Showing 102001 words to 105000 words out of 231198 words
Chapter 35 - TAKARI Book Complete by Zainab Makawa .txt
yayi kicin,kicin da fuskan shi,na iso da cup da lemon zan zuba mai,
Agaban shi na dan tsugun na gab dashi sai kamshin, turaren na da ke hawa mai kai,
Yana min wani irin kallon mamaki a fakaice,
Bayan nadan tsiyaya mai ne nadan dago kaina a hankali nace mai ga lemu na yasha
Hannu yadaga min kawai alarmar godiya,
Natashi a hannakali cikin tafiyar da ni ban masan cewa ina yin irinta ba, nabar gurinshi
wurin mustapha nanupa don shima in tsiyaya mai,
Ban karasa kawai wurin mustaphan ba naji karan cup din da na zuba ma sheriff lemo ya fadi,
Cikin sauri na aje cup da gwangwanin lemo agaban mustapha na juyo wurin sheriff da sauri,
Lemon ya zube a kasa har yadan taba mai rigan shi kadan,
Ruwan da ke gefe na bude nadan zuba mai daidai inda lemon yataba mai riga,
Cikin rudewa na cire gyalen da na yane fusaka na dashi na fara goge mai wurin,
Kaina da akai ma gyara sai kamshi ke tashi ya dan tsira ma ido
Yana kallon yadda gashina ya kwanta lub bakikirin da shi,
Ga kamshin mangashin dana turare na ya rude wurin ,,,
Idonshi yadan rintse kadan gabanshi nata faduwa,
Don shifa gani yake wanan kamar ba fadimar yar takarin da ya sani bace,
Saboda canzawan nawa yayi yawa cikin dan lokaci guda haka,
Idonshi yadan kara lumshewa yana mai dan maida nufashi, a hankaki ta yadda ba mai iya ganewa,
Cikin kidima naje da sauri nadauko moper na goge kasan , Sai faman yi mai sannu nakeyi,.
Saida na gama gogewa san nan hankalina yadawao daidai
Ko da na daga kai in kara yi mai sannu sai naga idon shi a lunshi sainadauka ko ranshi ne ya baci ,
Cikin sanyin murya nace mai dan Allah yayi hakkuri ba san zai zube mai ajiki ba ,,
Idon shi yabude wanda naga kwayar idon shi yai ma jajir ,saida naji tsoro,.
Hannu yadaga min alamari is ok,
Bayan fitar su sheriff ne muka zauna muna ba ummi da hjy labarin makarantar mu
Nafada mata yadda ake karatu a wurin da kuma salimat da na hadu da ita,
Wacce yanzu nake jinta tankar wata yar uwan na najikina,
Nan sukayi muna weekend saida sheriff da mustapha ba anan suka sauka ba su,
Washe gari sheriff yace min zaiyi baki,
Mudanyi mashi abincin da zasuci don wani meeting zasuyi
Shago mafi kusa natafi ta sayo duk wani abin bukarar da zamuyi amfani da shi,
Don mu a shago ake saida kayan abinci a can ba wai a kasuwa ba,
Abinci kala kusan biyar muka hada masu nida maman su Umar,
Saida muja gyara falon yayi neat sai kamshi ke tashi ko ina, da sanyin A C
A,babban dinning table muka hada masu wurin yayi kamar za ai wani dan kwara,kwaran walima,
Su hudune suka shigo dai almustapha da ke tare da sheriff ko yaushe, suka zama su biyar,
Sun gaida ummi da hjy cikin ladabi da girmamawa,
Bayan dan hiran lafiyar jikin ta da sukai mata wanda duk kusan bayanin hajiyar mu ne ma mai basu ansa, don ita ummi bata magana,
Nice shigo falon cikin wata doguwar riga ja, wacce a hannu ta kawai da kasar rigan keda ado,
Saida na gashe su tunkun sanan na juya wurin da sheriff yake nai mai bayanin abinci is ready
Wani irin kallo yai min wanda ban iya fadan dalilin hakan,
Ina cikin damuwan naji muryan wanidaga cikin bakin yana fadin masha Allah,
Ahmad kai keda kauna haka akasan nan kuma ban sani ba
Sai naji sheriff dake kokarin jawo plate agaban shi yace to aikaga yanzu ka sani ko,
Batare da jin kunyar kowa ba a wurin shi mutumin ke ce min
Sunan shi Ali Baba don Allah yana son in soshi, dama yadade ya son mata mai irin duk siffan dake gare ni bai samu ba,
Ashe ma wanan mugun yana da ita a gida yabarni kulun ina cigiyar yar matashiya, mai,,,,,,,,
Sheriff dakatar dashi da fadin Aliyu is enough don Allah kazo gaban yar yarinya kana faman zuba shirmay kamar wani karamin yaro,
Wanda aka kirada Aliyu yace to be Frank ba wasa a zance Ahmad naga sister ka kuma ina so
Idan har ba zaka taimaka min ba nida kaina zan bidi so a wurinta gakuma ummi a gari,
Bai kakarasa yasake ce mai ban fa son shirmay wanda ke karatu zaka zo ka damay ta, ka koya mata shirmay,
Aliyun yana dariya yace o shirmay ko zaka gani in shir may zan koya mata
Sai ya sauko daga kujerar da yake zaune yadan tsuguna kasa yai kasakasa da muryan shi yace ma sheriff ina wuni yaya,
Gabadaya falon suka sa mai dariya banda sheriff da ya dan tsuke fuskan shi,
Yace ma Aliyu dan iska wanan ta wuce yaudar ka ka koma can wurin yan duniya irin ka kuyi tayin duniyar cinku,
Yace Iam telling you wanan karon wlh ba wasa acikin magana na Ahmad,
Nidai ina gama zuba masu abinci na wuce ciki abina batare da nasan ya suka karasa ba,
Ina shiga dakin kiran wayan salimat ya na shigowa mani,
Nadauka tare da yi mata sheri ina cewa anty amaryan ke nan,
Tanbayana tayi bata gan mu ba masallaci wanan weekend din,
Sai ina fada mata cewa wlh su ummi ne da hjy sukazo muna weekend harda yayan mu
Fada takama min tace lalai fadima baki da kirki yanzu har su ummi su zo arasa wanda zaikirani yafada min cikin ku
Hakuri na bata nafada mata cewa suna nan ai tukun don sheriff na wani dan aiki ne,
Taimin alkawalin zata zo zuwa marance insha Allah,
Ina jin hayaniyar su sheriff har suka gama suka fita,
Inda Aliyu ke ce mai yakirani muyi sallama dan Allah ko kallon shi baiyi ba don takaici,,
Sai kuma gani nafito zanje gurin maman Umar dake aiki a baya,
Duk da sheriff yasan cikin rashin sani nafito amma saida yaji haushina sosai,
Aliyu na mai dariya yace brother in-law kaga ikon Allah ko ga ta tafito da kanta,.
Banko waige su balle insan sunayi wurin da zani nasa kai, har zan shige sai naji shi yana cewa yar uwa dan tsaya min inzo pls
Waigawa nayi kowani angul banga kowa da yake ma magana ba sai ni don haka sai na dan dakata mai,
Ya tako cikin tafiya gayu har inda nake tsayee,
Yace shi sunan shi Aliyu baba dan kasar Nigeria ne shi mutumin katsina ne aiki yazo yi a wanan kasar daga Nigeria,
Kuma baida mata amma ya gane ni yana so na kuma yai ms sheriff bayani komai,
Mamaki yakamani kamar ni yar aiki wanan dan gayun zaice yanaso
Sai nadan leka don inga ko da mai ganin mu
Aiko sheriff ne tsaye cikin wani irin mugun kallon da yake min ina nai abinda ba daidai ba.
Dayagane cewa na ga sheriff ins jin tsoro sai yace min ba matsala zaidawo ya gan ni amma may ye suna na
Cikin sauri zan wuce nace mai fadima,,,,,,
🐎ZEEE MAKAWA
✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
5⃣9⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
Almost true life story
Cikin hikima da dabara Aliyu baba yafara koya min So,
Saboda bayan tafiyan su sherrif yakawo muna ziyara alokacin ni bani gida ina school
Noban wayata yace salim ya bashi zai kirani yaji ko banda bukatar komai,
Salim bai fada min ba lokacin da na dawo har kusan kwana biyu,
Misalin tara na dare naga komai da nakeyi nasamu guri nadan zauna indayi nazarin wani takardan da muke da test akanshi cikin sati mai zuwa,
Wayana naji yana kara, cikin mamaki nadauka don nasan cewa ba, a kirana a wsnan lokacin,
Bakon noba ne nagani mai kiran don dai dama daga Salimat ne sai Sheriff din mu ko shi ba koyaushe yake kirana ba,
Sai kusan karshen wata zai kiramu yaji ko muna da bukatar wani abu,,,,
Cikin girmamawa nayi sallaman, , adayan bangare naji an,ansa min tare da yar sautin murmushi,
Bayan haka sai dan shiru ya biyo baya,
Can naji maishi na fadin fadima baki gaidani ko,
Ya salam nace don jin sunana da mai shi yakira, balle ko ince ai wrong noba ne,
Yakara ce min hakana sai nace mai ina wuni to yace min lfy, yatambayeni ya karatu nace mai Alhamdullah,
Ya ce min kin san kodawa kike waya kuwa, nace mai a,a sai yace min
Ina waya ne da Ali baba abokin Sheriff Ahmad,
Dam gabana ya fadi don natuna cewa sheriff yai muna fada sosai akan duk wace take kula maza zai dakatar da karatun ta yai mata aure,
Tuna hakan da nayi yasa nafara bashi hakkuri kamar wace tayi wani laifi
Nace mai don Allah yayi hakuri kada ya kara kirana don in yabari akaji za,afadama sheriff,
Dariya nabashi yace min to wazaiji aishiyasa ma yakirani yanzu don yasan cewa ina daki na ni kadai,
Hakana yaita min dadin baki irin na maza, ina jin shi duk na matsu takashe wayan saboda sai ina ganin kamar za,azo akamani ina wayan,
To tundaga ranan yake kirana duk dare da sunan wai mu gaisa,
Da haka da haka yaita cusa kanshi gareni, tun ina iya boyewa har na fara rashin boyewa ko gaban waye ma zai iya kirana kima musha hiran mu,
Yanzu hankalina ya kasu gida biyu ga karatu ga soyayya, Ali baba akaina kuma duk biyun ina kokarin kulawa da su,
Yanzu karatu mu ya fara nisa sosai don gaskiya bamu da lokaci irin da,
Gashi kuma tunda mukazo bamu taba zuwa hutu makkah ba
Ko anyi hutu a madina muke tsaya abin mu muyi hutun mu Bamu zuwa ko ina,
Salim ne yatafi makka bayan mun samu wani dan gutun hutu,
Bayan yadawo ne yake sheda muna cewa ai sheriff yai aure a dubai wata yar Nigeria ce amma acan take zama wai yar kasuwa ce,
Nayi murna so sai da jin cewa sheriff yayi wani aure,
Nace ma salim ya labarin nafisat sai yake ce min ai tana Nigeria amma ance wai basu rabuba don Abba ya hana sheriff ya bata takarda,
Kawai sainaji dadi wlh har cikin raina don ban son rabuwar su da nafisat sam,
Amal kuwa saida ta gama jin labarin da salim ke min sai, tayi dan guntun tsaki tace wanan ai auren shirmay ne
Kaji ance mata yar kasuwa aikai kasan babu wani abin kwarai aciki sai barikan ci kawai,
Duk da sheriff yake dan uwanta ne amma, Sai naji haushi kalman nata
Naga cewa ai yin auren yafi mai daraja da zama hakana ba mata,
Yau dagani har Amal da mama su Umar agidan maman salimat mukayi ni don tayata aikin taron mijinta da zai kawo mata ziyara daga nageria
Saida mukaga komai yayi tsab mukayi mata sallama muka bar
Lokacin da muka iso namu gidan sai muka tarar da baki
Sheriff ne tare da wata mata fara sol da ita, saida bata da tsayi don ina iya cewa gajera ce,
Da murnan mu muka tare shi, wanda yaji dadin hakan har cikin ranshi,
Nice ma na kula da matar wace ke zaune gefe tana wani shan kamshi,
Nagaisheta nai mata sannu da zuwa, a yatsine ta ansa min,
Azuciya na nace taupa abin jiya yadawo ke nan,
Amal ma a gadarance tace mata sannu,
Wanda hakan ya nuna sheriff baiji dadin hakan ba shima,
Maman Umar takawo masu dan abin sha tana tambayar su komay za,a dafa masu,
Da hannu ta nuna adauke abin shan kamar wace aka aje ma kashi agabanta tace ita bazataci komai, ba sai sunje hotel,
A hankali na duka zaukwashe kayan sai sheriff yai min ahannu alamar indakata da shi,
A hankali yazuba lemon stwberry, a cup din wanda yai sanyi sosai sanan ya jawo wani dan gutun snack ya na ci,
Bansan lokacin da nai ajiyan zuciya ba wacce har takai mai akunen shi
Da sauri yadan kalloni yana mamakin ajiyar zuciyar nawa,
Wanda dama mamakin yadda yaga nakoma yakeyi , don a kulun yagani sai yaga na kara wani irin girma,
Hira sukeyi da salim inda na dan tashi a hankali na koma kan kujerar dake falon gefe guda na zauna
Saidai daga inda suke muna jin hirar komai, niko irin kallon da matar ke min ne yasani komawa gefe na zauna,
Don ina zaton ta san cewa ni yar aiki ce kuma gani ina watayawa kamar kowa,
Wayana ne yadauki tsuwa alamar kira ya shigo ,
Duk wanda ke falon saida yadan kalleni alkarayi ,,,,
Dan basarwa nayi har kiran ya katse, ido sheriff yadan zubo min ganin kiran ya katse ne yasa shi dan kauda kai
Kiran nawa aka karayi cikin rashin damuwa nadauki kiran tare da dan yin murmushi a fuska na
Bandamu da barin wurin ba don nasan babu mai jina a inda nake kuma nai tsabar keantar da muryana bamai jin abinda zan fada,
Bayan mun gaisai sanan na tambaye shi ya aiki, yace ba wani nadai gane inbani nakiraki ba watau ke baki iya kirana fadima,
A hankali nace natuba zan fara kiran,
Abin mamaki dariya naji ya kwashe dashi, sai nadan yi murmushi nima daga inda nake,
Sai yafara magana da dan saurisauri yake ce min jirgi zai shiga shine ya bugo min don muyi sallama zaije wani akine a paris,
Sau biyu muna hada ido da sherrif yayin da nake wayan, sai nadauke kaina daga gefen su nacigaba da wayana ,,
A hankali naimai fatan alheri tare da Allah tasa
adawo lafiya ina mai yin murmushi cikin kashe murya na,,,
Daidai lokacin da nakashe wayan nawa ne muka ido hudu da sheriff din mu wanda yazubo min idon shi da suka dan sauya daga fara,a zuwa fushi,
Sai naga ashe kusan kowa dake falon ni yake kallo ban sani ba
Mikewa nayi abina nawuce wurin maman Umar a kitchen,
Tundaga wanan lokacin sai hiran nasu yadan rage karfi sosai,
Nasamu ta hada masu abincin labawa mai saikin dahuwa ga dadi,
Najera a tire nadauko nakai masu har gaban su na aje,
Ina cewa ga abinci nan nasan zaku iya cin shi don ba mai nauyi ne ba,
Sai alokacin yadan sake fuska kadan yai ma matar da ko sunan ta bai gabatar muna ba balle yace muna ai matar shi ce,
Abincin suke ci hankali kwance har da ita matar sai salim da ke taya su cin abincin,
Amal tace wai yaya bakuwa ce kayi don bamu santa ba, kuma na ganku atare,
Yanajin dadin zama da kan nen shi sosai don yana son su saboda sune mafi kusanci da shi fiye da kowa,
Murmushi yayi kadan ya kalli salim tace baka fada mata tayi sabon anty bace,
Saida Amal ta dan kalli matar tace to, nida ke gefe ina kokarin jona tv na juyo da sauri ina fadin masha Allah,
Gaskiya munyi farin ciki kuma muna mata sannu da zuwa da fatan zaki kula muna da dan uwa fiye da komai a rayuwan ki,
Koba komai tadanji dadin hakan don tasan nafi Amal dama tunda har nai mata fatan alheri,
Sundan kai wani lokaci a tare da mu anata hira tsakanin shi da yan uwan shi,
Inda aziza ta fahinci cewa yana son yan uwan shi sosai saboda bataga abinda yake ba muhin manci ba kamar su,
Don ta kula ko awaya yake magana dasu zaidade suna hira yana nuna jindadin shi,
Saidai tasan cewa bata sami karbuwa ga Amal ba sam
Shakata guda ne ni saboda tace niba yar uwsn shi bace ta jini amma yada yake kula dani yana daure mata kai so sai,
Wayana yakara tsuwar kira again,
Wanan karon salimat ce ke kirana