Showing 201001 words to 204000 words out of 231198 words

Chapter 68 - TAKARI Book Complete by Zainab Makawa .txt

mahaifiyarta tai mata kuma taja mata kunne akan ta tabbatar da ta tafi, ganin yaran da aka haifar mai dan haka zai sa yadan wanke zargin da yake mata,
Haka ko akayi dan washegari, ya shirya musalin karfe tara na safe da ganin shi tasan cewa can zai tafi,
Dai steps din din karshe take ce mai ai mata kwatancen gidan don taje ta dibo yaran,
Kallon mamaki yai mata tare da zargin wani abu daga gareta dan haka yace mata tabarshi kawai basai ta tafi ba ,
Tagane nufin shi amma sai tace indai dan abinda yafaru ne jiya dan Allah ya yi hakkuri aikin shedan ne, insha Allah bazata kara maka mancin haka ba,
Allah ya kyauta kawai yace yasa kai yafita inda Bashir ke jiran shi awaje,
Har sun dan fara hanya kiran Amal ya shigo a wayar sheriff bayan sun gaisa ne Amal ta tambaye shi lafiyan mu sai kuma tace mai ga hjy tsohuwa da ma itace ke son magana da shi,,,,,,,,


🐎ZEEE. MAKAWA🐎




[12/4, 11:19 PM] ‪+234 703 300 7734‬: ✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
9⃣0⃣


🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎


Almost True Life Story,,,


Muryan hjy yake saurare yana murmushi kawai dan yasan cewa wani sabon fitina take son kirkirowa kawai,
Jin yai shiru yasa hjy ta tambaye shi ko yakashe wayar ne cikin harshen kanuri take tambayar shi,
Cikin sauri yace ina sauraren ki hjy ina jiran ki gamane
Sai kuma ta fara kuka kamar kulun tana kwararo mai addu,a tana mai sa mai albarka, da neman mai tsari a,rayuwar shi,
Jin kukan zai kashe mai zuciya yasa shi saurin kashe wayan,
Ya lunshi idanun shi a hankali, tare da ajiyar zuciya
Can bude idon yana kallon shimfidaden titin da suke tafiya akai,
Bashir ne ya ce mai tazo dawani sabon zance ko,
Hmmm kawai sheriff ya ce mai yace ban ma santa inda zan fara wanan zancen ba ,
Yadan juya inda Bashir ke zaune yana jan mota yace
Wai akawo ta Abuja taga yara, dan tana son ta zauna da su,
Bashir yace aina san za,arina wallahi wai waya fada mata, aida sai an yi sunna kawai a fada mata,
Ido kawai sheriff ya lunshe yana murshin jin kalaman Bashir,
Dan daga shi har Bashir din kowa yasan halin hjy tsohuwa,
Kawai shi fatan ako dayau she yasa mu su rabu lafiya da yar tsuhuwar duk shima yasan cewa duk cikin jiko kin ta, tafi ji da shi,
Idan kuma har ya furta cewa kada tazo gaskiya komai ma zai iya faruwa
Shiko bazai so ace ansamu wani akasi daga gare shi ba,
Dariya Bashir yai mai yana mai cewa rigimaman mata kawai duk fitina take bida,
Daidai lokacin yakarya kwanar shiga gidan mu ya ce wa sheriff ka shereta kawai idan ta, tambaya kace mata ni ne naki zuwa dauko ta,
A lokacin aka wagale masu get din gidan, mlm Basiru da ke zaune waje saman wata farar kujerar rubo ya taso zuwa inda suka Parker motar su dan ya bude masu kofa,
Bashir ya cewa sheriff wanan mutumin wallahi tausayi yake bani so sai ,
Batare da sheriff yabashi duk ansar maganan shi ya bude kofar motar ya fita, zuwa cikin gida_

Zaune nake a kasan carpet tsakiyar dakina, ina shan perpper soup din kan rago wanda yasha kayan yaji,
Sai kunun kanwa wanda gwago ta dama min ,yar aikin gidan ce tagwadawa gwago yadda zatai amfani da gas din duk da haka gwago bata yarda ba saida ruwa yai zafi aka bata ta dama min tana ta mamaki,
Yar aiki wata Bunufiya ce badai za,ace mata tsohuwa ba matar,
Saidai gaskiya tana da kirki so sai ga ladabi kamar may, dan har kasa take rusun,nawa mutum,

Yau atamfa ce a jikina cikin wanda salimat ta dinko min a sokoto,
Atamfar ja ce sai fararen flowers da akaimata hade dan kallan kore mai haske,
Zani da rigane dinkin ya karbi jikina so sai ya zauna min dan dagwas ajikina,
Da sallama shigo dakin, dakin da keta kamshin turaen wuta mai dadi cikin wanda salimat taimin tanadi tun a saudiya , ne tace idan na haihu inyi amfani da shi,
Kamshin turen wutan da na room fresh ya hade da kuma dan karnin jego da duk yadda akayi sai andan ji shi,
Idon shi ya sauka a kan a miyar da ke gabana kamar wace akasa sha dole ashe ita dan dai tunda na haihu bakina gaskiya baida test ko kadan,
Gwagoce ta tursasa ni sai nasha shi,
Idon shi ya sauka a kaina daga inda yake tsaye a kofar dakin, yana min wani irin kallo,
Sai kunya duk ya kamanu a lokacin don tunda nake sheriff bai taba ganina hakaba don bantaba sa atamfa yagani ba,
Inda naje zaune yanufo yadan duka yana mai rage tsawon shi,
Alokacin nace mai inna kwana cikin wata irin murya mai kasala,
Hannu na dake dauke da cibin da nake shan pepper,soup yadanko yakai cibin da miyar abakin shi,
Dan danon kayan yaji yadaki harshen shi da sauri ya hade ,yadan kalleni cikin tsusayi sai ya mike tsaye zuwa wurin gado inda yaran ke kwance suna barci tun da su gwago sukai masu wankan safe suke wanan barcin,
Yai ma kowanin su addua, ya shafa masu sannan yajuyo yadawo inda nake zaune,
Cikin wata irin murya mai rauni yace min Fatima,
Sai naji duk wani irin kunyan shi ya kamani har nakasa koda motsawa in sha soup dina,
Shima din wani irin kallo yake min wanda har nakasa koda daga kai in kalli inda yake tsaye,
Ji yake yi duk wani kasala ta lulubeshi lokaci guda,
Fadima ce mace da duk duniya zai kalla yaji wani sha,awarsa ta motsa mai a lokaci guda,
Yarinyar da tun tana yar karama komai nata shawa take bashi saboda idan ka kalleta zakaga komai nata anmatashi dan dagwas zabban sha,awa, yadaure,
Yace Fadima, yana mai jawoni zuwa jikin shi ,jinayi yana mai sun,sunar wuya na har zuwa kaina,cikin wani irin sallo,
Fatima ni kadai nasan irin wahalar da rashinki kusa dani ya jawo mani, a gaskiya nasha wahala, daki ka wuto kika barni ni kadai,
Jin yace shi kadai yasa nadan daga kai nakalle shi, dan dai nasan cewa ga mahaifiyar shi da kuma yan uwan shi har da matar shi,
Ya ce yes of course, ina fatan bazaki kara bari na ba irin haka,na,
Mukasan ce atare har mutuwa insha Allah, barabuwa a tsakanin mu,
A hankali na furta mai insha Allah nima fatana kenan,
Cikin sauri yakara jawo ni ya manne ni gam ajikin shi yace may kikace,
Ganin yadda yanayin sheriff din ya sauya lokaci guda yasa wani irun tsoro ya bakunci zuciya,na,
Daganin shi yana cikin wata irin yanayi na muguwar sha,awa a lokacin
Jin da yayi bazan kara bashi ansa ba yasa kara dan matse ni kadan yana may lunshe idon shi yana wani sakin ajiyar zuciya,
Munkai wani dan lokaci a hakan can naji ya dan sasauta rikon da yai min yace,
Godiya ta, tabbata ga Allah Fatima har kullun ina may kara gode ma Allah ubangiji da yabani ke a matsayin matata kuma uwan 'ya'yana,
Ina mai gode ma Allah da duk irin baiwar da yai min na mallakar mace kamillah kamar ki ,
Jin wanan kalaman na sheriff yasa na kara narkewa a jikin shi ina mai jin dadin irin wanan yabon da yai min a lokaci guda,

Saida naga cewa shetiff yadan samu natsuwa sai na dan zare jikina cikin nashi, a hankali daga rugumar da yai min wani irin ajiyar zuciya naji yayi a lokacin,
Tausayin sheriff yakamani so sai dan na tabatar da lalai yana tare da sha,awa sosa, kuma yana kewata dan kusan wata uku kenan yanzu rabon shi dani,
Yadan dade zaune a bakin gado na ,dafe da kan shi har zuwa wani lokaci,
Sai naga ya mike tsab daga inda yake zaune yadogo kai yakallr ni,
Idon shine suka kada sukayi jajir duk kasala ta sauko mai dakuma wata irin sha,awa,
yai hanyar fita waje, batare da yakara kallon inda nake ba,
Ido kawai nabishi da shi cikin tausayi da kuma fargaba,
Kamar mariya tana jiran yafitane ta shigo dakin tana ce min zasu tafi kasuwa ne da wata yar makwabciyar mu sheriff ne zai aike su,
Shiru nadan yi ina nazari can nace ma mariya ta kula da kanta to amma ya suka san cewa akai wata a makwabtar mu har zasu aike su,
Bankara ganin sheriff ba sai bayan sallar azahar ya shigo
Har zuwa lokacin su mariya basu dawo ba,bayan na gaishe shi cikin girmamawa
Sai kuma na,dan dukar da kaina kasa ina mai tambayar shi har yanzu su mariya basu dawo bane daga gurin aiken,?
Shiru yayi yana kallo na cikin mamaki yace ai bashi ya aike su ba,
Waya yazaro yana tambayar Bashir ,bashir din yace shiya aike su sayen wasu kayan mata da bai san masu kyau ba,
Amma yai waya dasu yanzu zasu dawo, don suna kan hanya,

Sai bayan sallah magrib nakira wayar hjy umma muka gaisa natambayi lafiyar su dakuma su safiya,
Tace min duk lafiya suke, jin nai shiru batare da nai wani magana ba yasa,
Umma cewa kodai an hai hu ne fadima , shiru nayi kawai wanda yanuna mata cewa an haihu din,
Dan in kauda zancen umma na ko,karin tambayana sai ce mata nayi abani safiya,
Mamaki tayi wai ace cikin wanan zamanin ansamu mai kunya irin na mutanen da,
Bayan mun gaisa da safiya take tambayana ko may aka samu sai kawai naji ban iya fada mata,kai tsaye,
Amma dan tagane sai ce mata nayi ga sunan dai suna jiran zuwan ki,
Ke uwar su,
Cikin sauri da mamaki tace har guda nawa fadima nakara ce mata kizo ki gane su mana,
Inajin suna murna kamar a fili su je murmushi nayi dan jin dadin yadda suke kulani tamkar wata yar uwar su ta jini
Saida daga karshe nake sheda ma safiya cewa muna Abuja,
Tai wani tar karan murna tace min kina nufin dady babies yazo Nigeria, kenan,
Ina gama waya da su sai nakira Salimat nafada mata inda tai murna sosai danjin cewa na haihu
Itama dai tambayana tayi ko may na hai fa nace mata baby As,amau, dai tasa mu kan,ne ,
Ihun murna tayi tai ta hamdala ga Allah tace fadima dama na fada maki auren ki da Sheriff akawai wani baiwa da Allah yai ma wanan auren naku da sheriff,
Dariya kawai nakama yi mata dan jin taci gaba dayi min nasiha,
Rugaiyya, kan fada takama yi min akan gaskiya ban kyauta ace har kwana kusan hudu da haihuwa ban fada mataba sai yau take ji,
Nabata hakkuri tace min ita gaskiya tayi fushi saidai tazo dan sheriff da yaran shi amma badan ni ba,
Nace mata aiko hakan ma angode,ba laifi,indai har zaki zo din,,
Ita ko Amal tunda shehi yakoma madu da sabon labari take ta farin cikin kasancewar hakan
Tasan cewa ashe ba son banza muke wa junar mu ba ta alakace babba,
Duk da ba wani shakuwa mai karfi ke tsakani da sheriff ba tun farko,
Nasan cewa i,zuwa yanzu akwai fahitar juna so sai a tsakanin mu,
Wanda har yaka indan uwa na cikin wani hali zanan yau da gobe dole guda ya gane komay ke damun shi,
Kusan kwana ukun da mukayi a garin Abuja zan iya cewa akwai abinda ke damun Sheriffudeen din mu azuciyar shi sai dai yakasa furtawa,
Dan haka tunda dare na kulla araina cewa yau zan tunkare shi dan jin komay ke damun shi arai,
Kafin ya shigo gidan na tsantsara kwaliya irin na jan hanjalin maigida, tayadda bazai iya aiwatar da komai ba idan munyi ido biyu,
Hakako akayi dan cikin yar damuwar tashi yashigo ko yau din ma, bayan yadan yi hugging din na nadan wani lokaci ,
Sai ya sakeni ya koma bakin gado yai zaune yasa hannun shi yarike habar shi dashi,
Sai naga alamar yau damuwar har yafi na kullun yawa ma,
Nakuwa ci sa,a yaran na wurin su gwago tun da suka sha nonon safe, kuma nasan cewa zasu dade suna barcin safe,
Kofar dakin nakoma nasawa key, nadawo nasamay shi inda yake saidai wanan karon ya mike kafar shi,guda
Dayar kuma tsayar daita, ya yi yasa gwaiwar hannunshi akai don yaji dadin dafe goshin shi da tafin hannun shi,
Matsawa nayi jikin shi nadan jingina kaina da kafadar shi nasa hannu na guda nazagaya ta bayan shi, tayadda har muna jin bugun zuciyar junan mu,
Wani irin kallo yake min a cikin mamaki idonshi kar acikin nawa,
Nakalleshi idoncikin ido nasakar mai wani irin lalausar murmushi,
Nayi mai hakane don in samu damar aiwatar da nufina akanshi,
Don kawai in san may ye damuwar mijina, da har baida kuzari a kwanan gabadaya acikin damuwa yake,
Cikin wata irin murya nace narasa komay ke damun Sheriff dina acikin kwanakin da yakamata ace yana cikin farin ciki da walwala a rayunshi,
Sai nakara kallon shi karo na biyu nasakar mai wani munafukin murmushi,
Dan kuwa yau nayi niyar rike mijina da a hannu akan komay ke damuwar shi zan tayashi warwarewa insha Allah,
Cikin wata murya naban tausayi ne yadan daga ni kadan yagyara muna tsayin mu
Can yace min fatima bakomai ke damuwa na ba sai abinda da yan uwan haihuwa na suka sani aciki kawai,
Yanzu yadace ace duk cikin su koda mutum guda yakasa kirana mu gaisai
Balle har yai min murna samun karuwa fadima may narage masu da zasu dinga yi min haka,
Duk al,amarin su kusan nawa ne ,bada sanin Abba ba nake zuwa inda suke in masu alheri daidai gwargwadon hali,
Kusan sune nafarko danafarayi wa text batun haihuwar nan,
Amma wai ace har yau bawanda ya ko kirani ko kuma text din,
Wani iri naji azuciya nasan lalai sherif na cikin wa i hali don agaskiya dan uwa yabaka baya bakaramin tashi hankali bane,
Dan amin irinshi nani zafin shi na kumasan irin halin da mutum ke shiga,
Nace mai kayi hakkuri sheriff kamar yadda kasaba yin hakkuri da su insha Allahu wata rana zasu gane gaskiya su dawo hanya ai,
Murmushi yayi kadan yace bazaki gane bane,ai har in hjy mama tana raye ba,amu taba shiryawa da su ba saboda mugun akidar da take cusa masu,
Dazaran taga cewa muna dan shiri da gudan su ta shiga zariya kenan sai taga ta yi nasaran raba mu da may shi,
Murmushi nayi nace may idan har hjy mama ta hana yan uwanka mu amula da kai baga mu ba nida su Amal da Salim,
Ko bamu isheka ba, nafada ina mai kara tabbatar da ansar tambayana a idon shi,
Hancina yadan ja kadan yace aiku yan uwanane na na shakikai,
Amma su yan uwan haihuwana ne na jini kin ga ai dole indamu da rashin kulanin da basuyi,
Yace Anya fatima ko maraya yafini sanin rashin sanin zafin mahaifiyar mutum idan bata agida,?
Nakalle shi cikin natsuwa na ce mi,shi kadai fi su gata,,
Yakalleni yace min anya kuwa,?
Kware da gaske nace mai rashin mahaifi ko mahaifiya daban taka matsalar daba ai
Ganin danayi cewa yana cikin damuwa har yanzu yasa na sako may zancen wasa,
Nace kaida keda hjy tsohuwa a hannu ina kai ina maraici,
Murmushi mai yar sauti yayi man jin na anbaci hjy tsohuwa
Natare shi da fadin halin alherin da ta koya ma shi zakaci gaba da gabatar masu duk abin da sukai ma wanda ba daidai ba , kansu sukayi wa,
Nace nasan halin mijina da mutunci da kuma son kyautatawa na bayadashi,
Haka kada ma ka nuna masu cewa rashin tayaka murna da basuyi ba yadamay ka,
Kai mutum ne mai daraja da dauka musaman ga duk kan yan uwa,
Wanda harci ka ga yan uwa har yanasa amanta da wata hjy mama da zurian ta can,
Balle yanzu daga ka zama mai iyali, kan ka fiye dasu, da su aje iyali ba,
Kaga kenan kafi su koga idon jama,a, a addinan ce ma kafi su daraja,
Ban taba zaton zan iya tsayawa agaban sheriff in furta koda kalma daya ne mai tsawp ba sai gashi yau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login