Showing 102001 words to 105000 words out of 184071 words
Chapter 35 - ZUMUNCIN MU A YAU Complete By Aisha Yau Kura.txt
dasu ba ya shiga yi har Anty Reemah na tsokarshi..
Ita kuwa juya wayarta ta dinga yi ta rasa wani irin sako ne wannan dake bukatar nutsuwa,
ita dinma zuciyar sai bugawa take da sauri sauri,
abu daya ta kawo a ranta kuma tayi saurin kawar dashi dan tasan ba mai yiwuwa bane,
Hilal yayi mata zarra ta kowani bangare,
nan take ta kauda tunaninta ta ajiye wayar ta shiga bayi,
wanka tayi ta fito ta sanya wani plain material lemon green da jar flower a jiki,
ta sanya jar hula a kanta ta gyara dakin ta fita dan zuwa yi ma Musaddiq abinci,
karo sukayi da Husnah a kofar dakin tana kokarin shigewa ciki,
"Har kinyi wanka, kaii kin huta, ni su Mummy sun hanani katabus,
bari inyi wanka zan sameki a kitchen,
dariya Nadeeyah tayi na ganin yadda jikin Husnah ke rawa ta karasa fitowa a parlon,
wannan karon ba kowa a parlon sai Musaddiq da budurwar,
hada ido sukayi tayi mishi Murmushin da ya sanyashi sukurkurcewa ya bita da ido,
saida ya daina ganinta sannan ya dawo da hankalinshi gurin wacce ta kira kanta da *FAIDA*,
"kana jina ko,
ta fadi tana kallon cikin idonshi,
"Eh yauwa, inaji,
kikace wani level ma?
"200l ta fadi tana murmushi, ta cigaba da cewa
"dama Mum tace min i will like u,
gashi daga farkon haduwarmu i like everything about u,
i love you!,
wani irin murmushi yayi ya shafo sajenshi hade da jan hancinshi yace
"dats nice,
i like u too,
saidai anya zaki iya kuwa? liability ne ni,
komai yi min akeyi,
komai fa, infact ko toilet zani sai an rakani,
dariya yayi wacce bai san ta fito ba yace "Kuma gash---
wata dariya yaji wacce ta sanyashi kasa karasawa,
bata kalleshi ba ta bude drawer gurin dining ta dauki abun da tazo dauka,
shima dariyar ya cigaba dayi yace "yauwa Nadeeyah zo,
matse dariyarta tayi ta karaso inda suke,
"Gani,
"zauna ki bata labari na,
zama tayi tace
"Karki ce dan yana yayana ko dan yana zaune anan,
gaskiyar kawai zan fada miki,
"yaya Musaddiq a cikin dubu kafin ki samu daya irinshi sai kin tona,
he is very nice,
bashi da fushi sam,
baima iya shi ba,
yanada kyautawa fiye da tunani, sannan yana son a kula dashi da kuma cikinshi, gaskiya kinyi dacen samun yayana,
yhu are very lucky...
Tana kaiwa nan ta mike hade da kallon yadda ya kureta da ido,
dariyar tsokana tayi mishi ta wuce kitchen,
Dan tabashi yaji anyi nan ya dawo cikin hayyacinshi,
ya salam ya fadi a zuciyarshi,
abubuwan nan dake faruwa dashi game da Nadeeyah ba lafiya bane,
ya kasa tantance menene shi,
"Ko a ya kake kayi min!
muryarta ta sake maidoshi cikin tunanin da zuciyarshi ta tafi,
hankalinshi kacokan ya dawo dashi kanta yace
"Menene So?
Ya akayi kikaji kina sona daga ganin farko?
Menene kikaji game dani har kika gane kina sona,
Nan Faida ta gyara zama domin kwararrace a wannan fanin, bata san adadin samarin da tayi a rayuwarta ba,
yadda ta maida kudi take watsarwa ko ina haka ta maida namiji
*SO*
Gamon jini ne,
so wata halittace wace take kwance a cikin zuciya,
Halittar na iya daukar mutane da yawa,
saidai kowa da muhallinshi,
Soyayyar iyaye tanada gurinta,
soyayyar yan uwa, aboki da sauransu suma akwai muhallinshi,
sai kuma main the main,
soyayyar Abokin rayuwa,
wannan soyayya ce wacce ke faruwa a lokacin da mutum bai shirya ba,
Tausayi siga ce ta soyayya,
duk wanda kake tausayinshi to tabbas soyayya ce ta jawo haka,
damuwa,
yawan damuwa da mutum wannan ma alama ce ta soyayya,
Tsayuwa cikin rai,
mutum ya zauna a ranka babu dare babu rana ko yaushe tunaninshi kakeyi wannan shine kankat, domin ko shakka babu soyayya ce mai karfi ta shigo lamarin,
kamar yadda yanzu ina sanyaka a idona naji my heart beats for u,
ban taba jin wani abu game da wani da namiji ba sai akanka,
Surutanta take tayi shi kuwa ya tafi can wata duniyar,
murmushi kawai kake gani a kan bakar kyakyawar fuskarsa mai cike da annuri,
komai na Nadeeyah ke mishi yawo akanshi,
"I'm in love ya furta a hankali,
kallonshi Faida tayi hade da mikewa tace wawww, alhamdulillah,
sama tayi da gudu dan kaiwa maman ta albishir,
bai ma san tanayi ba ya shafa kanshi har lokacin yana furta kalmar
"I'm in love,
bayanshi ya jingina jikin kujera yana fitar da murmushi mai sauti,
wasu irin numfarfashi yake fitarwa wanda duk fitarsu suke tafe da zazzafan kaunar Nadeeyah,
muryarta keta yin amsa kuwwa cikin kunnenshi,
"Yhu are very lucky,
kasa ya koma ya mike kafarshi yace
"yhu are the lucky one Nadeeyah,
and I'm the luckiest,
Muryarsu ya jiyo a kitchen yayi saurin zuwa kofar kitchen din ya nade hannuwanshi yana kallon duk wani taku da tayi a kitchen din,
da ido Husnah ta nuna mata shi,
saida ta shanye dariyarta ta juyo tace
"mun kusa gamawa,
angon mu,
muma dai mun kusa hutawa,
amma dan Allah a bari mu dawo daga Gombe ko Husnah, ta karashe tana taba kafadar Husnah,
kusa dashi Husnah ta dawo tayi mishi rada a kunne tace
"Yaya nidai bata min ba,
bata da class,
kaji wani ihun da tayi da sunan wayewa,
samm batayi kama da matar yayana ba,
bai dauke idonshi a kan Nadeeyah ba yace
"Tunda ba tayi miki ba sai mu canza wata auta,
yana kaiwa nan ya bar kofar kitchen din,
bazai iya kara kwana daya ba tare da ya sauke wannan nauyin son a zuciyarshi ba,
dakinshi ya shiga ya kwanta a gado hade da dauko wayarshi,
Hilal ne kadai zai tayashi sauke wannan nauyin,
daga bakinshi kadai zataji ta saki jikinta dashi ta kuma amince mishi,
layin Hilal din ya kira,
da farko yaki shiga sai da yayi sau uku, ana ukun ne yayi sa'ar ya kunna wayar,
cike da Annashuwa Hilal ya dauki wayar da bashi da masinayar itace yankewar farin cikinshi na lokaci mai tsaho.....
"A kasalance Musaddiq ya furta kalmar
"I'm in love main man,
cikin shauki Hilal ya jingina jikinshi a karfen balcony ya sauyawa wayar hannunshi mazauni zuwa kunnen dama yace "Wowww,
is this a dream or?
REALITY Musaddiq ya katseshi hade da lumshe manyan idanuwanshi,
sajen fuskarshi ya fara shafawa yana fadin "i don't knw how Hilal, na tsinci kaina a tarkon kauna, ganinta kadai yana tsaida duk wani magudanar jinin jikina, idan najiyo muryarta nakan rasa nutsuwata in daburce na shiga rudani Hilal,
Na rasa yadda zanyi in tunkareta da kalmar soyayyata,
walhy sonta yayi min mugu kamu ba tare da na farga ba,
ya karashe fadi yana mai taba gefen da zuciya ke adane a cikin kirji,
Daddadar iskar da ta kada Hilal ya shaka jikinshi ya mutu tubus saboda haroro yanayin da suka shiga shi da dan uwanshi daya,
har yana ganin ma yanayin nashi yafi na Musaddiq,
saboda wani irin sonta da yake ji a dukkan sassan jikinshi ba zuciya kadai ba,
A kagauce ya kauda tunanin yace "who is the lucky one my Guy,
"call me lucky a ranar da zan iya tattaro kalaman so in fada mata,
"Wait wait Kyari,
u mean baka fada mata ba?
gyada kanshi yayi fuska a dame yace "na kasa Hilal,
wallahi i can't,
dariya Hilal yayi yace
"lallai baka shirya soyayya ba,
a shagwabe musaddiq yace
"kai zaka tayani fada mata,
i knw zaka ce baka son raini,
plss u have to help me out dan na gaji da wannan ciwon takurar,
" it's well Hilal yace yana dariya sosai,
fada min wacece , sannan ka turo min numberta Asap in tsara maka ita,
cike da fargabar kar ya fada mishi sunanta yace bazai iya ba saboda baisan raini ko kuma wani abun daban yace
"promise me in na fada maka bazaka ki fada ba?
"Haba ai kaima kasan ko wuta take zan bita in fada mata for u,
bare a cikin gari take kuma mutum ce kamar mu,
kai dai kawai fada min everything about her,,
*NADEEYAH...*
*Hilal i'm in love with Nadeeyah....,*
Tartsssssssssaas....
wayar hannun Hilal ta subuce ta fadi a kasa...........
Mrs Tijjani Shattimah.......
[04/04 10:04 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣3⃣
By *Aysha Ya'u kurah*
Sulalewa Hilal yai a hankali yayi zaman dirshan a gurin,
kallon wayarshi yayi wacce yake jiyo muryar Musaddiq yana fadin
"kana jina?
Hello Hilal are u der?,
girgiza kai Hilal ya shiga yi yana fadin
"nooo dis is nt true,
da sauri ya mutstsike idonshi ya bude dan ganin ko mafarki yakeyi,
k'ara wayar da glass dinta ya tarwatse ta sakeyi,
hannu na rawa ya mika shi ya janyota,
dannata yayi ya sanya speaker,
nan take muryar Musaddiq ta sake gauraye gurin
"Pls Mana,
kai kadai kake understanding feelings dina,
kai kadai ne zaka taimakeni, wallahi i love her....
Toshe kunnuwa Hilal yayi kalmar *wallahi I love her* ta dinga amsawa cikin kunnenshi,
runtse idanuwanshi da suka zama kamar gauta yayi kirjinshi na duka kamar ana daka,
duk yadda yaso yayi kuka hakan yaki yiwuwa a gareshi dan ba sabawa yayi ba,
kuka...
sam bazai iya tuna ranar da yayi shi da girmanshi ba,
A hankali yake maimaita
"Why Nadeeyah,
why nt order gal,
ya Allah...
ya karashe hade da dafe kanshi,
daina jiyo muryar da yayi ne ya sashi saurin daukar wayar,
juyata ya dinga yi a hanunshi yana jin haushin dalilin da yasa ya mallaketa tun farko,
screen guard din daya fashe ya zare.. nan hoton da ke daure kan screen din nata da Musaddiq ya fito baroro,
maida wayar yayi da sauri saboda wani abu da yaji ya taso mishi,
Dakyar ya iya mikewa ya shiga dakin,
rub da ciki yayi yana hango wa kanshi halin da zai shiga,
yaso Nadeeyah kamar rayuwarshi,
daidai da second daya bata taba fita a ranshi ba,
sai gashi yau Musaddiq da bayan iyayenshi bashi da kamarshi shi yake son abun da yakeso,
juyi ya dingayi a gado ya rasa abun da zaiyi yaji sanyi cikin ranshi,
komai ya daina aiki a jikinshi,
Zainab ce ta fado dakin da gudu,
drawershi ta bude ta shiga tana fadin "boyeni yaya, Anty zata dukeni,
yadda ta rufe kofar da karfi ya sa takardun saman drawer zubowa kasa,
jiki ba kwari ya mike ya tattarosu ya zubasu a kan gado,
nan take zuciyarshi ta raunana da yayi tozali da zanen da ya gama satin da ya wuce,
tsugunawa yayi ya janyoshi ya zuba mishi ido,
dariyar dake matukar burgeshi yayi nisa cikin kallo ba tare da sanin halin da idanuwanshi ke ciki ba...
hannu yaji kan kuncinshi ana share mishi hawayen da baida masaniyar zubarsu,
dago kai yayi ya kalleta itama nata idon ya ciko da kwalla,
da sauri ya hada jikinshi da nata ya saki wani irin kuka mai tsayawa a zuciya,
ita kuwa da karfi ta saki nata wanda ya janyo hankalin su Anty Reemah da Papa da shigowarshi gidan kenan,
Da sauri ya turata waje ya sama dakinshi key,
Hinad dake lekenshi tayi saurin komawa itama kukan ta saki dan abin da bata taba gani bane tun tasowarta kuka a idon Hilal,
takardun ya tattaro yayi musu runguma kamar zai maidasu ciki, a lokacin kukan da yakeyi ya ci karfinshi dan har sheshshekarshi su Anty Reemah sunaji,
babu irin bugun da basuyi ma kofar ba yaki budewa,
da yaga sun matsa sai ya tattara duka takardun, ya zaga baya ya sanya musu wuta,
ganin hayakin dake fita ta kasan dakinshi ya sanya Anty Reemah sakin Kuka sosai tana fadin "dan san annabi Muhammadu Hilal ka bude kofar nan,
Papa kuwa ranshi ya gama baci ya dinga dukan kofar,
ko gezau batayi ba dan mugun karfi gareta,
murya a kausashe yace
"Muktar bude kofar nan,
wallahi kaji na rantse in baka bude ba zanyi maka mummunan furu---
bude kofar yayi ya tsaya a gurin,
har lokacin idonshi bai bar zubar ruwa ba,
da sauri Anty Reemah ta karasa tana share mishi hawayen, itama masu zafi na fita a idanuwanta,
Rungumeshi tayi tana tambayar dalilin zubar hawayenshi,
kamar ta sake kunno wutar cikin zuciyarshi haka ya kwantar da kanshi a jikinta yana kuka kamar karamin yaro,
Papa bai bi ta kanshi ba duk da shima ya shiga tashin hankalin ganin hawayen dan nashi,
bayan dakin yaje yaga komai ya kone sai toka,
dawowa yayi da sauri rai a bace yaja hannun Hilal,
"meye wannan?
Yanzu in abun nan da kayi yazo da tsautsayi fa?
dan iskanci ka rasa inda zaka sa wuta ka kona takardu sai a nan,
karkatar da kai kawai Hilal yayi baya ma gane fadan da Papa ke mishi,
abubuwa da dama ke mishi yawo a kai,
"Papa please,
Anty Reemah ta fadi cikin sigar tausayawa,
bai kalleta ba yaja tsaki ya fita shima zuciyar ta shi a karye take,
baisan me ya sanya Hilal kuka ba,
amma yasan koma meye ba karamin abu bane...
Anty Reemah kuwa zaunar dashi tayi tana rarrashinshi tana tambayarshi abun dake damunshi har ya sanyashi zubar hawaye,
kwanciya yayi a jikinta wanda har ya manta rabon da ya kwanta a jikinta haka,
Mugun tausayin kanshi yakeyi dan ya rasa makomar zuciyarshi,
"Tell me Babana,
menene?
Cikin muryar kuka yace
"Mum pls don't ask again,
ki zauna anan karki tafi ki barni,
hannu tasa ta share hawayenta ta fara shafa mishi kai,
Hinad ce ta shigo dakin ido jajur hannunta da plate din farfesun kifi ta tsuguna a gabanshi tace
"yaya ka tashi kaga nayi maka abun da kakeso,
"harda zobo mai dadi, Zainab ta fadi itama har lokacin bata bar kukan ba,
runtse idonshi yayi hawayen dake kwance ciki suka jika gashin idon,
Cikin muryar Kuka Hinad tace
"Yaaayaaa plss ka daina kuka dan Allah,
ka fada mana abun dake damunka,
Muryar Papa sukaji da karfi yana kiran Anty Reemah,
amsawa tayi tace tana zuwa,
"ki ce mishi ya fito mu tafi Masallaci,
tadashi Anty Reemah tayi tace
"Tashi kuje kuyi Sallah kaji,
in ka dawo sai ka fadamin damuwarka koma meye in shaa Allahu zanyi maka maganinta....
A tare suke jerowa kai kace wa da kani ne,
har Hilal ya dan dara Papa tsaho, bai tambayeshi abun dake damunshi ba dan baisan ji saboda kar nashi hankakin ya tashi,
nasihohi ya dinga mishi akan yadda rayuwa take
"dama dole a duniya mutum bazai samu abinda yake so daidai ba,
dole yau zuma gobe madaci,
Ganin hawaye a idonka ya fara tabbatar min da yanzu ka fara sanin me duniya take ciki Hilal,
wacece ita??
Wani irin kallo yayi ma Papa ya dauke kanshi dan baisan sake zubda wani hawayen,
lallai mahaifi daban yake,
yasan abun da zai raunata Hilal har haka bai taba wuce soyayya,
"Papa mu bar maganar,
she is dead,
"subhanallah Papa ya fadi cikin tausayawa,
hannun Hilal ya rike cike da rarrashi ya shiga bashi hakuri dan tsaff ya yarda ta mutun ne...
Dakyar Hilal ya ci wani abu sannan ya tashi ya wuce daki,
da ido iyayenshi suka bishi suna tausaya mishi dan sunsan mecece soyayya,
basu san tashi har gara ace mutuwar tayi da abun dake shirin rabasu ba,
Five missed calls ya samu a wayarshi na Musaddiq,
yana kokarin kira Musaddiq din ya sake kiranshi,
bai bari yayi magana yace
"ka fada mata?
Gyaran murya Hilal yayi yace "karka damu,
Nadeeyah is all urs in shaa Allah,
godiya ya shiga yi mishi wanda ya sanya Hilal ajiye wayar a kan gado,
wani irin tagumi ya zuba zuciyarshi na kukan rashin abin da ta dade tana dakon so,
yafi awa biyu zaune a haka...
Da wuri ta gama komai ta ciro wayarta a charge ta kwanta tana game,
bini bini ta duba lokaci,
ta kosa taji wani irin sakone wannan da har yake da lokacin badashi,
ganin da tayi goma ta gifta harda minti goma yasata fara rubuta mishi sako,
kafin tagama taji karar shigowar sako,
da sauri ta goge ta bude sakon...
*A rayuwa kowa yana tafe da kaddararsa, duk wanda Allah ya rubuta kaddararka ta zama tare dashi ne, to baka da dabara sai ka zauna dashi, naso kiyi zurfin karatu ta yadda zaki kere wasu matan kema a sanyaki cikin jerin masu ilimi sannan kiyi aure... amma hakan bazai yiwu ba saboda kaddararki batazo a haka ba, _I love Nadeeyah_ .... wannan itace kalmar da dan uwana yace in isar miki, Musaddiq na matukar kaunarki Nadeeyah, da fatan zaki amshi soyayyarshi, domin kun dace matuka, kuma nasan bazai barki ki zubda da hawaye ba, Allah ya barku tare kanwata take care.....*
Tana kaiwa karshe taji wani irin jirin da Allah ya taimaketa a zaune take, dan ta fadi,
Ya Musaddiq ke sonta,
"innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
ya zama dole gobe tayi shirin tafiya Gombe kuma ta zauna a can,
ina zata iya da bala'in Badar,
su Anty Raudha,
uwa uba Mummy da ta dau burin duniya tasa a kan shi,
inaaa samm bazama ta taba nuna taga text dinnan ba,
da sauri ta kashe wayarta ta dukunkune cikin bargo....
*MAFARKI*
_Hannu tasa ta cire akan farar fuskarshi da ta koma jaaa saboda kukan da yaci, "rau rau idonta yayi murya ta fara rawa tace "Yaa Hilal, me ya sameka, wanene? Hannunta kawai ya rike dan kukan yaci karfinshi ya kasa magana, hawayen dake makale cikin idonta ya fara zuba kamar fanfo, a shagwabe tace "Dan Allah ka fada min, menene? Zaiyi magana kenan ya hango wani farin haske dan karami ya doso inda suke, hannun Nadeeyah ya rike yana janta yana fadin ta kyaleshi tazo su tafi, mikewa tayi duk da kankantar haske haka ya rinjayeta ta dinga binshi tana waigen Hilal da ya sunkuyar da kanshi kasa sautin kukanshi ne kadai ke tashi a gurin....
A firgice ta tashi zufaa duk ta jikata,
janyo wayarta tayi da sauri ta kunnata,
bata bari ta gama settling ba ta latsa number Hilal,
lokacin karfe 1 a nigeria,
tasan dakyar yanzu in bai yi bacci ba,
saida ta kira sau uku bai daga ba,
kwanciya tayi taji duk babu dadi dan so takeyi taji ko lafiyarshi kalau,
yana idar da Sallah ya bi bayan kiran da tayi mishi,
hannu na rawa ta dauka tace
"ina