Showing 126001 words to 129000 words out of 184071 words

Chapter 43 - ZUMUNCIN MU A YAU Complete By Aisha Yau Kura.txt

dashi daga gidan,
sunyi matukar farin cikin haďuwa da juna......





Sai bayan isha'i suka koma gida,
fitar tayi ma Nadeeyah daďi dan dama zama guri daya ya isheta,


Tun daga waje suke jiyo shewar su Raudha kamar wadanda akayi ma albishir da gidan aljanna,



A darare Nadeeyah tabi bayan Musaddiq dake rike da ledojin da suka dawo dasu,


"oyoyo my dear broo,
Faida ta faďi haďe da nufo inda Musaddiq yake,


Sakin fuskarshi yayi yace

"Manyan baki ne a gidan, welcome,
ya kike?


Ledojin hannunshi ta amsa tace

"am fine, bari in rage maka nauyi,


Wani miyau mai ďaci Nadeeyah ta haďiye wanda bata san daga inda ya taru zuwa bakinta ba,


Tana kallon yadda Faida keyi ma Musaddiq fari da idanuwa tans kwarkwasa jikinta,


Hanyar sama ta nufa a hankali kamar mai koyon tafiya,

ďaga Murya Faida tayi tace

"Ina wuni Amarya...

cakk.. Nadeeyah tayi a gurin ta kasa juyowa ta bata amsa,


Cike da kirsa Radiya tace

"uhmm, kaji inda ake girmama na gaba,
a duk zaman da nayi a gidan nan Nadeeyah bata taba yunkurin gaida ni ba,


"Hmmmm naga deal Anty,
gashi yanzu ma ta wuce ba tare da kallon inda muke ba,
ai ko ba komai mu yan uwanta ne na jini,

amshewa Radiya tayi da cewa
"nifa ban ga laifinta ba,
dan taga little na rawar jiki akanta ne,
shiyasa bata damu dayi ma yan uwanshi biyayya ba,

yo ko Mummy ma bata gaisar wa bare ni,
jiya Mummy 10missed call tayi mata bata dauka ba,
amma ina jiyo muryarta da Hafeezu suna waya...



"Kinga laifinta, Raudha ta faďi tana hararar Musaddiq,

Zaiyi magana Faida ta rigashi da cewa
"Haba Aunties, kuyi hakuri plss,
may be amaryarmu kunya takeji, dan Allah kuyi mata uzuri,


Daďi Musaddiq yaji har cikin zuciyarshi,
duk tunaninshi Faida shigarwa Nadeeyah tayi,
baisan duk part of der plan bane,


"Thank u my sister,
plss ki fahimtar dasu,


"Karka damu dear,
zasu fahimta,
amma kaima ka ďan fahimtar da ita,
kasan baka da kamar yan uwa da mahaifiyarka,
"auchh Faida ta faďi cikin siririyar murya,
na barka a tsaye kuma dawowarka kenan,
muje in rakaka ďaki da kayan sai ku fito kuyi dinner da Amarya,


Da sauri Nadeeyah ta haye sama ta murda kofar ďakin ta shige,
mamakin yadda akayi wa ďakin gyara na musamman ta tsaya yi hawayen dake shirin sauko mata suka kafe,
zanin gadon da aka canza ma abun kallo ne,


"Did u like it?


Waigowa tayi ta kalli Faida da ta shigo haďe da jefo tambayar,

Wani irin kallon zaki sani ta gani cikin idanunta wanda yasata saurin kauda idonta ta wuce cikin bayi,


tana jiyo muryarsu da Musaddiq a cikin ďakin suna dariya yana yabawa kokarinta,


Shi bai dauki hakan da yakeyi komai ba saboda yasan matsayin da ya ajiye Faida,
yana dai biye mata ne dan bakonka annabinka,
baya son yin abun da zata ga yayi mata wulakanci,


Hular kanshi ta cire haďe da shige mishi sosai,
cikin wata iriyar murya tace

"zan iya taimaka maka kayi wanka,

hannunta ya cire kan button din rigarshi yace

"noo never mind,
in na shirya zamu fito,
gefen fuskarshi ta shafo tace

"okk dear,
sai ka fito,


gyaďa kai kawai yayi cike da kosawa,
tana fita ya saki ajiyar zuciya ya wuce bayin,



Kukan da ya tsani ganinta tanayi shi takeyi bilhakki,
bayanta ya rungumo yace

"Sorry baby doll,
su Anty basu san wacece ke ba,
nasan bazaki ķi gaishar dasu ba, kiyi hakuri kinji?


Fisge jikinta tayi da karfi ta cigaba da kukan da takeyi,

daukarta yayi ya fito da ita daga bayin ya direta akan gado,

yadda take kukan yana matukar taba mishi zuciya,

zaunar da ita yayi haďe da rungumeta sosai a cikin kirjinshi yana rarrashinta,


Saida yaji ta fara ajiyar zuciya alamar tsayawar kukan sannan ya ďago fuskarta ya share mata hawayen,

"wannan kukan na shagwaba ne ko na jin daďi,
faďa min,
ya karashe cikin tsokana..


"Nima ban sani ba,
ta fadi tana turo bakinta gaba..


Bakinshi ya daura a kan nata yayi mata light kiss yace

"kin sani mana,
da bakiyi shuru ba ko,
daukarki zanyi in kaiki gurin su Anty sai sun baki hakuri da kansu,


Zaro ido tayi cike da tsoro tana niyyar yin magana ya rigata,

"kiyi hakuri, plss ko yaya ne ki dinga gaishe su,
nd Mummy ko bata kiraki ba ki kirata,
ko ba komai mahaifiyarki ce,


Danne kuncin da ya taso mata tayi na yadda suka juya maganar,


"Babu ranar da zata tashi bata kira Mummy da Mami ba,
saidai Mami ta dauka Mummy kuwa sam bata dauka,
sannan su kuma mugun tsoronsu ke hanata fitowa inda suke,
bata san meye kirsa ba saboda tayi yarinya ta sani,
amma a cikin shawarwarin Hajiya Zubaida ta sama wa kanta mafita...



Kwantar da kanta tayi a kirjinshi tace
"kayi hakuri yayana,
in shaa Allahu zan gyara,


Lumshe idonshi yayi ya sake kankameta yace

"shiyasa nake sonki, sosai sosai, rikita ta ya dinga yi da kalamai masu daďin sauraro,

Bata gama tabbatar da tana sonshi ba sai da taga yadda Faida take mishi,
ya zame mata dole ta dage in ba haka ba tana ji tana gani Faida zatayi sanadiyyar raba su....





Murďa kofar tayi haďe da shigowa ba tare da sallama ba,
aiko tayi gamo,
dan yadda ta samesu saida tayi dana sanin shigowa dakin,

wani irin kishi ne ya taso ya tokare mata zuciya,
ji takeyi kamar ta shako Nadeeyah ta kasheta kowa ya huta,


Dakyar kafarta ta iya daukarta ta fita waje tana sharar kwalla,


ganin haka yasa su Anty Radiya zagayeta suna tambayarta ko lafiya,

girgiza kanta tayi tace
"aikin nan da kamar wuya,
munyi kaďan mu raba wannan auren,

wannan aikin mutum ďaya ce zata iya shi,

*uwa*,

mahaifiya ce kaďai keda wannan karfin,
in har son rabasu da gaske kukeyi sai kusa mahaifiyarku tazo,
ni bazan iya ganin takaici ba,
tana kaiwa nan ta wuce daki kirjinta kamar zai faďo kasa....





Assalamu Alaikum...

"Ameen wa alaika salam, Shamsuddeen ne yau a office dina,


Har kasa ya tsuguna ya gaida Daddy,

"tashi tashi,
ga guri ka zauna,
kuna nan lafiya,
sosa keya shamsu yayi yace "lafiya kalau Daddy,


"To Madallah, ai haka muke son ji,


Cike da kunya shamsu yace "dama nazo kawo maka katin bikina ne,
jibi in shaa Allah za'a daura,


Duk da abun ya sosa ran Daddy sai ya danne yace

"Mashaa Allahu,
aiko banji ba,

kaii na tayaka murna,
Allah ya kaimu, yasa ayi damu,


Dabaibayi shamsu ya shiga yace
"kayi hakuri Daddy,
wallahi banda option ne,

nan ya bashi labarin duk abin da Radiya take mishi,
sannan ya daura da cewa har yanzu tana lagos gidan Musaddiq bata dawo ba,

a gigice Daddy yace

"Whattt!

Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Tabdijam,

nagode sosai shamsu,
dubu dari biyu Daddy ya ciro a drawer yace
"Dan Allah kayi accepting wannan a matsayin sadaki...


Sosai Shamsu ya tausaya mishi kuma ya kara ninka girmanshi da yake gani.....





Wacece ma me wannan Sunan?

Daddy ya tambaya yana zana takardar dake gabanshi,

Hajiya Martai kawata ta Maiduguri,
wacce take zuwa duk wani sha'ani nawa ta kwana,

"uhmmn sai akayi yaya?


Dama mijinta ne ya mutu a sokoto,
gobe da wuri za'ayi jana'izarshi,

"Ayya,
to Allah yayi mishi rahama,
sai kin dawo,


Cike da murna Mummy tace "nagode kwarai,
ka fitar dani kunya,

da ido kawai ya bita har ta shige ďaki,
ticket din jirgin da Malam Ali ya kawo mata ya juya,
bazai taba hanata ba,
so yake yaga gudun ruwanta,


A gurin yabar ticket din ya mike ya fita waje yana mamakin irin halayyar 'yayanshi,


Raliya ya kira a waya ta tabbatar mishi da ita tana gida yanzu ma zata zo gidan,

kashe wayar yayi ya kira Reemah,


Cike da mamaki tace

"Wallahi Daddy bani da Masaniya,
yanzu Radiya tana gidan Diku,
innalillahi wa inna ilaihir rajiun,


Kwantar mishi da hankali tayi ta kuma tabbatar mishi yanzu zata kirata ta sata ta koma gida,


"Karki damu Reemah, mahaifiyarku ma ta shirya tafiya, ki barsu kawai,
so nake in ga gudun ruwansu,


A sanyaye Anty Reemah ta kashe wayar ta faďa ma Papa abinda ke faruwa,
duk abinda da akeyi a kunnen Hilal dake gaban system dinshi,


Ajiye assignment Hinad tayi ta dawo kusa da Anty Reemah ta bata duk labarin da ta kunso daga gurinsu,
ta kuma ce sunce ko sati biyu bazata yi a gidan ba,
wallahi mantawa nayi ban faďa ma Yaya Hilal ba,
i'm very sure Nadeeyah na cikin matsala,
"ya kamata a taimaka mata ASAP mum...



Rufe system dinshi yayi ya mike ya nufi sama,

number Musaddiq ya nema, saida ya kira sau uku sannan ya ďauka,

yadda yaji muryarshi ya tabbatar mishi da abun da yaji,
dan a lokacin sun gama zagin Nadeeyah kenan saboda ta shiga kitchen zatayi abinci,


Hilal baiyi wata wata ba ya kashe wayar,


Number Nadeeyah ya kira,
tana tsaka da kuka lokacin,
duk tunaninta Zainab ce dan ita ke kiranta kullum da wayar Hilal,

Cikin Muryar kuka tace

"Zainab kuna nan lafiya,
zakiji muryata haka,
mura nakeyi sosai,
ki gaida su Anty,
tana kaiwa nan ta kashe wayar...



Wani abu yaji ya taso mishi,
tuni ya cire Nadeeyah a ranshi a matsayin macen da yake so, amma tana nan makale cikin ranshi a matsayin jininshi wacce ke yawo a dukkan sassa na jikinshi,

waya yayi dan neman visa..

Wurgi yayi da wayar saboda tsabar bacin rai, dan sunce sai nan da 3days saboda jirage na hutu,


Safa da Marwa ya dingayi a cikin dakin ya dinga jin kamar yayi tsuntsuwa ya ganshi a nigeria........






Mrs Tijjani Shattima.......!
[20/04 7:01 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 6⃣1⃣
By *Aysha Ya'u kurah*






Yana hangota ya nufo inda take da sauri cike da murnar ganinta,


Yasan zuwanta zai sanya su Anty Radiya su bar mishi gida ya samu sakewa da matarshi,
baisan komai daga gurinta yake fitowa ba,


"I missed u alot Mummy nah,

"Missd u more little,

nace bari inzo inji ko nayi ma Nadeeyah laifi da har yanzu bata daukar wayata,

nan take wani abu ya ďarsu a cikin ranshi,

"kodai da gaske ne dasu Anty Raudha ke cewa saboda yana tsananin sonta ne yasa bata girmama mahaifiyarshi da yan uwanshi,
hango yadda Faidah take yi musu biyayya yayi a zuciyarshi yace

"ina ma abar sonshi ce haka da yan uwanshi,

Kauda abun yayi a ranshi yace "Sorry Mummy,
wayarta nada matsala ne,
kullum sai ta ce in gaishe ki,

"Au to Madallah,

Muje inga gidan ďana,
gaskiya little nayi matukar farin cikin auren nan da kayi,
kaga yadda ka canza,


Tsaki yayi yace
"Dan Allah mummy kice ma Anty Radiya ta koma gida,


Cikin dabara tace
"dama Radiya bata tafi ba,
karka damu tun da nazo tare zamu tafi mu barka ka huta da amaryarka,


Cike da jin dadi ya buďe mata motar ya shiga ya tada ta,

cike da shauki yake hango su Anty Radiya sun barshi shi kadai a gidan shi da matarshi,
so yakeyi ya bata kula ta musamman wanda zai mantar da ita duk bacin ran da ta shiga a farkon amarcinsu,


Wani irin sonta yakeji har cikin bargonshi,
baisan dalilin da yasa kullum kamar ana dada hura wutar soyayyarta cikin jininshi ba,
in ko yana tare da ita jinshi yakeyi a sama kamar su biyun kadai aka halitta a duniyar,

Murmushi yayi haďe da karawa motar gudu......



Yana Parking tace

"Washh yunwa,
da fatan anyi min abinci?..


"Baki da matsala Mummy,
Nadeeyah tayi miki abincinta mai daďi,
nuna mishi jin daďinta tayi tace
"yayi kyau ďan albarka.....




Gaurayewa gidan yayi da ihun su, suna kiran sunan Mummy,


Kallon gidan tayi cike da jin dadi tace Mashaa Allah,
gida yayi kyau little,
Allah ya kawo min jikoki suyi ta yawo a gidan sai ya zama complete..

Dariya yayi sosai yana duban ta inda zaiga rabin rayuwarshi,
hangota yayi cikin dogon hijab tana sakkowa daga sama fuskar nan dauke da murmushinta mai kyau,


Gaban Mummy tazo ta tsuguna ta gaida ta,
dagota tayi cike da kissa ta rungumeta tace

"mun sameku lafiya?,

"lafiya lau Mummy,
ya hanya?


"Hanya ba daďi,
muje in huta sai inci abinci,


"Ki fara cin abincin Mummy,
Faidah ta faďi tana rike mata hannu,
kyafta mata Anty Radiya tayi wanda hakan yasa ta nufi gurin dining din ta zauna,


Zama Musaddiq yayi a gefenta ranshi wasai dan yasan Mummy zata ji daďin girkin matarshi wanda saida aka kai ruwa rana kafin su barta ta shiga tayi,


Kamshin da ya karaďe gurin ya sanya Mummy faďin


"Mmmm Masha Allah,
nayi missing abincinki Nadeeyah,

Murmushin jin dadin kalaman Mummy tayi,
duk wani bacin rai taji ya gushe cikin zuciyarta,


"Shinkafa zakici ko tuwo?
Faida ta tambaya tana bude warmers din,


"Saka min tuwon,

Malmala biyu ta zuba mata sannan ta bude miyar ta fara karto kasan da serving spoon tana zubawa,


Kallon kallo Radiya da Raudha sukayi wa juna,


Kafin suyi magana Mummy tace
"samin naman mana,

"Babu a cikin nan,
saidai ko a stew,
bude stew din Faidah tayi ta fara zakulowa nan ma ba nama,


Hankalin Nadeeyah ba karamin tashi yayi ba, dan tasan tayi miya da naman saniya, ganda da na kaza,



Wata siririyar ganda Faida ta dauko cikin stew din tace
"luckily an samu bpomo...



Jan kujerar Mummy tayi ta mike haďe da cewa
"Nagode, yunwar ma bata dameni ba,

Faidah zo ki siyo min Nama a waje,
tana kaiwa nan tace
"ina ne dakin da zan kwana?

Ko akwai BQ,
in akwai a kaini can in yaso da safe sai in nemi hotel kar in takura ma little da Amaryarshi... ta karashe dauke da murmushi a kan fuskarta,



"Wallahi ke da gidan danki babu abinda zaisa ki kama hotel,
Raudha ta faďi tana hararar Nadeeyah da Musaddiq,


"In ba rashin sanin darajar na gaba ba, ki dauko tafiya tun daga kaduna har nan amma ki tarar da abinci lami,
tsiyar ýaýan talakawa kenan, basu san inda suke nuna makonsu da tattalinsu ba,
Allah ya kyauta,



Hannun Mummy Radiya ta kama tace
"yi hakuri Mummy,
muje sama ki huta,
yanzu zan miki farfesu,

"a'a karku damu,
kuyi mata uzuri,
inaga ko taga naman ba yawa ne,


Gaban Nadeeyah taje wacce tuni hawaye ya jika gaban hijab dinta tace
"daina kuka yar albarka,
in banci nama yau ba gobe zanci,


Sake sunkuyar da kai Nadeeyah tayi tana jin wani irin zafi a cikin ranta kamar zata mutu,
tana jin su sunata maganganu har suka haura sama..



Kallon Musaddiq tayi wanda shi din ma ita yake kallo idanuwanshi jajur,
ya rasa inda zaisa abun da idonshi ya gane mishi yau,
ya jira ta kare kanta amma baiji ko kalma ďaya daga gareta ba,


Ashe haka kike?
Shine tambayar da zuciyarshi takewa tata,


Bai taba tunanin rashin girmama mahaifiyarshi har ya kai haka a gurinta ba,

ganin irin kallon tuhumar da yake mata ne ya sanyata takowa inda yake,
tsananta kukanta tayi wanda a lokacin ya ke ganinshi kamar na raini,
dan tasan baya son yaga hawayenta,

"ka yar-----

"Plss Nadeeyah ya katseta haďe da ďaga mata hannu,

juyawa tayi ta ruga daki da gudu tana kuka mai sauti sosai,
tana ganin sanda suka arta ciki a guje suna dariya...





Waiii...
lallai Faidah akwai kaifin tunani,
dama tace ke kadai ce zaiga an taba ya hassala,


Shhhhh....
Faida tace haďe da rage murya,

"bazamu taba kuskuren maida maganar nan ba sai ranar da aiki ya cika,
mistake kadan na iya watsa efforts din mu,



Bakinsu suka kama sukayi gumm suka cigaba da zaman tagumi suna jiran shigowar Musaddiq....





Sosai suka ingiza zuciyarshi, Mummy na tausarsu tana hawayen munafurci tace


"Ni ban san me nayi ma Nadeeyah ba,
iya kauna na nuna mata,
kowa yasan ajizancin dan adam ai, da sai tazo ta bani hakuri....



Naman da ya siyo ya ajiye mata ya tashi ya fita rai a bace najin har lokacin bata je ta bawa Mummy hakuri ba...





Koda ya shiga dakin kasa yi mata magana yayi ya faďa bayi dan watsa ruwa,


Kukan ta da yake ji har cikin bayin shi ya sake dungunzuma zuciyarshi,
"ita dadi ne ma yayi mata yawa,
ita ce tayi laifi kuma itace ta ke kuka,
yana fitowa ya sanya kaya ya dauki pillow ya kwanta akan kujera haďe da toshe kunnuwanshi,


Tafi awa tana kuka bai kulata ba, shima yin na zuci yake,


Ita kadai ce a duk duniya zatayi mishi abin da tayi ya kyaleta,
duk rashin fushinshi yakan yi action akan mahaifiyarshi dan yana matukar kaunarta kamar yadda take kaunarshi,,



Da yaji kukan yaki karewa ya mike ya dawo inda take,


"Ko zaki je daga waje kiyi kukan?
kinsan in dadi yayi maka yawa babu abinda bazakayi ba!



Kalamanshi sun sosa mata rai sosai tace

"Ka sakeni sai in tafi can wani guri inyi kuka na,


Kanshi ya juyar gefe zuciyar mai hakuri ta baci matuka,
murya a kausashe yace


"Sau biyu kenan kina furta min wannan kalmar,
dan kinga ina sonki, kuma kina ganin bazan iya rabuwa dake ba shiyasa kike threatnn dina da ita ko?


Cikin kuka sosai tace

"Ni dai bazan iya ba,
gara kawai mu rabu ko----

Wani mugun mari ya ďauketa dashi haďe da shake wuyanta,


"Gara in kashe ki nima in mutu da kalmar da kike son kasheni da ita,
samm baya ko ganin yadda ta rike hannunshi tana kakari saboda yadda idonshi ya rufe da bacin rai da hawaye,

Saida yaji tana wani irin kuka kamar mage tasha damka sannan ne jikinshi yayi sanyi ya saketa ya zauna a gurin yana rusa kuka,

"why did u want to lv me,
why?
Meyasa kike son gasgata mafarkina?


Duk da wuyanta na mata makaki hakan bai hanata sakkowa inda yake ba,

Tasan bata kyauta ba,
duk dan halak hakan zaiyi in yaga abun da ya faru yau,

wani ma zaiyi fin hakan,


Cikin jikinshi ta shige kamar mage ta kwanta haďe da rungumo wuyanshi tace
"am so sorry,
dan Allah ka yafe min,

Wata irin runguma yayi mata kamar zai maida ita cikinshi yace

"Dan Allah karki rabu dani,
no matter how hard tins are plss my love,

bata bashi amsa ba tayi kokarin sanya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login