Showing 63001 words to 66000 words out of 184071 words

Chapter 22 - ZUMUNCIN MU A YAU Complete By Aisha Yau Kura.txt

mu gana,
in baya raye to dan Allah ka bani tarihin shi wanda zai iya warware min komai,



Papy baiyi magana ba ya fito da wayarshi,
dannata yayi hade da karata a kunnenshi,
"Hello Maimunah,
hadani da Anni a waya,

Papy na....,

Ruwaidah ta fadi murya a shake, "Mama na,
kuka kike yi?

Kukan ta sake fashewa dashi kamar zata tsaga wayar,
rage murya yayi yace "wanene, daina kukan and tell me,

M-a-mi ce ta fadi tana ajiyar zuciya,
tsaki yayi a hankali, yasan abin da aka mata bai taka kara ya karya ba,
"yi hakuri Mamanah,
jeki kai mata inji dalilin saki kuka,
da dan gudunta ta tashi taje kitchen inda Mami da mai aikinsu ke kwashe mangyadan da ta zubar,
a darare tace "Maami Papy ya kiraki,
kwafa tayi ta goge hannunta a jikin tsumma ta karbi wayar,
yana jin sallamarta yayi saurin amsawa,
ba tare da jin dalilin kukan Ruwaidah ba yace
"ina Anni?

tana bacci lafiya dai ko,
mami ta tambaya cike da zullumi,

ajiyar zuciya yayi yace "lafiya kalau Maimuna,
gobe da safe ku shirya guraren tara zan kira Badamasi yazo ya taho daku kaduna,


zama Mami tayi gabanta na tsananta faduwa tace "Dan Allah ka fada min abin da yake faruwa,
ina JAMAL da HAFEEZ?,

murmushi yayi cike da tsokana yace khairan in shaa Allah ruďaďďiya,
ke dai ku shirya kinji,
gyada kai tayi har lokacin  gabanta bai daina faduwa ba...




Kallon Baffa yayi bayan ya ajiye wayar yace "Sanin abubuwan da ka tambayeni wannan sai maihaifiyata tazo,
domin nima ban san kaina ba, tashi nayi na ganni a hannun mahaifiyata ba tare da uba da yan uwa ba,
ni kadai na rayu a gabanta,
tare muka sha wahalhalun rayuwa,
na dai san a kullum tana fada min ina da uba, amma bata san inda yake ba,


A lokacin da Ma'u na tsaye to tabbas da ta kai kasa,

kokarin mikewa takeyi Papy yace "inna dawo ki zauna ayi komai a gabanki,
yau da za'a bincika zuciyata a gani to tabbas da an gano tafi takarda haske,


kallon shi Ma'u tayi tace "ďan nan ina ganin dai kamanni ne,
dan mu nan bamu da da namiji ko daya,
sannan duk wasu y'an uwa namu na kusa duk sun mutu,

kasan Allah yana iya halittar mutane masu kama da juna, akwai su da dama sab--- katseta Hafeez yayi cikin girmamawa yace "Goggo wannan ya wuce kamanni kawai,
akwai jini mai karfi,

ki duba girman makarantarmu duk daliban dake ciki ace dani kadai ya shaku har ya kaini gidanshi cikin iyalinshi,
sannan kuma idan kika ga Jamal da Ruwaidah a nan ne zaki tabbatar da su ďin jinin mu ne,


Daka mishi tsawa Goggo tayi "kai dalla rufe mana baki,
manya na magana kana yi saboda tsabar rashin kunya,
tashi ka fita kaba mutane guri,

mikewa Hafeez yayi yana fadin kiyi hakuri,
harara ta bishi dashi har ya bacewa ganinta sannan ta dawo da kallonta kan Papy tace

"to bawan Allah mun gode da ziyara, sai anjima,

sake gyara zama Papy yayi yace "Inna, bazan boye miki ba, barin gidannan a guri na sai da daddare,
sannan gobe da wuri zanzo domin kuwa ina hango cikar burina na sama da shekaru arbain da doriya zai tabbata,

cike da faduwar gaba ta kalli Baffa da ya kasa dauke idonshi a kan Papy,
yanayin maganarshi,
da komai irin nashi ne,
gayu, gogewa da yarinta ne kadai ya banbanta su,

taba shi Goggo tayi tace
"lokacin Sallah ya kusa tashi ka shiga kayi alwala,

da sauri Papy ya kalli agogon hannunshi yace "uku da kwata ne yanzu Inna lokaci baiyi ba,

tun Goggo na daurewa kar ta fara nuna mishi halinta,
har saida ya kaita bango ta dakawa Baffa tsawa tace "ya tashi su wuce daki,

wannan mutumin in ba aljani bane to maye ne,

jiki a sanyaye Baffa ya tashi yace ma Papy "yaya Sunanka,
da sauri papy yace "Abdallah" nan Baffa yayi ajiyar zuciya yace "ba SAIFU bane,
Ma'u ba saifu bane,
duk tunanina shine shiyasa na cika da tsoron ya za'ayi wanda ya mutu ya dawo,
nasan ni na binneshi da hannuna,

kallon Papy Goggo tayi tace "kaji ko,
dan Allah tashi ka fitar mana a gida,
kuma karka sake zuwa kaje can ka nemi ubanka..

Nan tsakar gida suka barshi zaune yana ta nazarin abubuwa,

kodai da gaske bashi bane mahaifinshi,
sai da yayi wasu yan mintuna sannan ya tashi hade da gamsar da zuciyarshi koma meye in Anni tazo zata warware mishi komai....




Ita kuwa Goggo safa da Marwah ta dinga yi a daki tana tunanin ta inda wannan mutumin ya fito,

tasan a hannunta saifu ya cika,
kuma a gabanta aka binne shi, anya ba aure Baffa yayi ba lokacin da yake tafiye tafiyenshi,

katse mata tunani yayi yace "Ma'u wannan yaron ko dai dan Hardejo ne,
kodai..... saurin katse shi tayi murya a kausashe tace "ko kuma naka ba,

ni zaka ciwa Amana Muhammadu,?

ashe dama kayi aure a boye ban sani ba,

"Nan jikin Baffa ya fara rawa yace "wallahi banda Atika ban taba auren wata mace ba, daga ke sai ita,

kwafa Goggo tayi cike da masifa tace "gaskiya zatayi halinta ai gobe,
da bana son yaron nan ya dawo gidannan amma gobe da kaina zansa Hafeez ya kawo shi dan a warware min wannan kullin,

ina ganin watan jin kunyarka ne ya tsaya,

saboda sanin yana da gaskiya shiyasa yace "Allah ya kaimu,

komawa yayi ya zaune a zuciyarshi yace "shi yaushe ma ya kalli wata mace a matsayin mace har ya aureta,
har yanzu gani yakeyi duk duniya babu macen da ta kamo kafar ma'u a komai,
sauran mata duk kallonsu yakeyi kamar gumaka,
tsaki yayi yace "Ma'u batayi mishi adalci ba,
tasan bazai taba cin amanarta ba,

amma babu komai gobe gaskiya zatayi halinta...



Haka suka kwana dukkansu zuciyoyinsu ba dadi,
kowa da abun da yake sakawa a ranshi,
har gari ya waye Baffa bai bar hango fuskar Abdallah ba.....



**********●●●*******

Karfe biyu da rabi suka iso kaduna,
Hotel din da su Papy suka sauka can Badamasi ya wuce dasu,

bayan sun huta a masauki suka ci abinci sannan ne Mami ta tambayi Papy dalilin zuwan nasu,

bai amsa ta ba saboda yaga Anni ta dan kashingide tana son tayi bacci,


Ruwaidah ya daura akan cinyarshi yace "me Mamana tayi miki jiya kika duketa,

irin kukan nan da tayi nasan ba karamin duka kikayi mata ba,


Harararta Mami tayi tace "ai badan Anni ba walhi da sai na balla hannunta sai ayi dauri,
kaga daga nan ma huta da barna,
turo baki Ruwaidah tayi hade da tura kanta cikin kirjin Papy,

"ni kike turowa baki,?
mami ta tambaya tana nuna kirjinta da yatsa,

a ina ta turo miki baki,
ki kyalemin uwata ta huta,

shikenan dan bana nan bazatayi abin da takeso ba,


Mikewa Mami tayi tace "ko kai da kana nan sai ka tayani,

man gyada na zaune cikin jarkarshi ta dauko tukunyarta ta wasan yara wai zata soya dankali,

tasan jarkar tafi karfinta haka tasa karfi ta yar da ita kasa,
gaba daya kitchen da store babu inda bai samu albarkar mai ba,

"tabbb...
ai Mami kin ma mata da sauki, da kin cire hannun ne sai a sa mata na roba..

harara Papy ya jefa gefen da Jamal ke zaune yana latsa waya kamar bashi yayi maganan ba,


"shikenan dan ta zubar da mai sai a duke ta,

ba koyon girki takeyi ba,

in bata koya ba waye zai dinga tayaki aiki,

"Na yafe Mami tayi saurin fadi tayi hanyar bayi tace "ka cigaba da shagwaba yarinyar nan,

ta riga ta maida mu kamar kakanninta,

bayan Ruwaidah Papy ya shafa yace "rabu da Mami kinji,

zan siyo miki kayan abincinki ki koya da kanki ki dinga dafa min inci kinji ko?
Gyada kai tayi tace "kuma bazamu samma Yaya Jamal ba,

dariya papy yayi yace
"eh mana wama zai bashi,
yaje can yaci jagwalgwalon Mamin shi,


dariya sosai Jamal yayi yace "opposite,
Kuma in na kara ganin kin taba ma Mami ko da gishiri ne sai na yanka hannun da wuka,
murguda mishi baki tayi tace "ni da Papy zai siyomin nawa me zanyi da naku,
ko kitchen din mami ma bazan kara shiga ba,

"yauwa Good Girl,
muna komawa zan yi miki cefanenki,
karki kalli kayan Mami sun tsufa,


mikewa Jamal yayi yana dariya yace "har abincin Mami ma kar ta kara ci papy,
ta dafa nata da kanta,

dakuwa Papy yayi mishi ya fita daga dakin yana dariya....



Suna idar da Sallar la'asar Papy yace su shirya zasu je wani guri,

manufar shi nakin fadawa Anni shine kar ya fada mata suje bashi bane hankalinta ya kara tashi,

gara in suka je yaga bata sanshi ba sai su tafi ba tare da ya daga mata hankali ba,

tun yana shekara bakwai ya yankewa kanshi daina matsa mata akan maganar mahaifinshi,
domin ya kan ganta cikin tsananin damuwa duk ranar da yayi mata maganar,
a irin yadda ya taso yaga ta wahala akanshi shi yasa baya san ganinta cikin damuwa ko kadan...



Biyar saura suka isa kofar gidan,
motar Mummy Hafeez ya gani a cikin gidan,
Addu'a ya fara yi zuciyarshi na Allah yasa kar su hadu su wulakanta bayin Allahn nan,

gabanshi bai tsananta faduwa ba saida ya jiyo muryar Radiya,

farin sani yayi mata akan rashin mutunci,

dake wa yayi ya karasa ciki dasu,

Sallama sukayi dukkansu suka shiga cikin gidan,

daga cikin daki sukaji an amsa Sallamar,

mikewa Goggo tayi ta fito dama zaman jiransu take,

tana fitowa idanuwanta suka sauka kan Anni,
baya taja kamar zata fadi bakinta na rawa tace,

H-an-ne.......



Mrs Tijjani Shattima.....
[18/03 8:06 AM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 3⃣9⃣
By *Aysha Ya'u kurah*




Kallon rashin sani Anni tayi mata dan bata gane fuskarta ba,

nan dai ta fadada murmushinta tace "Na'am barkanku da gida, dafatan mun sameku lafiya,

Goggo dake tsaye jikinta na rawa kamar mazari tace "lafiya lau,

matsawa tayi gefe tace ku shigo ciki,

tabarmi Mummy ta fito dasu tace "a'a Goggo bari su zauna a waje yafi iska..


Bayan sun zazzauna an gaggaisa, Goggo ta kalli Hanne kirjinta na duka uku uku tace "baki ganeni ba ko Hanne?,

gyada kai Anni tayi tace "ban ganeki ba,


gyara zama Ma'u tayi kishi ya motso mata ta fara charge ta kalli Papy tace
"wannan ce mahaifiyarka??

Eh!!
Papy ya fada yana mai jin dadin an gane mahaifiyarshi a gidan,


"TABDIJAM Goggo tace "tana kallon Anni,


Wato Hanne ke kika haifeshi,?

wannan karan mamaki yasanya Anni cewa kwarai ni na haifeshi, dana ne,
lafiya??

Idon Goggo ya rufe ta manta da yara a gurin tace
"wato dama cikin shegen da kika dinga yawo dashi a tsakanin jalingo da Gembu dama Mijina ne yayi miki shi,

kenan lokacin da nake tausayin ki in su Harira suna tsangwamarki ashe kallon sakarya kike min mijina ne ya kunsa miki,


kallon Radiya tayi tace "maza tafi shagon Gidado ki kira min Baffan ku,

kafin Radiya ta mike Baffa ya shigo gidan da sallama,

yana ganin wucewarsu ya mike a shagon Gidado hade da amso musu lemu,

Goggo sam bata basu damar amsa sallamar ba tace "yauwa gara da Allah ya kawo ka,
nuna Hanne tayi tace ka gane wannan,?


kallonta yayi yaga samm shi bai taba ganinta ba,

ita kuwa Anni kallo ta bishi dashi idonta ya ciko da kwalla tana fadin
Alhamdulillah,
Alhamdulillah,

zama Baffa yayi yace "ban santa ba,
wacece ita?

Tafa hannu Goggo tayi tace "yau ni naga Bariki,

Hannen ce baka sani ba?

Hannen gidansu Inna wuro kanwar Harira,

wacce ta kunso cikin shege aka korota daga garinsu ta dawo nan,

ashe kai ka kunsa mata,
gashi dai kamanni sun bayyana min komai,
wallahi kaji kunya, ta karasa fadi tana haki..


"innalillahi wa inna ilaihir rajiun kawai Baffa da Papy ke fada,

ganin shurun da Baffa yayi ya kara hassala Ma'u ta fara surfafa masifa da bala'i,
babu inda baya rawa a jikinta,

da dai Anni taga shuru bazai taimakesu ba tace.

"Wallahi tallahi ban taba koda magana dashi ba...


shuru Ma'u tayi tana hararar Hanne tana fadin rainin hankali, uban wa zaki rainawa hankali?


"gyara zama Anni tayi ta kalli Baffa tace "in ka yarda dani ka bani dama inyi maka bayanin komai,

idonta ta mayar kan Goggo tace "in kikaji labarin abinda ya faru, da kuma yadda ya faru ni nasan gode min zakiyi ba zargi da zagi ba,

ni ko a yau Allah ya dauki raina walhy naji dadi saboda zan cika buri na,


kullum bani da tunanin da ya wuce ta yaya zan wankewa Abdallah zuciyarshi,

ta yaya zan hada shi da mahaifinshi,

nasan duniya tana da fadi wata rana ina da yakinin Allah zai amsa min addu'ata,

sai gashi ta dalilin Hafeezu adduar da na dade ina yi Allah ya amsa...
Alheri danko ne...



Kallon su Radiya dasu Hafeez tayi tace "dan Allah ko yaran nan zasu dan bamu guri,

"babu inda zasu, Ma'u ta fadi tana tafa hannu,


kallon Jamal Mami tayi tace "dauki Ruwaidah ku tafi mota,
noke wuya tayi tace "um um,
zare mata ido Mami tayi zatayi magana Anni ta dakatar da ita,
"zo takwara,
zo kuje ku siyo min Goro kinsan kin fishi wayau naki yafi kyau,

Jiki na rawa ta mike zata wuce ta taka kafar Radiya,

da karfi ta hankada ta cikin ihun azaba saboda tsinin takalmin tace "ke makauniya ce?

baki ta bare ta fara kuka idonta kyar akan Radiya,

da sauri Hafeez ya ja hannunta suka fita yana rarrashinta,


Harara Mummy ta sakarma Radiya tace "sai kace kina yi da sa'arki,

turo baki tayi tace "mummy zafi wallahi,

"tashi ki bamu guri dalla,mummyn ta fadi a hassale,

da sauri Goggo tace "babu fa inda zata,
gyara zaman ki,
abun kunya ce suka kwaso suji kunyar su kadai,


Girgiza kai Anni tayi tace "babu komai ma,
zauna! labarin an yishi ne, ba kirkirarre bane,
kaddara ce..





Kamar yadda kika sani ni kanwar Harira ce,
mahaifina asalinshi dan Gombe ne,
mahaifiyata ce yar jalingo..


Allah ya jarabceni da soyayya da dan kanin babanmu,
mun dade tare dashi,

kullum in na fita tallan nono a gurin yake zama har ya kare, mu tafi gida..


wata rana nono na yayi kwantai, yakai ni dare,

a hanyar mu ta dawowa gida kaddara ta afka mana,

kaddarar da dan adam bai isa ya tsallake ta ba,

kaddarar dake sanya rayuwar budurwa da iyayenta cikin mawuyacin hali...

kaddarar da ta sanya Mahaifina rasa rayuwarshi...



Bayan an fahimci ina dauke da ciki,
saboda tsabar kunya irin ta fulanin "da" mahaifina ya kashe kanshi ta hanyar fadawa cikin teku, a cewarshi bazai iya fuskantar jama'a ba..

mahaifiyata da kishiyoyinta suka sani a gaba,

bani da katabus cikin kauyenmu,
ko kofi na taba babu wanda yake dauka,

haka in na fita gari an dinga darewa kenan,


shi kuma wanda yayi min cikin an nemeshi ko sama ko kasa an rasa,

daga baya ne muka samu labarin mutuwarshi,

nan fa na cire duk wani tsammani na samun mijin aure,


saboda tsabar tsana da iyaye da yanuwana suka min na fita hayyacina na kare na lalace,

mahaifiyata ma kunya ta sanyata ta rame,

saida abin ya isheta tace "in shirya in tafi jalingo gurin mahaifiyarta,

To acan ma hakan take domin kuwa saida na gwammaci zama a Gombe da zaman jalingo,

duk ranar jumma'a sai Yakumbo kakata ta turani Gembu gidan Harira saboda gudun kunyar jumma'a,

tana tsoron kar mutane su shigo su ganni,

gaba daya yan uwa sun tsane ni ta ko ina,
bani da gurin shan iska...



wata ranar jumma'a mai cike da ban alajabi da tsoratarwa,
Jumma'ar da manta ta ga yan uwan mutanen kauyen Gembu abu ne mai matukar wahala..


Tun cikin dare nake jin kaina kamar bani ba saboda yadda cikina ya dinga murda min,

a hakan Yakumbo tace in fito in wuce Gembu,

tun a hanya cikin ke murda min har al'amarin yaso fin karfina,

cikin ikon Allah cikin ya lafa min har muka shiga cikin kauyen,

a daddafe na karasa cikin kauyen nayi gamo da tashin hankalin da yasanya cikina kadawa har kafata ta gaza daukata,

ina kallonka sanda ka dauko matarka da wata mace kuna gudu,

da rarrafe na bi bayanku har nazo lungun shiga gidanku,

nan gaba daya karfina ya kare, haihuwar ta taho min gadan gadan,

Cikin ikon Allah na haifi 'yata mace,
dankwalina na cire na nadeta dashi hade da mahaifar,

koda na duba ta na dinga jijjigata na tabbatar bata raye,

anan ne nayi kuka sosai har muryata ta dashe,

ban kara sanin inda hankalina yake ba saboda zubar jinin da nakeyi..

Iska mai karfi ce ta taso a kauyen wacce kafin ruwa ya sauka saida ta dauke gidaje,


wannan iskar ita ta farkar dani nayi saurin mikewa da gawar yata na fada cikin gidan ka,

koda na shiga babu kowa a gidan sai kasar da ke tashi tana rufe ko ina na gidan,

Daki na shige da sauri,
har cikin dakin kasar ke shiga saboda iskar ba ta wasa akeyi ba,

Iskar na lafawa ruwa ya tsuge kamar da bakin kwarya,

A nan ne naji ihun jariri daga waje,

da sauri na fito na iso gurin na hango dan Mala'ikan Allah cikin zani kwance a kirjin mahaifiyarshi,


Share hawayen idonta tayi tace
"Allah shi ke raya Matacce a lokacin da yaso,
in ba Allah ba waye zai raya wanda kasa ta rufe idonshi,

ko da na dagoshi jini ne ke fita daga cikin cibiyar da ba'ayi mata yanka da kyau ba,

nan take nayi daki dashi na gyara yankan cibiyar na daureta da tsumma,

ruwan bai tsagaita ba sai can gurin magriba,

yana tsayawa na kunshe yata na mayar da ita cikin gawar da Allah ya nuna ikonsa akanta,


A tare na rufesu da kyau saboda ko yadda aka zuba kasar wata rana ruwa ka iya dago gawar saboda sam kabarin baiyi zurfi ba..




A lokacin ne na fahimci wani abu guda daya game da cikin da nayi,
wannan abu kuwa shine bak'in zare mai shara shara wanda babu mai ganinsa sai ubangiji,

wannan zaren kuwa shine zaren kaddara!

kaddarar rainon Abdallah ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login