace and so what,
Kallonta yakama yi a kufule,
Ita ko kodar bataji ba, irin halin nan na kasaitatun mata,
Daga haka baikara cemata komai ba ya kwanta zuciyar fam da wasiwasin,
Tunda safe muka hada masu break fast din su tsab ,
Amal takira shi tace mai ko salim ya kawo masu abincin su inda suke ne sai yace mai aa kawai sujirashi gayan zuwa suci tare,
Kowa ya zauna a table din don cin abincin sai ni kadaice ban zo ba,
Salim yace yafada min suna jirana,,,,
Salim na fada min duk saina rude don gaskiya ban taba cin abinci agaban shi ba,
Table din nazo na zauna kowa na cin abinci niko sai wasa da cibi dake hannu kawai nakeyi,
Aziza ta kalli sheriff takali fadima tace man kici abinci mana yar uwa
Dan murmushi nayi nadan dibi ruwan chayi dake gaba nadan kurba kadan sai naji gaskiya ban iya sake jikina a gaban shi hakan,inci abinci,,,
Tana kallon shi taga ya ture kayan abinci ya mike ya ce mata zai je yadawo ta zauna nan ta jirashi zai je yadawo,
Ido tabishi da shi don mamaki tabas akwai wani dan feeling da sheriff ke boye wanan yariyar amma koma dai maye zata bincika,,
Ga mamakin ta sai kuma taga yanafita nafara cin abincina nomal kaman bani bace nakasa ci dazun,,,,




🐎ZEEE MAKAWA
✈✈✈TAKARI✈✈✈
πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£
πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£
6⃣0⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Ya Allah ka azurta muna dukkan Aluman Mususllumi da lafiya, arziki ilimi mai amfani a rayuwar duniya da lahira,
Jinjina da fatan alheri gare ku masoya na asali yan huguma groups gabadayan ku ina kara maku fatan alheri,
Banta mantawa da ku yan uwa na asali ,Anty,Hafsat yusuf, Anty,Mariya SB, Mama farida ,Anty Safiya mai huguma, Maman Rufaida, daduk wani wanda ya cancanci in rubuta sunan shi ban rubuta ba, nagode, nagode, nagode maku kwarai da karfin gwiwar da kuka bani, tun farko har yau gani ga shafi na sitin daidai cikin hikimar ubangiji,,,,,πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘


Almost true life story ,,,,


Aziza ce a masaukin su dake cikin masurin hotel din nan mai suna, Al,ni,imati
Waya takeyi cikin kasaita da nuna isa ita wata kawar da taje Turkey sarin kayan furniture's
Ai kawai kibari hindu, duk maganin su zanyi har shi din,
Ai tunda nasamu har ya shigo hannu to shi sunan shi sorry don nan da wani dan lokaci sai yadda na juya shi,
Ke dai kibi sannu aziza don kinsan cewa in badon taimakon Abu sultan ba da babu yadda zai amince ya aure ki haka,
Kidibi tun lokacin da kike binshi amma ko kallo baki ishe shiba,
Saukin ki guda da Abu sultan ya shirya muna wanan plans din cewa ke, marainiyace kuma ga mijinki ya mutu kina son miji mai mutunci wanda keda tsoron Allah da kuma kauda kai ga abin duniya ,,,
Shewa suka danyi ta cikin wayar tace mugu wai shi nan ustaza kada
Komai wayon shi sai naci kudin nan,
Gabadaya sai na mallake komai nashi sannan in barshi a tutar ba bu,
Wani dan guntun shewa suka kara yi, tace nasan ki mutumiyar baki da wasa ga duk wani abinda kike so,,
To su yan uwan fa ya zaki dasu,
Tace kai haba Hindu saikace kin mata da kowa cece aziza kuwa,
Motsin da taji kamar ana murda kofan dakin su za,a shigo shine ya hana takara sa zancen tace ma kawar nata Hindu sai wani lokaci ma karasa,
Mao kula da sashen sune yadau kowa sherrif kayan da yasayo a reception room,
Tana kwance tui da ita samar gado daga ita sai wani dan towel da ba ko rufe mata habar kataran ta guda ba,
Yana gani yadan kauda kai gefe, kadan
Duk da take matar shi ce ta sunna bai son irin halayyanta saman don ita nata matsalar bata da kamun kai ko kadan,
Abinda yafara notice ke nan irin tantiran matan nan ne ita
Sai bayan Abu sultan yasa shi ya fada tarkon su ne yake dan gane wasu daga cikin halaiyanta, da basuyi mai ba,
Abu guda ne tana kula da duk wani bukata nashi sai kuma yana ganin tana kula da duk dokan da yasa mata,.
Saida ya gama kintsa jikin shi sai ya koma saman kujeran dake fuskantar gadon ya zauna ya jawo system din shi suna fuskantar juna,
Yana cikin aiki take, ce mai amma gaskiya na yaba da halin wa yan nan kanen naka wlh,
Dan murmushi yayi na jin dadi har cikin zuciyar shi,
Tace saidai ita Amal akwaita da dan jan aji ba kamar Fadima take ba don duk kusan hiran mu da fadima mukayi shi ,
Ai halinsu ba guda bane su nada banbanci so sai,
Da irin wanan kissan tai ta jan shi hira akan mu shi ko duk sai yaji dadi a ranshi cewa matat shi na son yan uwan shi,
Kenan baza,a samu matsalar komai ba daga gurin ta akan su,,,,


Tafe nake acikin sauri amma tunane ya,addabeni sosai ,agogon hannu na na duba da sauri sai kuma ,nakai kallo na ga katon agogon dake makale bakin shiga department din mu,
Tabbas ya nayi latti har ankusa rufe shiga class din don ka,idace hakan,,,
Sauri na kara na isa class din dai lokacin da malamin shima zai shiga,
Guri na samu nazauna gami da yin tagumi, don dai gaskiya komai ban fahita ba daga lecture din na yau,
Gashi kuma salimat bata shigo ba yau kasancewa mijin ta yazo ganinta
Ana tashi ban tsaya jiran komai ba kamar yadda mukan dan saba yi indan muntashi sai mundan tsaya mun fahintar da junan mu tukun
Yau taxi na tare zuwa gida don ban son in wahal da yusuf yazo ya kaini kuma ace yadawo daukan su salim,
Ina sauka nadauko kudi zan mika wa mai taxi mukayi arba da sheriff wanda motar su ke shigowa kwanar gidan mu a hankali,
Yana baya zaune shida aziza, tun cikin motar yai min wani mugun kallo,
Zan shige gida cikin tsawa ya kira suna na cak na ja natsaya wuri guda,
Ina kikafito cikin rawar murya nace mai school yace ina yusuf yake da baije yadauko ni ba har na shigo taxi
A,hankali nadago idona da sukayi dan ja kadan nace mai ban son ya wahala ne ni banda lafiya ne shiyasa yau nadawo nabar su Amal, sai anjima Yusuf zaije yadauko su,,
Bina yayi da kallo kawai yace matar nashi tafito motar tashiga ciki yana zuwa,
Duk da ranta ya baci amma sai ta dake ta nuna aiba komai, ta bini muka shiga cikin, gidan tare,
Daki nafada nadan rage nauyin kayan jikina,
Nafito dagani sai wani dogon wandon da riga mai yar guntun hannu, dai dai iya damtsen hannu na, kaina nasa mai hula baka,
Inda take zaune tana waya duk kamshin ta ya karade falon namu kamar ba mace ba,
Abin sha na hado mata cikin tire na aje mata agabanta, najuya nabada baya
Ido ta bi bayana dashi har nakai saman kujera na zauna kafa na guda nadan taushe guda yana kasa,
Acikin ziciyar ta tace kai wanan yarinyar Allah yayi halittan shi wallahi jita kamar ita tayi kanta yar karama da ita amma komai nata acan acan gwanin ban shawa, wlh,
Wanan dai nasan cewa na isa haihuwar ta da ace ban bar kauye ba,aure akai min da wuri da gaskiya zan iya haihuwar ta,
TV na kuna mata tasha ralabawa suna wani film na ban dariya aciki,
Ganin da nayi ta gama wayan yasa nace mata ga abin sha nan tasha kafin agama abinci,
Dan murmushi tai min kadan tace ai a koshe nake kedai saidai ko zuwa anjima,
Ban kwashe kayan ba sai na barshi agabanta, namaida hankalina gun TV,
Da na kula wasan bai mata dadi ba sai nafara bata labarin wasan a hankali, ina dan mata bayani,
Amma kaina yana saman kujerar da nake zaune,
Hausana dariya yake bata don ji takeyi kamar larbci nake yi ba hausa ba,
Tace min nako taba zuwa Nigeria, kafin in bata ansa sai aka turo kofar falon tare da sallama, shi,
Naji kunyar yada yazo yasamay ni ba wani kayan kirki ajikina wlh,
Don inda nasan cewa zai dawo ne da ban fito hakana ba, falon ganin da nayi dagani sai itane yasa ni fitowa a hakan
Almustapha zai shigo dauke da ledar sai yai sauri yatare shi ya karbi ledan da ke hannun shi yace ya koma wancan bangaren su salim ya jira shi,,
Saida yai kamar zai dan da ki aziza da ledar dake hannun shi, cikin tsigar wasa sai ta dan noke cikin kujera,
Ganin suna dan wasa da junan su yasa nai niyar barin falon,
Da hannu ya nuna min inzauna, sai na koma na zauna saman kujeran din
Magani ya bare a hannu shi sai yadan kalli inda aziza take yace mata tazuba min drinks a cup,
Daman wanda nakawo mata yana nan ban dauke ba,
Tadan tsiyaya min ta miko mashi tana wani dan murmushin kissa,
Maganin da nake sha ne na hana ni ciwon mara yasawo min ashe,
Cikin mamaki na karba dole na wasta abakina yamiko min ruwan juice din yace in hade da shi,
Sai ya miko min leda mai dauki da pada har kusan sunki uku,
Duk kunya ya kamani narasa inda zan sa kaina don nauyi,
Duk abinda ke faruwa aziza na kallonmu cikin mamaki don dai bataji nace mai ga abinda ke damu na, ba cewa kawai nayi banda lafiya shine ya juya yaje yasayo min wanan kayan
Saida yaga nadan sha maganin san nan yatashi yakoma inda aziza take zaune yadan zauna gab da ita yana mata magana kasakasa murmushi kawai naga tayi mai ,
Yamike tsaye yana fadin sai sun dawo kenan acikin hausar shi da ba ta kware ba,irin hausan kanuri,
Idona a,TV yake amma zuciyana na wurin balaguro
Sai mamaki nakeyi ashe sheriff ya iya soye wa,
Ita wanan da alamar tafi nafisa farin jini gurin sheriff don nafisa ko kwatan kwacin haka bata samu ba,
Muna hada ido da ita sai muka sakarwa juna da murmushi,
Tace min amma dai yayanki na son ki da yawa gashi har yasan time din period dinki,
Ban bata ansa ba saidai dariyan da nayi kawai,
Anan inda nake mai nauyi yadauke ni saboda haka maganim ke min,
Sheriff yadawo ya samay ni kwance a kan kujera nadunkule wuri guda ina barci na hankali kwance ita ko aziza tana charting da Hindu tana nuna mata irin kayan da tayi oda akasar Turkey,
Kallon tausayi yai min ji yayi kamar ya dauke ni yakaini saman gado daki na, don yasan cewa idan na tashi jikina zai min ciwo a haka,,,,
Maman Umar yakira yace tazo ta tadani zuwa daki in kwanta,
Wayana yadan yi tsuwa kafin in farka daga barcin a,hankali yadauki wayan yayi hanyar waje da ita hankalin aziza bai kai gareshi ba tana can tana hira da hindu,
Kallo sunan mai kiran wayan yayi sai yaga narubu, Al noor, baro,baro
Ya maimaita sunan a hankali alnoor,,,,,,,,
Ya danna pick kafin wayan takara katsewa yasa, a kunen shi ba tare da yace hlo ba,
Muryan Ali baba yaji yana cewa sweet sahiba, mun gama meeting din ga shinan zan taso yanzu jirgin mu zai tashi,
Jiyayi kamar ya wurgata da wayan kasa ta raratse a kasa don ta kaici,
Watau ashe koda ya hanani kula da Ali baba, saida na kulashi,
Kai amma Ali baba yakai katon shege ji yayi kamar afili yake ya shake shi don takaici,
Nan da nan barebarin suka hau,
Jin shirun da Alin yayi yasa yake cewa hlo hlo,
Muryan sheriff da tai kama da ta zaki yace kai dan iska na fada ma cewa kafita hanyar wanan yarinyar tun farko to tana da aure a kanta
Inba hakaba zan iya halaka ka wlh ,,,,yana mai kashedi cikin kakausar murya,
Alin baba ya kalli wayar tamkar sheriff yake kallo a filin yace lalai ashe za,a ji mu da kai ke na Ahmad lawan zanna ai ban taba son abu inyi saurin jayewa ba da sauri,,,,
Abincin da bai ciba ke nan ranan saboda bacin rai,
Yasa noban na Alin a block,,
Kamar kada yaba ni wayana yakeji saidai kuma yace bari kawai ya mayar min dashi, tunda yayi blocking line din,,
Ai zai kama ni nan gaba indai ban daina ba ,
Abinda bai sani ba duk layin na Alin gudu uku ina dasu, a wayana,,
Amal tadawo cikin fushi don na bar school batare da najirata ba kuma Yusuf yace bashi ya dauko ni zuwa gida ba yau,,,,,
Maman Umar ne ke fada mata cewa banda lafiya ne shiyasa nadawo da wuri yau,
Sheriff na can saman kujerar dinning yana magana da Mr William, a video call,
Wurinshi tawuce direct kamar bata ga aziza ba,,,
Yayanmu sannu da aiki a hankali yadago yace, mata baiji ta gaida aziza ba,,
Cikin dan turo baki tace nafa gaisheta bata dai karba min bane,
Murmushi kawai aziza tayi mai nuna da magana gaba,
Saida suka ci abinci su ka huta tukun duk lokacin sheriff' yana gidan mu yana ta aikin wasu takardun masu yawa,
A hankali yake tambayar Amal da salim dake gefen shi,cikin yaren kanuri,
Batare da yadago kan shi ba yace mata tun yaushe nafara waya da Alin baba,
Gaban Amal yafadi dajin wanan tambayan don batai zaton jin haka gare shi ba
Cikin dan rashin gaskiya take gaya mai cewa gsakiya bata sani,
Abinda yakeyi ya wane ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login