Showing 66001 words to 69000 words out of 184071 words

Chapter 23 - ZUMUNCIN MU A YAU Complete By Aisha Yau Kura.txt

nuna Baffa tace "danka, ita ta sani na dauki ciki har sanadiyar shi nazo har wannan kauyen..

Da fari a kullum ina tunanin ni kadai ce Allah baya so a duniyar nan da ya jarabceni da yin cikin shege a cewar bahaushe,

haduwata da Abdallah na fahimci dama nazo duniya ne domin shi,


koda na koma gida Yakumbo tayi tayi ta rabani dashi,
a lokacin ne na nuna musu nima ina da hakki akan dana, tunda ni na haifeshi,

babu wanda ya taba samun labarin bani na haifeshi ba,

A lokacin da na bijirewa yakumbo sai ta koreni tace in tafi gurin uwata ita bazata iya da wannan abun kunyar ba,

bani da kudi haka na goyashi saboda bashi da kayan sawa,
ga rashin karfi nawa da nashi,


Cikin ikon Allah muka samu motar zuwa Gombe,
saida muka kwana uku a hanya muna tafiya,

duk kauyen da muka tsaya anan zan roki ruwan zafi in mishi wanka,


wata baiwar Allah ce ta hada min da wani maganin da nasha har na samu karfin jikina,
sannan ta bani wanda na barbada ma cibiyarshi hade da gishiri,


koda muka isa gida nan ma akayi min caaa ana Allah wadai dani,

ban saurari kowa ba na shiga gurin mahaifiyata na roki gafararta,
nace mata zan tafi neman abun da zan rike ďa na,

Bata kalleni ba amma shashshekar kukanta shi ya tabbatar min da tana cikin tsananin damuwa,

har na kai kofa ta kirani,

dawowa nayi naga ta kwanto gefen zaninta ta fito da kudi masu yawa na furar da takeyi ta bani ba tare da ta kalleni ba,

Murmushin farin ciki nayi na dauki wannan kudin a matsayin sa min albarka tayi,
nan nayi mata sallama na fita,

A tsakar gida sai zunde na sukeyi, babu wanda ya kula da halin da zamu shiga ni da dana,
su dai burinsu in rabasu da abin kunyar da na dauko musu,



cikin gari na wuce dan neman aikin da zanyi in ciyar da kaina,

Da farko a wani kango muke kwana wanda ake gininshi kullum,

kayan sawa na dasu nake dukunkuneshi saboda bashi da na sawa,
da safe in masu ginin sun zo sai in goyashi in tayasu dan in samu wani abun rikewa a hannu,

a haka har mukayi sati daya a cikin gurin,

Ranar da muka cika kwana takwas Abdallah ya tashi da ciwo mai zafi kamar bazai yi ba,

saboda rashin sanin abin yi na zauna na tasa shi a gaba nayi ta kuka,

daya daga cikin masu kula da gidan ne ya tausaya min ya dauke mu a gurin ya kaimu wani shagon kwano yace mu dinga kwana a ciki,

Sannan ya nemo min bedi da yawa da icce da tukunya yace in dafa mishi ya dan sha ruwan in mishi wanka,


kafin inyi mishi godiya naga ya fita ya karbo wata kwarya,

tuwon dawa ne a ciki da miyar kuka,

nan na hau ci kamar karamar zakanyar da taga nama,


A haka dai muka cigaba da rayuwa har na samu aikin shara a wani gurin gwamnati,


saida na shekara biyu ina aiki a gurin,
a lokacin Abdallah ya fara girma amma yau da lafiya gobe babu,


kullum matsalar cibiya yake fama da ita,

saida ya shekara bakwai sannan na kaishi asibiti,
anan ne ake fada min tarin datti ne ya shiga cibiyar,

jinjina tsawon rai irin nashi likitan yayi da na bashi labarin yadda na sameshi yace "lallai yaron nan Allah yana san saukar da rubutacciyar aya ta dalilinshi,

anan dai likitan yayi mishi aiki,

cikin lokaci kalilan ya samu lafiya muka dawo aikinmu,


kullum tare muke zuwa yana tayani,

A gefen gurin da nake shara akwai wata makaranta,
da naga yana yawan zuwa gurin ya tsaya, kuma yana sha'awar karatun, sai na kaishi makarantar, islamiyya ma yana zuwa ta allo sannan ina koyar dashi a gida..


gwagwarmaya babu irin wacce bamu sha ba ni dashi,


Lokacin da ya gama makaranta, ya fito da sakamako mai kyau,

gwamnati ce ta dauki nauyin cigaban karatunshi saboda hazakar shi,

A lokacin da yake karatun ne muka dan fara samun sauki saboda in aka bashi kudi a nan gida yake barin su,
ya gwammaci in ya dawo gida muyi amfanin da kudin,



*Nasara*
ta Allah ce amma ni zan iya cewa ita ainihin kalmar ma'anarta shine Abdallah,


shekarar da ya gama jami'a aka bashi aikin koyar da yan aji daya a makarantar,

duk inda yaje a unguwarsu zakiji Ana fadin *Abdallah Hanne*,
da sunan da yake amfani kenan ko a makaranta,
ko kuma ace uncle Abdallah.. yaran unguwa yake tarawa yayi ta koya musu karatu..


jan majina tayi dan kuka na neman cin karfinta ta cigaba da cewa "tunda muke da Abdallah sau daya ya taba cemin

"Ina Babana *ANNE* sunan da yake kirana kenan tun yana yaro,

a ranar nayi kuka sosai wanda ya tayar da hankalinshi,

tun daga ranar duk gorin da ake mishi bai damunshi,
saboda yasan wani mai uban ma bazai nuna mishi jin dadi ba,

A kullum saidai in dinga fada mishi kana da uba,
kai ba dan shege bane,
kai dan sunna,
aure ne ya samar dakai,



Kullum addu'ata Allah ya hadani da mahaifin Abdallah koda sau daya ne ya ji wannan farin cikin da yayi dakon su shekara da shekaru,

bayan ta kai aya ta kalli Papy da ya fita hayyacinshi saboda tsabar kuka tace
"shine mahaifinka Abdallah,
wannan shine ya haifeka!


Rungume Anni Papy yayi ya tsananta kukanshi yace "duk duniya babu na biyunki Anni,

saboda ni kika bar gida, kika bata rayuwarki da lokacinki!

saboda ni kika ki yin aure,

saboda ki inganta rayuwata kika hana taki ta zama ingantacciya, why Anni,
Why??
Ya karashe yana kuka sosai,


Itama kukan takeyi tace "bani nayi ba Abdallah,
Allah ne,
yin Allah ne,
in ba Allah ba waye zai rabaka da iyayenka,

babu mamaki yayi haka ne domin ka zama nagartacce,

ya rabaka da danginka ne dan ka zama gawurtaccen mutum,

babu mamaki da kana gida duk wadannan abubuwan bazasu samu a gareka ba,

dalilin da yasa Allah ya barka da rai bayan ka shiga karkashin kasa ba karamin dalili bane..


Maimuna ma ta taka rawar gani a cikin rayuwarka,

tasoka a lokacin da kowa ke kiranka da dan gaba da fatiha,
Duk kushe ka da akeyi a lokacin kamar ana zugata ne,
ta tubure sai ta aureka,

Maimuna ta nuna mana kauna lokacin da kowa ya kyamace mu,


Cikin Kuka Mami tace "kinyi jarumtar da ko kwatanshi banyi ba Anni,

hadasu yayi ya rungumesu yace "banyi regretting rashin tashi a cikin yan uwana ba,

domin babu abin da ban samu ba a gareku,
uwa,
uba,
mata,
kawa,
Aboki,

ni ko me zancewa Allah,

babu abin da zance sai tarin godiya a gareshi da ya hada ni daku....




Shuru ne ya dan ratsa gurin,
sai ajiyar zuciyar kuka kawai ke tashi,

kallon farin ciki Baffa yakewa Papy,
fuskan nan tasu jike sharkaff da hawaye,


Hannun shi ya kamo ya sake fashewa da kuka yana fadin *SAIFULLAH*,
Ma'u dana ne,
*SAIFULLAH*,

jinina ne Ma'u......





Mrs Tijjani Shattima.....
[19/03 8:17 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣0⃣
By *Aysha Ya'u kurah*




*Rayuwa takaitacciya ce. Kada ka cika ta da damuwa. Kada dogon Buri ya dauke hankalinka daga mutuwa. Aikata alheri a kowane lokaci watakila shi zai zamo mabudin Aljanna a gare ka*.





Alkalamina bashi da karfin rubuta irin gigitar da Ma'u tayi,
a zaune take amma jinta take tamkar a tsaka tsaki take,
ita bata kai kasa ba haka bata kai sama ba,
jinta take kamar wacce take lilo a tsakiyar iska,
gaba daya hanyoyin sadarwa na jinin jikinta da kwakwalwarta sunyi balaguron wucin gadi..


Jin hannu da tayi cikin nata ya sanyata dawowa cikin hayyacinta a firgice,

kallon hannun tayi hade da mamallakin hannun,
ido cikin ido sukayi Anni tace
"Da fatan kin gamsu da bayani na,
da fatan kin tuno abubuwan da suka faru kamar yadda kika ji na fadesu,
yanzu kin yarda da maganata na cewa ban taba magana da mijinki ba,
na yafe miki zargin da kikayi min,
domin a yau bana fatan abun da zai bata min rai,
a cikin farin ciki nake matuka na ganin Abdallah na ya samu abinda yayi shekara da shekaru yana kawaicin tambayarsa duk da nasan babu ranar da zata fito ta fadi ba tare da yayi tunanin rashin mahaifi ba,

kullum in na kalli murmushinsa nakan hango damuwa a bayan murmushin,
wannan suna da ake kiranshi dashi na *ABDALLAH HANNE*, yana matukar yi min ciwo,
ansha zuwa gabanshi a kirashi da dan mace,
duk damuwar da Abdallah zaiyi bai taba yarda yayi ta a gabana ba,
sakin Goggo tayi hade daga hannun sama tace "Alhamdulillah,
Allah zan cika maka alkawarin da na dauka na yin azumi duk ranar da ka cika min buri na...

Murmushin farin ciki Baffa yayi yace

"Alhamdulillah,

Allah mun gode maka da ka dawo mana da saifullahi,
ina ma Allah zai dawo da Suwaiba ta dawo taga dan biyun ta,
sai dai kashh Allah baya barin wani dan wani yaji dadi,

kallon Mamaki Anni tayi ma Baffa tace
"kana nufin Abdallah yan biyu ne?

Kwarai kuwa Baffa ya fadi yana gyara zama,
Gaba daya ya manta da Ma'u da bai samun katabus in tana guri, ya cigaba da cewa
"su biyu mahaifiyarsu ta haifa, kamar yadda kika sani shi mun dauka ya mutu,
to ashe shi din ne rayayye ita kuwa Suwaiba tabi mahaifiyarsu,

watanni kenan da mutuwarta,
ta rasu ta bar 'ya'ya uku,
HAFEEZ shine babba,
sai Nadeeyah da Zainab,


"_Hafeez_"

Papy ya maimaita wasu hawayen masu zafi suka biyo bayan furucinshi,

"Tabbas jini ba karya bane Anni ta fadi tana share nata hawayen,

soyayyar da Abdallah ya nunawa Hafeez daga ganin farko ashe ba haka kawai bace,
ashe Jini ne yayi aikin shi,
dalilin zuwan Hafeez karatu Gombe ba karatun bane,
wannan haduwar itace silar zuwanshi,
duk inda alkhairi yake baya taba faduwa kasa banza ta karshe tana goge idonta da gefen hijab dinta,


waya Papy ya dauko ya danna number Hafeez,
"Kana ina ne?, ya tambaya murya a shake,

"Muna kofar gida, mu zo ne? Hafeez ya amsa cike da girmamawa,

"eh kawai papy yace ya kashe wayar,

Hankali a tashe ya shigo gidan saboda yanayin da yaji muryar yasan babu lafiya,

kusa dashi yaje ya tsuguna
"Gani Papy,

Wani irin kallo yayi mishi wanda yake nuna tsantsar soyayya ga mai yinshi,
hannunshi ya rike hade da hada jikinshi da nashi da karfi,

"kai jinina ne Hafeez,
ashe kai dana ne,
ina ma nasan wannan tun ranar farko,
da kome zakayi tare zamuyi shi,
da ban barka kayi wahalar komai da kanka ba,

cikin rashin fahimta
Hafeez ya da dago ya kalli idon Papy da yayi jajur,
zaiyi magana Papy yayi saurin kada kanshi yace "kai jinina ne Hafeez,
kai dan yar uwata ne,
dan wacce muka kwanta a mahaifa daya ne,


Wani irin kukan farin ciki ne ya kufcewa Hafeez,
duk yadda yakai da hangenshi bai hararo kusancin nasu har ya kai haka ba,

shidai yasan kamannin Baffa sosai yake gani a jikin Papy sai fari da ya banbanta su,

sake rungumeshi Papy yayi yace "yau ranar farin ciki ce ba ta kuka ba,


Mummy da karyayyar zuciyarta ta tsumu sosai tace
"kukan ya zama dole,
kuka ne na farin ciki,

Shi yanzu nasan kukan tunowa da Suwaiba yakeyi,
share hawayen tausayi tayi tace "ina ma Lokacin da suwaiba ta debo mai tsawo ne ta ga wannan ranar,



kallonta Papy yayi yaga ita din ma tana dan yanayi dashi yace
"kema yar----

cike da murna Baffa ya katseshi da cewa yayarka ce,
ita ce Babba,
nuna Ma'u yayi yace
"wannan ita ce ta haifeta,
su biyu ne,

Allah yayi wa Halima rasuwa da dadewa,

sai ita kadai ta rage mana,
ashe wani farin cikin na tafe zuwa garemu,
ashe ina da rabon ganin Magaji na kafin kasa ta rufe min ido,


Wannan kalma ta *MAGAJI* ita sanya Goggo jin wani dumi tun daga kanta har cikinta,


Ido ta zurawa Baffa da yake ta sambatu a gaban Papy da Anni,
duk yadda taso su hada ido dashi sam yaki dan gaba daya ya manta Allah yayi halittar ta a gurin,


Yasan dai tana makale cikin ranshi amma ganin Papy ya sanyashi mance duk wata soyayya in ba tashi ba,

ji yakeyi ina ma ace da kuruciyarshi da sai yayi zagaye da Papy a bayanshi ba tare da ya gaji ba..



Wani irin kugin taji a cikinta tunda Anni ta fara basu labarin shi dawo mata,
ganin yadda tun yanzu Baffa ya ki koda kallonta ya tabbatar mata da lallai akwai aiki a gaban ta,


Mikewa tayi da niyyar tafiya bayi dan cikin nata jinshi takeyi kamar zata kasayar da ya'yan hanjinta,

Tana mikewa taji kafarta tayi mata nauyi saboda yadda zawon ya taho mata gadan gadan,
dakyar ta daga kafarta,
tana dagawa zanin jikinta ya sabule ta feso shi ba tare da sanin inda zashi ba,


Wani irin ihu Radiya ta saki tana fadin "I'm dead" wayyo Allah na,


"Dariyar Ruwaida ce ta cika gurin tana yi tana fadin
*nyan nyan nya* disgusting!

Papy kagani da kace "in an min abu in dinga hakuri Allah zai saka min, yau gashi naga ni da idona,
wayyo cikina,
she deserve more old lady karo mata,,

Janyota Mami tayi da karfi ta sake maida idonta cikin mayafinta kamar yadda kowa yayi a gurin,

kunnenta taja tace "ke wace irin yarinya ce,
in sake jin kince pim kiga abun da zan miki,


Mummy ce ta tashi da sauri tana tare Goggo tana fadin Goggo lafiya,

Hawayen takaicin da Goggo ke rikewa ya zubo a kuncinta,

cike tsoron ganin hawaye a idon wacce babu abin da ke sata kuka Mummy ta ja hannunta sukayi bayi,

shi kuwa Baffa maida kallonshi gurin Radiya dake kuka tana kyankyame jikinta yayi yace
"je ki wanke jikinki mana,
ko so kikeyi warin ya kashe mu,
baki ganin muna cikin farin ciki ne,

karaff kalamanshi a kunnen Goggo,

wani Kukan ta sake fashewa dashi a zuciyarta tana tambayar kanta ta inda aka samo matsalar,

Damuwa ce karara a fuskar Mummy dan iya rayuwarta bata taba ganin hawaye a idon Goggo ba,
bayan ta gama kimtsa ta suna jiyo muryar Baffa yana basu Labarin Suwaiba da 'yayanta,

ita kanta Radiya cike take da mamakin yadda yake basu labarin suwaiba da 'yayanta dan a da ko labarinsu baya son ji bare ya ba wani,


Kallon Goggo Mummy tayi tace "kiyi ma Baffa uzuri, shekaru sama da arbain rabonshi da dan da ya cire rai da kasancewarsa a duniya,
sannan kuma shi kadai ya zame mishi namiji,
kinga dole yayi farin ciki,
ni kaina cikin farin ciki nake,
dan a yanzu na fita a sahun ni kadai,
mun zama biyu, ďan uwa dadi gareshi Gog----

dogon tsaki taja wanda ya katse mummy da karasa maganar ta,

"Ba tun yau na lura da cewa ke din bakya kishi na da kanki ba,
inama Allah Halima ya bar min ya daukeki Goggo ta fadi cikin gushewar hankali,

Zaro ido Mummy tayi zatayi magana ta jiyo muryar Baffa yana kwala kiranta,
bai bari ta amsa ba cikin doki yace "fito muje gidanki suga Nadeeyah,

ki kira muntari in yana gari shima ya dawo gidan sai su hadu,

Jaka Mummy ta dauka tace ma Goggo "kiyi hakuri, gobe zan dawo,

ko kallonta batayi ba,
idonta na kan kofa tana jiran ganin Baffa ya shigo dan su hada ido ta samu dukkan madafun ikon hanashi zuwa,


Anni da Mami ne kadai suka leko suka yi mata sannu da jiki, sannan suka wuce,,


Shurun da taji a tsakar gidan ne ya bata damar lekowa,
babu kowa a gidan sai Radiya dake tsaye daga ita sai undies, tana ganin Goggo taja mata tsaki tace
"walhy kin cuceni, sam bazan iya cin abinci ba yau,

gashi Mummy ta tafi ta barni, nidai gaskiya baki kyauta min ba,
kuma ga kashin ki nan walhi bazan kwashe ba,

Hadiye miyau mai daci Goggo tayi ta wuce daki tana saka abubuwa marasa kyau da zata aikata,

saken da tayi na ganin cewa babu wanda zai shigo rayuwarta shi ya janyo mata wannan matsalar......




♡♡♡♡♡♡!
♡♡♡♡♡♡♡♡!
♡♡♡♡♡♡♡♡♡!


Nayi kyau Momma!!

Kallonshi tayi sama da kasa,

jan wando ne a jikinshi ya dan matse daga kasa sai green riga ta dafe a jikin tayi mishi kyau sosai..

Murmushi tayi ta gyara mishi kwalar rigar tace "First class kyau ma,
kaima kasan u are excellent!


Rungumeta yayi hade da yi mata peck yace
"zan fita ur ---
prayer is needed ta karashe hade da cewa "kana da bukatar tuna min ne,
dariya yayi ya dauki keyn motarshi,
har ya kai kofar fita daga dakin tace
"baka fa fada min sunan diyar tawa ba,

waigowa yayi yana dariya yace "tooo expensive, nawa zaki siya?,

Dariya tayi sosai tace "abun da yafi komai tsada a gurina zan biya,

*TEE NA*

Murmushi yayi yace "luv yhu Momma,

*Umm Nadeeyah* is the special one.. my Omri...

Ya karashe hade da fita da dan gudu gudu,

zama tayi tana maimaita sunan farin ciki na ratsa ko ina na jikinta.....




A kofar gida yaga Raliya tsaye tana tsaki tana kallon drivernta yana duba mota,

tsayawa yayi yace "Maman fadeel fita zakiyi?

"Eh Taheer motar kuma ta samu matsala,

Ayya,
shigo muje in kaiki mana, Taheer ya fadi yana fitowa a mota,


Girgiza kai tayi tace "bazan matsa maka ba,
jeka kawai walhy,


Babu wani matsi Allah,
saidai in motar ta miki karama ya fadi cikin tsokana,


Dariya sosai tayi ta bude ta shiga ta cema drivern ya kai motar gurin mechanic...



Dadin da yaji baya misaltuwa na sanin gida zataje...

kwatance ta fara mishi taga yana ta kai kanshi tun kafin ta fada mishi,
murmushin jin dadi tayi ta kasa tsokanarshi saboda kar tasa yaji kunya....


*******

Tun karfe biyu ya sauka a airpot din Abuja,
bai tsaya jiran wata wata ba ya dauki drop har kaduna,

zuwan nashi na aike ne a ganin Anty Reemah,
bata san shi zuwan nashi ya wuce aiken da tayi mishi ba,

Musaddiq ne kadai yasan da zuwanshi dan shima ya matsa a kawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login