Showing 93001 words to 96000 words out of 231198 words

Chapter 32 - TAKARI Book Complete by Zainab Makawa .txt

shiga dakin nata, tana duke tana ta faman gyaran takardun ta,
Wani littafi mai hoton wasu ma,aurata nagani a gefen ta sai na jawo nadan fara diban hoton dake jikin bangon
Nace mata gaskiya sunyi kyau sosai wallahi,
Sai tadan,diba tace ai yan uwan mu ne wanan bashir kenan dan yayan ummin mune, ita kuma matar yar uwan su ummi ce ta haifeta,
Cikin littafin na bude na fara karatu, sai naga sunaye ne mutane da lambobin su birjit,
Batare da ta waigo ba Amal ta,ke ce min sunayen abokaina ne da mukayi karatu da su a bauchi,
Ina ta karantawa tana dan yi min bayanin wasu masu mahin manci, daga cikisu,
Har nakai ga wata Khadijat Abdullahi dogon daji,
Zubur na mike don jin sunan dogon dajin dayi,
Nace mata ita tasan dogon dajin ne bata waigo ba tace min a,a ita kawai a school suka hadu da ita Khadijat din amma yar kano ce,
Nace Anty,Amal tace ummm dataji kiran ba na wasa bane sai ta dan waigo ni,
Nace dongon daji fa sunan garin mu ke nan,wata wata kila, ita Khadijat din yar garin muce,
Don Allah ki taimaka min ki buga mata waya muji ko Allah yasa yar garin namu ne, ita din ne,
Nakara cewa don Allah Anty Amal ki taimaka min kikiramin ita,
Batare da ta waigo tace min to naji, amma sai kin kwashe min wa,yan,nan takardun kin mayar,
Babata lokaci natashi na kwashe duk kayan da ra baza saman gadon
Har abinda batace ba saida nayi mata adakin
Ya,mutsa fuska tayi tana fadin, ke nifa Khadijat ba wai muna wani shiri da ita bace,
Ko wanan lanbar ma ina karba ne tana gurin kada taji daban shiyasa nace abata,
Nakara cewa haba Amal tace o Amal ko nace anty Amal,
Tace min in kawo wayana takira ta,
Aikafin takira layin Khadijat din saida takira kusan mutum uku kafin takira tana fada masu cewa tana kasar saudiya,
Saida taga dama don kanta tai dialing din noban khadijat din
Yako shiga amma har wayan ya katse ba a dauka ba,
Kusan kira biyu mukayi ba,a daukan wayan,
Dole muka kyale amma raina a bace,
Washe gari tunda safeg
Ina saye da yar doguwar rigar danayi sallah da ita ajikina ban riga na shiga wanka ba tukun,,,,
kirana aka yi ta intercoms din daki na
Cikin sauri sauri na sauko batare da na canza kaya ba,
Ina zuwa nadinga jin wani iri kugi da huci a saman ,dakuna kamar wani irin halitta ne yashigo muna,
Kusan duk kowa yana tsaye ina zuwa sai nake tambaya ko may ke faruwa haka na ne,
Almustapha ne yace min in shiga dakin matar sheriff ne sautin ke fitowa gashi kuma Sheriff bai gida yatafi wurin judging tunda safe,
Ba bata lokaci na fada dakin, Nafisat ce kwance cikin wani irin hali ga. kwalaben sirup nan kusan kala biyar tayar a kasa gefen gadon ta,
Ina shiga na tallabo ta aiko sai kokarin sakewa takeyi kamar mara rai,
Saketa nayi da sauri na fito dakin nata cikin tashin hannankali,
Nace ma almustafa yasa adauko min zuma da madara da sauri,
Ana kawowa nayi dibara nabude bakinta na tura mata kusan cokali biyu na zuma,
Aiko yana shiga cikin ta tai wani irin yunkurin amai, saida kowa ya watse don sun dauka ko ta shake ni ne,
Sheriff ne tsaye da kayan games ajikin shi yana mamakin ihun da yake ji tun shigowar shi get,
Sai gashi kuma yaga kowa na batun gudu,
Cikin tashin hankali mustapha ke mai bayanin abinda ke faruwa,
Dasauri ya haura sama dakin nata koda ya shigo tana kwance sharbat da ita saman jikina,
Ga wani irin amai da take kwarawa,
Maman su Umar na tsaye daga kofa rike da goran zuma da na madara,
Cikin tashin hankali yake kallon ta yana tambayar may yasa may ta haka,
Ban kai ga bashi ansaba idon shi ya kai ga kwalaben kayan mayen da ke zube kasa gefen gadon ta,
Cikim tashin hankali ya fidda idon shi waje don mamakin
Wani aman ta kara zubowa mai wari,
Sainace wa maman Umar ta miko min goran madaran da ke hannu ta shima cikin hikima na dura mata shi Allah ya ban sa a,a ta sha sosai,
Sai wani irin amai ya zubu mata, sai kawai jikin ta ya sake ta
Duk sheriff ya rude yama rasa may zaiyi,
Ganin da yayi mata haka yasa yace mu kamota muje asibiti,
Nace mai idan mun kaita asibiti haka za,a tuhumay ka sosai kai ma,
Yagane may nake nufi shi yasa shi yin shiru don hukumar kasan saudiya indan sun fara binciken lamari sai sun gano harda abin da ba suyi niya bincike ba sai sun gano shi, ga mutum
Nafada mai cewa zata samu sauki sosai,insha Allah idan ta farfado saboda naga irin haka a makwabciyar gidan su hajiya laila ,
Dakin na gyara mata tasa sai abin kamshin daki da nasa don dakin ya rage warin da yakeyi,
Abinci naje kitchen nadafa mata maidan nauyi saboda nassn cewa tana fafadowa zata bidi abinci ne taci,
Sheriff duk mamakin wanan yarinyar ya kama shi ,, yace,kai yarinya karama da shegen wayo da dabara haka,
Ummi tashiga cikin wani irim yanayi na,damuwa,
Tayaya har Alhji zanna ya bari danshi ta auri wanan yarinyar da bata da tarbiya ko kadan,
Ita dai tasan cewa duk da Alhj zanna mutun ne shiru shiru,
To amma bai yadda da aikin assha a gidan shi
To ta yaya zai ma Ahamad wanan hadin haka,,
Sai misalin karfe ukun rana nafisat ta farka daga barci tana mai dan bude idon ta da yai mata nauyi sosai,
A hankali ta bude su gabadaya idon ta ya sauka kaina ina tsaye gefe guda,
Ina kallon ta,ta kara lunshi idon nata tayi kamar zata tasahi amma ta kasa, yun komai,,,,
Matsowa nayi kusa da ita ina mata sannu,
Ta yunkura ta tshi saikawai taji ai bata iyawa sam
Nagane nufin ta sai naje kusa da ita nadan tallafa ta ta bayan ta sai tayi kokarin hanani amma ganin da tayi bafa zata iya ba
Saita hakkuri da intaimaka mata din,
Saina kara riko saita dan dago daga kwance, nataimaka mata muka sa,uko daga saman gadon
Munkai tsakar dakJain's ga sheriff fuskan shi murtuk kamar bai taba yin dariya ba
Wani wa,wan kallo yai muna, nikan sai na noke kaina
Da taimako na nasamu taci abinci sosai tako shi,
Ganin da nayi sheriff yadawo dakin yasa ni fita waje
Sai a lokacin nasamu nadan gyara jikina tsab nafito shar dani,
Noban wayan yar dogon daji ya fado min a rai na tashi nadauki waya zuwa dakin Amal
Ina shiga tace min gaskiya fadima bansan cewa baki da zuciya ba sai yau wlh,
Nagane nufin, ta don haka, Kafin taci gaba sai nace mata kowa yataimaki wani Allah na taimakon shi, saboda Allah nayi saboda kuma Sheriff wanda hakan ba karamin rufin asirin shi bane
Cikin jin haushina takara kiran labar wayan amma sai bai shiga ba,
Haka na hakkura nakoma dakin nafisa nasamu ta kara yin barci
Dakina nadawo daniyar indan kwanta kafin anjima kadan
Barci mai nauyi yadauke ni sai gab da sallah magrib na farka
Nayi barcin kusan awa hudu,
Sallah nagabatar cikin sauri, sai nayo waje domin yuwa nake ji banci komai tunda safe dana danci kwai kadan ,,,
Saboda ina fara ci natuna da aman da nafisat tayi sai na kasa ci,
Ina fitowa falo saiko mukayi arba da hjy tsohuwa da Abba, sai
Da ihu naje nafada mata ajikin ta ina murna na manta da duk wa yanda ke falon zaune
Saida na natsu san nan naga wayanda suke tare, cikin ladabi nagaida kowan su nai masu sannu da zuwa
Abinci naga batar masu sai kuma masaukin da aka kai kowan su,
Fafir hajiya tsohuwa tace ita sai dakin ummi zata sauka ko kuma na Amal,,,,
🐎ZEEE MAKAWA🐎








✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
5⃣6⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎🎁NASIBI WRITERS associations
🎁
🎁N🎁W🎁W

Almost true life story,,,


Washegari natashi tunda safe na hada masu break fast, yadda yaka mata tare da taimakon su yumma,
Saida kowa ya kamala,break din ya sanan aka dawo falo aka zau zauna,
Ina tsaye ina hada kayan da suka gama cin abinci da su sai naji Allah Alhaji lawa zanna yana cewa a kamalo mai kowa da yakamata a kira mai agidan,
Falon yai tsit kowa na jiran ana sauraren abinda za a ce masu,
Wani takarada Abban yafitar daga cikin aljihun jallabiyar shi,
Sai da,ya fara bude taro da addu,a tukun sannan ya, kallo kowa dake falon,
Hjy tsohuwa tana zaune kusa da ummi,
Salim da Amal su gefe guda suma zaune,
Sai Sheriff da nafisat dake zaune kusan wuri guda
Duk da ba karfin jikinta take ji ba daurewa kawai tayi tadan fito tana yatsinar fuska,

Alhaji zanna yace ubana mun zo ne wannan kasar don mu tatance wani takarda sako da aka tura wa hajiya acinkin kayan da aka kai mata sako daga nan,
Sai lokacin Sheriff ya dan daga kanshi yadan kali Abban da ke magana ,mamaki yakeyi don bai san kowa yaba da sako zuwa wurin hjy ba,
Jin falon yai shiru yasa Abban yace ma hajiya tsohuwa ,
Hajiya wane ya aika maki da sako,
Sai tace wanan yariyar mai kula da ku, tana dan waige ,waige ko zata gan ni,
Cikin mamaki sherrif yace fadima
Ta kware itace,
Ta aiko min da sakon wani magani dana taba saye na ciwon kafa da kuma na idanu,
Acikin sakon ta jefa wanan takardan
Ta nuna takardan da bakin ta daidai inda Abba ya aje takardan
Sheriff yace mai takarda ya kumsa Abba,
Sai Abban yace yanzu kuwa zaka ji,
Don inba zuwa nayi da hjy taga lafiyan ka kuma taji zancen daga bakin ka,ba ,ba,zata taba yarda cewa lafiya kake ba,
Saboda Abba yasan cewa kazafi akai wa nafisa a takarda don ba halinta ba ne
Asani shi diyan Aminin shi suna da tarbiya sosai,
Salim akasa yaje yakirani,
Lokacin ina nagama wanka ina gyara jikina kafin hjy tsohuwa tafito inda sukeyin mitin,
A cikin sauri da kuma shakku na isa falon gidan
Inda suke zazaune ana jiran in, iso,
Gefen kujera nasamu nadan labe cikin ladabi nakara gaida su,
Alh zanna ya kalle ni azuciyar shi yace kai mutun abin tsoro ne,
Ji wannan yariyar da ko yaushe nake ganin kirkin ta wai itace yau take wanan kullin sherin don kawai ta raba ma yara hannkula, su,
Ina gama gaishe su sai Abba yace min fadima "nace na,am Abba
Yace, ke ,ce kika aikawa hjy da sako nace eh yace harda takarda aciki
sai nayi dan shiru ina tunane. takardan may ke nan kuma,
Yace ke ce sai nace eh cikin rudewa,
Abba yace Alhamdullahi,
Yace Ahmad wani irin zama kakeyi da matar ka har yakai wanan yariyar taima hjy sako akan azo a ceci rayuwan ka kafin , nafisa ta halaka ka,
Zubur na mike ina nuna kai na nace la,la,la haram, haram bani bace,
Bantaba rubuta wasika ga kowaba zuwa Nigeria,
Tsawa Abban yadan daka min, yace bayan mun tambaye ki kin ce muna kece ki, aika,
Ina kuka wi,wi, ina sharban majina,
A hankali sheriff yadan daga yakalle ni cikin tausayi,
Saboda yasan cewa koda nice ma din ai ba karya nayi ba saidai kassh,
May yasa fadiman tai mai haka, saboda yasan cewa ko shi yakai karan nafisa gurin Abba abinda zai faru ke nan
Abba baison ace ga laifin ta sam,
Shiyasa yake hakkuri da komai taimai ,
Saidai fa gefe guda na zuciyar shi tana ce mai bani ce nayi wasikan ba , akwai dai, gaskiya,
Nafisa ce cikin karfin hali tana magana tace Abba bansan ko mai nayi wa wanan yariyar ba,
Ta hana ni shakat agidan mijina,
Idan nai magana yace min ita din amana take gareshi,
Hjy tsohuwa tace ke rufe muna baki zuriar yan sheri aiba don Allah kuka mamaye min jini na ba,
Ta Allah ba taku ba,
Abba na jin hajiyan shi sai yadan yi murmushi don yasan cewa bakin jinin Amina ce yashafi duk danginta,
Jin kukan danakeyi yai yawa yasa sherrif dinmu yin maga a wurin,
Yace, Abba ina takardan Abba yadauko takardan ya nuna mai yace gashi nan, daga nesa inda yake zaune,
Yace bani son kaga abinda aka rubuta don sheri ba kyau,
Saboda ni nasan cewa ko yaushe ne ma waya kana fada min lafiya lau kuke da matar ka,
Tashi yayi har inda Abba yake yace rubutun zan gani kawai bawai zan karanta bane,
Dan dagowa da takardan yai mai kadan,
Da sauri ya waiga gefen da Salim da Amal ke zaune yace cikin ku wake da wanan handwriting din,
Salim yadan waiga gefen da Amal take zaune yana dan kallonta cikin mamaki,
Yace mata ko ke ce tadan girgiza kanta cikin alamar, rashin gaskiya, tace ,a,a
Kawai dai sheri ne ni nasan ba gaskiya bane,
Tausayi naba Salim ganin irin kukan da nakeyi ga kuma Abba nata min fada ina kuka cikin gumza,,
Amal ce ta rubuta ni nace ta rubuta mu aika wa hjy tsohuwa da shi ko zata zo ta ceci yayan mu daga bala,in da nafisa ke son jefashi cikin wanan kasar,
Kowa waigawa yayi inda salim din ke magana,
Har zaici gaba sai kawai yaji saukar mari a kumatun shi, sheriff ne yai mai wanan marin masu kyau,
Sheriff yace shine tundazu ana magana kai shiru ka share mutane ,kasa anata cin zarafi yar mutane,
Abba ya daga hannu shi ma sheriff yace kyale shi,
Ai nasan cewa zasu iya tunda uban su ne yakawo wanan takardan,
Inda yayi halin dattako aida bai bari takardan yakai hannu hajiya ba,
Ita kuma hjy tsohuwa ta cabe zan cen da fadin Shehi baida laifi don ko bayan nasa an karanta min takardan
Saida na kirashi don inji daga bakin shi sai naga ai baima san komai gamay da sakon ba,

Duk bayanin da sukeyi baisa nadan tsagaita kukan da nakeyi ba,
Sheriff yai min magana da larabci wai inyi hakkuri inyi shiru,
Mai hakkuri bai iya fushi ba dama, ummi ce tafito falon cikin kamala,
Don ko ina na jin ta arufe yake lif baka iya ganin komai nata saboda wani zunbudede hijjab da tasa,
Fuskan ta na saye da wani farin medical glass da man mai
Idan zatayi karatu nake ganin tana sa shi,
Guda guda take take takawa a tsakiyan falon,
Guri ta samu gefe guda ta zauna a hankali,
Shiru tadan yi yayin da duk falon kowa yai shiru, saboda mamakin fitowar ta,
A hankali ta dago kanta tace, yaya lawal nadauka ko da kowa zai ce Shehi bai kyauta ba don naji kana cewa ubansu ne yakai sakon tundaga nan har nigeria


Ke nan da sanin shi yakai sakon takardan da yara suka aika ma Umma dashi ki,
Ta dan girgiza kai tace Allahu akbar, tace
Ina zaton kai mai kareshi ne don kusan kafi kowa sanin kowaye shehi din,
Kamar yadada shi wanan din ta nuna sheriff da kai ,
Ke kokarin rufe zancen don gudun bacin ranka ina haka shima shehin ke yi, don gudun barna goma, tsakanin kaida aminin ka,
Inda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login