Showing 147001 words to 150000 words out of 184071 words

Chapter 50 - ZUMUNCIN MU A YAU Complete By Aisha Yau Kura.txt

su Mummy,
a sannan ne Raliya take faďa mata Daddy ne ya hanata yace in tayi sai ya saba mata,
dafe kai Reemah tayi tace


"Daddy yayi fushi da yawa, wallahi ko maganar Mummy baya son ayi mishi,


"Addu'a kawai zamu cigaba dayi danni ita kadai ke bani tausayi ba su Anty ba,
dey deserve it... Raliya ta faďi rai a bace...

sun dade suna hira suna nemawa mahaifiyarsu mafita....







Kwanansu Sheik Uku suka shirya komawa gida da yan uwa dan suje suga inda yake,

kyautar ban girma yayi ma su Mummy wacce zata mantar dasu talauci na wucin gadi,
tayi murna sosai da wannan kyauta dan saida tayi kamar zata mishi sujjada,
har suka tafi baisan cewa Mummy matar Daddy bace,
ya dauka kawai a gidan take zaune, ya dai san yayar su Papy ce....



*Cyprus...*

Da yake mansion din Sheik yana da matukar girma hakan yasa ya kwashe dukkansu,
harda Husna da suka taho da ita dan ta haihu,
dadin duniya babu wanda bai jiyar dasu ba,
duk companies dinshi saida ya nuna musu harda na wasu kasashen,

Saboda murna ya cire wani babban companynshi dake Holland ya mallakawa Papy a matsayin gadon mahaifiyarshi,
sannan ya bawa Hafeez wani abun shima,
gaba ďaya ya kasa controlling kanshi akan zuri'ar yayarshi....




Kwanansu biyar a garin akayi ma Husna tiyata aka ciro mata baby girl saboda haihuwar tazo da Matsala,

lokacin su Daddy sun koma Nigeria,
murna a gurinsu ba'a magana saboda dama cikin na yawan bata wahala,


Papy da kanshi ya shiryawa Mummy tafiya dan taje gurin yarta taga jikarta,


Ita dai a kullum haushin kanta takeji na biyewa zuciya tayi wa Suwaiba abubuwa marasa dadi kafin mutuwarta,
gashi yanzu danshin su take raba taji dadi,
lallai da ta hana auren Hafeez da Husna da sai takaici ya kusa ajalinta,
kullum bata da addu'ar da ta wuce Allah ya dawo da Nadeeya cikin koshin lafiya dan danta ya samu farin cikin rayuwa,
a yanzu ko ita bata samu farin ciki ba 'yayanta su samu,
ta fahimci farin cikinsu shine nata,
ďan zaman da tayi da su Radiya ta fahimci cewa ba kowani ďa bane ke sadaukar da farin cikin sa akan iyayenshi,
a nan ta koyi basu farin ciki,
in ta gansu cikinsa tasan itama zata kasance a ciki...






Ranar Suna Daddy ya sanya wa yar suna Suwaiba,
sosai dangi suka nunawa yar gata dan ta samu kaya na gani na faďa,


Mummy ta sake tsorata da ikon Allah da tazo taga daular duniyar da dangin Atika ke ciki,
inama Suwaiba na raye tazo ta dandani arziki,
wayyo,
ita nata dadin a lahira ta ďeboshi.....





Na fa lura da wani abu Anty,
Raliya ta faďi tana sanyawa Nour ďiyar Husna pampers,

"Me fa?
Anty Reemah ta tambaya haďe da gyara zama,


"Na kusa yin siriki, Raliya ta faďi tana murmushi..


"Wa kenan??


"Dadina dake ganewa Anty Raly,
Husna ta faďi tana ajiye kofin shayi,
ni ai tun tuni na sani,

Jamal ya hanani faďi,


"Kaii nifa ban gane ba,
wai me kuke nufi?
Anty Reemah ta tambaya cike da mamaki,


"Y'ata ta wajenki tayi kasuwa, soyayya sukeyi da Jamal,

Mikewa Anty Reemah tayi tace
"to ai ba sai kun faďa min ba, kuma iyaye ne,
in akwai alheri Allah ya tabbatar...



Dariya sukayi haďe da tafawa suka ce Ameen Ameen,
ashe zamu sha biki...


Hinad da ta doso dakin ta juya da sauri ta nufi waje cike da murna,
tasan tunda Anty Raly tasa baki Allah ya kusa cika mata burinta,
soyayyar Jamal ta zame mata tamkar jini da hanta,
bata jin akwai abin da zai cire mata sonshi cikin ranta,
kamar shima yadda Jamal din keji game da ita saboda kyawawan dabi'unta,

zuwanshi kasar yasake sanya shakuwa mai karfi a tsakaninsu, wacce har ta sa aka fara diga ayar tambaya akansu.....






Zaune suke a katafaren parlon sama suna duba ayyukan da gwamnati tayi approving,


Zanen da Hilal yayi wannan karan na musamman ne,
cike da yabawa sheik ya kalli zanen karshe yace

"Bravoo alaika ya Hilal,
Allah ya albarkaci hannunka,
yanzu kaga sai dai kawai mu fidda kudi a hau aiki,

Murmushi Hilal yayi zaiyi magana Irfan ya faďo parlon babu ko sallama,
kusa da Sheik yaje ya zauna haďe da faďin

"Masa'ul khair Aby,

kallonshi yayi sama da kasa yace

"uhummm,
kudin naka sun kare kenan,
sosa keya yayi yana hararar Hilal yace
"Eh,
akwai wani business da nasa kudi na,
inaso inyi clearing ne bani da cikon kudin,
20mill ne kawai,

"I struggle to get 5 thousands aday nd u are calling 20mil only,
it's well dear,
zanyi maka addu'a Allah ya baka,

Lokacin da na kiraka ina farin cikin ganin yan uwana kaima kazo su ganka kazo?

Kayi ignoring dina so yanzu ni bani da abun yi maka,
yana kaiwa nan ya kalli Hilal yace

"My dear gobe ka sameni a office sai mu fara shirye shirye ko?

Cike da girmamawa Hilal yace

"Okay sir, Allah ya kaimu...


A tare suka mike Sheik ya raka Hilal har kasa sannan ya wuce dakin da Husna take dan duba lafiyarsu...




Rike gaban rigarshi yayi saboda jin shakun da akayi mishi ta baya, yana da tabbacin Irfan ne dan irin kamshin turarenshi ne ya cika gurin,
ganin yana daďa tamke shakan yasa Hilal yanka rigarshi ta gaba saboda ta kama wuyanshi sosai,

iya karfinshi ya sanya ya cire hannun Irfan haďe da hankaďa shi baya.


Taba wuyanshi yayi yana tari kaďan,

saurin rike hannunshi yayi dan kare kanshi murya a kausashe yace

"Wai menene?

Fisge hannun Irfan yayi ya nuna shi da yatsa..
warning mai karfi ya karta mishi na kar ya sake taka kafarshi cikin gidannan in ba haka ba wallahi sai yayi ajalinsa,


Dariya Hilal yayi yana gyara singlet dinshi zaiyi magana yaji muryar Maleekah a bayanshi,


"Hey akan ka yake?
In yazo gidan nan gurinka yazo?

Kayi aikin gabanka ka bar kowa yayi nashi tunda gidan ba naka bane kai kaďai!



Cikin zafin nama ya shako wuyanta dama yana da cikinta na yadda yake ganin an barta tana facaka da kuďi ba tare da an sa mata ido ba,

sakin keyn motarta tayi saboda azaba tasa hannu tana kakari,


Hannu Hilal yasa ya banbareshi a jikinta haďe da shake mishi nashi wuyan da karfi,

naushi mai karfi Irfan ya sakarwa Hilal a ciki da gwiwar hannunshi,

da sauri ya sakeshi ya durkushe rike da cikin saboda azaba,
gaba daya jikinshi ya dau rawa dan jin ciwon yake har tsakiyar kanshi,


ihuu Maleekah ta saki tayo kanshi ta hankaďe Irfan dake kara tattaka cikin Hilal,
girman gidan baisa kowa yaji ihun ba sai maigadi,
lokacin da ya iso har Hilal ya gama fita hayyacinshi,
cikin kuka tace ma mai gadin ya kira Abbu,
a ruďe ya nufi cikin gidan,
a parlon kasa ya samu Abbu ya fito daga ďakin da Husna take, yana ganinshi yasan ba lafiya,


Nufar gurinshi yayi a tsorace yana tambayarshi abun da ya faru,
bai jira ya gama faďa mishi ba ya fita tsakar gidan da sauri,

daga can gate ya hango motar Irfan sai horn yakeyi yana shirin fita,
inda yake jiyo kukan Maleekah ya nufa,
ganin Hilal a kwance yasashi yin gudu gudu dan ganin abinda ke faruwa,
cikin kuka Maleekah tace

"Abbu Hilal zai mutu,
plss help him,
daukarshi Sheik yayi cikin tashin hankali yana tambayarta abinda ya faru,
bata iya bashi amsa ba ta bude mishi motarta ya sa Hilal a ciki shima ya shiga,
rufe motar tayi ta shiga mazaunin driver ta figeta da gudun gaske...




Asibiti mafi kusa suka je,
lokacin da suka isa Hilal na fitar da numfashi dakyar,


Saboda gigita Sheik baisan takalmin kafarshi ya fita ba,
suna shigar dashi nurses suka shigar dashi emergency,
da sauri likita ya iso gurinshi da taimakon gaggawa,
Allurar pain relief sukayi mishi kafin su gano abun da ya sameshi...




Rungumeta yayi a jikinshi yana rarrashinta,
labarin abinda ya faru take bashi cikin kuka tana zagin Irfan,


Cike da tashin hankali ya zaro wayarshi ya latsa number Irfan,
a kashe yaji ta yayi kwafa haďe da saka abubuwan da zai mishi in Hilal yaji sauki....




Allah ya taimaka babu abin da ya samu Hilal,
zafin buguwar ce ta sanyashi fita hayyacinshi,


Hamdalah Sheik yayi suka nufi ciki gurin Hilal, bacci suka sameshi yana yi hankali kwance,


Zama kusa dashi Maleekah tayi ta kama hannunshi tana murzawa a hankali,
sai a lokacin sukayi tunanin kiran su Papa faďa musu....





Hakuri sosai sheik ya bawa su Papa ya kuma yi musu alkawarin hukunta Irfan hukunci mai tsanani,


"Ah haba,
yarinta ne,
dan Allah ka kyaleshi,
wata rana bazai yi ba,
Allah ya rubuta sai yayi ciwo,
Irfan sanadi ne kawai,
mu dai cigaba da addu'a Allah ya shirya mana su,
Papa ya karashe fuskarshi dauke da murmushi...


Jin shi kawai sheik yayi dan ya riga ya kuduri niyyar hukunta Irfan,
yadda yake jin Hilal a cikin ranshi baya san wani abun da zai taba shi.......





Karfe uku na dare Hilal ya farka daga baccin da ya samu,
Hinad dake zaune a gefenshi ta sakar mishi murmushi haďe da kamo hannunshi,

"Sannu Yaya, ya jikinka,
gyada kanshi yayi ya kalli Anty Reemah dake kokarin ďagashi zaune,
Karfi yayi da jikinshi dan kar ta wahala ya mike zaune haďe da jingina da pillow,

"Me zaka ci in kawo maka?

"Bana jin yunwa Mum,
ya bata amsa yana yamutsa fuska,


"Ai ba dan yunwa zaka sha ba, haďa mishi tea,
papa ya faďi yana miko mata flask...


Tea mai kauri ta haďa ta mika mishi ya fara sipping a hankali,

Buďe kofar su Sheik sukayi, hannun Maleekah rike da wata leda,

"Alhamdulillah, Sheik ya faďi yana nufar inda Hilal yake,

"Are u okk My son?
Murmushi Hilal yayi yace

"yess sir, karka damu, da kun tafi gida dare yayi...


"Nooo dole mu zauna muga yanayin jikinka,
kayi hakuri Hilal, in shaa Allah sai na dau mataki akan Irf---

Plss sir,
Hilal ya katseshi haďe da rike hannunshi
"wallahi na yafe duniya da lahira, kaddara ce,
tana kan kowa, haushina yake ji yanzu, with time komai zai zama normal..



Cike da so da kauna Sheik ya dinga yi ma Hilal godiya da fatan samun lafiya dawwamamma...




Kofin dake hannunshi yake kokarin ajiyewa saboda yadda Maleekah ta kureshi da ido,

kallon Anty Reemah yayi yace "Kuje gida i will be fine here, karku damu,
ina zee dina?



"Tana gidan Mimi Turaki,
can na sauketa dan kar ta haukace mana,
Meerah ma sai kira takeyi kasan dazu ta tafi Malaysia..
Anty Reemah ta bashi amsa tana gyara zaman hijab dinta..


"Yess ta faďa min,
Allah ya maidota lafiya,
plss kuje gida,

Maida dubanshi gurin Sheik yayi shima ya rokeshi da su tafi kar su matsawa kansu,
haka duk suka shirya tafiya dan sunga lafiya ta samu a gareshi...




Chips da chicken salad Maleekah ta buďe ta ajiye a gabanshi ba tare da tace komai ba,
bin bayan Sheik tayi dan tasa shi ya jirata,
tana ganin motar su Anty Reemah ta bacewa ganinta ta fito cikin motar tace mishi tana zuwa,
da yake su larabawa babu ruwansu da bin diddigin 'yayansu in suka yarda dasu sai ya kwantar da sit cikin rashin damuwa ya lumshe idonshi....





A rufe ta samu chips din ta sake budeshi har lokacin da zafinshi,
gefen gadon da yake zaune ta zauna ta buďe tana kallonshi,
ita yadda yake rufe ido ma dariya yake bata,
shi a dole bai san haďa ido da ita,


"Ya Hilal,
ta faďi a saitin kunnenshi,

da sauri ya buďe idonshi dan muryar Nadeeyah yaji,
bashi da dabarar dauke idonshi cikin nata domin kallon da yake mata na daban ne,
yadda ruwa ya kwanta a cikin idanun suka sake kayata kyawun idanun su suka tsuma Maleekah ta ajiye chips din ta kamo hannunshi,
wannan wace irin masifa ce,
a yanzu gaba daya zuciyarta da gangar jikinta sun gama na'am da cewar tana son Hilal kuma tana son karasa rayuwarta tare dashi,

" *I LOVE YOU*

cikin narkakkiyar murya kalmar ta fito ba tare da shiri ba,


Runtse idonshi yayi hawayen dake kwance cikin idanuwanshi suka bayyana kan yalwataccen gashin idonshi..


zuciyoyinshi ne suka shiga kara kainin bashi shawara,
wannan tace
"Allah ne ya dawo maka da Nadeeyah ta wata siga,
wannan yace
"Duk wanda yaso Nadeeyah to ko bazai ki Maleekah ba,
haka nan sukayi ta rikirkitashi...


Bai ankara ba yaji kwanciyar fuskarta kan tafukan hannunshi,
hawayen da ya ďigo a kansu shi ya sanyashi buďe ido da sauri haďe da ďago fuskarta,


Share mata hawayen ya shiga yi zaiyi magana tayi saurin shigewa cikin jikinshi,


"Plss don't say a word Hilal,
plss....
daureshi tayi da jijiyoyinshi kamar tasan abinda yake shirin faďa,
har ga Allah baya kin Maleekah domin wani sashi na zuciyarshi yayi na'am da ita,
saidai sashin da ya mutu da wata soyayyar daban yaki aminta ya farfaďo,
baya tunanin har ya mutu zai iya son wata 'ya Mace kamar yadda yaso Nadeeyah,
ya zame mishi dole ya amincewa Maleekah domin ya daina jin abinda a kullum yake yunkurin mantawa dashi,


Hawayen dake cikin idonshi ya ďigo a kan fuskarta yace

"I love you too Maleekah......





Mrs Tijjani Shattimah.....
[09/06 11:14 AM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 7⃣0⃣
By *Aysha Ya'u kurah*




Eidukum mubaarak wa aiyyamakum Sa'eedah taqabbalallaahu minnaa wa minkum,wa kullu aamin wa antum bi khair. Eid-el Fitr Mubarak.

Allah ya maimaita mana Ameen.....




Sake kankameshi tayi cike da jindadi tace
"nt too,
i want u to love mee more nd more,

Murmushi yayi haďe da dago fuskarta yace
"Will u teach me how to love u more more more?

Hannayenta ta makalkale a wuyanshi  tace
"we will love each oda more than life itself,

ďaura kanshi yayi kan goshinta yace
"Dare yayi,
go home hoping to see yhu first thing in the morning..
narke mishi tayi tace

"Yaci abinci ko itama taki ci in ta koma gida,
hannu yasa ya ďauko chips din yace suci tare..

gyara zama tayi a kan gadon ya dinga bata a baki itama tana bashi,
duk wani nauyin da Hilal yake ji a cikin zuciyarshi ya ragu,
jinshi yakeyi kamar sabon mutum...

Saida suka gama ci sannan tayi mishi sallama haďe yi mishi alkawarin zuwa da sassafe.....






Cikin wata ďaya soyayya mai karfi ta shiga tsakanin Maleekah da Hilal,
tun yana jin sonta kaďan kaďan har Allah ya jarbceshi da muguwar soyayyarta, domin ita ďin gwana ce gurin sace zuciya,

Wannan soyayyar da sukeyi Sheik jinta yake duniya Allah ya gama mishi komai da ya bawa yarshi mutum irin Hilal,
jira kawai yake yaji ta bakinsu ya shirya komai cikin kankanin lokaci dan bazaiso yajashi ba saboda masu kawo mata hari kar su hure mata kunne,
shi ko yanzu ne yake jin dadi saboda zai samu surukin da zai iya barwa ragamar dukiyarshi ba tare da tunanin komai ba,

Su Papa kuwa gani sukayi tafi karfinshi saboda Sheik ba karamin mutum bane,
sai da Sheik ya nuna musu bacin ranshi sosai saboda banbanta kansu dashi da sukeyi....


A ranar da Maleekah taje mishi da maganar yayi matukar farin ciki,
nan take ya kira Daddy da Papy ya sanar dasu sannan yace basai kowa yazo neman aure ba domin Hilal nashi ne,
sati biyu ya sanya bikin saboda bashi da wani shirin da yake dashi,

jin haka Jamal ya sanar da Papy wacce yake so domin a haďe auren gaba ďaya,

Farin ciki a gurin Anty Reemah ba'a cewa komai domin Allah ya gama mata komai,
ta samu nagartattun surukai wadanda zatayi alfahari dasu...

*(wannan shine result of kyakykyawar zuciya)*



********

Tun ana saura sati ďaya biki Maleekah da kawayenta suka fara shagalin biki,
abinka da yar drama,
babu inda labarin aurenta bai zaga ba,
daga mai kushe Hilal saboda bai kamo kafar samarinta a haďuwa ba, sai mai yabawa zarrarshi na samun Maleeka da maza kewa rububi,
babu wanda yasan abinda Allah ya ganar dasu ya sanyasu suke kaunar junansu sai su biyun da kuma wanda yasan waye *Hilal Kangiwa....*



*******

"Ya kira wayarta yafi a kirga bata ďaga ba,
tun yana kira cikin marmari har ranshi ya baci ya ajiye wayar a gefe,
duk yaji ringing sai ya dauka itace yayi saurin daukar wayar,
in yaga ba ita bace sai ya ajiye wayar ya saki tsaki,
rabon da ya sata a idonshi tun shekaranjiya da suka tafi Egypt yin wani bikin a can..
bai san fushi takeyi na kin binta da yayi,
taso su tafi bikin tare yaki, dan ya fi son yayi zamanshi yayi hidimarshi cikin yan uwanshi...





Karfe Sha ďaya ya kira layinta na Egypt yaji shi a kashe,
hakan ya tabbatar mishi da yanzu ta shigo tunda jibi ne daurin auren,
Shiryawa yayi cikin kananan kayan sanyi masu taushin gaske,
yana matukar missing dinta dan ta koyar dashi soyayyarta mai sanyi,
gashi bai iya soyayya ba dan in yana yinta gaba daya zuciyarshi yake sallamarwa wanda yake so...

Saida ya biya ta wani gift shop ya siyo mata wani abu dan yaji dadin bata hakuri...




A kofar gida ya sameta tare da kawayenta tana musu sallama,
cikin shigar da yake matukar so ya sameta, jallabiya har kasa da gyalenta,



Cikin gidan ya shigar da motarshi ya fito ya tsaya haďe da harďe hannu yana jiran dawowarta,

Minti biyu kaďai ta kara tazo tana shirin wucewa ciki,
kallo ya bita dashi har ta kusa yi mishi nisa,


"A wife is angry wit her Hubbi!!, ya faďi cikin wata irin muryar da baisan yana da ita ba,

Duk da taji sanyin jin muryarshi da kuma sunan da ya kirata dashi hakan bai sa ta tsaya ba,

“Getting angry doesn’t solve problems,

"Ana Aseef  “ya Radhi’a”
plss don't be mad at me... 


Ajiyar zuciya tayi haďe da tsayawa zuciyarta na maimaita kalmar
*Radhi'a*
duk wani bacin rai da ta kunsa na tunanin Hilal baya sonta kamar yadda take sonshi ta kaudashi,

Sanyin dake kadawa a garin ya haďu da wanda ke kaďuwa cikin zuciyarta ya sanyata cikin wani irin yanayin da takeji tamkar su biyu kadai Allah ya halitta a duniya,


"plss my love, ya faďi cikin raďa a saitin kunnenta,

Lumshe idanuwansu sukayi a tare saboda qamshin da kowannensu ya shaka na juna,

a hankali ta juyo ta fuskance shi haďe da shagwabe fuska,
yadda ta turo baki yasan magana ce zata biyo baya,

Cikin sauri ya fiddo wata red flower dake makale a bayan wandonshi,

Saitin hancinta ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login