Showing 18001 words to 21000 words out of 231198 words
Chapter 7 - TAKARI Book Complete by Zainab Makawa .txt
gefe na nuna mata kudin da na samu yau, Ido ta zaro waje
Ina kika samu wanan kudin fadima na fada mata ,yadda akayi tai shiru nawani dan lokaci.
Sai,tace min mutafi gida to.
Koda muka isa gurin hajiya itama saida tayi mamakin wanan kudin masu yawa ,,, ta,dinga samin albarka tana ta washe baki,,,,
Antyna Rugaiyya nasamu waje, zaune gefenta nima nazo na zauna ashe, kuka,takeyi a wajen bansani ba saida na yi mata magana sai naji tai min shiru nakai dibana ga fuskanta sai naga hawaye,,,
Rugumay ta nayi ina kuka nace mata may yasa may ki yar uwata ,,, kuka yakara kubce mata,,,,
Tace fadima baki ganewa ne ke,,,,yanzu don Allah haka zamuyi ta bautawa hajiya bazata maida mu gida ba,,, idan har tace sai mun biyata kudin jirginta ai ina gani dai yanzu ta samu ko
Amma wanan ai bauta mukeyi mata cin amanar yai yawa,,
Nadafata nace aikin san tun agida aka bata mu ,, muyi mata bauta ko ,,, saboda haka sai muyi hakuri har ranan da Allah zai kawo muna mafita,,,, Dan Allah ki daina wanan kukan hakana pls,,,,,,,,,,
🐎ZEEE MAKAWA 🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
[10/3, 19:49] +234 703 602 1388: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
1⃣9⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKWA🐎
Gaskiya muna saki a wanan zamanin da wasu abu biyu da manzon Allah Annabin Rahama yai kwadai ta muna yinsu zai kaimu Aljanna barin su zai iya kai mu wuta. Hakin,makwabtaka da Zumunci ,,,,, Allah ubangiji yabamu ikon kula da makwabtan mu da kuma yin zumuci da yan uwan mu Ameeen👏👏👏👏
Yan uwana yan Huguma group ina maku godiya kulun tare da sauran yan wani group da ban fadi sunan su ba,,,,,,
Almost true life story
Ni fadima na iya bidan kudi kala,kala kamar yadda kusan kudi baya isan TAKARI , Duk wani sallon bara da sana,a an koya min na iya gani yar shekara sha uku zuwa sha hudu,,,,,
Amma hajiyan mu tana alfahari da ni sosai wlh saidai bata fadi a,gabana acewanta idan ta yabani a,gabana zan yi sanyi indaina samo mata kudi,,,,,
Watan Azumi ya kama ibada akeyi yanzu sosai yan kasar mu ta Nigeria dama wasu sauran kasa she ,sun cika garin makka da kewayen ta sosai,,,,,
Munji dadin wanan cikar don kasuwar mu ta budu so sai
Muma muna kokari wurin zuwa ibada,,, Rugaiyya tabamu shawaran kulun kafin, mu fara sana,a mu ,ko,karta mu ,shiga cikin Masijid muyi , Dawafi
Yauma kamar kulun misalin karfe sha dayan rana nakusa cikin dandazo jama,a ina Dawafi,,, kafin in fita in fara bara don bamu abinci saida Yamma muke yi,,,,,
Dandazon yan Serbia sokayo kaina duk sun matse ni banko iya nunfashi saboda kowa nason ya kai bakin kofar shan madara,,,,,
Ji kawai nayi an,dagoni Cak daga cikin rutsun da aka matseni, An ajeni gefe guda,
Saida na maida nunfashi na daidai naga wani mutum dogo, fari, kyakyawa gabana yana min fada ,cikin harshen larabci muryan shi kamar yana lalashina amma daga yanayin fuskan shi fada yakeyi min,,,,
Ke wata irin yarinyace wai kina ganin taron yan Serbia kowa na kaucewa ke bakijin tsoron su ,zo su, tatakaki, su wuce ,,,,
Nidai tunda nasamu na tsira ban ko tsaya nai mai godiya ba na wuce abina ,,,,,,,,,
Bayan kwana biyu da yin wanan rutsun cikin haram da nayi fitar kutsu ,,,,
Dadai da angama sallah azahar lokacin baran mu yayi ke,nan .
Saidai ni nakan canza hanya ne bani zama guri daya,,, idan nai kwana daya ko biyu sai in can wata kofar in kuma canza sallon barana
Yau ma kamar kullun sabuwar kofa na sake ina zaune kamar wata mara hannu ina bara sai naga anzo daidai kwanon bara na , an ,aje, min kudi sabbi fill acikin kwano ,,,,
Koda na daga kai inyi godiya sai naga mai,shi har ya wuce ko,,,,, bayan maishi, kawai nagani amma cikin daga murya nake mai godiya,,,,,
Kudine masu yawa nagani ,Aiko baran da na bari ke nan ranan ban kara zama ba.
Kwana uku tsakani kuma na canza wata kofa don zan canza kama ,,,,,
Kofar da ake shiga da gawa don ayi mata sallah itace na zauna na kawo wani nama na aza akafa na sai kuda ke bi,,,,
Duk da nasan ba kowa ke bi ta wanan hanyar ba sai lima,mai da wasu manyan malamai da mutanen masu son yawan ibada su ke yawan bi wanan hanyan sai ko idan andauko gawa ,,,,,
Idan mun zauna muna yawan samun sadaka daga yan uwan mamata,,,, bakowani mai bara ke yawan zaman nan ba don wasu tsoro suke ji,,,,,,,
Muna zaune tare da yan tsirarun almajiran da ke waje jama,a nata bautar Allah aiko sai a,kace ga gawa nan za,a shigo dasu na wasu mutanen da sukayi hatsari ,,,,,
Cikin Almajiran mu Atika da take zaune kamar gurguwa aiko sai ta manta yadda ta nade kamar musaka,,,, dadai taji ana fadin tarik tarik tarik aiko saita mike tsaye tana shirin gudu,,,
Wata mata, dake gefenta zaune tare da mijin ta tanuna ma mijinta Atika,,, tai, mai bayani cewa itace fa, zaune kamar gurguwa, dazu,,, saiko ya mike, yadanko wuyan Atika ta baya, nan suka fara rikici, tana fadin yasake ta tun suna yi su biyu har takai sunfara ji
Jama,an da ke,wurin ko sukayo kanta wasu na duka wasu na fadin akaita wurin jami,an tsaro,,,,, muna zauna saiga wata da gudu take fada muna ai ankama Atika,,, nan tashiga yi muna bayani ,,,, kafin kace kwabo yan bara sun shiga watsewa saida wanda ke da nakasar gaskiya,,,,,,
Maimakon in gudu sai kawai na nufi gurin da aka kewaye atika ana duka tanata tsala ihu,
Wani balarabe ya rike mata wuyan riga ta baya,,,,
Duk tausayinta ya kamani,,,,
Sai kawai nai kukan kura nafada cikin taron nadauko naman da nasa akafa kamar gyambo na jefa ma taron aiko sai aka watse da gudu ,,, daidai lokacin jami,an tsaro suka iso suma saiko naja hannu Atika muka ar,ta da gudu nace mata mu raba hanya,,,
Ina cikin gudu na ji an,fisgoni anzaunar dani bisa wani abin sallah har jamian tsaro sukazo suka wuce mu kaina na duke,,,,,,,
Saida naga lalai sunyi nisa sai nayi niyar mikewa in gudu
Muryan wanda ya jawoni ranan daga cikin taron Serbia wa naji,,,, yana fadin ki tsaya nan har sugama bincke ,,,, duk wanan maganan baiko waigo inda nake ba,,,,,
Ana tada sallah la,asar namike nabi jam,i akayi sallah tare dani ,,, koda naga an,kusa sallamewa sai na sulale a hankali batare da sanin wanda ya taimakeni ba,,,,
Kafin ace haka har lbr yakarade yan bara cewa ankama Atika Ankama Atika,,,,
Koda nadawo gida ban fada ma kowa ga abinda ya faruba yau,,,,,
Cikin dare na fara barci kawai naji ana tashina ,,,, nikuma lokacin ina jindadin barci na don dan lokacin da muke samu muyi barci kadan ne ba muda time,,,,,
Jin murya hajiyan mu danayi shiyasani mikewa dasauri ,,,barci na ya watsake kamar bani ba.
Waje ta fito dani sai naga wasu mutane su uku tsaye maza biyu da mace guda,,,
Hajy tace masu itace wanan ko sukace eh itace
🐎ZEEE MAKAWA 🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
[10/3, 19:57] +234 703 602 1388: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
2⃣0⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP & KAINUWA WRITERS GROUP🐎
Yan uwa musulumai muso wa "yan uwan mu abinda muke so wa kan mu,,,,,,
Almost true life story
Ido na kara ra budewa inga ko suwaye ke bidana cikin wanan daren
Gaskiya ban san su ba kuma ban taba ganin su ba ma,
Babu abinda ya fado min a raina sai abinda ya faru dazu a wurin bara
Aiko sai naji gabana yai wani dam,,,,,,
Muryan daya daga cikin mutanen ya katse min tuna ne na, ,,,,
Yace fadima munzo ne muyi maki godiya ,bisa ga irin taimakon da kikayi wa yar uwa guda dazu,,,,,
Agaskiya ba kowane zaiyi irin wanan taimakon ba ,,, kuma inba don ke ba agaskiya yau Atika da dubun ta ya cika gaskiya,,,,
Ni,ko sai wiki wiki nake yi a gefen su ,Don gaskiya banso hajiya tasan wanan zancen ba don zata iya duka na,,,,,
Sukayi wa hajiya godiya suks wuce abinsu
Tab suna wucewa aiko hajiya ta ja min kune tana fadin ashe baki da hankali ki,kaje ceton wata maimakon ki gudu shine ke wai gaki uwar tausayi ,,,,,
Aida ankamaki da kin raina ma kanki wayo , idan halinki ne gobe ki koma
Duk fadan da takeyi kaina yana kasa ban daga kai na ko kalli inda take ba,,, fada iya fada dai nasha shi wurin hajiyan mu ranan,,,,,
Lokaci ya ja yan umarah sukazo suka rage yawa bakamar lokacin azumi ba.
Yanzu mun fi bada karfi da ,"yan buga buga,sayar da kaya da abinci , dakuma yan aikin da,ba,arawa,,,,,, kafin lokacin aikin hajji yayi.
Ni,kan dan kewaya gida je muna dan yin aikatau saidai ni gaskiya ban faye son wanan ,irin aikin ba nafison bara da talla yafi mun,,,,,
Ko da muka dawo gida daga wurin bidan kudi ,, yau nasamu hajiyan mu da wasu mata a gidan mu,,,
Saboda haka ban tsaya inji ko suwaye ba,,, sai nadan fita waje,,,,
Wai ashe wasu matane yan kun,giya sunzo gurin hajiya ne suji idan zata shiga a,dashe ,,,, saboda tana da yara aiki gwargawado ,,,,,
Ma,ana akwai kudi sosai a wurinta
Inaji dasu Yumma da anty Rugaiyya suka dawo hajiya na basu shawaran cewa zata fara zuba adashe indan ankwashe mata sai mu dawo gida Nigeria dazama kwatakwata don ita ,ta fara gajiya da zaman TAKARI
Rugaiyya bata yarda da wanan shawaran na hajiya ba saboda tasan halin matan TAKARI basu da tabbas,,,
Kowa na iya cutan dan uwan shi,,,,
Bayan kowa yayi barci sai Rugaiyya ta tadani ,taimin alamar mufita waje,,,,,
Bayan munje waje shine take fada min shawaran da hajiya ta fada masu ,, duk da yarinya nake sai kawai naji ban yarda ba,,,
To amma may ye abin yi kafin dai mu tashi muka tsaida shawar guda,,,
Abinda hjy zinaro taima hajiyan mu ban manta da shi ba don har gobe yana cikin zuciyar hajiya , Kuma Zinaro itace sillan zowan mu wanan kasar,,,,
Amma daga karshe yaudaran hajiya tayi ba ko lbr ta.
Yanzu duk wani abinda muka samu zamu raba biyu muba hajiya rabi, saura kuma mu boye abin mu ba wanda yasani
Saboda muma munyi wayo mukuma dan san mutane kadan
Duk da hajiya bata barin mu muna shiga mutane sosai kulun fada take muna.
A, cikin irin wanan yanayin narashin nayi muka samu gyaran wani shago,, kamar yadda kuka sani cewa, indan lokacin aikin hajji ya gabato jama,a daga kowani ,yanki , na, kasan suna shigowa gari don saida kayan ,
Saboda baki mahajjata masu zuwa aikin hajji
Irin hakan yana kawo muna samun kudi sosai ,,, akan, dauke, mu aikin gyaran shago sauran wuraren masana antu,,, akasari su sai wanan lokacin suke bude shago.
Idan mahajjata suka wuce baza,akara budewa ba sai kuma wata shekara tadawo,, Za,a bude ta,,,,,,
Mun samu wanan aikin a,wani babban shagon saida kayan sawa na zamani , na maza da mata da yara moderate masu kyau ,,,
Sai kuma gefe guda kayan gyaran daki ne kala,kala irin na matan zamani gudan gefen shagon kuma kayan kitchen ne na zamani masu kyau iri, iri ,,, shagon karshe na kayan turare ne kala kala masu kamshi sosai.
Wata hajiya tasamo muna wanan aikin gyaran wurin,
Munyi aiki sosai mun gaji yauce rana ta karshe da zamu gama aikin mu ,,
Kuma za,a sallamay mu mutafi,,,
Ina cikin shagon kayan sawa ina dan gyaran wani wuri,,,
Dai dai,ta inda nake tsaye naga wallet din wani mutun yafadi ,kasa amma banga fuskan mai shi ba,,, ina dai iya hango kafar shi,,,,,,,
Da sauri na sauko daga inda nake nazo nadauki wallet din bandai bude ba inga ko may, ye a ciki ba,
Cikin sauri sauri nake ta diban kafar mutane ko zanga takalman mai wallet din ban gani ba,,,,
Gabda zai zauna cikin mota ni kuma na sheko da dan gudu ina bidan mai wanan wallet din sai nayi arba dashi zai shiga mota,,,
Cikin sauri na nufe shi ina daga mai hannu ,alamar su tsaya,,,
Koda ya waigo sai yaga aidashi nake magana,,, sai yadan tsaya yajirani,,, Yana mamakin ganin wanan yarinyar kuma a shagunar shi,,,,
Mika mai wallet din nayi kawai na juya batare da na tsaya ko yin wani bayani ba,,,,
Mamaki yakama shi, yasan dai ko babu kudi acikin akwai kusan riyar dubu dari ga kuma American dollars gefe guda aje ,,,,,,, gashi kuma na kawo mai abinshi babu wata alamar da ta nuna antaba komai acikin wallet din,,,,
Cikin mamaki yake binta da kallo yana fadin anya kuwa wanan yarinyar ba aljanna bace kowa ,,,
Ko ina sai na ganta kuma bidan kudi zanga tana bida yau kuma gashi Allah ya bata kudin amma sai ta dawo min da su,,,,,
Kuma batare da ta tsaya ko in bata wani abuba daga ciki,,,
Yakoma don ya ganta ,,, saidai ansamu akasin hakan maimakon takoma cikin shagon ashe bata shiga ciki ba,,
Wucewa tayi zuwa wani shago dake gefen su sayen kayan sanyi don su sha,,,,,
Ko ina andiba ba,a,ganta ba babu ko almarta acikin shagon,,,,,
Azuciyan mutane wurin sai suka kama mamaki anya kuwa mutunce ma yagani kuwa kodai ya dan shiga tunane har yaga kamar hakan,,,
Kusan zai wuce yaji Rugaiyya na fadin ina fadima ,, ina fadima tazo su tafi gida,,,,
Ahakan yabar wurin saidai yana kiyastawa azuciyan shi wata,rana zaiganta ai,,,
Yana barin gurin tadawo da kayan sha niki,niki acikin leda,,
Suka dan samu wuri gefen da babu kowa suka sha
Dazasu wuce mai kula da shagon yai masu godiya yabasu kudin da oganshi yabayar araba masu,,,,,
Kudine masu yawan gaske saboda jindadin yadda sukayi decoreting din wajen yayi kyau sosai .
Shiyasa aka basu kudi masu yawa don yabawa da aikin nasu.
Cikin murna da farin ciki suka wuce gida,,,,
A hanyane fadima ke fada masu aita sinci wallet din wani mutum amma dai tayi sa,a taga mai shi har tabashi abinshi.
Sukaina ta dafe kai don takaici tace fadima ki mayar mai fa?
Ashe har yanzu baki da wayo ke, kudin da muke bida kamar mutashi sama Allah ya ba ki shine zaki mayar ma mai shi,,,,,
Rugaiyya dake gefe zaune tace au dake ce ashe bazaki mayar mai da kudin shiba kenan,,,,
Gaskiya fadima bata,kyauta ba inji mari aida bataso inta da ta kawo muna mu muraba,
Hmmm inji Yumma aiko an baku baku zaku kashe su ba hajiyace zata kwashe su duk inda kuka aje su,,,,, shin wai kunsan duk lokacin da muka fita sai hajiya ta caje kayan mu.
Ni ma,ranan da nabar zabirata agida nakoma indauko shine nasamay ta tana ta cajin kayan mu
Naikamar bangane,ta,ba nadauko abina nafito,,,
Hmmmm ai intasan wata batasan wata ba,,, kawai sai anwayi gari ta bide mu bata gan mu ba,,, don daini nakusa gudu daga wurinta ,,,bintu tace zatai min hanya mutafi kasar yamal mu zauna can,,,,,
"Ke,Mari kada kifara hakan wlh kibari kawai mu koma gida yadda muka zo,,,
Insha Allahu bamu dawama cikin wanan ukubar dole watarana gida zamu.
Haka sukai ta shawara a tsakanin su har suka isa gida,,,,,
🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
[10/3, 20:41] +234 703 602 1388: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
2⃣1⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎