Showing 198001 words to 201000 words out of 231198 words

Chapter 67 - TAKARI Book Complete by Zainab Makawa .txt

da hattara yaranta sun ji shi ga jama,ar gari so sai wallahi,
Hira akayi so sai tsakanin mu da malam.shehi ko in ce wan mahaifin mu ,
Inda ya jajanta mu na rasuwar mahaifin mu,
Yakuma ya ci gaba da muna nasihar rayuwa,
Yace ya jin jina ma irin rayuwar da inna tayi da mu shiyasa ake cewa amana tana hannu hagun mutum,
Gaskiya gaskiya tana nan a damarka da sune mutum zai tsalake siradi ranar lahira,
Haka nan idan baka da dasu koda kataba tsamanin zakaci ribar rayuwar duniyar da ta lahira,
Yakare da cewa ina mai jinjina maku tare da mahaifiyar ku wace ta iya rike gaskiya da amanar ku,
Duk munyi shiru mun natsu muna sauraren nasihar da Shehi ke muna,
Yace yau gaskiya da amana yasa duk kun kai ga samun nasarar rayuwar ku,
Haka akai wani lokaci cikin kulawa da kuma kara kaunar junan mu,,,
Tunda safe motocin da sheriff yazo dasu suka Parker kofar gidan inna akai masu loading tafiya inda mu da su gwago da matar maigari zamu bi jirgi zuwa Abuja,
Cikin irin shigar da nasaba yi a saudiya yau shine a jikina ,
Yan kauyen mu sun fito tab dan yi min fatar alheri da kuma kara taya mu farin ciki,
Tun cikin dare innar mu tai ta min nasiha ajan zaman duniya da kuma koyi da sunnan ma,aiki, S A S W,
Harda maigari wanda yake min kamar uba cikin masuyi mun rakiya zuwa airports,
Karfe sha biyun rana har angama muna checking din komai mun shiga motocin da za su kai mu Maitama gidan Sheriff,


🐎ZEEE MAKAWA🐎


πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘




✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£
πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£
8⃣9⃣
BY
🐎 *ZAINAB**IDRIS**MAKAWA*🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎


Almost True Llife Story,,




Mota guda muka,shiga nida sheriff sai kuma wata doguwar mota mai kama da kifin ruwa, ita su gwago da matar maigari suka shiga
Mariya da yaran suna tare da,su,
Kusan tun ranan da sheriff yazo kasar mu ban mutaba kebewa ba sai yau,
Driver na tada mota alamar zamu bar airport din ke nan sai kawai naji sheriff yadan lalubo hannu na,
Ya danke cikin nasa gami da sauke wani irin ajiyar zuciya,
Yace min fadima kiyi hakkuri ki daina wahal da rayuwar mu hakana pls,
Sai naji jikina yai sanyi da kalaman shi, sai naji kawai ya bani tausayi,
Dan gaskiya sheriff bai can canci haka ba daga gareni,idan har nai la,akari da irin taimakon da sheriff yai min a,rayuwa ta,
Musan man wanan na karshen da yai min nataimako akan inna ta, wacce nafi damuwa da al,amarinta,
Ban san lokacin da na dan kwantar da kafada na saman nashi ba, ina mai a,jiyar zuciya,
Dan kokarin kallon fuskana yayi a lokacin, sai yaga hawaye nakeyi kawai,
Dan murmushi yayi yace min may kuma na kuka yanzu tunda ga ki gani ni nai maki alkawarin ba, Aziza ba kowani irin ma,sherancin abu bazai kara zuwa kusa da ke ba,
Kaina yana a kafadar shi still ina dan she,shekar kukana
Nadan dago kaina ina mai kallon shi cikin murya maiban tausayi na ce mai amma dai ba zaka kara barin mu zauna guri guda da ita badai ko,
Batare da ya juyo ya kalleni ba yace min kin riga dai kin tsorace da al,amarin Aziza ne kawai ba abinda da zata iya yi maki,
Kara narkewa nayi a jikin shi kamar zan shige mai, kaina na saman kafadar shi still nace ba tsoro bane,
Kawai dai ina tsoron ta rabani da mijina ne kawai, uban diya na,
Shiru yayi bai ce min komai ba a lokacin saidai yar sautin murmushi, shi dana ji,
Ashe har mun,kawo gidan nashi na maitama ban sani ba,
Jin muryan masu gadin gidan dake muna sannu da zuwa ne yasani gane cewa mun shigo gidan ko,
Badon naso ba nadaga da kafadar sheriff ina mai gyara Mayafin kaina da kyau, ta yadda ba za,a iya gane fuskata ba sosai,
Gidane na gani tsantsarare ginan zamani don tsaywa musalin shi zai bata min lokaci ,hawa guda ne,
Sama da kasa kawai, amma fadin gidan yakai wani tsayi mai tsawo gaskiya,
Yadan kalle ni bayan yasan cewa na zauna da kyau a sit din yace ina fatan ginar gidan zai maku,
Idan akwai abinda bai maki ba sai kiyi min bayani in sa a gyara maku,
Cikin mamaki na bude baki da zumar in mai godiya sai kawai yasa yar yatsar shi a bakin shi ya ce min shiiiiiiiiiii alamar inyi shiru,
Dole na rufe bakina ba shiri tunda an hana ni furta komai,
Kofar motar a ka bude muna, a lokaci guda, mukafito, daga ciki,
Yan officer din su ne na nan Abuja suka zo tariyar mu da kuma taya ogan su samun karuwa,
A hankali nake takawa kamar maijin tsoron kasa bakina fam da duk wani addu an da yakamata in yi a lokacin,
Sai kallo nakeyi yadda Naira ya sha kashi anan, a gaskiya na tsinke da al,amarin sosai sai naga kamar wanan ginan duk ya cuna ma gidajen Sheriff,
Wanan irin ginan na sheriff ya tamfsa abin abin kallo ne gaskiya,
Sai a yanzu na tuna cewa su gwago da yaran basu karaso ba, dan haka dan dakatawa nayi dan su iso mushiga gabadayan mu,
Isowar su naci gaba da tafiyana a hankali suna biye dani rungumay da yaran a jikin su,
Sheriff yadan tsaya nisa dani kadan yana muna wani irin kallo cikin so da kauna,
Don ji yake tamkar a lokacin ya rungumay ni don wani irin so da sha,awar mu dayake ji kamar ransa zai fita don so na da yaran,
Azuciyan shi mamaki yakeyi waiyau shine keda wanan baiwar na diya biyu a lokaci guda,
Ya lumshe idon shi yadan karasa takowa muka shige cikin gidan atare dashi lokaci guda,
Sai da nakarewa ko ina kallo da ido tunkun na sai nadan waigo nakalli inda sheriff yake tsaye ,
Alamar godiya nai mai da ido ta yadda bakowane zai fahinci may mukayi wa juna ba,
Duk a falo muka sauke yar gajiyar mu inda masu aiki suka gabatar muna da abinci,
Ganin su gwago a gajiye suke yasa shi yi min magana cikin harshen larabci, ya zai tafi yaga inda yakamata mu sauke bakin mu, kai kawai na gyada mai,
Sai a lokacin su gwago suka dan sake jikin su suka fara mamakin irin abincin da aga jib ga agaban mu, wai mu kadai,
Hassan nai yai dan motsi wanda ke ta faman barci tun a jirgi, gwago ta miko minshi wai in bashi nono yasha,
Saida gabana yafadi a lokacin,
Sai nace mata barin da kewaya kafin in zauna tare da mariya muka shiga daya daga cikkn dakunar da ke kasan ,nadan zagaya ban daki, dan inji dadin zama,
Dakin ba laifi dan haka muka zauna ciki dayani nida mariya,
Ganin nafito daga bayi yasa mariya fita dan ta dauko min hassan din kusan a kofar dakin suka hadu da gwagon mu,matar kawu dauke da hassan wanda ke ta faman mutsitsiri a cikin showell
Mikon min shi gwago tayi ,daniyar inba shi nonon
Baki na turo dan in akwai abinda banson ji yanzu shine ace yaran zasu sha nono,
Dan har ga Allah bana son jin wanan bada nono da gwago ke damuna dashi,
Muryan gwago naji tana cewa , oh ni Salamatu kun gamin yarinya
Nafa lura da take taken ki sarai bakya son jin zancan shan nono,
Indan baki badu nono suka koshi ba may kike son aba su
Bayan ga abincin su Allah ya hore masu wadataccen nono bawai babu ba,
Baki nakara turo idona yai ja kamar may shirin yin kuka,
Gwago ce ta gyara min yadda zan rike yaron da kyau dan yaji dadin shan nono,
Daidai na daga riga na kenan zan sawa yaron nono a baki sheriff ya shigo dakin da sallamar shi,
Cikin sauri na sake rigar ina mai gyarawa sa kyau dan kada yaganar min nono na,
Gwago dake tsaye sai abin yabata mamaki tace shin wai mi kika nuhi na fadima,
Yaro najin yunwa kuma ke bi nono duk kin lulubi shi rub,
Wani mugun haushi gwago tabani alokacin ya take son inyi, agaban sheriff take son in bude nono ko kuwa may take nufi,
Cikin mamaki yake kallon mu tsakanin ni da gwago dan jin may ke faruwa,
Yadai daure yana kallon gwago yace ko madara za ,a sai masu ne,
Cikin sauri gwago tace a,a wallah, mizai sa atai zuwa sayen madara bayan wanga da Allah yabba su, ya wadatar da suwa,
Gwago tace yanzu kam dai ai ga uban su nan in kin gadama sai ki yi wadda zakiyi,
Tasa kai tafita dakin tana fada so sai dani, ina ganin tafita nai wani ajiyar zuciya kamar wace aka cirewa kaya alokacin,
Yaron yaci gaba da tsala ihu sosai ,
Cikin sauri sheriff yakaraso inda muke yace haba dai abashi nono yasha mana,
Ki daure ki bashi nasan ba dadi amma pls kiyi hakkuri ki basu abincin su ,
Cikin jin kuya ga kuma idona har sun kawo kwalla alokacin,
Nadan daga rigana kadan natura wa yaron nono, abaki,,
Ganin cewa yaron ba iya kama nonon zaiyi ba ni kuma bawai na iya bane gashi kuma gwago tayi fushi tafita,
Yasa sheriff ya gyara daga rigar nawa sama da kyau yace bari kiga yadda akeyi,
Cikin jin kunya nai sauri kama rigar da niyar in gyara rufewada sauri ya kamo nono yaturawa yaron abaki nan da nan yakama yafara tsotso, yana wani ajiyar zuciya,,,
Wani irin masifar zafi nake ji lokacin da yaron ke ta zukar nonon,
Ban san lokacin da na fara rintse idona ba saboda wani irin masifa da nake ji,
Da zafin yai min yawa ai ban san lokacin da nakai kwance saman jikin sheriff ba ina wani irin dan ihun zafi,
Wani reaction yaji a jikin shi lokacin kamar an mai wani, shock, yaji,
A haka har yaron ya koshi ya sake nonon da kan shi, ganin yaron yai barci ya sake nonon yasa sheriff ya dan kwantar da yaron a gefe guda,
Ji kawai nayi sheriff ya rungumoni so sai zuwa jikin shi,
Kasan cewar mundade hakan bai faru ba a tsakanin mu yasa na kyale shi,
Fuskan shi ya yi kokarin hadawa da nawa, mukai ido hudu lokaci guda,
Sai naga yai yar murmushi kawai yakau da kan, shi gefe guda,
Daurewa nayi dan nasan cewa shaukin so ke diban shi a lokacin,
Sai nasa hannu na a fuskan shi nadan shafo fuskar a hankali sai naji yai yar ajiyar zuciya,
Sajen fuskan shi nadan kama shafawa a hankali cikin murya mai taushi na ce mai
Kayi hakkuri da abinda nai ma ka yafe min pls bazan kara yin wani abu batare da sanin kaba in sha Allah,
Bai iya maganana ba alokacin kuma bai iya hanani ba dan saboda ji yakeyi kamar yau ne farkon fara kebewar shi da mace a duniyar nan sai yadinga ji dama a haka zasuyi tazama daga shi sai fadima da yan diyan su,,,
Karar wayan shi ya dakatar da shi daga tunanen da yakeyi a lokacin,
Ganin mai kiranshi a wanan lokacin yasa shi yadan, mike zaune da sauri yana mai man,na wayar shi a kunnen shi,
Cikin girmawa yake ansa mai tankar yana ganin shi a fili,
Bayan sun gaisa da Abban yake tambayar shi ko har yanzu yana garin namu ne,
Ya ansa mai da a,a mun dawo Abuja yau din nan, Alhaji,Lawal Zanna yakara tambayar shi msi haihuwar fa ya ansa mai cikin ladabi yace har da su,
Hamdallah Abban yayi da yaji hakan, ya cigaba da fadawa sheriff' cewa hjy tsohuwa ta tayar masu da hankali, akan cewa sai taje garin da yaran suke ta gane su da idon ta,
Yar dariya yayi yace zankira gida akai mata waya muyi magana da ita duk yadda mukayi zan kira in fada ma
Sukayi sallama da Abba din lokacin sheriff yadan mike zaune da kyau yabini da kallo dai dai lokacin da nake kokarin gyara daurin dankwalin kaina,
Yace cikin larabci hjy tsohuwa tana son dauko mai wata sabuwar rigima kuma,
Murmushi kawai nayi dan nasan kowaye hjy tsohuwa na kuma san fitinar ta sosai,
Bayanin yadda tsarin dakunan gidan suke sheriff yai min inda yace min,
Zamubar wa su gwago da sauran baki dakunar kasa inda dani dashi zamu zauna cikin dakunar dake sama,
Dan haka idan motar kayan mu sun iso sai asan inda za akaiwa kowa kayan shi,
Yadda yai min bayani naiwa su gwago amma sai suka su dai abar su suzauna daki guda ya ishe su,
Mariya da Aisha kuma suka zabi guda su ma, inda zasu zauna, ciki, duk da na so Aisha tazo mu hau sama tare amma kuma saina kada abar mariya ita kadai
Mamaki kawai mukeyi irin wanan gidan da sheriff ya kwankwatsa acikin Abuja,
Dagani Naira tasha kashi so sai, agurin, dan irin gida haka kai kasan sai wani da wani,
Don a gaskiya yafi na saudiya tsaruwa sosai, dan komai na gidan abin kallo ne, sabo new murder ne aka zuba ciki,
Sai kusan la,asar masu motocin mu suka iso, garin Abuja bisa jagirancin Bashir,
Wanda dama duk wani al,amarin sheriff a hannun bashir din yake, kusan kowa yasan wanan tundaga gida har ma,aikatar su,
Abin mamaki sai ganin malam Basiru nayi cikin matafiya, ana shigo da kayan mu sai gashi,
Ina zaune falo yazo ya zauna kasa gefe na yace hjy barka da gida mun samay ku lafiya ko ,
Duk kan mu munyi mamakin ganishi tare da su
Gwagoce mai kokarin tambayar shi tafiyar harda shine daman za a zo tafiyan murmushi kawai yai mata,
Ya ce ai daga bayane aka yanke, tafiya da shi saboda yazo yaga gurin da muke dan masu zowa sunna,
Duk yadda yakamata aiwa bako haka nasa aiwa bashir saboda a gaskiya tausayi yake bani sosai,
Nasan shi tun ina yar karama yana da kirki, matar shi kuma yar uwar su Gajiye ce, ,
Duk gida ya kici may da baki yau kala kala, don kusan kowa na gidan yau ne farkon zuwan mu wanan tankamaymay gidan na sheriff

Duk wani kulawa a gaskiya su gwago da matar maigari suna iya kokarin su wajen kula da lafiyana da na yan yaran,
Duk da yaran bawa ni fitina ke gare su ba ko dayaushe cikin barci suke,
Tun ranar da mukazo da yamma, Sheriff ya wuce gidan nafisa dan acan zai kwana,
Sai a,lokacin yake sheda mata zancen haihuwa na,
Tadai yi kokari ta danne kishin ta kamar yadda mahaifiyar ta ta umurce ta tayi kokari nunawa sheriff jin dadinta so sai na samun wanan karuwar da akayi,
Har take tambayar shi yau she zata tafi sokoto, ta dibo yaran,
Yace mata ai yaran da uwar duk suna nan cikin Abuja
Tayi mamakin jin cewa muna cikin garin kuma ba,a gidanta ba,
Sheriff yace mata muna maitama, gidan shi na can,
Cikin zaro ido take ce mai a sabon gidan shi zamu zauna ke nan,
Yabata ansa da eh dama saboda mu yagina shi dan kada muzo Nigeria bamu da gurin sauka,
Duk yadda taso ta taushi zuciyar ta ta kasa wanan karon kuka ta samai sosai akan cewa bai mata adalci ba dan itace yakamata ace ta koma can in yaso mu sai mu dawo nan inda take,
Da mamaki yake kallonta don tayi mugun bashi mamaki sosai saboda abinda tace
Azuciyar shi yace shin ko batasan matsayin fadima agurin shi bane da har zata furta wanan kalamin,
Shi wanan gidan damay yafi wancan da zata ce wai itace ya dace tashige,
Ganin idan har ya tsaya sauraren ta ranshi zaifi nan baci, yasa shi shigewa dakin shi yabarta nan tana kukan bacin rai,
Maman ta takira tai mata bayanin duk yadda sukayi dashi,
Uwar tace Nafisa ban san lokacin da zakiyi wayau ba shin wai har kin manta yadda muka samu kika koma gidan shi ,ko,
Fada sosai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login