Showing 66001 words to 69000 words out of 231198 words

Chapter 23 - TAKARI Book Complete by Zainab Makawa .txt

son abu zai iya hakuri yayi abin,
Don haka ma yasan cewa ko wanan auren na abokin nashi ba,ra,yin shi bane ,
Don tunda suke baitaba jin yai mai zancen wata mace ba saida zancen
Tsohuwa dana mahaifiyar shi,
Sai ko kwanaki da yai mai zancen yana son form din makarantar su don ya siyawa sister dinshi,,,
Kafin su rabu saida suka dan tatauna so sai kan zancen,,,,

Yau a gajiye yadawo gida, dom haka yana dan bukatar hutu kadan,
Wanka yayi kafin lokacin sallah yayi ya wuce masallaci bai dawo wa sai an idar da sallah isha,i,
Acikin shigar jalla biya fara kal, mai yar guntun hannu yake,
Zaune yake saman kujerar yadan kishin gida kadan kafanshi mike a saman wani dan stol dake gaban kujerar, ,,
Hannu shi guda ya sa ya dafe kan shi, kamar wanda kan shi ke mai ciwo,,,,
Nasan cewa idan yana cikin wanan irin yanayin bai son damuwa sam
Saboda nataba, yi mai katsaladan watara naganshi zaune irin,hakana nadinga buruntu da kayan da nake jerawa a dinning har cup ya fado ya fashe,
Aiko ya mike tsaye ba shiri, naji ya ce Ya, Subahanallah,,
Kofa yanu min da in fita falon ,
Nikuma ina kokarin nuna mai cewa zan kwashe glass din da yafashe, ne
Wani uban tsawa yadaka min ban san lokacin da bar falon ba, don tsoro,
Ina zan yarda wanan katon yamake ni,
Saida nabari yafita nadawo na kwashe glass din ina yi ina waigen hanyar shigowa,
Shiyasa yau dana ganshi a hakan nake taka tsantsan da aikina,
Hankalina na ga abinda nakeyi sai kawai , ban san cewa anty NAFISA ta shigo falon ba,
Jin muryan shi kawai nayi cikin wata irin tsawa yake magana Idon shi ya yi ja alokacin ,,,
Yace Nafisat nafada maki tun jiya Umurni na baki ba wai uzuri na ce ki kawo mini ba ina fatan kin gane,
Yadda yai maganar shi ya ba kowa dake falon a,lokacin, tabbacin ba alamar wasa acikin zancen nashi,
Da sauri ta juya rai bace ta shige dakin ta yabita da harara,
Muda ke tsaye a gefe wani irin mugun kallo ya watso muna,
Yamike yabar falon cikin bacin rai shima,
Nikan ko a jikina don nasan wanan fadan manya ne, kuma mata da miji,
Dakinta na shiga don in gabatar mata da abincin su na dare,
Waya nasamay ta tana yi cikin fada, take magana
Yanzu ummi kamana zaice wai tunda zai yi baki dole sai naje kitchen da kaina na shirya masu wani abincin alfarma, irin ta mu ta gargajiya, wai yan aikin shi basu iyaba
Yo ni ina zan iya girki ko na mutun biyu bale na mutun fiye da ashirin,,,
Gaskiya saidai yaji kunya amma na fada mai cewa bazan yi komai bani,
A bangare wace take cewa ummi hakuri naji tana bata , tana cewa abinda zaki samu lada kuma zai jidadi kila ya baki kudi masu yawa a sanadin hakan,,,
Duk hakkurin da ake bata bata yarda ba sam dom tace ita bata da matsala akan kudi dashi don ko ma may tace tana so zai siya mata, ne,,,

Niko tunda naji wanan hirar ta nafisa sai na dan shiga halin damuwa don nasan cewa koma su waye zasu zo suna da matukar mahin,manci a gareshi,
Don haka na kudiri aniyar zan fidda shi wanan kun yan isha Allah,
To saidai matsalar ban san wani rana bane bakin zasu zo muna,
Almustapha ne yafado min a rai,
Nasamay shi yana shirin fita,
Da dan saurin nakarasa inda yake, shiko yana gani na sai yadan dakata min,
Bayan nagaishe shi ne nake tambayar shi don Allah ko yasan ranan da bakin Sheriff zasu zo,
Yace min aibanda gobe ne zasu zo abokan sheriff ne da da matan su, da suke zaune nan kasar saudiya sune zasu zo ziyar shi don suga amaryan shi,,,,,,,
Naidai nasamu almustapha yai min bayanin komai a cikin hikima,
Najidadin jin wanan bayani sosai duk da bayanin yazo min a kuraren lokaci,
Banshiga cikin gida ba direct wurin su Rugaiyya na nufa,
Naimata bayanin komai acikin tsanaki ba mu bata lokaci ba maka kama shirye,shiyen kayan da za mu bukata wurin aiyukan,
Tun wanan, lokacin ban samun zama gida ina nan ,ina can, sai zirga zirgan nakeyi kawai,,,

Duk da ya lura da cewa ba wani shiri da nafisan kewa bakin nashi , hakan baisa yadauki wani mataki ba,
Ido kawai yasa mata don yaga gudun ta,
Azuciyan shi kuma,yasan abinda ya kulla zai matan nadaukan fansa,
A,na mu bangaren bayanin da mustapha yai min na taron abokin shi guda da sukaje wani dan kasar mali
Shi mukayi amfani da shi muka dan can za namu salon,,,,,
Washegari, tunda safe muka tashi masu gyaran gida nayi masu yin girki suna yi,
Nai decoration din wani fili dake cikin gidan da duk wani abu da ba hause ke gyara gida dashi,
Hjy laila ce ta taimaka muna da duk wani abinda zamu bukata,
A fanin abinci munyi masa, da miya tuwon shinkafa da miyar ganye, tuwon alkama da miyar kubewa,danye, danbun shinkafa yaji carvege, sai pepper soup nakifi da na kayan cikin rago,
Sai fura da nono mai kauri wanda yasha sanyin fridge,
Ga kunun tsamiya da sugari, har da shimkafa da wake da salad,
Komai an shirya gwanin sha,wa, Idan kagani sai ka dauka ko agida Nigeria ake wani buki ,,,,,,


Tunda ya iso haraban gidan yaga canji sosai har takai idon shi ya hango mai haraban da muka gyara inda za a ci abincin
Batare da ya nufi gurin da aikai decorating din, ba ya wuce cikin gida direct
Ya mai jin dadin hakan da yagani
Itako tana zaune falo tasa wani material, ja,dinkin shi yadan matse mata jiki,
Ta bayan ta yazo yadan rugumay ta kadan saboda farin cikin abinda yaga tayi don sai yau yadan fara cire shakkun ta da yake,
Godiya da taji yana mata yasa tatsaya sororo tana, kallon shi cikin mamaki,
Kafin yai wani magana itace tafara magana,
Tace ban fahince ka ba fa habibi,
Murshi yadan yi yajawo zuwa cikin jikin shi yana fadin wanan surprise din haka,
Tace na may ke nan fa, na taron bakin da kikai muna,
Tadan daga hannu ta alamar aa bata da masaniya ita,
Cikin mamaki ya ke kallon ta takara cewa wlh ban san may kake magana ba aikai
Ture ta yayi daga jikin shi rai bace,
Idan bake bace towa yayi wanan aikin ,cikin ikon Allah dai dai lokacin na shigo falon cikin shigar irin ta hausawa
Atamfa ce zani da riga koriya da dan ratsin flawer yello cikin jikin atamfar dinkinta yadan matse min jikina dan dagwas,,, sai gyale dana dan yafa yellow akai na
Da kagan ni, Duk alamar girma ya dan bayana min, dan kuguna yadan ciko cif cif ,kirjina yadan kunburo alamar dai nadan kosa komai na girma ya baiyana sosai ,ajikina,
Ban ko kula da su ba ina kokarin nuna wani dan center carpet da za,a dauka zuwa waje
Kallo duk suka bini dashi na mamaki,
Sai a lokacin nagan su tsatsaye,,,
Batare da wani damuwa ba nadan gaishe su cikin girmawa,
Nacigaba da abin da nake yi abina,
Da mamaki yabar wurin zuwa sama inda dakin shi yake,
Yau gezena,shadda yasa mai ruwan chuculate,, dinkin tazarce ne ,,,sai hula yar zanna bukar yar asali da yakafa akan shi ,,,,agogon company rolex yasa a hannu shi takalma bakake, suna wani irin kashe ido,
Yusuf ne yabugo mai waya cewa gasu nan sun iso ,
Cikin fara,a nake taron bakin zuwa cikin katafaren falon mu, daguda guda sukai ta iso wa gidan har suka gama zuwa,
Saura mutum guda ya rage baizo ba, wanda naji suna cewa Ali baba ,, wai ai baida iyali anytime zai iya iso, daga yamal,,,
Agaskiya duk wanda yazo wanan yar walimar taron amaryam Sheriff din mu ya yaba da irin tarbon da akai mai sosai,
Zirga zirga nake tayi cikin jama, don gabatar masu da abin tabawa ,,
Gefen mata daban na maza daban amma duk da haka ana iya ganin juna don duk guri gudane,
Wata yar matashir mata fara yar kabilar yarbawa ce, da baby ta, ina ganin haihuwar fari ce mata,
Yaron yanata kuka tunda sukazo, tayi lalashi yaron yaki yin shiru,
Kusan kowa a wurin ya tausaya ma yaron yadda yake ta faman tsala ihu,
Zuwa nayi na karbe yaron a hannu ta nawuce cikin gida dashi, da ita,
Ruwa nasa masu zafi nai ma yaron wanka wurin cire pampers naga a she kashi yaron yayi,,,
Naimai wanka na gyarashi tsab tabani wani kaya na saka mai,
Lokacin da muka fito wajen taron, mu tararda har an fara cin abinci kowa sai yabawa yake yi da irin girkin da akayi,
Nafisa tana gefe fuskata babu ko alamar fara,a
Tun matan abokai na janta da yar hira har suka gaji su ka kyaleta,,
Tana ta wani matse fuska kamar mai jin warin mutane,
Muna ji suna hiranta kasa kasa suna cewa wanan ai ta tsofe ma Ahmad
Wata kuna tace yo ai auren zumunci ne inbashi ina zaikai wanan ai gwago ce,,,
Gyalen da nasa yana da sulbi sosai, gashi kuma ban iya yafa gyale ba dama sai dai inyi rolling din kaina kawai, gyalen yanata sabule min,
Ga kuma yaro a hannu na, duk na tsawala ina kokarin mika yaron wurin uwar shi sai gyalen ya karkare faduwa kasa,
Subbahanallah aiko idon maza caaaaa akaina cikin sauri na jawo gyalen na mayar akaina, daidai lokacin naga sheriff din mu yai min wani irin kallon banza
Wanda banji dadin hakan ba,
Duk sai naji na tsargu wlh,
Don ni ban san may nayi ba,
Daga inda yake yaga nadan shiga damuwa sai yadan yafito ni da hannu, Sukaina ce ke fada min yana kirana,
Cikin ladabi na isa inda suke zaune shi da su Yusuf,
Fura yace min in debo masu a cups,
Nakai masu furan sai santi sukeyi,,
Ga al,adan su duk wanda zai tafi sai ya aje wani kyauta mai muhinmanci arayuwar ma,auratan wasu na bada kudi masu yawa, suce aba ma amarya wahalar girkin ta,
To muma dai haka din ne don wani katon tire aka dinga zuba duk wani gift da aka samu a wurin
A gaskiya ba laifi don dai an samu alheri so sai,,,
Muna kallo bakin mu suka dinga barin mu da guda daguda har suka watse suka bar mu mukadai agidan,
Saida na ga duk mun gyara ko ina agidan sanan nasamu natsuwa,
Kayan gift din na hada wuri guda na nufi cikin gida da su wurin anty nafisa,
A Falo na samay shi zaune yana waya daganin shi yana cikin nishadi yau
yana ganin zan wuce da kayan gift din,inkai ma,anty nafisa,, dakinta sai yadakatar dani da hannu
naja nayi tsaye cak wuri guda,,,
Ina sauraron shi inji mai zai ce min,
Yana gama wayan ya dakai diban shi gare ni
yace min in,bude komai yagani a gaban shi na ,aje kayan
nan na duka nadinga cire kayan guda gudu ina kuma karanta mashi,sunan wanda yaba da gift din
Abin mamaki ina kai ga na karshe sai naji yace min, duk gift din kayan sawan in dauka,
Kudi kuma in dauka in raba ma duk wanda mukayi hidimar dashi,,,
Saura in,dauka,cikin mamaki nadago kaina don jin zancen shi,,,
Zan yi magana ya dago min hannu yace min ya isa
Jiki ba kwari na tashi don in wuce,
Sainaji yace min yagode da fitar dashi kunyan da nayi,,
Ina dan murmushin jin dadi ban san cewa anty nafisa tana bayana tsaye ba tun lokacin da na fara nuna mai kayan,
Gani ta dayi tayi murtuk da fuska yasani dan ja tsaye ,
Kauce mata nayi nadan bi ta gefen ta nawuce abina da kayan
Muryan ta naji tana magana cikin tsawa take cewa wanan ai wulakanci ne,
tayaya zai dauki kayan yaba yar aiki
Acikin azama naji yace mata wace,ce yar aiki,
Nida take gani zaman kaunar shi da suke ciki daya yake dauka, ba matsayin yar aiki nake ba.
Yace ko kin taba ganin yar aiki tafidda shugabanta kunya kar yadda taga nayi a yau din
Yace ko kintaba yakara tambayar ta cikin tsawa,,
Nidai na wuce abina nabarsu nan yana ta gagasa mata maganganu masu zafi,
Bayan na aje kayan dakina gurin Rugaiyya na tafi,
Na bata labarin yadda duk mukayi da Sheriff din kan gift din su,,
Ta dafa min kafada tace fadima halinki ne na alheri ya ja maki,
Duniya ance indan baka da kudin da zaka taimaka wa mai kudi to kataimaka mai da karfinka,
Kinga kinfitar shi kunya ,
yin hakan yasa shi jin dadin alherin da kika mai a yau ko mai yai maki kin can can ci hakan ne fadima,
Tana fadi tana har hada kayan ta don zuwa gida na mika mata kudin duka nace mata ta aje cikin wanda muke tarawa,,
Ashe duk kudin na a cikin jikin ta nan take boyewa gudun kada a sace muna,
Saida ta hada komai tadauki jakar ta da dan abincin da zata kaiwa su hajiya da su Umar,
Kawai sai naji banji dadin da zata wuce ba jinayi dama muntafi tare don ina kewan su hajiya, ina son ganin su ina son in kwanta tare da su muyi ta waka da labari har barci yadauke mu kamar yadda mukeyi kullun,
Ina kallo ta wuce ni raina yai min baki,kirin






Rugaiyya har ta kai kusa da gida ashe bata sani ba yan bagaladi suna biye da ita,
Tundaga unguwar su sheriff din mu suke biye da ita tunda sun san cewa duk bakin da akayi sun koma garu wan da suka fito, su,,,
Bata ankara ba kawai taji sun kewaye ta sun mata circle, ba ta da daman gudu,,,,,,,,,,




🐎 ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
[10/4, 14:31] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
4⃣6⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA 🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎


Allah ka tai Maki Musulumi Duk Inda yake,,,, ,Ya Allah Karufa ma Kullumin musulumi na Duniya Asiri Ameen


Anty Halima Garko


Almust true life story,,



Wa,iyazu billah abinda kawai take fadi kenan idon ta a rintse ,
Inbanda Allah ba wani abinda take iya fadi,
Basu yi wani dogon bincke ba suka gane cewa takaru ce ita bata da takardan zama yar kasa,
Rugaiyya bata basu wani wahala ba don haka bata wani sha wuya ba, wurin su,
A, haka suka tafi da ita zuwa inda ake tara kamamun irin su,,,
Duk wanan abinda yafaru a idon wani makwabcin mu ne, yana ganin an wuce da ita ,
Da saurin shi ya isa gidan hajiyan mu yana sheda mata duk abinda yafaru,
Sun yi kuka sunyi bakin ciki sosai wlh,

Ina can dakina jiki ba kwari tunda anty na ta,tafi har na kwanta sai naji bana jin barci , duk da gajiyan dake jikina,
Don haka sau,kowa nayi daga kan gadon na zauna kasa,
Kanya gift din da aka bani na jawo ina fitar wa guda guda ina kalon su,
Duk kusan dogayen riguna ne har guda hudu nace a raina sai muraba nida Rugaiyya na
Sai kuma dikin shadda redmaid masu kya kusan guda uku suma nazabi guda nace biyu in bata tasa don tana son irin wanan kayan tun muna kano,,,
wani kwali da najawo waya ce mobile cellular mai shegen kyau, cikin kwalinta tare da tarkacen ta,,,
Aiko ina ganin wayan ban san lokacin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login