Showing 153001 words to 156000 words out of 231198 words

Chapter 52 - TAKARI Book Complete by Zainab Makawa .txt

din da abin cikin, cikin nawa yayi, kawai,
Wani irin yunwa na farfado dashi, wanda har jikina rawa yake yi,
Duk wanda ke kusa saida yai mamakin irin abincin da naci, yau,
Nida kowa yasan cewa bani cin abinci sai gashi nakusa share plate guda ina gamawa na kara kwantawa, sai barci,
Haka sheriff yakwana kusan a zaune ranan don da na motsa abinci zanci,
Sai yakasan ce duk wani motsi nawa idonunshi na akaina musanman rana yana tare da ni,,
Sai bayan kwana biyu na san cewa a,asibiti nake kwance,
Nayi mamakin hakan kware da gaske don ban san ko mai yakawo ni ba,
Sai lokacin da askarawan saudiya suka shigo gurina don suyi min dan bincike,
Abinda nasani kawai na iya fada masu,
Suka rubuta tare da shaida wa sheriff cewa an kusa cin nasarar gane ko waye wanan mutumin,
Saida jikina yai min karfi sosai aka sallamo ni daga asibiti,
Bayan sun tabatar da cewa lfy ta kalau, har baby nawa,
Saibayan kamar sati guda aka gaiyaci Sheriff a office din bincike sun gane cewa yaron da yai yunkurin shaka min wanan powder daga Yamal yake,
Kuma bincike ya nuna cewa sun dade suna bibiya na ,
Sai a wanan ranan Allah yaso basu sa,a,
Sheriff najin cewa daga Yamal suke sai, ya mike tsaye yana fadin Alin Alin
Bayan an gane cewa Ali baba ne yaturo su kuma daga shi har su , sun bar kasan tun wani dan lokaci
zuwa kasar turawa inda Alin din ke aiki yanzu,
Wanan abin yaiwa Sheriff ciwo so sai saida kuma yasan cewa komai dadin dadewa zasu kara hadewa da Alin din insha Allah,
Kowa yaji mamakin cewa wai Alin ne yaturo atafi dani a cewar shi wai dole ne sheriff yai min na aure shi,,,

Kulawa ta musan man nake samu so saidaga sheriff tare da sauran yan uwan shi,
A haka na fara rubuta jerabawa na karatune sosai babu kama hannun yaro,babban burina shine in sama sakw na results mai kyau dan in amfana da abina nsn gaba,
Kusan ko yaushe, ina samun sakon cards da kuma gaisuwa da fatan alheri daga Sheriff,
Saida mukayi first exam din mu sheriff ya ce ma ummi yana son ya kaini kasashen waje s diba lafiyar jikina dakyau da na baby shi,
Jin haka yasa sam bakawo komai ba a,raina jin danayi cewa zamu tafi ganin likitane,
Amma sai nake cewa Salimat yanzu duk irin kokarin da likitocin saudiya sukayi akaina za,ace kuma sai ankaini wani guri,
Nace mata nidai gaskiya nafi gamsuwa da aikin su tunda su, yan uwa nane musulumai
Wa yan can ko kafirai ne wa yanda ba sa kaunar cigaban musulumai sam,
Salimat tace ai saikiyi shin dake da baby da baby duk mallakan shi ne kuma kudin shine zai kashe bana ki ba iyakar ki, zama ajirgi yar uwa,
Dole haka na Salimat ta shirya min kayana a yar karamar kit muka tashi zuwa Riyadh da marance saboda tafiyan dare zamuyi zuwa kasar paris ,,
Tun a madina da mukayi sallama da su salim da sukayo muna rakiya,
Nafara ganin canji ga sheriff,
Sai a wanan tafiyar nasan cewa ashe dama ban san kowaye sheriff Ahmad lawal ba,
Saboda ya canza min ga sheriff din da nasani ya koma ma min wani can da ban,
Wata irin mahaukaciyar soyayya yake nuna min wanda bantaba sanin cewa akwai shi ba har za,a iya yiwa mace shi ba,
Tunda muka kasance a guri guda koyaushe kusan sheriff ya man,ne a jikina
A marci kawai yake ta faman kwasa abinshi, al,amarin yaki barinsa balle, yaji na gundure shi,
Sai kuma wani sabon shagwaba yazo min wanda ni sam ban ma san cewa ina yi ba sai fama langabewa nakeyi
Wanda iyakar gaskiyana ke nan saboda ban saba irin haka tare da namiji ba,
Sheriff yakoma min kanar wani wawa saboda yawan like min dayake har takai yadan daina fita wurin harkokin sa sosai, koda yaushe yana like da ni
Saida fadima taga abin banawasa bane ya sa taimai maganar abinda yakawo ta
Murmushi ya yi yajanyo ta zuwa jikin shi yace mata haba Fatima aikwai wani likitan da yafi iya,awone a yanzu,
Kiya addu,a kawai Allah ya sauke ki lafiya ki haiho mi baby mai kama da ke ,
Kunya ta kamata, ta kwantas da kanta sosai a kirjin shi,
Cike da shagwaba tace to amma aini ce min kayi zan zo a kara diba lafiyata ne so sai,
Ya ce in bada ke Fatima kina ganin cewa akwai wanda zai auna ki da kyau bayan ni,
Ya dan kara janyo ta kadan yace kidan kara daurewa nan da wani sati zamu koma gida insha Allah,
Danbuga kafar ta takamayi alamar ita bata yarda ba wayo kawai yake mata,
Yadan lunshe ido yace fadima bakya jin dadin kasan cewa atare da ni ne koko ya, ya ne a,
Tace ni kawai dai gida nake son komawa gurin su Amal,
Yasan cewa ba laifinta bane, don bawai ta saba dashi bane irin haka yasan cewa dama sai a hankali,
Saboda duk yadda yaso ta cire kunyan shi fadimar ta kasa hakan,
Satin su biyu cif a paris suka wuce kasar italy daga italy suka wuce dubai,
A ranan fadima ta godewa Allah da yai mata wanan baiwar da daukaka a,rayuwan ta,
Ina rungumay a jikin shi ,don haka yake min duk inda zamu indan har tare zamu fita,
Ajikin shi zan man,ne har inda zamu ba zai sake ni ba,
Wasu makullaiya ya miko min yace min makullaiyan moticin kune wanan keda su,
Nafisata saboda nasan cewa saudiya basa barin mata su tuka mota yasa za a wuce maki da shi Nigeria
Idan kintafi can zaki dinga amfani da ita,
Murna zanyi ko farin ciki, sai kawai naji baki na yana zuba godiya,
Yace mu a,a ni ban son godiya kinfi kowa sani,
So nake kawai ki so fiye da komai da kike so aduniya sai kuma sai zuria masu albarka da zaki dinga bullo min,
Daga karshe in kasance namijin dayafi kowa dace da gyaran wurin gado,
Murmushi na danyi nace mai insha Allah zan kwatanta,.
Murshi yayi kawai a ran shi yace badai wayau ba Fatima,
Sosai wanan karon ya matse ya ce min Fatima banda wani guri yanzu a rayuwana da ya wuce in samu zuri,a masu albarka indan kikai min haka nagode Fatima,,,
Wanan maganar da yayi ta karshe yasa yabani tausayi sosai ban san lokacin da na shige cikin jikin shi ba sosai,
Ji nayi ya nemo bakina ya man,ne da nashi, wuri daya, can wata duniyar na tsinci kaina irin duniyar mai nuna kalar kore shar,
Wanda kesa ka manta da kowa da komai naka,
Fatima sai godiya take ga Allah ubangiji subahanahu wata,ala da wanan baiwar da yai mata lokaci guda,
Matsalarta guda yanzu shine mahaifiyar ta da yan uwanta su ne matsalar dake da mun ta,
Idan ta tuna kowani irin hali suke ciki yanzu sai hankalinta yatashi so sai,
Don haka ko yau da ta tuno da su sai ta tsinci kanta da rashin walwala.
Da jin komai na duniyar yafita mata a rai gaba daya,
Lokacin Sheriff da yafita zuwa maikatar su na Abu Abdallah ya shigo masaukin nasu,
Hannun shi rike da yar briefcase din shi dake dauke da laptop dinshi da sauran takardun su,.
Ganin da yai mata cikin irin wanan yanayin yasa ya nufe ta da sauri yana mai aje yar case din shi saman kujera,
A gabanta ya durkusa ya dan kamo hannun ta ya ce may yafaru ne fatima,
May ye matalar ki fada min pls,
Duk sai tambayar yakara ruda ta, nan da nan idon ta ya dan ciciko da hawaye,
Sai hankalin Sheriff yakara tashi,
Yace haba fatima kada kimin haka pls ki fada min damuwar har in akwai
Farin cikin ki shine nawa fatima, don ke ce kusan duk wani kwanciyar hankalina,
A hankali nadan zamay daga rikin da yai min na ce,
Ina tuna maifiyatace da yan uwa na, saboda ban san irin halin da suke ciki ba acan,
Ba karamin dukar zuciyar shi wanan zancen yayi ba saboda yasan cewa gaskiya fatima ke yi,
Shi yakamata ya fara tuna wa da hakan tun kafin ta fara magana
Amma sai abubuwa suka sha mai kai har ya shafa da zan cen,
Ki kwantar da hankalinki Fatima idan har Allah ya sauke ki lafiya dole muje su gan ki da akwai shirin da nakeyi gamay da hakan,
Hakadai yai ta mata dadin baki har ta hakkura tadan kara sake jikinta shiko yai ta kwasar garan shi,

Ba karamin sayayya Sheriff yai min ba din kayane irin na matan manya na alfarma ya saya min
Suturu ne masu tsadan gaske ya saya min, irin kayan matan larabawa tsakiya ma su tsadan gaske,
Wasun su suna hade da alkyaba mai hade da hula,
Sai dogayen riguna different design masu kyau da daukar ido kowani da abin lailayan jikin shi,.su takalma da jakkuna kala kala,
Ita da kanta tace mai kayan sun isa haka,
Saboda cika mata ido da sukayi, ga kayan baby unicef da ya saya suma masu tsadan gaske,
Murmushi yayi da tace mai kayan sun isa hakana yace fatima shigar ki ta alfarma cikin suturu ne mutunci na banda wani buri arayuwa na banda in kyautatawa iyalina da yan uwana,,,,,,,


🐎ZEEE MAKAWA🐎
✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
7⃣5⃣
BY
🐎 *ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA* 🐎
🐎 *HUGUMA* *GROUP* 🐎


Almost true life story,,,,,


Jirgin da zai sauka birnin madina, ran daren Laraba muka shigo,
Salim ne yazo taron mu shida wasu mutum biyu, cikin farin ciki da kwanciyar hankali muka sauko
Kallo guda zakaiwa sheriff kasan cewa ya samu lafiya fiya da ,da ya wani murje yadan kara kaurin jiki kadan gawa wani haske da yakara,
Muna hada ido da salim naga yai min wani kallon mamaki, yana murmushi,
Mungama clearing na komi ,muka fito cikin air port din ,motoci ukune muka jera zuwa gida,
Katuwar pickup din dake bayan mu an lodo mata kaya saida ta shake fam,
Muna tafe salim nata zolaya na yanata mamakin irin kyaun da nakara cikin dan lokaci guda,
Ina jin duk abinda yake fadin saidai ban iya ansa mai alokacin saboda duk a gajiye nake
Ga wani irin barci da nake duk ya kara saukar min da kasala ajikina,
Maimakon mu tafi gidan mu inda muke sai naga mun yi parking a wani kyakyawan gida mai kyau da kuma girma sosai,
Sai alokacin Sheriff dake gefe na zaune yadan waigo yana kallona
Ya dan duko kadan daidai saitin kunne na yace min welcome to your new house, fatima,
Da sauri na mayar da dibana akan gida cike da tunane iri,iri,
Dan kallon shi nayi da mamaki sai kawai yadan daga min kai kadan alamar eh,
Cak naji nunfashi na kamar ya tsaya min saboda mamakin, jin wai wanan gidan gidan da zan zauna ne,,
A,zuciyana nace ni fadima diyar inna yar kulu ce zata shiga cikin wanan katafaren gidan mai kyau,
Ginan gidan yakai gina a gaskiya kowa yasan yadda gidajen saudiya suke da kyau da tsari kamar ba hannu yai aikin ba,,
A hankali na fito motar sheriff yafito inda nake a ya dan rika min hannu cikin kulawa da so da kauna,
Mukashiga cikin gidan gami da sallaman mu,
Kallon mamaki kawai nake bin gidan da shi, saboda irin tsaruwar da gidan yayi,
Motsi da naji alamar akwai mutum a gidan ya sani daga kai da sauri nakai kallona ta gefen da naji motsin,
Don in ga ko waye, hakan yai dai da lokacin da mama Umar ke kokarin bude falon gidan don mu shiga,
Mukayi ido biyu da sauri na ja hannu daga jikin sheriff na nufe ta da murna na,
Muka rungumay juna cikin murna da son junan mu,
Kafin in mata wani magana saiga salimat rugumay da As,mau tana muna lalai mar ha bbin,
Bansan lokacin da na sake maman Umar ba na nufe ta, na rugumay su,
Gyaran muryan da sheriff yayi ne yasa muka dan waiga ya tsaye inda na barshi hannu shi a cikin aljihun shi
Yana muna kallon cikin nuna alamar in bi a hankali pls,
Sukuma su Salimat cak suka tsaya gaba dayan su suna min wani kallon cikin mamaki,.
Murmushi na sake masu, gami da karasa ga kujerun da ke falon nadan zauna,
Ganin kallon yai yawa yasa na dan kalli kaina ina mamakin ko may sukaga na canza ajikina suke min wanan kallon,
Cikin natsuwa na dan kalle su nace anty Salimat, wai may nayi ne kuke min wanan kallon haka,
Kafin su bani ansa Amal ta fado falin da kusan gudu,gudu,sauri,sauri,
Tana zuwa ta fada min ta rungumoni ajikin ta, muka dan kankame junan mu cikin murna da an nashuwa da jin dadi,
Sai a lokacin naga UMMI tsaye, a bayan Amal, tana muna murmushi,
Tana fadin, a a tafiyan cikin, dare haka, aiko saidai jirgi kam,
Tsam,tsam na isa gareta saboda kunyar ta da nake ji na dan rugumay ta,
Haka aka hau murna da farin cikin dawo war mu lafiya,
Ganin da Ummi tai min na a gajiye nake yasa ta cewa ya kamata mudan huta kafin a kira sallah,
Kowa yace gaskiya kam,
Wata sabuwa wani kato bedroom mai dauke kayan alatu iri, iri Amal ta kai ni,
Mamaki duk ya cika ni jin cewa wai shine daki na,
Cikin mamaki da kuma nuna hankali nake karewa dakin kallo,
Fitar Amal ya bani damar cire kayan da ke a jikina a, hankali don duk a gajiye nake a lokacin,
Sheriff ya shigo dakin a lokacin shima a gajiyen yake saboda dan bata lokacin da jirgin mu yayi a Dubai kafin ya taso,
Ta bayana yadan zo yana kokarin tayani cire rigar,
Saida yaga ya cire saura yar breezeir kawai da dan bujen ciki yasa ya dan kyale ni, rigar barcin da nagani a saman gado nadauka, na sa ajikina,
Sai a lokacin na fahinci cewa ashe wai daki guda zamu zauna da ni da sheriff ,
Tirka shi, ga ummi ga su salim da Amal zan zauna da shi daki guda
Gaskiya da sake bazan iya ba sam
Yagane mai nake nufi sarai, saidai bai nuna min yagane ba, wanka yaje yayi yana fitowa ina zaune bakin gado har yanzu sai ce mun yayi bangaji ba ke nan tun da ban kwanta ba ko,
Nadai san cewa bazan yi wanka ba a cikin daren nan ba, ko,
Saida na dan bata rai nace, ni gaskiya dakin Amal zan koma,
Kafin in wani maga sai kawai naji ya kwantar dani ta baya a hankali,
Bada son raina ba dole na hakkura hakana na kwanta tare da shi daki daya,
Duk da gajiyan da muka kwaso hakan bai hana mu farkawa da wiri ba don yin sallah a suba ,
Sai dai ina idar,wa na kara kwantawa kuma ,sai wani barci mai nauyi yakara daukana,
Yuwa kawai ya sani farkawa, da ga barcin,
Wanka nayi nafito cikin shigar wata doguwar riga irin ta matan Brazil,
Rigar light blue ne, har kasa take saidai hannuwan ta shara shara ne haka bubude, cotton ne sosai sai wani sulbi da yauki takeyi, nasa yar gyalenta na daure kaina,
Saida naci abinci so sai na koshi a lokacin ne, nake tambayar anty falmata,,
Amal ke sheda min cewa ta koma gida tun bayan wucewar mu da kwana uku,
Gaskiya banji dadi da ta wuce bani a gari ba don,
Salimat da ke gefe take ce min fadima waiko kinga yadda kikawani kara girma ga fari dakikayi,
Kinyi wani kyau sai kace irin matan nan da muke gani a TV ko muji rabarin su,
Murshi kawai nai mata nace aike dama kullun haka kike cewa idan kin kwana biyu baki gan ni ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login