Showing 75001 words to 78000 words out of 184071 words
Chapter 26 - ZUMUNCIN MU A YAU Complete By Aisha Yau Kura.txt
ke amsata da kyar saboda laifukan da tayi mata ciki harda korar Badariyya da mijinta Yayi...
Da kyar Goggo ta yarda Zulai ta wanke mata bayi,
sai a sannan Badar ta shiga a kyankyame tayi fitsari ta fito da sauri,
kan gadon Goggo ta kwanta tana maida numfashi....
"Fito kici Abinci,
Goggo ta fadi tana fiffita tuwon a cikin faranti,
badan taso ba sai dan tana jin yunwa ta sakko a gado ta fito waje,
yadda yaukin miyar ke bin hannun Goggo da zulai yasa komawa daki da sauri,
da karfi tace
"Tuwo da rana tsaka Goggo,
kuma miyar yauki kamar majina ta karashe fadi kar zatayi amai,
wannan wace irin jarabawa ce,
kudi ta fito dashi a jakarta ta kira Rilwanu ya siyo mata Abinci a restaurant mai kyau....
ko kallonta Goggo batayi ba ta cigaba da kai lomar tuwonta...
Tunanin Musaddiq kwanta takeyi,
ta ya za'ace babu aure a tsakaninsu,
dan kawai sun sa nono daya,
Allah yasa Liman ya gano wani hadisin da ya halasta hakan,
in ba haka ba walalhi daga ita har shi saidai su mutu ba aure,
dan duk wacce yayi yunkurin aura sai ta kasheta.....
********
Danna wayarshi yayi ya kira layin wayar da ya ba Nadeeyah a karo na ba adadi,
har lokacin ba'a kunna wayar ba,
juyi kawai yakeyi a kan makeken gadonshi,
gaba daya ya rasa abinda yake mishi dadi,
tun dawowarshi daga gidan su Nadeeyah ya kasa sukuni,
ko abinci kwakwkwara bai iya kaiwa bakinshi ba,
bacci kuwa sai dai dan barawo ne ya saceshi bayan ya idar da Sallar asuba,
Ya gama sawa ranshi sha biyu nayi in yaji ba'a kunna wayar ba zai koma gidan koma me zai faru ya faru,
Soyayyar Nadeeyah na neman yi ma zuciyarshi illa,
yama za'ayi ya iya rayuwa babu ita,
kallon kofar da aka murda yayi yaga Momma ta shigo dauke da kayan break fast,
"Gud morning my Tee,
Morning Momma, kin tashi lafiya?
Lafiya kalau nd u?
Nt bad ya fadi hade da mikewa zauna,
'Tee me yake damunka,
yau baka fito ba kwata kwata,
sannan jiya ina lura dakai dakyar ka tsakuri abinci,
yar hirar da muka saba ma baka zauna munyi ba,
tell me,
meye matsalarka,
Bazai iya boye komai na daga dangin farin cikinshi ko akasin haka daga gareta ba,
gyara zama yayi ya rike hannuwanta,
raunanannun idanuwanshi suka tara ruwa yace
"Zan rasa ta Momma,
Nadeeyah zatayi ma rayuwata nisa,
Zan rasa farin cikin da ya ziyarceni a lokacin da na fidda ran zuwanshi,
Fuskarshi ta tallaba da hannayenta biyu cike da tausayin shi tace
"bazaka rasa ta ba,
baka taba neman abu ka rasa ba Tee baza'a fara akan wannan ba da yardar Allah,
ka kwantar da hankalinka kaci abincinka kamar ka sameta ka gama,
Anjima da yamma zan kira *Kawu Tidjani* in fada mishi ya taho muje nema maka aure,
Murmushin farin ciki yayi yace thank u Momma,
Allah yayi miki sakayya da aljanna firdaus,
Ameen my Boy,
tashi maza kayi wanka ka shirya ka tafi gym wannan tumbin da ka fara ajiyewa ka gyarashi kafin ranar aurenka,
shafa tumbin yayi yana dariya yace "ina tumbi anan Momma,
sai dai in so kikeyi ya shafe da bayana,
dariya tayi hade da mikewa tace "in kayi wanka kazo zan aikeka,
gyada kai yayi yace "to Momma bari in fara wankan sai inci abincin....
********
_Agadaz_....
*DIYA MURADUN AHMEDOO TIDJANI YALLO PALACE*
Karar busar algaitar dake fitowa daga katafaren gidan shi ya bawa mutanen gurin damar mimmikewa saboda alamu ne na fitowar sarki,
kirari dogarai suka fara yi cikin farasanci ana kodashi kamar yadda akewa sarakuna,
Cikin daya daga jerin motocin da aka jera mishi ya shiga,
nan ma fadawa suka dinga masa kirari har saida sukaga kurewar motar..
Wani katafaren gida motocin suka shiga,
da sauri aka bude mishi kofa ya fito suka taka mishi har kofar parlon,
suka murda ya shiga sannan suka juya dan shiga cikin gidan na iyalan gidan ne kadai...
Cikin kasaita ya taka ya isa can sama ya fada wani kayataccen parlor,
Zaune ya sameta kan dadduma jakadiyarta na danna mata kafa,
tana ganin shigowarshi ta tsuguna ta gaisheshi ta fita daga dakin,
Rawanin kanshi ya zare ya zagayo ta bayanta ya shiga daddanna mata kafudunta hade da cewa
"My Sheri,
wannan damuwar har yanzu bazaki daina ta ba,
shekara da shekaru kina tunanin abu daya,
haihuwa Allah ke bada ita,
kuma bai rubuto mu cikin wadanda suke da rabon samu ba,
kuka ne mai karfi ya kufce mata tace
"ina tsoron ranar da zamu wulakanta bayan ranka,
Mulkin nan ficewa zaiyi daga gidan nan,
kuma in ya fita babu irin wulakancin da bazamu gani ba,
zama yayi sosai ya janyota jikinshi yace
"SHARIFAH,
mulki na Allah ne,
shi ke bawa wanda yaso,
A lokacin da mahaifinki ya rasu,
kin taba tunanin Allah zaisa a bani mulki duk da ni ba danshi bane sai dan na kasance miji a gareki,
gudan jininshi wacce kika zama tilo,
Da Allah ya ga dama,
da fitar da mulkin zaiyi tunda sarki bashi da magajin kujerarshi, to da yake Allah ya rubuto ni din nan ni zan zama sarki shi ya sanya ya hadamu aure,
rashin bamu haihuwa kuma wannan shi kadai ya barwa kansa sanin dalilin hakan,
ta yiwu yayi wa wani can wanda bamu sani ba tanadin gujerar,
shiyasa ya hanamu samun magaji...
Share hawayen fuskarta tayi cikin gamsuwa tace "Allah ya kawo mana taimako,
A zuciyarta tana tunano rayuwar kuruciyarta wacce tasan tayi shi tare da wani wanda ya zamto jinin ta,
cikin kankanin lokaci kuma ya bacewa ganinta da tunaninta,
a yan kwanakin nan ne take tunano shi da suffofinshi da dalilinshi na barin gida...
Bata iya fadawa mijinta ba saboda ta kasa sanin hakikanin kusancinsu,
,
ko da yaushe ta runtse ido sai ta ganshi cikin mafarkinta,
tare da farin saurayi mai tsananin kama dashi,
saidai idanuwan saurayin sun fi nashi kyawu da girma,
karar Waya ce ta katse mata tunani,
Tana kallon shi ya dauki wayar cike da farin ciki,
"Kuna lahiya Saude,?
"lafiya lau kawu, an wuni lafiya?
"Kalau kalau ina Tahiru Yallo?
Yana nan lafiya kawu,
dama akan maganarshi na kiraka,
ya samu macen da yake so,
shine nace ka shirya kazo sai muje gidan iyayenta,
fadada murmushinshi yayi yace "to masha Allah,
tuzuru zai angwance,
Dariya sosai Anty saude tayi tace "haba kawu,
ai ko danye ne sharr,
nan suka cigaba da hira kamar ba surukai ba,
saida suka gama ya mikawa matarshi wacce ta zamto kawa kuma shakikiyar Anty saude,
nan suka shiga hirar yaushe gamo,
Anty saude tace "kizo fa tare da kawu,
dan tare zamu fara shirye shirye,
bazamu sa bikin da nisa ba,
Dariyar kasaita "Sharifa" tayi tace
"to wacece uwar in ba ni ba,
komai dani za'ayi,
gobe in shaa Allah zamu biyo jirgi mu iso.......
Mrs Tijjani Shattima....
[25/03 10:07 PM] Safiyya Umm Ab: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣4⃣
By *Aysha Ya'u kurah*
Juyi Musaddiq yayi a karo na biyu yace
"ka duba cikin aljihun wandona, plss ka barni inyi bacci,
tsaki Hilal yaja ya dauki wandon zai duba ya hango keyn a saman windon dakin,
jefa wandon yayi kan fuskar Musaddiq dan a cike yake dashi,
yafi 20mints yana tashinshi yaki tashi,
daukar keyn motar yayi yace "in kaga dama ka kai 4 kana bacci, idiotic being kawai,
murda kofar dakin yayi yana mitar yawan baccin safen Musaddiq,
wannan in ya fara aiki ya kenan,
sam Mummy bata kula da tashin shi,
shi kuwa saboda sabon da Papa yayi mishi tun asuba in ya tashi baya iya komawa bacci...
Zama yayi a parlor yana jiran ganin ta inda zasu bullo dan yayi alkawarin da kanshi yau zai kaisu makaranta,
yana son nunawa Taheer shi din mai babban matsayi ne a gurin ta...
Farin tight din da suke sawa a ciki saboda gajartan skirt dinsu ta dinga dubawa bata gani ba,
tayata dubawa Husna tayi har tsawon minti uku basu gani ba,
black kuma in suka sa korarsu gida akeyi,
da suka gaji da dubawa Husna tace "dan Allah zo mu tafi,
kar muyi latti,
kallon kanta tayi tace "nice zan fita a haka,
"to sai me,
nima bakiga bana sawa ba,
dama iyayinki ne, Husnah ta fadi tana nuna kafarta,
dauko school bag Nadeeyah tayi ta rataya, ta tura gashinta cikin hular makarantar da taki zama akanta saboda cikowar gashinta.....
Gud morning my PP,
Husnah ta fadi hade da zama kusa dashi,
"morning small aunt,
har kun shirya,
"eh yanzu zamu wuce ta karashe tana mikewa,
"ina kwana,
Nadeeyah ta fadi tana boye kanta a bayan kujera,
"Lfy kadai yace ya mike yana kallon Husna,
muje in kaiku makaranta,
zanje gida dauko ma Mum abu,
"yeyy... Husnah tace ta fara tafiya ya bi bayanta,
Yana gab da shiga motar ya dago kai ya kalli Nadeeyah da har lokacin tana gyara hular kanta,
Rufe motar yayi yana mata wani irin kallo har ta karaso gurin motar,
sam bai kula da skirt din Husnah da har yafi nata gajarta ba,
wani irin kishi ne ya turnukeshi, nan da nan zuciyarshi ta tafi tunanin irin kallon da Taheer yake mata da wannan gajerun uniform din,
kama hannun motar tayi zata bude yayi saurin cewa
"wait,
da wannan skirt din kuke zuwa makaranta?,
daga cikin motar Husnah tace "ya Hilal ka manta ne,
haka uniform din legacy yake,
"yes amma ai ana sanya wando ko,
ku ko kunya bakwaji makaranta ba ta mata zalla ba ku dinga tsilla tsilla da wannan skirt din,
maza fito kuje ku sa wando ya fadi yana bude kofar motar,
Agogo Husnah ta duba tace "ya Hilal munyi latti,
kuma bamu da legens fari sai baki ba'a barin mu muje school dashi,
"okay to sai ku fasa zuwa school din,
A firgice suka kalleshi dukkansu dan zasuyi submitting project dinsu,
marairaicewa Husnah tayi tace "plsss muje ka kaimu,
kasan dai muna shekarar karshe ne,
kullum cikin assignment ga project zamuyi submitting,
key yasa ya rufe motar yace
"ko kusa bakin ko kuma ku hakura da school yau,
da sauri Husnah ta fito tace "muje Nadeeyah,
Bayansu yabi da kallo yaja tsakin takaici,
tunanin yadda zaiyi ya rabata da skirt yakeyi,
a da uniform din school din na burgeshi,
ba kamar lokacin suna yara in su Anty Raly sun saka,
amma yanzu gaba daya ji yayi ya tsani makarantar ma ba uniform din ba,
Bai ga fitowarsu ba sai jin taba motar da Husnah tayi,
saida ya kalli kafafuwansu sannan ya shiga motar ba tare da ya samu gamsuwa sosai ba dan ba mage ba miyau.....
*****
Ke Badariyya,
Wai bazaki tashi bane,
tashi kije kiyi wanka ko bazaki makarantar bane?
Mikewa Badar tayi da mika hade da goge zufar wuyanta,
tun da ta taso bata taba azababen bacci irin na yau ba,
fanka ma kashewa Goggo tayi wai sanyi take ji,
shi kuwa a.c tun goma na dare ta kasheshi wai bazata sankarar da ita ba,
duk soyayyar da takewa Badar ashe ta nesa ce,
saboda ba ita ke hidimarta ba,
sannan kuma ita ma tana cikin nata kuncin dan Baffa bai dawo gidan ba sai 1 na dare suka dawo tare dasu Papy,
anan ma hirar suka zauna yi har 1:30,
ya nunawa Papy gurin da yake sa ran zai mishi gini in yazo ya dinga sauka,
Tana jiyo su dan ta kasa rintsawa,
tana jin Papy na cewa nan da shekara daya shima zai baro Gomben ya dawo nan kaduna cikin yan uwanshi,
ganin irin farin cikin da Baffa yakeyi shi ya sake tunzura zuciyar Goggo ta dau alwashin aiwatar da abin da tayi niyya shekarun baya....
"Gaskiya bazan sha wannan kunun ba Goggo,
walhi bazan karya da wadannan kazantar ba,
haba common tea ma sai kice bazaki bani in sha ba,
Badar ce ke maganar kamar zatayi kuka saboda takaicin karo da kunun da tayi,
tabe baki Goggo tayi tace
"Sai dai kar kisha,
tun da na tashi nake jiran Rilwanu bai zo ba,
ni kikeso in fita in siyo miki kayan shayin,
Da tsufana me zanyi da shayi ni, in kinga dama kar k----
Assalamu Alaikum,
sallamar da akayi ta katse Goggo daga karasa maganarta,
kaya niki niki taga Jamal da Hafeez suna shigowa dashi,
a bayansu kuma ta hango Anni da Mami,
papy ne ya shigo a karshe sai Rilwanu da Garzali suma dauke da wasu kayan,
fitowa Baffa yayi da sauri saboda jin muryar Papy,
kallonshi Anni tayi cikin zolaya tace
"Alhaji karka fadi,
irin wannan sauri haka,
shima saurin yazo ya ganka ne ya hanashi ya barmu sai anjima muzo,
Dariya Baffa yayi yace "marabanku,
ai sai ki bani kunya,
yanzu dai bari in boye murnata,
Dariya dukkansu sukayi Papy ya tsuguna ya gaida Baffa,
bai amsa ba ya dauko tabarma ya shimfida musu,
saida ya zauna sannan suka gaisa dukkansu cikin farin ciki,
Hira sosai Baffa sukeyi da Anni tana bashi labarin yarintar Papy har zuwa girmanshi, da irin nasarorin da ya samu,
gaba daya Baffa ya manta da Goggo dake tsaye kasake tana kallonsu, ko tafiyar Badariyya makaranta bata sani ba,
Kallon Anni yayi yace "tun jiya nake ta tunanin abun da zan miki in saka miki abin da kikayi min,
Na tattaro duk abinda na mallaka naga sun yi min kadan in baki a matsayin tukwicin abin alherin da kikayi mini na taimakon dana da kikayi har ya zama abun da ya zama,
na kwana ina miki addu'ar Allah ya sanyaki cikin farin ciki duniya da lahira,
Allah shi kadai zai biyaki da aljanna firdausi,
nagode nagode sosai Hanne,
Kafin Anni ta amsa Ruwaida tayi saurin cewa
"Ameen mijin Anni,
baban Papy,
kaka na ni kadai banda yaya Jamal,
garammmm
Goggo taji maganar kamar saukar aradu,
tsayuwace ta gagareta ta dawo cikinsu ta zauna saboda shurun da taji sunyi,
kallon kallo suka shiga yi a gurin Mami tayi saurin cewa Jamal ya kai Ruwaidah gurin su Nadeeyah,
"suna makaranta Hafeez ya fadi yana rike hannun sarkin katobara,
yace muje ki rakani..
Suna fita Anni tace "yarinta hoo,
ita a dole farin ciki takeyi taga babanta cikin yanayin da yafi na da,
"Yarintarta Ruwaidah akwai hikima a cikinta Anni, Papy ya fadi yana gyara zama..
Kallon Baffa yayi yace
"Baffa kana son sakawa Anni,
baka da abun saka mata dashi,
dan Allah ne kadai mai saka mata,
"abu daya zakayi ka kwatanta kyautata mata shine ka aureta,
Ta zamto matarka,
makwafin mahaifiyata,
wannan shine kadai zai sani farin ciki,
Anni ta ki yin aure saboda ni,
bata jure ganin kowa ya wulakanta ni, shiyasa ta hakura da aure domin taga auren wani mabudi ne na wulakanci a gareni,
Dan Allah Baffa ka auri ANNI,
kallon Goggo da ta kureshi da ido yayi yace
"INNA dan Allah kisa baki,
auren shi kadai ne abun da zamuyi mu saka mata......
Kafin Goggo ta gama tattaro amsar bayarwa Baffa yayi murmushi yace
"yo har sai ka roka,
ni da nake neman abun da zan bada tukwici,
ai na karbi wannan karramawar,
kuma in shaa Allahu zata ga karamci domin wannan din ma wani sabon karamcin ne da yake bukatar tukwici,
Dariya Mami tayi ta kalli Anni dake share kwallar da ta gangaro mata,
hannunta ta kama tace
"Alhamdulillah Anni,
dan Allah ki amince,
kuka ne ya kufce mata tace
"na Amince Maimuna,
wannan ya wuce tukwici,
domin kuwa zan shiga cikin jerin matan da nake fatan in mutu cikin sutura,
zan shiga jerin matan da zasu mutu ana maraba dasu,
hannu ta daga sama tace
"Alhamdullillah ala kulli halin,
Karkiyi saurin Hamdallah Goggo da ta gama charge ta fadi tana mikewa da kyar,
kiyi gaggawar maida murnarki domin a haka zaki mutu babu aure1,
Mijina bai min kishiya tun da jajayen sawunmu ba,
sai yanzu da muke rai a bakin rami,
in banda kwadayi ma me zakiyi da wannan tsohon,
me ya rage mishi da zaki suďa,
"Murmushin ilimi Anni tayi dan a ganinta kishi ne,
tace "ko ban samu abin sudewa ba zan samu martabar zama matar aure,
kwantar da Hankalinki bazan zo dan yin kishi dake ba,
zanyi aure dan in samu cikar kamalar da na dade ina nema,
"Aiko zaki mutu baki samu wannan kamalar ba in dai mijina zaki aura,
bakin da ya furta miki cewa zai aureki shi zai dawo yace miki ya fasa,
Shekeke Baffa ya kalli Goggo,
dauke kanshi yayi da sauri da yaga suna kokarin hada ido dan idanuwanta kan sanyashi manta komai, yace
"Aure babu fashi,
sati ma in shaa Allahu,
Kallon Papy yayi yace "ka daukesu ka maidasu gida sai ka dawo mu nemo magina su fara aikin ginin nan..
Sallama Papy yayiwa Ma'u dake tsaye galala masifarta ta makale saboda furucin Baffa,
Bin su tayi da ido har suka bacewa ganinta sannan ta fada dakin da sauri,
kofar bayin ta shiga bugawa tana masifa tana fadin "baka isa ba,
walhy Muhammadu baka isa ba,
alkawarin da kayi min kenan,
ni zaka butulcewa duk irin halaccin da nayi maka,
to wallhi ka fito nan ina jiranka, saidai ka zaba koni ko ita, dan wallhi bazan zauna da kishiya ba..
Yana gama wanka ya bude kofar ya fito ba tare da ya kalleta ba,
kaya ya dauko yasa yace
"Ma'u halacci babu wanda ban miki ba,
shekararmu sama da hamsin dake ban taba yunkurin yi miki kishiya ba da kaina ba,
sai yanzu da nake son saka alkhairi da alkhairi,
yanzu ke ba abun kunya bane ki ts----
ka kalli idona ka fadamin haka Muhammadu, ta katseshi da karfi tana juyo kafadunshi,
juyar da kanshi yayi ya dauki turare ya fesa yace
"kallon idonki na daina shi har in koma ga mahallincina,
kallon cikin idanuwanki sun sanyani fita cikin hayyacina har na aikata ma diyar cikina abubuwan da har na mutu bazan yafewa kaina ba,
ki rike idanuwanki in rike rayuwata da mu'amalata,
yana kaiwa nan yasa kai ya fita ya bar Goggo da masifa kamar zata ari baki,
kayan dake tsakar gidan yasa Rilwanu kwashewa yasa mishi a dakin waje..
crates din kwan Goggo ta farfasa su da tabarya,
ta dinga bin kayan tana tsine musu,
Dakyar Rilwanu ya kwashesu,
yana gamawa yayi mata sallama yace "gobe zai koma garin su,
mahaifinshi baida lafiya,