Showing 123001 words to 126000 words out of 184071 words

Chapter 42 - ZUMUNCIN MU A YAU Complete By Aisha Yau Kura.txt

sister,
ki kula sosai da mijinki da kanki, yanzu ku biyun nan kune sirrin juna,
ku kare ma kanku mutunci,
in abu ya dameki ki sameshi ki fada mishi,
ku tattala rayuwarku ke da shi,

Allah ya baku zaman lafiya, "Ameen Anty nagode sosai,

"bakomai dear,
a tashi a kama jiki, sai na jiki,
bata jira amsarta ba ta kashe wayar, ta cigaba da ayyukan gida....





Taimaka mata yayi ta koma bayin sannan ya fito ya sanya jallabiya ya fita da sauri dan nemo magunguna da abun karyawa,

ko kallon inda su Raudha suke baiyi ba,
hakan ba karamin dugunzumasu yayi ba suka mike suka nufi dakin da Nadeeyar take..



Jin karan ruwa ya sa su bude bayin a isgilance,

yadda ruwan ke shiganta yasata lumshe ido tana jin wani dadi na ratsata,
jin muryar Raudha da tayi babu zato shi ya sanyata bude kumburarrun idanuwanta,

kallon da suke mata ne ya sa cikinta kartawa ta fara rawar baki tana fadin

"ina kwananku,


"Lafiya kalau karuwar karshen zamani,
yadda maganar ta fito babu control ya sanya Nadeeyah jin wani irin bakin cikin da bata taba ji a kalamansu ba,

sunsha zaginta da kalamai marasa daďi amma wannan shine zagi mafi muni da taba cin karo dashi daga garesu,
maida kwallar idonta tayi ta dauke kanta a kansu,

Nan fa suka cigaba da zaginta suna aibata ta kamar wadanda sukeyi da sa'arsu,
kalamansu na batanci yana matukar sosa mata rai,
amma haka nan ta danne ta maida hawayenta haďe da fitowa ta dauki towel ta nade jikinta dashi saboda girmanshi,

bata sake kallon inda suke ba tayi hanyar fita daga bayin a dan hanzarce duk da tana jin zafin jikinta,

ta kama kofar kenan zata murda Raudha ta janyota haďe da dauke fuskarta da mari,


"Dan ubanki mu zaki mayar mahaukata,
mu zaki bawa banza ajiya,
ke har kin isa muna miki magana ki sanya kafarki kiyi waje saboda tsabar raini,

cike da masifa Radiya ta karbe da cewa
"kinga laifin yar matsiyata marasa asali,
Allah kadai yasan daga inda ubanta ya fito har muka haďa jibi da matsiyata irin su masu siffar munafukai,

wallahi tallahi in bakiyi dalilin da little ya sakeki ba sai mun sanya bakin ciki ya zama ajalinki,
ki fara counting days dinki, dan zuwan Badar da Faida bazai taba zama abu mai dadi a gareki ba,
shegiya yar iska,
mai sakin jiki gurin namiji a daren farko,


"kukan da Nadeeyah takeyi a wannan lokacin mai sauti ne, dan kalamansu yafi mari ciwo a gareta,
kalmar rashin asali da ake yawan fadinta a garesu yana matukar taba mata zuciya,
gaba daya ji tayi ta tsani zaman duniyan ma,
da Allah zai dauki ranta a lokacin da kowa ya huta da kwasarma kanshi zunubi akanta,
har suka gama zagi da aibata ta bata dago kai ta dubesu ba kuma bata fasa kukan da takeyi ba,
da suka gaji sai suka dungure mata kai da karfi haďe furta wani mugun zagi ga matattun iyayenta,

nan kofar bayin ta durkushe tana kuka mai sosa rai...



A gigice ya ajiye kayan da ya shigo dasu ya nufi bayin a hanzarce,
da sauri ya ďago ta kamar yar baby ya nufi cikin dakin da ita, duk tunaninshi ciwon ne ke damunta,
ajiyeta yayi duk ya ruďe yace
"bari in dauko miki riga muje asibiti,
bazan iya jure ganin kukan nan ba,
girgiza mishi kai tayi murya a dashe tace
"Naji sauki,
bana jin ciwon komai,

"to meyasa ki kuka?, ya tambaya cike da damuwa haďe da kwantar da kanshi kan hannunta da ya dau zafi sosai,


"Dan Allah yaya Musaddiq ka sakeni!!!


Yadda yaji maganar kamar an soka mishi mashi ya sanyashi ďagowa ya kalli cikin idonta da yayi jawur,
a hankali ya mike ya zauna sosai kusa da ita haďe da dagota itama ta zauna,

"Kiyi hakuri,
nasan na miki laifi sosai,
na wahalar dake kuma na saki kuka,
bazan kara yi miki komai ba in shaa Allah,
"dan Allah karki kara yin maganar rabuwar mu,
plsss...
ya karashe yana mai shafo gefen fuskarta,

tausayi sosai ya bata tayi saurin kauda kanta gefe,
bata da karfin gwiwar fada mishi dalilinta na san rabuwarsu,
yan uwanshi da mahaifiyarshi basa kaunar auren nan,
da zaiji ta tata da sun rabu ko hankulansu zai kwanta,
hannu yasa ya share mata hawaye ndake gangaro mata yace

"komai zaiyi daidai kinji,
bari in baki breakfast sai ki sha magani kiyi bacci.......






Ajiyar zuciya Marakisiyya tayi bayan ta gama sauraron labarin Badar,
ta tausaya mata matuka na ganin ta rabu da abin da take so lokaci kalilan kuma shi yana can yana jin dadinshi da wata,
nan ta tambayi Badar tana son ta taimaketa ne ta koma gida, ko kuwa so takeyi ta zauna anan ta koya mata sihirin da ta koya a gurinsu wanda zai sanyata tayi gaggawar rabasu,


zuciya marar kashi,
Badariyya bata dubi halin da take ciki ba tayi saurin cewa tana son koyon sihirin,

dariya Marakisiyya tayi a ranta tace
"dama so nakeyi ki koya mu hadu mu biyu mu tada Rugar gaba dayanta sannan mu nemi hanyar garuruwanmu,
a fili kuma ce mata tayi

"an gama,

wasu guraye ta fiddo daga jikinta ta mikawa Badar tace ta rufe idonta,
tana rufe idonta ta fara ganin kanta cikin wani sururin guri mai tsananin ban tsoro,
nan fa ta dada runtseshi haďe da kankame Marakisiyya tana ihu sosai,
bakinta Marakisiyya ta toshe dan sam bata so asan abun da takeyi,

sai da sukayi kusan minti 30 a haka sannan Marakisiyya ta kwace gurayen,

Wuri wuri Badar tayi da idanuwanta saboda tsananin tsoro,


"Kin tsorata ko?

Gyaďa kai kawai tayi tana fitar da numfashin wahala,


Wata dariyar Marakisiyya ta sake yi tace

"Lokacin jin tsoro ya wuce, nan ta kwance wata leda ta cigaba da cewa
"dafi kasar nan ki ayyana abu a ranki,
zaki ga duk abinda kike yana dawo miki kamar a mafarki, (tayi mata haka ne dan ta kara zura jiki da ita ta)..



*HUSNA*
ce ta faďo mata a rai wanda a sonta rayuwar su Musaddiq taso fara gani,

tana runtse idanuwanta komai na Husnah ya fara yi mata yawo kamar a film,


"Zaune ta gansu a kayataccen parlonsu Husnah na zuba ma Hafeez shagwaba yana rarrashinta,
komai na gidan su madaidaici gunin sha'awa,
babu abin da yafi girgizata ya sanyata cikin bakin kishi kamar ganin yadda fuskar Hafeez ke mata kwarjini da kuma girma kamar wani sarki mai daraja,


Saboda sabon shiga ce cikin sihirin shi ya hanata gano muhimmin abun dake tattare da Hafeez,
amma tabbas taga alamu na sarauta mai girma a tare dashi....





Saida ta gama duba lafiyar kowa taga duk suna harkarsu ba tare da sun damu da bacewarta ba,

Sai ta koma kan wanda take mammako da tsoron duba nasu,

aiko tayi mugun gamo,
domin kuwa yadda ta gansu a manne da juna ya 'ballo magani yana bata cike da rarrashi haďe da kwantar da ita a jikinshi ba karamin kai ganinta kasa yayi ba,

kankancewa idanuwanta sukayi haďe da yin jawur kamar gauta,

nan tayi saurin cire hannunta a kasar sihirin da Marakisiyya ta bata,

mikewa tayi tana safa da marwah haďe da cin alwashin rabasu kuma ta kashe Nadeeyar gaba daya,


Wannan shiga gonarta da Nadeeyah tayi wallahi sai tayi paying da rayuwarta,



Cikin kwarewa Marakisiyya ta koya mata duk wasu nau'i na tsafi haďe da bata wasu abubuwan da zata sha tayi wanka dasu,


"Hatsabibanci Marakisiyya ya sata koyon duk abubuwan a gidan,
ko ina kewayawa takeyi tana koyo haďe da haďa su da kanta,
duk yadda aka kai ga tsoron manyan gidan Marakisiyya bata wannan domin ga da ga zata zagesu tass,
shiyasa aka koma sa mata bulala a jiki,
ta zame musu karfen kafa,
basa iyawa da ita,


Tun ranar da taga Badariyya ta shin shino barinta gidan da taimakon Badariyya,
shiyasa tayi saurin shigar mata da bukatarta kafin ma a samu wata a gidan ta shige mata....




Mrs Tijjani Shattimah....
[20/04 4:18 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 6⃣0⃣
By *Aysha Ya'u kurah*






Cikin shashshekar kuka take tambayar doctorn abin da ke damun ďanta,
yanayin ruďewar da take ciki ya sanya doctorn dawowa kujerar kusa da ita,

"Calm down Ma'am,

"ba wani serious abu bane,
kawai damuwa ce da rashin cin abinci ya sanya shi zama weak, but with time zai samu sauki in ya kiyaye,
ko da baya san cin abinci atleast ya dinga ci ko kadan ne at the right time,
sannan ya daina damuwa ko yaya take,
thank Goodness bai taba zuciyarshi ba,
but yaso yayi affecting dinta,
plss ya kiyaye sosai cos life is very precious...



Wasu zafafan hawaye ne suka biyo ta gefen idonshi bayan ya gama sauraron abin da doctorn ya faďi

"Life is nothing without Nadeeyah,
ya Allah ka sassauta min..


Hannu Anty Saude tasa ta share mishi hawayen itama ta share nata sannan tayi ma doctorn godiya ta kuma yi mishi alkawarin kiyaye duk abinda yace mata,
har bakin kofa ta rakashi sannan ta wuce kitchen rai a bace,



Wani maganin kwari mai karfin gaske ta dauko haďe da juice ta dawo kusa da Taheer ta zauna, yana kallonta ta ďure maganin a ciki,
a hankali ya mike yana tambayarta abun da zatayi dashi,
ko kallon inda yake batayi ba ta daga juice din zata kaishi bakinta,



Wani irin karfi yaji a jikinshi haďe kabe juice din a hannunta, baki na rawa yace
"Are u out of ur senses,
poison ne fa,
so kikeyi ki kashe kanki?

"Gara in kashe kaina da irin kisar da kake shirin yi min Taheer,
gara in mutu kafin ka kashe kanka kasa min mutuwar ko'ina na jikina,
bani da wani muhimmanci a cikin rayuwarka,
akan mace kake so ka kashe kanka har kake kiran rayuwa ba komai bace in babu ita,
gara ka barni in fara mutuwa sai ka biyoni,
bazan iya jurar ganin gawarka ba Tee...
. bazan iya ba....
ta karashe tana kuka sosaiiii....




Kanshi ya daga sama da niyyar haďiye kukan da ya tokare makokwaronshi,

inaa sam ya kasa,
wanda yake kokarin haďiyewa ya fito da karfinshi,


Zaman dirshan yayi a gurin yana kuka sosai kamar karamin yaro,
bata hanashi ba dan itama kukan takeyi,
wallahi da zatayi arangama da yarinyar da tayi wa ďanta haka sai ta shake wuyanta ta kusa kaita lahira,
ita duk tunaninta cin amanar ďanta tayi,
domin ita tace ya jirata,
sai kuma yaji labarin aurenta,
duk da bata san wacece Nadeeyah ba taji a duniya bata ko san karo da mai sunan a rayuwarta,

Saida sukayi kukansu ma'ishi sannan Taheer ya rarrasheta ya kuma yi mata alkawarin daina tunani akan wacce ta zamto matar wani,
sannan ya roketa da Allah kar ta yi mishi maganar aure nan kusa har sai yayi niyya dan kanshi,


Badan taso ba ta yarda da kudurinshi,
tasa ma ranta nemo mishi yarinyar da zata maye mishi gurbin cin amanar da akayi mishi......



Lafiyayyen abinci ta shirya mishi ta dinga mishi hira,

"auu kaga damuwa ta dauke min hankali,
jiya *Mus'ab* ya kirani,
wai su *Aman* sun samu gurbin karatu anan university of Toronto,
ina ganin gobe ma suna hanya, bakaji daďi da naji ba,
dan zasu rage min kaďaici in ka tafi makaranta,
nuna mata jin dadinshi yayi yace

"mantawa nayi ban faďa miki ba, ni na nema musu admission din, Anty Nuwairah duk ta damu wai sunyi nisa,
saida taji a gida zasu zauna shine hankalinta ya kwanta,
naman karshe Anty Saude tasa a bakinshi tace
"Haka tace min,
ai naji dadi sosai, Allah ya kawo su lafiya, "Ameen ya faďi haďe da mikewa yace
"bari in watsa ruwa,
inaga gobe zani lagos,
Kudin Abba na companyn coffee ya fito,
sunce in je inyi signing.....

cike da jin dadi tace

"Kaii mashaa Allah, Allah ya kaimu goben......





**********





Tagumi tayi akan dadduma bayan ta idar da Nafila tana jiran a kira sallar asuba ta tashi tayi,
tunanin irin rayuwar da takeyi a gidan aurenta takeyi,
tunda tazo gidan ta auri zaman ďaki,
bata san kalar kitchen dinta ba domin yadda su Radiya suka kanainaye komai,
babu inda take fita kullum daga bayi sai ďaki,
bata da matsala sam da Musaddiq domin yana kula da ita sosai,
abinci ma in ya siyo da kanshi zai bata kuma ya kwashe kayan da kanshi dan shima tsoron tashin hankali yakeyi,
a da bata jin son Musaddiq a matsayin abokin rayuwarta, amma kwanaki shidan nan da sukayi tare,
halayyarshi ta samar mishi matsayi mai girma a zuciyarta,

Mutum ne mai gudun zuciya,
yadda bazai bata maka ba,
kaima karka bata mishi,
samm baya kwana da wani a ranshi,
sanyin halinshi shine abu mafi soyuwa a gareta,
tun ranar da ya kusanceta yaga irin kukan da tayi,
bai sake koda kwatantawa ba, duk ko da tsabar dannewar da yakeyi,
samm bayasan abin da zai sata cikin damuwa,
ya gwammaci matsuwar ta dameshi akan yasata cikin damuwa...



kiran assalatu ne ya katse mata tunanin da takeyi ta mike dan ta tashe shi ta kuma sabunta alwawarta,

Bargon da ya dukunkune ta yaye a hankali,
zufar da ta gani a fuskarshi ce ta sanyata zaunawa kusa dashi da sauri haďe sa hannu a goshinshi ta fara share mishi,
hawayen da ya jika saman idonshi shi yafi komai daga mata hankali,
a rude ta fara kokarin ďago kanshi ta kasa saboda har lokacin cikin bacci yakeyi,
gefen kunnenta ta kwantar a saitin kirjinshi taji yadda zuciyarshi ke bugawa da sauri da sauri,
ajiyar zuciya ya saki haďe da shashesheka ya sanya hannu ya rungumeta sosai a jikinshi,

"plss don't lv me,
i can't lv without u....


yadda yake maganar ido a rufe ya bata tabbacin mafarki yakeyi,
duk wata kunyarta ta nema ta rasa ta rungumo kanshi haďe da share mishi hawayen da yakeyi tace
"bazamu rabu ba,
in shaa Allahu babu abinda zai rabamu,
Allah ne ya haďamu,
shine kadai zai iya rabamu in yaso, "bazan barka ba!


Jin kalaman da yake a zahiri ba'a mafarki ba yasa shi buďe idonshi haďe da kwantar da ita sosai a jikinshi yace
"promise?

gyaďa kanta tayi haďe da cewa "Ummm,

"umm me?
Ya fadi yana daďa narke mata,

turo bakinta tayi a shagwabe tace
"um um,

dariya yayi yace
"kinsan nafiki iya shagwaba,
in na fara nawa gari zai waye mana ba muyi sallah ba,
kinji an tada kabbara, tashi muyi sallah mu roki Allah kar ya tabbatar mana da mafarkin da nayi,

juyo fuskarta yayi ya daura hancinshi kan nata numfashinsu ya gauraya da na juna yace

"i don't want to loose you,

hannunta tasa ta toshe mishi baki cikin zolaya tace

"hmmm...
muje kayi brush,

"bakina wari ko,

"ni dai ban faďa ba!


"laifin ki ne,
baki sani nayi rinsing baki na ba,


nidai ba ruwana,
kaji anyi sallama ko,
dan Allah muje muyi sallah,


"zakiyi bayani bari mu idar da Sallah,
ya faďi yana dariya haďe da nufar bayin......





Wai Mummy Faida bazata zo bane,
babu wani improvement fa,
kullum daďa like ma yarinyar nan yake,
can u believe that ko gaisheni bata fitowa tayi,
ni kam in bazaki turo Faida ba zan shirya in koma gurin 'yayana,

Daddyn Ra'ees ko daga wayata baya yi,
wannan bai dameni ba, dan nasan ina komawa gida zai huce,
burina inga munyi winning yarinyar nan ta bar rayuwar little,
Radiya na dire aya Mummy tace

"Karki damu,
Faida na nan tafe anjima,
mun gama magana da Hajiya Aliya,
in shaa Allahu komai ya kusa zuwa karshe,
kudai ku cigaba da taka tsan tsan kar Daddynku ya gano kina can, dan wallahi in ya gane ba zamuji daďi ba,
gyara zama Radiya tayi tace "bazai ji ba in shaa Allah,
ai kwana kaďan ya rage,

"To Allah ya nuna mana,

"Ameen Mummy, sai anjima....





Ki shirya zamu fita bayan la'asar, maida pillow mazauninshi tayi tace
"To Allah ya kaimu,

"Ameen Habeebty....





Karfe huďu da yan mintina suka fito a shirye tsaff gunin sha'awa,

Allah ya taimaka su Raudha sun tafi sama yin Sallah,
shiyasa taji dadin fita daga parlon...



Banana island suka fara zuwa gidan oganshi wanda suka saba sosai da matarshi, dan yawancin duk wasu muhimman aike Musaddiq ke zuwa,


Tarba mai kyau suka samu daga gurin Hajiya Zubaida,
mace mai mutunci da fara'a, ga sanin ya kamata,
wayayyar mace ce yar birnin kebbi,
yaranta uku duka maza,
babban cikinsu bai wuce shekara 18 ba,

Sai wanda take kira auta dan shekara 9,



Bayan sun gama dan taba kayan da ta kawo musu suka dan yi hira kadan sai Musaddiq ya bukaci da su tafi,
hana su tafiya tayi tace
"ku jira shi,
yanzun nan zai dawo,
tana rufe baki suka ji an murda kofar,



Alhaji Kamal Gumel ne ya shigo tare da ďanshi na biyu,
faďaďa murmushinshi yayi yace

"Ango kasha kamshi,
tare muke da Zubairu,
yanzu ya tafi siyomin kifi,
ai da nasan kana ciki da na tsaida shi,


cike da girmamawa suka tsuguna suka gaida shi,
amsawa yayi ta sigar mayar musu da girman haďe da zama yace

"masha Allah,
gaskiya Musaddiq ka iya zabe, Allah ya baku zaman lafiya,
nan hirar aiki ta kacame musu,
"ba karamin wahala suke sha ba na hutun da Musaddiq ya dauka, dan in yana nan aiki bai musu yawa haka,
akwaishi da azamar aikin office,
samm bashi da kasala a nan, saboda yanda mahaifinshi ya nuna mishi muhimmancin aikin da kuma inda suke fatan ya kaishi nan gaba,



Da Hajiya Zubaida ta gaji da hirar aikin tace ma Nadeeyah ta tashi suje karamin parlon,
ba musu ta mike tabi bayanta,


"Wannan hirar tasu ba mai karewa bace,
gara muyi tamu anan wacce zata amfane mu,
tambayoyi Hajiya Zubaida ta fara yi ma Nadeeyah,
kasa bata amsar su Nadeeyah tayi domin wasu bata san yadda zata sa mata ba,
dariyar manya Hajiya Zubaida tayi ta fara bata shawarwari kama daga kitchen har kwanciyar aure,
da irin ladan da mace ke samu a gidan aurenta,
sosai shawarwarin suka shiga Nadeeyah saboda haďawa da tayi da ayoyin Allah da kuma tarihan magabata,


Saida suka kara kusan minti 30 sannan suka fara shirin tafiya,

Sha tara ta arziki Nadeeyah ta fita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login