Showing 12001 words to 15000 words out of 95088 words
Chapter 5 - Samarin Bana Complete Book Writing by Rahamat Muhamm ad Rufa'i Nalele.txt
kwarai
Yace amma inaji ajikina baxaki samu yanda kikeso ba
Ta galla mai wata muguwar harara tace insha Allah xan samu fiye da yanda nake so mugu kawai
Kaga kaje kawai karka tsaya cikani da surutu 'dan rainin hankali kawai. Ta qarashe da nuna 6acin ranta
Yayi Murmushi Yace toh shikenan Allah yabaki lpy Auntyna saina dawo
Har yakai kofah Tace RAMADAN Yace na'am.
Taqara harararsa Tace kayi kyau Sosai. Tafa'da batare da tasaki fuskarta ba.
Yadawo gareta ya kama hannunta da shafa goshinta. Ba xafi agoshin Yace Allah yabaki lafiya Auntyna kema kinkyau Sosai
Tace kaci abinci ko Ya'daga mata kai alamar eh kana ya mata kiss a hannu ya fitta yana cewa natafi
Tabishi da kallo tana jin da'din qamshinsa.
RAMADAN yana futa bai da'de ba Abbas ya yaxo gidan
Da sauri SAILUBAH takeyin shiri burinta taje taga munin Abbas 'din da RAMADAN yace
Aiko bayan sun gaisa ta qura masa ido........
Eh Gaskiya ne
shi baqine bai cika kyau ba. Kuma da gaske yana da hakwara Amma basu sashi muni bah. Yanda tadinga tunanin xata gansa abin bai kai haka ba. Dan yana kyansa daidai gwargwado
Amma taji aranta Sam bata sanshi dan maganar gaskiya RAMADAN yayi nasarai jefa mata qiyayyarsa
Yace ya kikayi shuru haka kina kallona
Tace hmm ina takaicin abinda xan gaya maka ne
Yace duk abinda xai futo daga bakinki baxai ta6a xama takaici agareni bah
Tace ina da mijin Aure na.......
Da sauri ya kalleta cikin wani hali Yace maganar gaskiya kike gayamin dan.......
Ta katse shi da fa'din. Baxan maka qarya ba
Yayi shuru cikin wani yanayi narashin jin da'di
Can Yace toh Allah ya ha'dani dame kamarki ina barin nan
Tace ina maka fatan samun wacce tafini
Yace Nagode
Haka tana kallo ya juya motarsa yabar harabar gidan nasu
Tana shiga 'dakin Kakah kiran XEE ya shigo wayarta
Tace ya akayine XEE
Daga can XEE Tace hmm Ki saurari xuwana Tace Allah ya kawoki ta ajiye wayan
Kakah Tace yadai jikin naki Tace da sauqi. Tace Toh Madallah
Dama inasan cin tuwan dawa ne miyar ku6ewa. SAILUBAH tafa'di hakan cikin marairai cewa
Kakah Tace toh ai sai ayishi yau
Kusan qarfe shidda da rabi 6:30pm XEE taxo gidan nasu
Tace qawata ina cikin wani hali
SAILUBAH Tace ai in baki shiga ba a tambayeki dan rabuwarki da Surajo lokaci 'daya ba abubane wanda xai barki haka cikin Sauqi
Tace Kin san Allah na manta da wani Surajo dan nariga da nacireshi kwata kwata daga raina
Ni damuwata itace KHAMIS
Wayyo Allah na SAILUBAH yau yarannan ya rikitani
Ya jefamin sanshi araina lokaci 'daya
ashe dama duk wannan burgenin da Nake cewa yana yimin Ashe na fara sanshi ne dama haka so yake shiga xuciyar mutum farat 'daya
Wayyo ni XEE yaxanyi dasan Wanda na girma qaramin yaro
Saiga hawaye ya xubo mata
Cikin kuka tacigaba da fa'din watoh nafito daga department 'dinmu 'daxo ina tafiya ahankali dan wata gajiyace ta kamani lokaci 'daya
Ban kalli gabana Sosai ba. basai kawai nayi tuntu6e ba. Nayi taga taga xan fa'di.
Sai gashi ya yanko kwana......
Cikin sauri ya kama hannuna da janyoni jikinsa.
SAILUBAH Kaina ya sauka a qijinsa
SAILUBAH na shaqi qamshinsa
SAILUBAH saida xuciyata tabuga hankalina ya tashi dan jin wani fitinannan filing daya kusantoni
Sunkwi da kanta XEE tayi
Tayi shuru agun hawaye yana cigaba da xuba mata
Kana ta'dago ta kalli SAILUBAH da tasaki baki ido hanci tana kallanta
Tace wlhi jinayi dama in dauwama a haka a qirjinsa dan jin yanda qamshinsa yake shiga hancina
Daga nan saime..... SAILUBAH Tafa'da cikin buqata hankali tashe
By Hajju
Afuwa dan Allah MASOYA
[20/03, 17:09] 80k: [3:00PM, 17/11/2016] Rahamat Nalele 👯: 👯👯👯👯
*SAMAREEN*
👯 *BANAH*
👯👯👯👯
*TASU SALAN SOYAYYAR👯*
*Na Rahamat Muh'md Rufa'i Nalele*
Part 36 to 40
RAMADAN yayi Murmushi Yace ka kwantar da hankalinka pls dan Allah
Yace narasa tunanin da Xanyi RAMADAN Al'amarin ya shigeni Sosai
Kuma bansan ta'ina ni da ita xamu fara ba.
RAMADAN Yace hmm ka fita sanin ta inda xaku fara ai
Tunda bayau nasa ba baku Satan amsa ba ka share kawai abokina. Dan Akwai hanyoyi da dama.......
Ni Wlhi ban ta6a ganin Mara sanin abinda ya dace kamarki ba
Akan wane dalili xakiso qaramin yaro dan xubar da mutunci
Toh ai gashi nan alamu sunnuna RAMADAN ya gano Ki. SAILUBAH tafa'da cikin 6acin rai
Cikin wani yanayi XEE Tace ban damu da RAMADAN ya gano Sirrin xuciyata ba. Ni dai nariga da nayi tunanin xuciyata takamu dasan KHAMIS batun yanxu ba
Gwara ma da RAMADAN 'din ya ganoni nasan ba'abinda xai hanashi temakona
SAILUBAH Tace Amma.......
Cikin fusata XEE ta katseta da fa'din duk abinda xaki fa'da min Wlhi baxai shiga xuciyata ba SAILUBAH.
Dan narigada na gama fa'dawa tarkwan sonsa
Naga alamar bakisan rayuwa ba. Tunda bakisan miye so ba
Tashi SAILUBAH tayi tashiga toilet can tafitoh. Tace yanxu xa muje gidan Saudat 'dinne. ko sai anjima.
XEE ta harareta takawar da fuskarta
Murmushi SAILUBAH tayi kana taje ta dafa kafa'darta. Idan baki xama matar KHAMIS ba ai Al'amuran baxa suyi kyau ba
Kuma yanxu ne naga dace warku ke da shi
Ina san Kibi Komai ahankali dan in kikayi gaggawa abin baxai xo miki da kyau bah
Wlhi na fahimceki duk da gorin da kike yimin akan bansan so ba
Xanyi qoqari insan ya yake
XEE tayi Murmushi cikin jin da'din furucinta Tace nagode ma Allah dayasa kika fahimceni
Wlhi baxan 6oye miki ba. Damuwata ta qasu kashi biyu ne. Da qin fahimtata da kikayi da maseefar son KHAMIS
Naji sanyi araina ta 6angaranki. Yanxu yaxa muyi da KHAMIS
SAILUBAH tajah numfashi Tace inaso kirage xagewa akan san nashi
Tace ni Kaina bansan lokacin da xuciyata ta shagaltu da kallanshi 'daxo ba. Wlhi SAILUBAH bansan ya akayi nakamu da sanshi ba. Ban sani ba. Ina da aji
inada kamun kai.
Ke kin sani Amma lokaci 'daya na burkice. Tafa'da hawaye na xubu mata.
Yanxu ne SAILUBAH taji tausayinta. Tayi shuru tana tunanin ta'ina xasu fara
Can dai Tace bama rasa mafuta XEE kwantar da hankalinki
Can da yanma sukayi gidan Saudat rijiyar xaki inda suka tarad da ita Cikin damuwa
XEE Tace ya naganki cikin damuwa kina amarya
Tace ke dai bari. Ashe Auran mijin da yake da mata maseefa ne
Atare SAILUBAH da XEE sukace lafiya
Tace ba lafiya ba
Kunsan tunda aka kawoni gidannan ban qara ganin idan Mijina ba
SAILUBAH Tace kamarya
Tace Wlhi SAILUBAH Saidai inji muryarshi da shewarshi a 'dakin kishiyar tawa
XEE tawaro ido Tace duk soyayyar daya nuna miki
SAILUBAH Tace tab kuma sai kika xuba musu ido
Tace toh ya xanyi
Tana dai xuwa ta kawomin abinci tajuya tatafi........
Kan SAILUBAH tayi magana sai sukaji muryan Megidan nasu shi dasu RAMADAN
Da 6arin jiki yake CE musu kushiga tana ciki
Su RAMADAN sukayi cikin falan da sallama
Gaban XEE ya fa'di dake idanta na qasa batayi gigin kallan KHAMIS ba
Da murna Saudat Tace qannena
KHAMIS Yace Aunty Saudat ina wuni
Tace lafiya
RAMADAN ma ya gaidata
Yaqara da kallan Auntyn tashi Yace kutashi mutafi ko.
Ta hararesa da cewa toh yanxu mukaxo Yace toh xamu tafi kwa tawo
Tace haba mana 'dan Qanina dan Allah bamu mintina saimu tafi
Shuru ya mata
Saudat Tace kunga yayi shashinta ko
SAILUBAH Tace eh gashi nan kam Ko shigowa nan baiyi ba
Tace Wlhi xuwa anjima xakuji shewarsa shi da ita
SAILUBAH Tace hmm inda nice ke duk ubansu xanci wlhi. Dan saina dafasu ta cikin ruwan sanyi
Shawara 'daya xan baki itace kifuta daga har karsa kwata kwata Sannan ita kuma ki sake da ita dan bakisan abinda tataka ba. Sai kin shigeta xaki gane Komai. Daga wannan lokacin saiki San tawace hanya xaki 6ullo mata
Kina tashi da safe kigama aikinki da wuri sai kije kitchen 'dinta kice kinxo tayata aiki.
Duk yanda tayi dake akan kibari karki bari Ki kwantar dakai kimata ladabi da biyayya tanan xaki kasheta
Ya kasance Ki lixamci 'dakinta da xinmar kinxo tayata hira. Tanan Xaki gane inda tasa gaba
Shi kuma ko yaxo ya sameki a 'dakinta gaisuwace kawai xata shiga tsakaninki dashi kina gaishe shi kibar 'dakin dace musu sai da safe
Shi xai shiga cikin damuwar abinda yakeyi bai dace ba kuma me yake sashi yin hakan
Yayinda ita kuma xataji da'di aranta ta'dauka cewa ashema ke mijin baya gabanki. Kinga daga nan saita qara sakewa dake.
Ke kuma aidama ba xuwan Allah da Annabi kikeba sai kiyi saurin sanin Komai daga nan saiki 6ata mata shiri cikin ruwan sanyi. dan dama kin riga da kinsan Komai saike cafke mijinki tunda kinsan matsalar daga ina take
Amma fah kiriqe Allah a lamuranki bamai miki saishi bamai hanaki saishi
Tace hmm Nagode sosai Xanyi qoqari in gani Allah yasa mudace (AmEEn)
Dako kin temaki kanki dan Wlhi inda nice Sai dai axo rabamu dan ubanki xanci tunda mjin ba naki bane ke ke 'daya. Cewar XEE
KHAMIS ya qura mata ido na'dan daqiqu
RAMADAN ya kalli Saudat Yace Wlhi Aunty kima mijinki ladabi da biyayya karki biyema Auntyna Kinsan ita 6ata abu take Sam bata iya gyarawa ba
XEE ta kallesa Tace ai xata mishi biyayyan
SAILUBAH Tatashi tana cewa saita biyemun. kuma ban iya gyaran ba. Kasanni she'daniyace. Wlhi RAMADAN kafita daga idona in rufe.
Suma tashi sukayi harda XEE
RAMADAN Ya ha'da hannuwansa biyu Yace iyi hakuri toh
Ko kulashi batayi ba tafita daga falan.
Har waje Saudat tarakosu
RAMADAN Yace Aunty XEE da mota biyu muka xo kinga.....
Xaki shiga tawace in kaiki gida ko KHAMIS ya kaiki.
Da sauri KHAMIS Yace kaji ka da wani kwa'du.
Aunty LUUVAH xaka 'dauka tunda layinku 'daya ko nace gidanku 'daya
ko ba haka ba Aunty XEE ni saina kaiki gidan. Ya fa'da da kallanta cikin murmusawa
SAILUBAH tayi Murmushi tana fa'din aranta Lalle yarannan sun raina musu hankali. Yanxu haka sungama shirya abinsu xasu kawo musu wani alaye.
Tace hakan shine daidai. Tafa'da da shigewa motar RAMADAN
Ahankali XEE tashiga motar KHAMIS
RAMADAN ya 'daga mishi gira. KHAMIS yayi Murmushi ya shige shima natare da Auntys 'din nasu sun ganosu bah
Sanda suka fita daga layin RAMADAN ya tada tasu motar.
[3:01PM, 17/11/2016] Rahamat Nalele 👯: Suna tafiyar cikin nutsuwa RAMADAN ya kalli SAILUBAH ka'dan Yace Auntyna ki dinga gyara abu pls kidena 6atawa
Tayaya xa'ayi Ki gaya mata tashare mijinta.
SAILUBAH Tayi mai banxa
Shi kuma yanace sai tayi magana ya qara kallanta
Haba mana dan Allah Auntyna ki dinga gyara ki dena 6atawa ki dena xiga mutum yanxu kin xigata akan ta yaudari 'Yar uwarta inkece aka xoma ta wannan hanyar......
Da fusata ta katseshi da cewa. Waiwa ya gayama ni xugata nayi shawara na bata wacce ta dace da ita. Tafa'da da 6acin rai
Shuru yayi mata dama so yake tayi magana kuma tayi
Har suka qaraso gida bai qara magana ba
Yana parking tafuta daga motar da xafin rai. Yabita da kallo yayi Murmushi
itako tana xuwa 'daki tasaka key dan tasan ba barinta xaiyi ba
KHAMIS da XEE ko shuru kakeji acikin motar bamai magana acikinsu
Saima XEE ce da lokaci lokaci takan kalli KHAMIS 'din dan xuciyar tata hanata daurema kallansa
Da yayi parking a 'kofar gidansu ya kalleta cikin wani yanayi ya sanyaya murya Yace my Aunty mun'iso
Duk da XEE tasan sun iso hakan bai hanata kallansa cikin sauri ba. Dan muryar da yayi amfani da ita wajan yi mata maganar ta shigeta ba'dan ka'dan ba. Ya lura da hakan sarai. saiya futa daga motar yaxo ya bu'de mata motar kamar yanda masoyi yake yima masoyiyarsa
Tafi toh xata 'dau jakarta sai kawai yayi saurin 'dauka yana cewa da alamun gajiya atare dake my Aunty xanso in kai miki har gida idan kin amince min. Yafa'da da jifanta da wani kallo mesaka Sarki yayima Bawansa ladabi.
Da sauri Tace na amince. Ya qura mata ido
Tace lafiya kike kallona haka
Yayi Murmushi yace Wlhi wani tunani na shiga. Tunda nake dake Aunty XEE ban ta6a jin da'din muryarki irin tayau bah.......
Da'di kamar ya kashe XEE Tace sai yau ka ta6aji
Ya waro ido Yace kinga xan 'daure Kaina. Ai Kullun muryarki acikin da'din sauraro take
Tace toh Nagode
Ta shige gaba yana binta abaya yana qare mata kallo har suka iso falan gidan Yace mamah bata nan ne. Tace gashi dai daga dukkan alamu
Ta ibo drink taxuba mai a cup itama tasaka ma kanta kana Tace xanso kasha Qanina
Ya kar6a da Murmushi Yace banso shaba dan banajin shan Komai saboda damuwa Amma tunda kinaso nasha ba'abin da xai hanani Sha
Sanda ya Sha ka'dan Tace meya sakaka cikin damuwa Yace Wlhi Aunty wata nake So❤ saidai ta girmeni ban san ya xanyi bah
Da sauri ta furzar da drink 'din da yake bakinta ha'de da sakin cup 'din ya fa'di qasa......
jikake tass ya fashe
Tayi saurin xamowa daga kan kujerar da take cikin tashin hankali Tace wa kakeso kuma
Da sauri ya matso kusa da ita da ciro hankicif 'dinsa cikin nuna tsoro ya kama hannunta taji wani shock shima yaji Amma ya share ya fara goge mata hannun nata da gefan bakinta Yana cewa am sorry Aunty XEE na tada miki da hankali ko. Karki damu nasan baxata soni bah. Sai dai Wlhi baxan ta6a Auran wata mace ba in ba ita ba. Ya qarashe maganar da sake mata hannun nata
Aiko saiga hawaye ya xubo mata cikin kuka Tatashi xata bar falan.
Yace baxan ta6a yafema kaina ba idan har kika tafi cikin kukan nan kika barni batare da kin gayamin dalilinki nayin shiba
Juyowa tayi ahankali Tace KHAMIS nakamu tasan wani yaro wanda na girme masa gashi kaima kakamu dasan wacce ka girma. Ganin da nayi matsalarmu 'dayace shi yasani rikicewa har nayi wannan kukan
KHAMIS yajah numfashi ha'de da lumshe idansa yanajin kukanta har cikin ransa kana ya bu'de idan
Yace ki dena bana so bana san jin kukanki yana damun xuciyata pls kitsai dashi karci sakani cikin wani dan Allah
Ahankali XEE ta qaraso gabansa Tace shin abinda kafa'da haka yake
Yace akan me xan miki qarya. Yafa'da yana mai goge mata hawayan
Kawai ki share my Aunty xan kiraki anjima kiban shawa'a akan ya xan 6ulloma da ita budurwar tawa. Sannan kema kinemi shawarata akan wanda kikeso. Tunsa kinga mu SAMAREEN BANAH ne xan iya baki shawara yanda xakiyi dashi kema Kinga kyabani shawarar yanda xanyi da ita
Shuru tayi masa
Shiko har yakai 'Kofa ya juyo ya dawo dan yana so ya hanata bacci
Ya shafi gefan fuskarta Yace kimin alqawarin xaki cire damuwa aranki my Aunty
Tace idan na iya cire ko wacce damuwa araina ai baxan iya cire damuwar SO ba
Ya lakuce mata hanci Yace insha Allah xaki kasance da wanda kikeso dan shima yana MASEEFAR SONKI
Tace ya akayi kasan hakan bayan.....
Ya katseta da cewa saboda ko makawone yaji wuccewarki kawai yanasan Allah yayi halittar kyakkyawar mace anan
Tayi Murmushi Tace yanxu kai ka tabbatar da hakan
Yace Wlhi ayanxu bawanda ya kaini tabbatar da hakan koda ko Ya Surajo ne
Ta 'daure fuska xatayi magana Yace bye bye sai munyi waya Ya fitta
Tabishi da kallo
Sallar magriba SAILUBAH tayi tafa'da tunanin wani Alhaji Aliyu da ya kirata 'daxo wai abikin Saudat ya ganta dan Allah dan annabi tabashi dama yaxo gareta. Yanda yake rokwanta ne yasata bashi ixinin yaxo
Tana tunaninsa ne zaizo bayan Isha'i ne ko xaixo gobe bata sani ba
To ganin yanxu mah taji wayanta na ringing sai tayi tunanin shine
Ashe bashi bane wanine kuma wai Alhaji Aminu
Duk dai abikin Saudat ne suka ganta. Yana gaya mata dan Allah taso shi Yana Santa yana garin Abuja da xama. Baida mata. Kuma da maganar Aure xaixo gareta dan Allah tabashi dama yaxo gareta
Dan yanxu haka yana Cikin garin kano dan gobe yake san komawa Abuja
Toh fah😳 kunsan SAILUBAH da Alhazawan garin abuja ba qaramin so take musu ba dan ku'dinsu nan take taji ya wanta mata arai dan muryarshi nada da'di
Amma danta gwada shi sai Tace hmm banajin yau xaka ganni dan nagaji da yawo sai gobe
Kamar xai mata kuka yake mata magiyar tayi hakuri ya ganta dan Allah Tace toh kaxo Amma kasani minti biyar kacal xan baka
Yace angama ranki ya da'de
Bayan tayi sallar isha'i. Kyalliya tayi Sosai RAMADAN Yace Auntyna wannan kwalliya haka. Sam ta manta sunyi fa'da 'daxo taje takama hannunsa ta sakarmai kiss a kumatu Tace yau burina ya fara cika nayi saurayi 'dan abuja anjima xaixo
Da tsoro RAMADAN ya waro ido cikin wani yanayi Yace pls Auntyna Karki soshi dan Allah
Ta galla mai harara tare da sake hannunsa tana ta6e baki Tace Wlhi saina so shi
Kuma na ranshe da Allah kakorar min shi saina maka dukan tsiya
Yayi Murmushi Yace wasa nake miki baxan koreshi ba
Sam SAILUBAH bata yarda da murmushin da yayi ba. Dan tasan halinsa sarai fa'danta da cika bakinta baya hanashi korar mata su. Dan haka sai Tace suje 'dakin shi xata gaya mishi wani Abu
Haka ko sukayi gidansu dayin part 'dinshi
Suna shiga 'dakin tacire key 'din 'dakin nashi tafita da gudu ta kulle shi ta baya tana ai nasan maganinka
Ta window ta leqo tasheqe mishi da dariya Tace in yaxo ya tafi xan dawo in bu'deka. tana fa'din hakan tabar gun
Shuru RAMADAN yayi yana tunani
Gaskiya ta shamma ceshi dan yasa aransa ko ganinsa baxatayi ba xai koreshi Ashe ta ankare dashi
Yayi kwafah da fa'din ni da ke har abada muna tare da juna Auntyna
SAILUBAH na shiga gidansu saiga Alhaji Aminun yaxo
Sanda tashafe minti goma Sha biyar Sannan taje gareshi
Yace ina wini tauraruwa me haskake taurari
Tace lafiya da fatan kaxo lafiya Yace lpy lau
Tace toh Madallah
Nan ya qara fa'da mata shi ko Waye
Wai yana Saida 'dan kunne da tsarqa na xinare ne a Abuja iyayansa 'yan nan kanone sana'ar tasa ce takaisa Abuja
Sosai mutumin ya tafi da imanin SAILUBAH dan ganinshi da tayi kyak kyawa ga xaxxafar motar da yaxo da ita
Ta'dan dai bashi dama haka
Yace Yaji da'di xai turo iyayansa suxo dan bai ta6a SOYAYYA ba bayasan yaudarar mata
Kuma komai xa'ayi shi