Showing 177001 words to 180000 words out of 231198 words

Chapter 60 - TAKARI Book Complete by Zainab Makawa .txt

ta samay mu ba gaskiya ita bata ji dadin da na shigo gidan su ba da ciki a jiki na,
Duk da duhun da nake gani a wanan lokacin bai hana in wayence ba
Don kada mu taru mu zama daya da yar uwata, murmushin ta kaici nayi mata nace
Naji kewar ganin yar uwata ne shine na biyo ki har gidan ki tunda naga kin dauke kafarki da gidan mu,
Ai dole indauke kafata fadima don ina bakin cikin ganin ki da wanan cikin ajikin ki,
Mariya wacce bata ko zauna ba tace anty fatima tashi mu tai, tana mai kokarin jan hannu Aisha, zuwa waje,
Nace a,a mariya barin shiga dakin yar uwata mana in ga ni koda saudayane,
Muryan mijinta mukaji daga bayan mu, yace a,a yan TAKARI makkah ne yau gidan namu,
Yana min wani kallo cikin raini hankali,
Mariya tace ai gara da TAKARI da yan cin amana masu raba zumunci da karfin ta,
Ke mariya inji hafsi kada ki kawo wa mutane dibar albarka,
Don ke baki da kunya ,
Ita wacce tai laifin ta daure tai shiru sai kece zaki dinga yiwa mutane fitsara,
Zaman da ban yi ba ke nan a dakin yar uwar haihuwata, wace itace muna kamar uwa idan ba inna,
Yau gashi duniya ta zuga ta sai wulakanci take min akan tuhumar da take min ,
A hankali nadaga kaina na kalli hafsi ido tab da hawaye nace a gaskiya hafsi ban taba tunanen haka daga gare ki ba a rayuwa ta,
Nadauka cewa ko duk duniya sun guje ni kece mutum ta farko da zaki fara rungumata bayan mahaifiyata,
Dan girgiza kaina na cikin takaici na ce sai gashi kece agaba wurin nuna min kyama da hattara ta,
Kafin in karasa zancen hafsi ta cabe da fadin ,
Oho ke kin bata rayuwar ki shina kin kazo ni ki kashe min nawa auren duk mu koma gida mu zauna mu lalace ko, ,
Duk yadda naso in boye hawaye na wanan karo hakan bai yu,yuba don saida hawaye suka zubo min, daga idona suka diga kasa, don haushi da takaici,
Shi ko mijin ta yace ato in madai kin biye mata matsalar ki ce don dai ni wallahi har na fara shakkar hada zuria,a da ku ko,
Ashe dama yabon banzane akw maku,
Mariya tace kai mutumin banza mutumin wofi, ban bari takarasa ba narufe mata baki
Najata muka fito shin yan yar uwar mu rai bace,
Yan gidan dake hira sunyi tsit suna son su jiwo maganar da akeyi daga lungun hafsin,
Rai bace muka iso gida duk kan mu, cikin tashin hankali,
Tun a kofa mariya ke kuka tana kokarin fadawa inna irin cin mutuncin da hafsi da mijinta sukayi muna,
Murmushi kawai naga inna tayi na takaici tace halin hafsi ai sai ita ,


Duk yadda naso inyi barci da dare na kasa sai juyi nakeyi saman shimfidata,
Ina ta sake sake cikin zuciyata, ta yadda zan bullowa wanan al,amarin
Nasan cewa duk yadda zan yi bayanin cewa ina da aure ba yarda zasu yi ba don ba,aga zahiri ba,
Hakan yasa tun farko na ja baki na nai shiru har ranan da gaskiya zai baiyana,
Amma yanzu ya zama dole in fadawa yan uwa gaskiya koda kuwa baza su yarda da zancen nawa ba,
Duk yadda naso bama zuciya na magana akan kawai indake abin ya fassakara da zaran natuna da kalamin hafsi da mijinta sai inji wani irin kololon bakin ciki hawaye su dinga fitamin a idona,
Washegari da safe wayana dake hannun Abdull suna game shida Aisha mukaji yana tsuwar kira,
Cikin mamaki duk muka kawai wa wayan kallon mamaki,
Mariya uwar rigima ce ta dauka cikin gidimi tace sallamu alaikum
Jinda tayi ana fadin fadima fadima yasa tai saurin kawo wayar ta manna min, a kune na

Muryan salimat ne naji tana fadin fadima mutanen Nigeria anshige Nigeria an manta da mu, ko,
Da yar murna nada na kwana biyu banyi farin ciki ba nakira sunanta
Munkai wani lokaci muna magana da ita a wayar tana fada min yadda sheriff yadawo yake bida na a haukace,
A hankali na tambaye ta ko Aziza tabar saudiya,
Nan ta fada min dan abinda ta sani, takuma sheda min cewa ai ta dawo Nigeria ko ,
Nai murna so sai duk da ba a gari guda muke ba amma naji dadin hakan
Bayan mun gama wayan ne na tuna da lanbar hajiya umma, ba bata lokaci na kira layinta shima yashiga,
Da farko bata gane ni ba saidaga baya bayan nai mata bayani ne ta ce, haba fatima
Tunda kika tafi nake ta jiran kiranki amma shiru nadauka ma mun rasaki ke nan baza ki kara bidan mu ba,
Naidan murmushi nace zan bide ki mana hjy ai wawa ne kawai ke mantawa da halarci ,
Hjy umma ta bukaci in ba inna waya su gaisa,
Batare da tunanen komai ba na ba inna wayar suka fara gaisawa da umma,
Bayan gai suwa da kuma yar ja,jantawa irin ta manya sai hjy umma ke tambayar inna ko maigidan naya yasa mu zuwa Nigeria,
Duk da mamakin da ya rufe inna sai ta wayence zance tace bai zo ba tukun ,
Hjy umma tace zai zo ai insha Allaj fadima kurciya ne ya ci ai bai kamata ta wuta batare da sanin mijin ta,
Ina gefe naga wani irin kallo na mamaki da inna tai min
Sai naji duk jikina ya mutu, a lokacin,


🐎ZEEE MAKAWA🐎


✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
8⃣2⃣
BY
🐎ZAINAIB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎


Almost true life story,,,,




Tunda mahaifiyata ta gama waya da hjy umma naga jikinta yai sanyi sosai
Amma dai bata ce min komai ba sai kawai ta share zancen,
Tun ina dari dari, sai na fara sake jikina,
Shirun da naga tayi yasa nadauka cewa ai ba komai ne hjy umma ta fada mata ba,
Sai kawai na sake jikina naci gaba da harkokina, na yau da kullun,
Bayan wayan mu da salimat da kwana biyu sai gata har dogon daji,
Nayi farin ciki kwarai da zuwan Salimat, ko ba komai nadan rage samun zargin da yan kauyen mu ke mi kullun,
Ganin irin dankareriyar motar da yusuf mijin salimat yazo da ita,
Don ba shakar komai suke tambayar mijin salimat a masallaci da aka sallamay sallah, labari na,
Wani ke ce mai ashe tare mukayi zama saudiya da su,,
Yusuf, Bai san mai suke nufi ba dan haka sai ya ce masu a,a da matar sa ce da sukai karatu tare acan saudiya,
Sai kawai ya shiga yabo na kawai a gaban su,
Yana fadin cewa a gaskiya sunyi dace da yarinya mai ilimi da hazaka a garin su,
Ya ma su ai da,taimakon na har yasa mu matar shi ta kammala karatun ta,
Saboda ina da ilimi sosai a cikin makarantar mu,
Anyi, dace, Wani abokin mijin hafsi na cikin massalacin a lokacin da ake wanan hirar da yusuf,
Da sauri ya tambaya yace kana nufi fadima tai karatu a can saudiya,
Baban asamau yusuf, yai dan dariya yace sosai ma, kuwa don ta hada digree din ta ko,
Kafin suci gaba da hiran su ne wayan shi yai kara sai hiran tasu ta katse a lokacin,
A cikin harshe larabci muke magana da Salimat,
Tayadda nasan cewa innar mu ko mariya ba zasu fahinci maganar mu ba,
Na sheda mata cewa kada ta fadawa inna cewa nai aure pls, ban boye mata komai ba na sheda mata duk yadda ake zagina acikin gari,
Ran Salimat ya baci kwarai dajin cewa cikin da ke da uba kamar sheriff ake shegantawa haka, don rashin sanin daraja,
Tace min in bari kawai tafadawa inna gaskiya maganar ko zata fahinta
Cikin sauri nace mata dan Allah kada tace wa inna komai tabar har sheriff yazo da kanshi tukun,
Don ban san ko ya inna zata dauki maganar ba,,
Muna nan har mariya ta gama muna girkin abinci da ta dafa muna shikafa da mai da yaji sai salad da aka yanka,,
Katon sabon tabarma na shim fida muna a cikin rumfar inna,
Abdull ya kira baban Assama,u ya shigo daga ciki don yaci abinci,
Muma mariya ta, zuzzuba mana har da su Aisha da Abdull
Mijin Salimat yace a sokoto za su kwana don haka muka sake jikin mu so sai mukai ta hirar mu, hankali kwace,
Salimat tace min tana tuna nen zuwa yanzu sheriff zai iya gane cewa ban cikin kasar saudiya,
Ita a gaskiya ta so ta fada mai cewa ina Nigeria alokacin da yazo gidan ta a saudiya, Amman sai tsoro ya hana ta don ta na gudun yayi karar ta ga hukuma akan ta san da bacewar matansa,,
Ga kuma gwaunatin kasar saudiya da tsanani, so sai,
Nayi murmushi na ce ai bazai yi karar ki ba tace min, ke dan baki ga yadda hukuma ke ta bincike akan zancen ba ne,,
Tunda tumba taga motar baki a kofar gidan mu ta kasa zaune ta kasa tsaye, saida ta shigo gidan mu ganin Salimat don in ta tafi asamu abin fadi,
Sai da yamma so sai suka bar garin dogon daji zuwa cikin garin sokoto inda zasu kwana a wani katafaren hotel, mai suna five star,,,
Da zata tafi nabata kudi don ta sayo min yan kayan bukatu irin na mata,
Saboda tunda na shigo dogon daji ban shiga cikin gari ba ko ma agarin namu bana zuwa ko ina,
Washegari tunda safe muka hada masu breakfast saboda anan zasu dawo, su karya acewar salimat,
Inna tasa akai masu fura mai kyau na shimkafa zalla, yar asali dakan hannu,
Sai man shanu da su daddawa da kuka, duk ta hadawa Salimat, tsaraba,
Tumba ma takawo man gyada tace a basu shima kawu, ya kawo wa mijin anty zuma pure one yace yayi hakkuri da shi, ba wani tsaraba a kauye,,
Salimat tayo min sayayya so sai cikin garin sokoto, don da gani sakon ya fi karfin kudin da na bata,
Duk wani abinda tasan cewa za mu bukata nida Aisha saida ta sayo muna, shi,
Har mariya da Abdull duk sun samu nasu tsarabar,
Na rasa bakin da zanyi masu godiya wanan da wainiyar da sukayi min,,,
Sai gashi sukuma su ma murna tsarabar da inna da abokan arzikinta suka hado masu, har suna fadin wai kayan sunyi yawa ai,
Da za su tafi duk sai naji badadi a raina kamar in bi su na dinga ji,
Tai min alkawarin cewa zasu dawo badadewa ba insha Allah tunda sunga guri,
Kamar abin hadin baki su salimat sun tafi washegari sai mukaji tsayuwar mota a kofar gidan mu,
Cikin yan mintitika sai naga ana shigo da kaya irin na masarufi,
Kamar su shimkafa yar gwaunati da sugar tomatoes da man Turkey,
Mamakin kowaye kuma yakawo muna wanan kayan, haka duk ya kamani sanin cewa jiya jiya su Salimat suka bar garin na mu,
Don haka, nasan cewa ba su bane dai suka dawo,
Rugaiyyace ta shigo gidan da sallamar ta, ai,daga cikin dakin inna nake saman gado bansan lokacin da na dako wani wawan tsalle ba da yar ihu na nayo waje,
Cikin mamaki tace fadima shin,
Sai ta kalli inna da mariya da mamaki tace yaushe fadima ta zo Nigeria bata da labari,
Rugumay tana yi mun dade rike da junar mu muna irin gaisuwar larabawa,
Mariya sai dariya take muna,
Duk idon mu yakawo kwalla,
Ko ba komai ganin junar mu yasa zukatan mu ya tuna da wasu abubuwa da suka faru da mu a da, can,,,,
Sai can ta sake ni ta juya zuwa waje batare da tai muna wani magana ba,
Ita da mijin ta suka shigo wanan karon har ciki da sauri na koma na dan dauko Naifal di na lailaya, na koma kamar bani bace
Mun gaisa da shi cikin mutunci da girmamawa, ,
Mutumi mai fara,a da kuma son mutane don har ya ja Aisha ta zauna saman jikin shi ko,
Yaushe kika shigo Nigeria fadima nai yar dariyar rashin gaskiya nace mata na kai wata guda gaskiya,
Ta juya inda inna da mariya suke zaune, tace,
Gaskiya baki kyauta min ba ace kina cikin kasar nan amma banda labari haba dai fadima,
Yar dariya kawai nai mata nace mata ai kin san tunda na shigo dole ne in bide ki ,,,
Tace, Ko yanzu tun sati biyu da suka wuce muka so zuwa , mu diba su inna,sai kuma hakan bai samu ba,
Sai yau muka samu lokaci muka zo, ,
Bayan yan gaishe gaishen da mukayi a tsakanin mu da kuma inna,
Sai kuma hiran bayan rabo ya fara,
Nai mata godiyan irin dawainiyar da takeyi da iyayyena, da yan uwa na
Ta ce min fadima duk abinda nai masu kece sila don kinfi nan a gurina, murshi nai mata,
Duk hiran da mukayi da su sam bata gane halin da nake ciki ba,
Nai murna kwarai da na kula da cewa sam bata gane ina da ciki a jikina ba,
Kusan za su wuce ne take tambayana labarin sheriff
Sai da naji gabana ya fadi dam saboda ambatar sunar sheriff da tayi,
Sai ce mata nayi ai nabar aiki a gidan shi tun bayan barinta kasar saudiya,
Kamar da masaniya sai kawai ta shiga ba su inna da mijinta labarin Sheriff,
Irin arzikin shi da kuma taimakon mu da yayi a lokacin,
Na tambayeta labarin hajiya mai sharwali, tace min bata masan cewa sun dawo Nigeria ba sai kwanan nan ta ga wata makwabciyar mu ta can saudiya, itace ke fada mata, cewa hjy tana cikin garin kano,
Bayan tafiyan Rugaiyya wace naiwa alkawarin shigowa kano badadewa ba insha Allah,
Mariya ce takalleni lokacin ina ko,karin cire Naifal dina tace min gaskiya anty fadima ina son irin wanan shigar taki ,
Zanyi kokari in koya dan in yi,
Nai dan murshi nace mata ai zaki iya nan gaba sosai, insha Allah,
Inna ta raba tsarabar Rugaiyya ta aikawa kawu salihu da su Tumba har, da gidan dan isah ta aika masu dashi,
Nasa rai zasu dawo dashi kamar yadda sukayi min da tsaraba na sai kawai naji shiru har dare,
Malam musa mijin hafsi, suka hadu da abokin shi a majalissan su da suke hira, bayan sun dan gaisa har an fara hira sai abokin ke ce mai aiko yau kusan kwana biyar ina so mu hadu da kai mutumina,
Musa mijin hafsi yace make faru kake son gani na haka unguent mutumi na,
Ya ce maganar kaunar matar kace bakuwar saudiya,
Wani uban tsaki musa yaja yace ban son jin labarin wanan yariyar fitsarara da ita yarinya ba kunya ki ketare kasa har zuwa saudiya kije ki kama ai,kata fasikanci,
Wani daga cikin majalissan ya karbe da fadin ai in fada ma duk matan nan masu zama can saudiya, aikin da sukeyi ke nan na biyar mazan larabawa,
Kawai wai don su tara dukiya,
Musa yace to ai ita wanan ba abinda ta dawo dashi sai tsarabar shege,
Duk suka sa dariya, suna ce wa musa ai shine zai zama uban dan tunda shine mijin yayata, dole ko ya kula da dan da zan haifa,
Haka sukayi ta jansa da hira yana ta sake layi yadda yaso, yana aibanta ni,
Wanan mutumin da suka hadu a massalaci da mijin Salimat yace mai
Musa shin kai ka tabbatar da cewa cikin shege ne da ita, ko ko dai mai uba,
Shin ma musa kasan cewa wanan yariyar ashe har digree tayi a saudiya,
Dariya suka sa mai sukace digree din yan iska ko
Kai yaushe, kaje har kaji cewa wai tayi karatu zaku fara kirkiro wani sabon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login