Showing 135001 words to 138000 words out of 184071 words
Chapter 46 - ZUMUNCIN MU A YAU Complete By Aisha Yau Kura.txt
Mahaifiyata,
yana kaiwa nan yabi bayan su Zubair zuciyarshi cike da tunanin maganganun Hilal,
A kofar da zasu fita sukaci karo da Abbati,
da sauri ya nufesu yace
"yauwa Musaddiq tun dazu nake kiranka,
fito da wayar Raudha yayi ya nuna mishi text din da sukayi tayi da Radiya a daren jiya,
sannan ya kare da cewa kar kayi gangancin yarda da duk da zasu ce maka...
Is too late Musaddiq ya faďi yana mai share hawayen da yaki tsayawa a idonshi,
yana hango Hilal na matsama Zubair ya tada motar yayi saurin cewa
"Kayi hakuri zamuyi waya,
yanzu zamu je nemo Nadeeyah ne..
bayanshi Abbati yabi da kallo cike da tausayawa yace
"Allah sarki, Allah ya haďaka da matarka,
Cikin parlon ya karasa kanshi tsaye haďe da sallama dan ba mutunci bane ya kawo shi.......
Kamar yadda su Musaddiq sukayi yawon dubata haka su Hilal sukayi,
ganin babu alamunta yasa Zubair bada shawarar kai wa gurin police,, dan su zasu fisu iya binciken,
Hilal da ya shiga cikin tunani yayi saurin cewa
"Muje gurin hotel din nan da akayi accident,
Baya Zubair ya juyar da motar yayi hanyar 3stars luxury hotel,
tun kafin su karasa gaban su ke dukan uku uku,
ganin babu kowa a gurin sai wani mai shagon provosion ya sa su tsayawa gurinshi,
Balle motar Hilal yayi ya fito ya isa gurin mai shagon,
a tsorace mai shagon ya arta shagonshi dan duk tunaninshi irin area boys dinnan ne masu mishi fashi,
ya fara zuge shagon kenan su Musaddiq suka karaso,
Hannunshi Hilal ya kama yace
"Akwai hatsarin da akayi anan, an ce mace ce?
Dan Allah macen yar budurwa ce ko babba?
sannan ko kasan asibitin da aka kaita,
ajiyar zuciya mutumin yayi cikin yaren yarbanci yace
"Na gode ma Allah,
cike da tausayawa yace
"yar budurwa ce, bazata wuce 18yrs ba,
ga ragowar kayanta can da wasu suka fara sacewa,
sannan ban san asib-----
kallo ya bisu dashi suna rige rigen buďe dauko kayan,
Wani irin ihu Musaddiq ya saki haďe da rungumar akwatin sosai a jikinshi,
"Wallahi itace,
itace,
Nadeeyah ce,
Rike Hilal Zubair yayi dan kiriss ya rage ya faďa cikin wata katuwar kwata saboda firgici..
"Wani ne ya buge wata yarinya,
kaii ta bugu, dakyar in zata rayu...
wadannan kalaman su suka shiga yawo a kunnen Hilal,
"Nadee-----
Ihun bayereben ne ya sanya su isa gurin da Musaddiq ya yanke jiki ya,
labarin irin hatsarin da akayi ya bashi wanda yayi sanadiyyar tsayuwar zuciyarshi na wucin gadi,
duk wani haushinshi da Hilal yake ji nan take ya kau ya dinga kuka yana girgiza shi,
kamashi sukayi suka sa a mota suka nufi asibiti dashi,
shi kanshi Zubair kuka yakeyi dan a rayuwarshi ya tsani ganin crisis din soyayya,
tunda ya gama university rabonshi da sake soyayya,
tashin hankali ya hanashi kallon Faida duk da yayi mamakin ganinta har lokacin ba aure.....
Mrs Tijjani Shattimah......
[25/04 10:21 PM] +234 807 161 1811: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 6⃣4⃣
By *Aysha Ya'u kurah*
Gado nurses suka fito dashi da gudu saboda yadda Hilal ya cika musu guri da ihu,
bayansu yabi yana faďin
"Dan Allah karka mutu ka barni,
am not angry with u anymore,
plss wake up Musaddiq,
Zuciyar Hilal gaba daya ta karye, abubuwa biyu a lokaci daya,
wanne zai dauka?
kuka sosai ya durkushe a kofar dakin da aka shige da Musaddiq ya keyi,
tsugunawa Zubair yayi yana bashi hakuri haďe da share nashi hawayen...
"She is no more Doctor,
we tried our best but we cudnt save her,
ya Salam Doctorn ya faďi haďe da dafe kanshi,
"ina wanda ya kawo ta?
"Ya gudu saboda ance ya kira police,
accident case ne kasan,
2 accident cases duka mata kuma duk sun rasu,
"Astagfirullah....
"dayan yaki yarda ta mutu,
he took her to another hospital,
i knw by nw ya yarda,
"ya bani tausayi sosai cos shima yadda yake ba cikakken lafiya ce dashi ba,
girgiza kai Doctorn yayi zaiyi magana Hilal yayi saurin rike hannunshi yace
"Dan Allah ka nuna min gawar wacce tayi accident din,
wani irin kallo yayi mishi haďe da cewa
"Who are u?
Cikin kuka Hilal yace
"Matar uncle dina ta bata, we found out that tayi accident nd bamu san inda take ba,
cike da tausayawa doctorn yace
"Muje may be ka ganeta a jiki ko kafa,
dan fuskarta tayi damage,
bayanshi suka bi da sauri suna fargabar Allah yasa ba Nadeeyah bace,
dakyar Hilal ya iya kallon matar
wacce ta ďan manyata..
ajiyar zuciya yayi yace
"Alhamdulillah ba ita bace,
Suna gab da fita daga dakin ya hango hijab din da ko a mafarki ya ganshi zai ganeshi,
hijab din da Nadeeyah ke yawan sawa a koda yaushe musamman in yana gidan saboda tsabar girmamashi da takeyi,
rarumo hijabin wanda ya jike da jini yayi ya rungumeshi a jikinshi,
"Doctor ina me hijabin nan,
ina take?
Nurse din dake biye dasu tace
"itama ta mutu,
wanda ya kawota ya dauketa yace bai yarda da aikin mu ba,
zai canza mata wani asibitin,
i told him komai nata ya daina aiki, yaki yarda,
nasan yanzu ya yarda,
Runtse ido Hilal yayi yana kuka haďe da yin dana sani kala kala marar amfani,
"Dana san haka rayuwarki zata kare so quick da ban bari son Musaddiq ya rinjayi naki a cikin zuciyata ba,
da nayi iya kokarin da zanyi in maidaki tawa,
da na girmama bukatuna akan nashi da har yanzu kina nan da ranki,
wayyo Allah na,
Allah yayi miki rahama Nadeeyah...,
Allah yayi haďaki da manzon rahama...
Zubair me rarrashi shima kukan ya zauna yana yi sosai,
Doctorn ne ya koma rarrashinsu haďe da basu shawarar su kira gida su faďi...
Wayar shi ya ciro a aljihu ya kira Anty Reemah,
ringing biyu yayi tayi saurin ďauka,
"Tun dazu nake jiran kiranka,
ya aikin ka kammala?
bai bata amsa ba sai sheshshakar kukanshi da taji,
Zaune tayi a gefen gado haďe da wurgar da rigar da ta dauko zata sa,
"Me ya faru?
"Mum Nadeeyah ta mutu,
sun kashe Nadeeyah,
sun kasheta...
"innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
ajiye wayar tayi tana ta maimaitawa tana kuka tana dadawa,
Hinad da ta jiyo ta tayi saurin katse wayar da takeyi da Jamal ta rugo dakinta da gudu,
"Allah ya jikanki Nadeeyah,
"Mum wacce Nadeeyar?
Hinad ta tambaya haďe da kwalolo ido waje,
Nadeeyah dai Hinad, Nadeeyarmu,
nan fa dakin ya gauraye da kuka babu mai ba wani hakuri,
Allah ya taimaka Zainab na bacci da abun sai yafi haka...
*Aboki Kangiwa*
ka shigo nigeria kenan,
Daddy ya tambaya cike da dakiya dan kar Hilal ya gane halin da yake ciki,
"Daddy Nadeeyah is no more,
Musaddiq ya saketa,
su Mummy sun koreta,
mota ta bigeta ta mutu..
Rike kirji Daddy yayi yace
"Karya ne Mukhtar,
dan Allah ka karyata kanka,
Nadeeyah na nan da ranta,
na faďa ma Musaddiq ya nemo min ita,
kuma wallahi rayayya zai kawo min yadda na bashi,
ba matacciya ba,
karka sake kirana har sai Musaddiq ya nemo min abin da na bashi,
cikin koshin lafiya na bashi ita, hakan nake son ya dawo min da ita,
"Shima yana tsakanin rayuwa da mutuwa Daddy,
dan Allah kazo,
wallahi Nadeeyah ta mutu..
kashe wayar Daddy yayi ya kifa kirjinshi akan pillow saboda raďadi da yake mishi,
kuka kawai yake son yi amma yaki zuwar mishi,
haka ya kwana da sake saken yadda zaiyi ya sanarwa da Papy abinda ke faruwa....
Da asuba ya daure ya kira Anni dan ita kadai ce wacce zata iya saita abun,
Anni ta girgiza matuka dan har hawaye sai da ya fito a idonta,
dakyar ta iya faďawa Baffa wanda ya rikice yana kuka haďe da sambatu sosai....
Papy kuwa tunda ya gama waya da Anni hankalinshi ya kasa kwanciya,
kiran Hafeez yayi yace
"ya shirya zasu tafi lagos ance Musaddiq ba lafiya, rai a hannun Allah,
Sosai Husna ta marairaice tana kuka saidai su tafi tare,
hakan kuwa akayi a safiyar suka yanki ticket dukkansu harda Mami,
kowa cike da fargabar abunda zai je ya tarar....
A airport din su Daddy suka jira zuwan su Papy dan su karasa tare,
Yanayin da Papy yaga Daddy ya ďaga mishi hankali matuka,
kusa dashi ya matso yace
"Kayi hakuri Alh Mukhtar,
cuta ba mutuwa bace,
in shaa Allah zai tashi,
kukan da Daddy baiyi ba jiya shi ya saki mai karfi haďe da rungume Papy,
share hawaye Anni tayi tace
"Mu karasa can asibitin dan Allah,
ba sai mun tsaya munyi magana anan ba...
jiki a sanyaye Papy ya kama hannun Daddy yana bashi hakuri har suka isa gurin motocin da abokin Daddy ya turo musu...
A kofar dakin da aka sa Musaddiq sukaga Hilal rungume da Hijab har lokacin idonshi na fitar da ruwa,
daga shi har Zubair babu wanda ya runtsa,
yana ganinsu ya mike da sauri ya rungume Daddy yace
"Wallahi Daddy sun kasheta,
Nadeeyah ta mutu,
muje kaji daga bakin doctor...
A ruďe Mami tace "Wace Nadeeyar,
sai a lokacin Hilal ya lura dasu,
nan wani sabon kukan ya kwace mishi ya shiga basu labarin abun da yaji da kunnenshi,
Abbati da ya kira Daddy yace su haďu a asibiti shima ya daura daga inda ya sani,
nan fa guri ya kaure da kuka,
sun ma manta a asibiti suke,
Jan Daddy gefe Abbati yayi yace "Ni yau zan koma india,
yara kuma sun wuce katsina,
na faďa ma Raudha in ta samu miji tayi aure,
kayi hakuri dan Allah,
Allah ya haďa mu da alkhairi,
Murmushin yake Daddy yayi yace
"Allah ya albarkaci rayuwarka Yusuf,
ai kayi kokari,
nagode sosai,
Duk da Papy na cikin tashin hankali hakan bai hanashi mikewa da niyyar yi ma Abbati magana ba,
rikeshi Daddy yayo yace
"Ya cika dan halak,
kowa hakan zaiyi in yaji abin da suka aikata,
"Dan Allah ka yafe min proff,
da sauri Papy yace
"Haba,
mu su waye da zamu tsallake hukuncin ubangiji,
itama lokacin da ta dauko kenan,
rayuwarsu ta jin daďi na gidan lahira in shaa Allah,
yadda ya karashe maganar cikin rauni ya sanya su sake wani sabon kukan,
Duk papy yadda yakai ga matsewa ya kasa saboda shima a karye yake,
nan ya zauna ya rufe fuskarshi yana kuka sosai,
a duk faďin gurin nan babu wanda yakeda karfin bawa wani hakuri.....
Reemah...
ki kira danki kice mishi ya dawo min da ďana,
tun daren jiya da ya daukeshi ya fita dashi har yanzu basu dawo ba,
ki kirashi ya dawo min dashi,
tunda shima yana san Nadeeyar in ta gama idda sai ya aureta kuje can ku karata,
tunda ke baki san ciwon kanki ba,
ki haifi ďa ya dinga juyaki...
Mummy na kaiwa aya Anty Reemah tace
"Ina airport,
danki yana asibiti, ďana bai kai ga yi mishi illa ba,
ita kuma wacce kika tsana din da zata dawo gidan duniya da babu abinda zai hana ban aura mata Hilal ba,
ai da nasan yasota tun farko da saidai Musaddiq ya hakura tunda shi matsayin uba yake a gurinshi,
saidai kashh...
yayi nauyin bakin da ya jefa rayuwar Nadeeyah cikin garari,
yanzu tunda kunyi sanadiyyar da ta zama gawa,
sai ku fara murna ku nema ma Musaddiq hurril aini,
tana kaiwa ta katse wayar cike da ďacin rai,
bata taba yi ma mahaifiyarta musu ba,
amma a yau ta kai bango sosai wanda har ya sata fadin maganganu cikin ficewar hayyaci....
A gigice Mummy ta nemi guri ta zauna tace
"Nadeeyah ta rasu,
innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
Raudha dake kiran wayar Abbati tana kuka tace
"Whatt...
ta rasu?
"Wallahi ta rasu,
yanzu Reemah ke faďa min, itama tana hanyar zuwa..
Daukar trolley Radiya tayi da sauri tace
"Nidai ba ruwana,
yanzu nan zan tafi gida gurin 'yayana,
Allah ya taimakeni Shamsu bai san labarin nan ba,
kallon Raudha tayi tace
"Allah ya daidaita ku,
Mummy,
na tafi kaduna sai kun karaso, tana kaiwa nan ta ruga da gudu da jakarta tana mai dana sanin biye ma zuciya....
A tsure Mummy ta mike ta kira wayar Mahmoud tace ya tambayar mata Zubair wani asibiti suke,
Mahmoud ya rude sosai ya kira Zubair dan jin abinda ya faru,
sunan asibitin kadai ya iya faďa mishi ya kashe wayar saboda tashin hankalin da suke ciki na cewa Musaddiq ya shiga Coma,
Kiran Mummy yayi ya faďa mata sunan asibitin,
bata jira abinda zaice ba ta mike ta sanya gyalenta suka wuce tare da Raudha,
burinta Allah yasa ba'a faďa ma Daddy abinda ke faruwa ba,
tasan yadda zata lauya zancen har ya gamsu da ita..
Kuka ta kakalo ta dinga yinshi cikin motar da zata kaisu asibitin...
Da Hafeez ta fara karo yana zaune a bakin gate din asibitin yana kuka sosai,
Husna dake tsaye a bayanshi ta dafa kafadunshi a tsorace itama kukan takeyi,
kukan rashin Nadeeyah da kuma kukan hali irin na Mahaifiyarta,
Mummy na ganinsu ta fito daga cikin mota ta nufosu tana kuka,
da sauri Husna tace
"Dan Allah karki iso nan da dramarki Mummy,
kun kasheta,
hankalinku ya kwanta,
sai kuyi celebrating ai ba kuka ba,
Cike da mamaki ta kalli Husna tace
"Auta ni kike faďawa haka,
har kin yarda zan iya kashe Nadeeyah da nake so kamar raina,
"So indeed,
yaushe kika fara sonta?
So bayan rai ko,
wallahi alhakin Nadeeyah bazai barku sukuni ba,
i ha----
toshe mata baki Hafeez yayi yace
"Don't say anymore,
uwa uwa ce,
rungumeshi tayi tana kuka sosai haďe da bashi hakuri..
bayanta ya shiga shafawa yana kwantar mata hankali,
yasan irin kaunar dake tsakaninsu,
abin da mahaifiyarta tayi bazai taba shafar zamansu ba saboda Zuciyar Husna kamar gold take saboda kyalli....
Bayan sun tsagaita kukan Doctor ya basu shawarar da su bi manyan asibitoci su duba gawarta a samu a sallaceta cikin gaggawa,
Suna cikin yanke shawarar yadda zasuyi Mummy ta faďo gurin da suke tana ihu mai haďe da kuka,
babu wanda a cikinsu ya kalleta bare har yasan abun da takeyi,
Ganin tana neman cika ma yan asibitin kunne yasa wasu Nurses cewa tayi hakuri ta fita daga waje, tana damun patients dinsu,
"Sirikata ta mutu sannan ďana na
kwance rai a hannun Allah zaku ce inyi shuru,
bazanyi shurun ba,
ya Allah ka sassauta min,
wayyo Allah na shiga uku,
Gadan gadan Daddy ya nufota dan ta kure duk wata dauriya tashi,
tana ganinshi gab da ita tayi saurin mikewa tana share hawayenta,
cike da kissa ta faďo jikinshi tace
"Ance Nadeeyah ta mutu,
daga sokoto na biyo jirgi na iso nan direct,
me ya samu Nadeeyah,
me ya sameta?...
ta karashe tana kuka sosai,
Ran Hilal ya baci matuka na rainin wayon da tazo dashi yayi saurin mikewa zaiyi magana Jamal ya rikeshi,
danne hannunshi yayi yace
"Karkayi magana,
duk lalacewa ita ta haifi mahaifiyarka,
dafe kai Hilal yayi yace
"shine abun da nake jin haushi matuka,
ina ma ace bare ce,
wallahi hukuncin da zan mata ba mai sauki bane..
Raba jikinshi yayi da ita haďe da kama hannunta ya fara janta har suka fita waje,
bayansu Papy yabi yana cewa
"Kayi hakuri Alh Mukhtar,
ka kyaleta sai mun koma gida,
yanzu fatan mu Allah ya bawa Musaddiq lafiya,
kuma Allah ya bayyana mana gawar Nadeeyah cikin gaggawa,
Bai saurare shi ba ya hankaďata ta tafi tagaga zata faďi,
riketa Raudha tayi jikinta na rawa itama na tsoron yadda taga fuskar Daddy...
"Sanda zakiyi tafiya na hanaki?
Girgiza kai Mummy tayi cike da tsoro tace
"A'a,
"Da kika isa inda zaki har kika aikata abun da kike so na hanaki?
Nan ma ta kuma girgiza kai hawayen gaske na bin idanunta,
"To kinga yanzu ina da ikon yin abun da nakeso babu wanda ya isa ya hana ni,
ko akwai?
Durkushewa tayi tana kuka tace
"Dan Allah kayi hakuri,
wallahi sharrin shaidan ne, bansan meye ya ingiza ni har na aikata hakan ba,
Dariyar takaici Daddy yayi yace
"To nima bari in ďan aikata aikin shaidan kadan,
dan baya kyautawa, kullum ya dinga zabarki yana bari na,
gara ya haďamu dukka,
"Kije Na Sake ki!!
Kalmar akwai daďi ko?
Ya tambayi Raudha dake kuka mai sauti...
girgiza kanta tayi tace
"ko kadan bata da dadi Daddy,
dan Allah kayi hakuri,
"Hakane kuma,
bata da dadi in ku za'a furtawa,
Amma in ku kuka sa a furta tafi komai dadin sauraro a gareku,
ko da yake ďaya ce na faďeta dole kiji rashin dadinta,
"Na sakeki Zainab... ya sake maimatawa yana mai kallon cikin idonta,
A wannan lokacin daskarewa Mummy tayi ta kasa motsi saboda tsabar firgici,
ita kuwa Raudha magiya ta shiga yi mishi,
ko biyun har yanzu baku ji dadin furta shi ba?
Da sauri Papy ya sanya karfinshi ya janyeshi haďe da cewa
"Ba girmanka bane,
kayi na ďaya na daukeshi a matsayin gargaďi, ya isa haka,
Dan Allah kayi hakuri ka maida uwar 'yayanka,
"Wani irin kallo Daddy yayi mishi yace
"Ko za'a haďe sama da kasa bazan dawo da Zainab ba,
yadda Nadeeyah ta bar duniya haka Zainab ta bar rayuwata har gaban abada,
Sannan ke kuma Raudha,
ki nemi gidan wani uban bani ba,
dan bani da masaukin zawarawa a gidana,
ita kuma Radiya kuyi mata kyakykyawan albishir kafin ta isa gida,
mijinta ya angwance da yar Mutunci ba irin nawa 'yayan ba,
yana kaiwa nan ya wuce ciki Zuciyarshi na kuna na haďa zuri'a da Mummy....
Kukan da Mummy takeyi na munafurci da na gaske duk ya kafe,
burinta taga Musaddiq da saboda inganta rayuwarshi ta rasa mijinta abun kaunarta,
duk yadda taso ganinshi bai yiwun mata ba saboda yadda Daddy yayi rantsuwar in ta shigo ciki bayan wani sakin sai ya bita da duka,
Baffa ma yace
"tana shigowa zai tsine mata albarka,
duk yadda Anni taso basu hakuri abin yaci tura...
Haka nan ta juya ta tafi Raudha na binta a baya tana kuka wiwi,
Atm suka tsaya dan cire kudi,
Mummy na tura atm dinta taga an sa mata invalid,
jiki a sanyaye tace ma Raudha
"bari inyi miki transfer mu samu kudin jirgi mu wuce kaduna,
karki damu komai zaiyi daidai,
share hawaye Raudha tayi ta bata