Showing 87001 words to 90000 words out of 184071 words

Chapter 30 - ZUMUNCIN MU A YAU Complete By Aisha Yau Kura.txt

take,
duk inda yasan tana zuwa yaje ya duba shuru,

Allah kadai yasan inda ta shiga,


Itama Mummy ba karamin tashin hankali ta shiga ba,

saidai tasan bazata bata ba,
ta yiwu tana can tana kulle kullenta,
shiyasa ma ta kwantar ma Baffa da hankali...



A ranar da Mummy tazo gidan, ginin da akeyi har yakai linta,

aiki maginan sukeyi ba dare ba rana dan Papy baya son ginin ya wuce wata daya,


Tasha mamaki da takaici,
har ta dan yadawa Baffa habaici tace
"bari a gamawa amarya nima insa ayi ma Goggo irinshi,

karaff

kalamanta cikin kunnen Papy da ya doso kai zai shigo,

nunawa yayi baiji ba,
suka gaisa ya gama duba ginin, yaga komai yayi mishi yadda yakeso,

yana matukar son ganin Anni cikin jindadi shiyasa zai wadata ta da komai na bukata a cikin gidan,
ko gishiri baya fatan ta neme shi koda na second daya ne......



Bayan tafiyar Mummy Papy yace ma Baffa
"ko za'a fitar da kayan dakin Goggo sai ayi mata renovating in yaso itama sai a sake mata sababbi,

nan take Baffa ya saki murmushi,
guilt din da Mummy ta tafi ta barshi a ciki ya sakeshi,


Albarka ya shiga sawa Papy kamar zai ari baki,
farin cikin da yake ciki a wannan lokacin ba mai misaltuwa bane,
ashe akwai ranar da zaiga danshi namiji har ya dauke mishi nauyin abu mai girma haka,

alhamdulillah ya dinga jerowa babu adadi...



Washe gari ko Mummy Baffa bai fadawa za'ayi aikin dakin Goggo ba,
da kanshi ya cire kayan da yasan masu muhimmaci ne sauran yasa aka fitar dasu zuwa bola,
duk wani takarcenta da take yawan ce mishi maganin basir,
hawayan jini da na neman budi,
duk ya zubar dasu,


Gadonta mai runfa ya kira yan gwangwan suka tafi dashi,

abubuwan da suka fado daga saman gadon Allah yayi yawa dasu,
ba tare da ya kula dasu ba yasa Garzali da sauran samarin suka tattaresu suka konesu tass,
harda dan akushin Goggo da ya fado kayan ciki suka far fashe.....


*(shin ina Goggo take ake yi mata wannan ta'asar,)* abeg ummu iman nd Siyama help me luk fr her... ku hada kudi kubawa Meelah ta nemo ta...






Yagar naman farfesun kazar dake gabanshi yayi da sauri hade da kara wayarshi a kunnenshi,

"yes Mum,

daga daya bangaren Anty Reemah tace
"Hilal har yanzu baka wuce Abuja ba?

"on my way mum,
meyasa kika damu, 6pm ne fa jirgin zai tashi,

"dis is madness Hilal,
hanyar taka ce,
pass 3 yanzu kana da assurance din kaiwa Abuja 5:30 or 40,
ka maida hankalinka dani wallahi,
wannan ai iskanci ne,


"ohhhh calm down sweet heart,
tare da little kaninki zamu tafi,
ni zanyi driving, sai su dawo gobe da Malam Ali,


"cikin sarkewar murya tace "ban yarda ba,
karka soma yin wannan mahaukacin tukin naka,
maza ka bani Malam Ali!

"ummmm am nt a kid anymore haba mana,
ki bari pls kar kisa a raina ni,
in shaa Allah your Mukhtar will come home safe nd sound,
kiyi min addu'a,
yana kaiwa nan ya kashe wayar gaba daya dan yasan bazata fasa kiranshi ba, sai ta jishi a jirgi zata hakura...



A gaggauce yayi sallama da Mummy suka fito daga parlon lokacin da sukaji horn din Malam Ali,


Husnah na hangoshi ta rugo da gudu ta karbi jakar hannunshi ta turo baki,

"yanzu zaka tafi?
haba my PP,
shikenan da bamu dawo ba bazaka jiramu ba,


Bakin yaja yace "oya kara turoshi shi gaba,
dariya tayi sosai tace
"Allah da gaske da ka tafi baka jirani ba ko waya ka kirani bazan dauka ba,


Gurin motar suka karasa yace "dama nayi niyyar baki wata kyauta,
na fasa..
leda ya mikawa Nadeeyah dake tsaye tana murmushi,
"amshi wannan ke,
Husnah ta lashe,

Tura daya ledar cikin motar yayi yana dariya,

bude motar tayi da sauri tana fadin
"sorry my pp,
dauko ledar tayi cike da kosawa ta fito da abun dake ciki,


waya ce sabuwa dal mai tsadar gaske,

wani irin ihu ta saki tana fadin "thank u yaya Hilal,
u are the best,


Da kafada Musaddiq ya zunguri Nadeeyah dake tsaye kamar statue, murna ta hanata magana,

kallonshi tayi zatayi magana, yace "ke bazakiyi godiyar bane,
oya say it out kema,
*Yaya Hilal u are the best*,
yadda yayi da murya kamar mace yasata sakin dariya sosai harda rike ciki,
shima dariyar yakeyi,


Duk wannan abun da sukeyi a kan idon Badar da ta shige ciki tun shigowarsu gidan,
dakyar ta iya danne tukukin da ya yaso mata, ta saki labulen windon da karfi,


Shi kuwa Hilal tsintar kanshi yayi cikin nishadin ganin dariyarta mai kayatar dashi,

wani masifar sonta ke ratsashi kamar dama a cikin jininshi akayi halittar son,

ya shagala sosai cikin farin ciki shiyasa baiji muryarta tana mishi godiya ba,

tabo shi Husnah tayi tace
"Ana maka magana,

kallonta yayi ya saki dan murmushin da ba kowa ke ganinshi ba yace

"never mind, ki godewa Allah, nd ki kula da karatunki,

murmushi tayi tace "inshaa Allah, Allah ya kiyaye hanya ka gaida min da kowa da kowa,

gyada kai yayi suka shiga mota yaja suka wuce,
saida suka fita a gate din sannan ya iya maida hankali kan tukin da yakeyi,

gaba daya jikinshi yayi sanyi,

gani yakeyi kamar wannan rabuwar da zaiyi da Nadeeyah itace rabuwarsu ta karshe,

"ko dai mutuwa zanyi,
saurin taka burki yayi saboda yadda tunanin yazo mishi,


kashe motar yayi yace "malam Ali dawo ka tuka,
ya bude baya ya shiga malam Ali yaja suka wuce,


Har suka isa Abuja ya rasa asalin abin da ke taba zuciyarshi akan Nadeeyah,


Addu'a kawai yayi na Allah kar ya kawo sanadin da wani zai zo ya kwace mishi ita,

badan yanada abubuwan yi ba da ya dawo nigeria har ta gama secondary school ya sama mata university a cyprus,

cikin damuwar da ya rasa dalilinta yace
" in shaa Allah tana gama school nan da 5month zai dawo da ita cyprus,
gara tana gabanshi,
hakan kadai zai hutar da zuciyarshi,
zai cigaba da tunasar da ita muhimmacin karatu har ta gama secondary...


Text ya tura cikin layin da ya sai mata..



*Kyawun alkawari cikawa, Dan Allah ki kula, ki maida hankali kan karatun waec, nd ur line ya zama personal, kar ki bawa ko wani namiji ko macce numberki sai wanda ya zamto shakikinki, take care*....





Husnah na miko mata wayar bayan ta gama setting dinta,
text din ya shigo da sunan

*Arc Kangiwa*

karanta text din tayi hade da murmushi,
saboda sabo da rike wayar Husnah yasa ta iya wasu abubuwan,
reply tayi mishi



*In shaa Allah will keep my words,
Allah ya saka da alkhairi thanks for caring*



Yana gama karanta reply dinta ya ajiye wayar,

inama zai iya ce mata
*I love you*


Yana matukar son ganin reply din da zai hana mishi sukuni ya sanya shi yawo cikin sararin samaniya kamar yadda jirginsu zai lula,


saidai kashh..
bazai iya ba,
domin tanadin da yayi wa soyayyarsu ba na yanzu bane,

sai ta mallaki dukkan hankalin kanta,
sai ta koyi duk wasu nau'ika na soyayya,

yana son yin soyayyar da a tarihi ba'a taba samun kamarta ba,

cije lebe yayi domin hango yadda zai maida ita sarauniyar shi,
kuma sarauniyar matan duniya....



*(A bari ya huce)*.....
🤪😜😝




*MAFARI* ......
*(kauna)*



*Shin so samu ne*

Nidai rubutuwa nakeyi,
mijin Nadeeyah na cikin ukun nan,
Allah ya riga ya zaba...
muje zuwa a Mafari....



*Team Hilal*
*Team Diku nah*
*Team Taheer*






Mrs Tijjani Shattima......
[01/04 3:08 PM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣9⃣
By *Aysha Ya'u kurah*






*MOROCCO*


Kuka sosai Shareefa keyi tana kwala kiran Doctor,
Doctor....


kokarin cire oxygen din Ummu Ayyu takeyi hawaye na tsiyaya ta gefen idonta,
hannunta Sarki Tidjani ya rike yayi saurin maida mata oxygen din,
girgiza kai ta shiga yi hawaye na tsare da dan uwanshi,

Allah kadai azabar da mai rai yakesha yayi da yazo gangara,
dago idanuwanta da suke lumshewa tayi tana musu alama da akwai abin da takeson fada musu,

zuwan doctor ne ya sa suka matsa gurin suna kuka dukkansu babu mai ba wani hakuri,
ganin Doctorn na girgiza yana cire oxygen din ya sanya Shareefah matsowa a gigice tana tambayarshi,
bai ce mata komai ba ya zagaya ya cire drip din da ke taimaka mata ta samu karfi a jikinta,
bin bayanshi Shareefah zatayi taji hannun Ummu Ayyu ya riketa,
damke hannun tayi cikin kuka tace
"Kiyi hakuri ummu na,
nasan zai canza miki magani ne,
bari in tambayeshi,
tari ummu ta fara yi da karfi tana fadin
"a'a, ki tsaya a nan in cika a gabanki,
shima likitan yasan rayuwata yanzu bata da wani sauran amfani,
amfaninta a gareni da Allah bai dauki raina ba ya barni in sanar miki da sirrin da ya dade a rufe,

gyara zama Shareefah tayi tana sauraron mahaifiyarta,

Shareefah.....

ta fadi a wahalce saboda fitar maganar ma wahala ce a gareta,

"na aikata abubuwan da ban taba tunani akansu ba,
na aikata abubuwan da rana irin ta yau bata taba zuwa min a kwalkwata ba,

*YAREEMA*....

*YAREEMA A....DA....*

nan ta shiga tari sosai har tana jirkitowa daga kan gadon,

kuka mai karfi Shareefah ta fashe dashi tana kallon Doctor dake tsaye yana monitoring heart beat din Ummu,
doctor help me,
kayi wani abu dan Allah,
girgiza kai yayi yace
"babu abinda zaiyi amfani a wannan ranar Shareefah,
not even power,
just listen to her before its late,
"may be what she is going to tell u will be a relief to her,

hannun Tidjani ummu ta kamo tace
" *HAJJA*,

*RUGAR HALDON SASSOUNBOROUN*

ku nemi Hajja yar Riga,
zata fada muku komai game da

*YAREEMA... AD...*

kasa karasawa tayi saboda yadda tayi wani tarin da ya hado da gudan jini,
nan ta shiga fisge fisge suna danneta suna kuka sosai,
murya can kasa take cewa

*da na sani, da na sani, na cuci ka....ina*

kalmar da dunga fada kenan har ta cika da ihun da ya ratsa ko ina a cikin katafaren asibitin.....


*(Shin masu zalunci basa tuna wannan ranar, ranar da babu wani wanda zai iya taimakonsu, ranar da babu wani sauki sai saukin Allah da na abun alkhairin da ka shuka, shin in ka shuka tsiya baka tunanin wannan tsiyar ta zame maka kaya mai nauyi ranar da rayuwarka zata zamo ba taka ba, shin menene kazantar duniya da zata sanyamu mu dinga kauce hanya har mu dauki nauyin hakkin wasu muyi dakonshi, rayuwa kalilan ce, wallahi tsakanin mutuwa da rayuwa kamar kiftawar ido ne, yanzun nan komai na iya canzawa, dan Allah yan uwa ko me zamuyi mu tuno da wannan ranar, ranar da take tafe ga dukkan wanda yake numfashi a doron kasa, ba'a dauketa ga kowa ba dukkanmu zamu tafi, Allah kasa mu cika da kyau da imani)*........






********

Orange rigar da ta saba bacci da ita ta dauko ta saka ta sanya bakar hula,

minti minti ta duba wayar da ta barta a gida ta dawo ta tarar babu missed call da text ko daya daga gurinshi,

abin da bai taba faruwa ba tun da ya bata wayar,
dauko wayar tayi ta hau kan katifar da aka siyo dominta ta fara dannata,
tunanin tura mishi text takeyi taji ko lafiya,
lallai sabo turken wawa,
tayi matukar sabawa da ganin sunan *Arc kangiwa*
a cikin inbox dinta,
har ta rubuta text din, ta kasa turawa tanata juye juye da wayar a hannunta,


karar wayar yasata bude ido da sauri dan ta dauka shi ne,
ajiye wayar tayi kirjinta na duka saboda dadin da taji na daukar shi ya kirata,
saida wayar ta kusa tsinkewa lokacin ta saisaita kanta tayi saurin ďauka

"Kin kwanta ne?

"Ummm ta fadi kamar da gaske baccin takeyi,

"shikenan ya fadi kamar abin tausayi,
dariya tayi tace
"idona biyu kana san wani abu ne?

"Nidai na gaji..
zan bar gidannan,
shikenan ku dan kunci abinci baku damu da nawa cikin ba,
ki kwanta kawai ya karashe hade da kashe wayar,
yaye abun rufarta tayi ta kalli Husna dake dariya da waya a hannu tace
"muje kitchen pls,
bata kalleta ba tace "muyi me?
irin kallon da Badariyya ke mata yasa ta kasa bawa Husna amsa dan kar ta ambaci sunan Musaddiq ta fada mata bakar da zata hanata bacci,

ficewa tayi a dakin ta wuce kitchen,
tuwo ta gani guda biyu a cooler Daddy,
har ta fara zuba mishi ta tuno baya san tuwo,
gas ta kunna ta dafa mishi indomie da fish source din dake fridge,
tana gawa ta soya mishi kwai ta kai mishi kan dining,
dakinshi ta wuce ta fada mishi abinci na kan dining,
da sauri ya tsayar da ita ya dauko coke mai sanyi a fridge dinshi,


Zama yace tayi ta tayashi hira,
bata mishi musu ba ta zauna,


kallonshi takeyi yana cin abin kamar wanda yunwa ta gama cinyeshi,
dago ido yayi suka hada ido tayi dariya hade da sunkuyar da kanta kasa,

shima dariyar yayi yace
"kallona kikeyi ki gama kwashe rahoton yadda nake cin abinci ko, zaki sani,

dariya sosai tayi tace "wa zan fadawa in na kwashe,
saidai in barshi a cikina duk ranar da na hadu da matar da zaka aura, labarin cikinka zan fara bata, dan in bata kula dashi ba akwai matsala,

dariyar shima yayi yace
"ai basai kin fada mata ba,
day 1 zan fada mata,
tayi wasa da komai banda cikina, har saima na jira wani ya fada mata,

dariya ta sakeyi, kafin tayi magana taji ya dauki waya shima yana dariyar,


"Main man, how far,
hope ka kwashe, nasanka da kwashewa,

tsaki Hilal yayi yace
"Duniya ba gaskiya Musaddiq,

kasan na baka labarin Irfan da yake san cutar mahaifinshi,
to yau throughout muna tare,
saboda naki amincewa da bukatarshi,
kuma na rubuta letter zuwa company akan wannan business din fake ne, yau saida guy dinnan ya kusa kasheni,

Allah ya taimakeni da Meerah muka tafi,
ita ta kira police suka tafi dashi, but alhamdullilah..
anyi bailing shi dan kar Babanshi ya sani amma i promise not to work der again,
bana son abun da zai kara hadani da Irfan,
nd sai na nemi mahaifinshi na fada mishi irin cutar da suke mishi a companynshi,


Ajiye cokali Musaddiq yayi yace
"gaskiya gara kabar aiki a gurin,
kar yazo da tsautsayi wata rana,

dan ma kai ya samu,
da su mune ai sai dai mu kusa kashe shi,

"gerraut Hilal ya fadi yana dariyar da tunda ya dawo baiyi ta ba,
dariya Musaddiq yayi yace
"ka fa raina ni,
irin girman uban nan ma baka bani,
bakomai yaran zamani,
sai da safe,

sosai Hilal yayi dariya harda kyakyatawa ya kashe wayar dan kar Musaddiq yasa cikinshi ya murda,
shiyasa in ya shiga damuwa mutum na farko da yake fara kira Musaddiq ne,
dan yakan mantar dashi damuwa,
haka shima Musaddiq Hilal yana solving ko wani irin problem dinshi,
saidai in bai fada mishi ba,
yana gama cin abinci ya kalli Nadeeyah dake kokarin tashi yace
"ina zuwa?


"Bacci nakeji ta fadi kamar zatayi kuka,
"ni kadai zaki bari a parlor, ya fadi yana kwaikwayonta,

Murmushi tayi tace "dan Allah kaje ka kwanta kaima,

"To miss problem solving,
thank u,

dariya kawai tayi ta wuce daki,


Daddy dake tsaye yana kallonsu daga sama ya wuce daki zuciyarshi cike fal da farin ciki da tunanin Allah yasanya abinda zuciyarshi ta kitsa mishi ya tabbata,

hango futurn danshi yayi a tattare da Nadeeyah,
ita kadai ce macen da ta dace da yanayin rayuwar dan da ya tashi cikin taron mata cike da rauni kuma a sangarce,

badan Hilal dake sanyashi a hanya ba, yasan da Musaddiq ko sanin menene kalmar Namiji bazaiyi ba,

Addu'a sosai Daddy yayi na Allah ya tabbatar da tunaninshi kuma ya sanya ta zamo alkhairi a gurin danshi.....






Kasar Nigeria,
kasar who u knw ba what u knw ba,

washe gari tun safe Daddy ya kira abokinshi GMD din NNPC towers dake Abuja,
bayan sun gaisa suka dan taba hira,

kafin Daddy ya gabatar da bukatarshi Dr Barau ya rigashi da cewa
"Musaddiq har yanzu bai gama servn ba?

"saura watanni in shaa Allah Daddy ya bashi amsa yana dariya,

"okk to ba matsala gobe akwai yara 6 da za'ayi ma interview a

*EXXONMOBIL*

ka turomin shi sai su hadu su 7,
in ya karbi nysc cert dinshi sai a hada a cikin takardunshi,

cike da farin ciki Daddy yace "ina ne Exxonmobil kuma?


Dariya sosai Dr Barau yayi yace "Nigerian EXXONMOBIL, Oil nd gas company ne,
American multinational oil nd gas cooperation,

yanzu ake daukar yara,
so gara yaran mu su samu tun yanzu, kaga nan gaba sun dade a ciki, lokacin da karfin mu zai tafi sukuma lokacin zasu mike,


Fadin irin farin cikin da Daddy ke ciki ba kadan bane,
dama kiran da yayi mishi kenan,
matakin farko da zai fara sanya Musaddiq zama cikakken mutum shine aiki,
in yaga ya fara samun kudinshi na kanshi zai nutsu sosai ya nemo girma ya daura ma kanshi,

godiya sosai yayi Dr Barau sannan ya kashe wayar,
Mummy dake tsaye da flask a hannu ya fada ma,
ita ma cike da farin ciki ta sauka kasa ta kira dukkan yan uwanshi ta fada musu,


Raudha dake lagos tasan in ne Exxonmobil,
dan haka ta fara koda gurin tana sanyawa Mummy shirin fara nemo mishi mata yar masu kudi ko sarauta,

dariyar farin ciki Mummy tayi tace
"ba sai kin fada ba,


Matar Little dina zata zamo yar gata gaba da baya,

yar da iyayenta basa kyashin kashe mata dukkan dukiyarsu,
yar da zata ayi aman kudi daga ko wani bangare,

biki ne wanda nake shiryashi tun kafin yau,

biki ne na garari.......




Mrs Tijjani Shattimah......
[01/04 3:08 PM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣8⃣
By *Aysha Ya'u kurah*



*Kaduna, Niger, Abuja, Nasarawa, direct,*

wani dan saurayi ke tsaye jikin zungureriyar mota yana busa taba yana fadin sunan garuruwan da zasu,
nan aka fara tururuwar shiga motar kowa na fadin inda zashi,


cike da hanzari ta karaso gurin motar tana fadin kaduna,
kallon motar saurayin yayi yace

"Baba motar ta cika saidai Ko zaki hau baya kan kaya, 

"karfe nawa wata motar zata zo to,  ta fadi cikin gatsali

"keeee

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login