Showing 1 words to 3000 words out of 126208 words
Chapter 1 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf
*ALK'AWARIN ALLAH*
_HUGUMA_
0️⃣1️⃣
"Allah ya taimakeki" lafazin da ya shiga kunnenta kenan,lafazin da a bakin mutum daya
take jinsa,furucin da ko mutuwa tayi ta dawo bata jin zata kasa tantance daga bakin wanda
yake fitowa dare da rana,a hankali ta waiwaya fuskarta qunshe da murmushi,yana tsaye daga
bayanta kamar koda yaushe,wannan annurin data saba gani kan fuskarshi kowanne lokaci na
nan shimfide saman fuskarsa,kwarjini cikar zati da haiba cakude saman kyakkyawar
fuskarsa,batasan me ya shigeta ba,sai taji bacin rai ya sauko mata a take,b'acin ran daya
sanyata ta dinga ja da baya,ja da bayan daya zama silar data soma ganinshi dishi dishi,yana
tsaye hannayenshi goye a k'irjinsa,dubanta yake ba tare daya tsaidata ko yace mata komai
ba,saidai annurin fuskarshi ya ragu cikin kaso d'ari zuwa kaso ashirin cikin d'ari.
A firgice ta farka,sa'annan tayi zumbur ta miqe tayi zaman dirshan saman gadon
nata,dukka hannayenta ta sanya ta dafe kanta dasu bayan ta dora gwiwar hannunta saman
cinyoyinta,gashinta mai tsaho da sulbi ya sako ya rufe fuska da hannayen nata gaba daya,inda
zaka ga fuskarta a sannan zazzafan hawaye ne ke layi saman kuncinta,inda ace tana da iko
data hana kanta mafarkinsa,da ta isa data hanashi bayyana a duniyar mafarkinta,sam ko kusa
ko alama bata da buqatarsa a duniyar mafarkinta kamar yadda bata da buqatarsa a zahiri
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" idan ka kasa kunnenka da kyau zakaji tana fada cikin muryar
kuka.
Ta jima cikin wannan yanayin kafin ta iya lallashin zuciyarta,kanta ta dago sannan ta sanya
hannayenta guda biyu ta tattare gashinta baya ta daureshi,kyakkyawa kuma sassanyar fuskarta
datayi jajur ta kuma tasa saboda kukan data yi ta fito fes duk da qarancin haske da d'akin keda
shi,a hankali ta zuro qafafunta qasa sannan ta yunqura ta miqe,kai tsaye ta nufi wata qofa dake
kallon gadonta ta murda ta shige.
Mintuna biyar kyawawa tayi ta fito daure da alwala,ta bude ma'ajiyar kayanta ta fidda after
dress da hijabi ta sanya,sannan ta nufi wani kebantaccen waje dake daura da gadonta tahau
saman abun sallar dake shimfide a wajen ta kabbara sallah.
Ita kanta batasan adadin lokutan data kashe zaune saman abun sallar ba,don sam bata
marmarin sake komawa barcin da tayi mafarkinsa a ciki,saidai shi bacci ba wanda yafi
qarfinsa,saboda haka sanda yazo yayi awan gaba da ita bata shiryawa hakan ba,sai jingina da
tayi da jikin gadon,carbin hannunta kuma ya silale ya fadi nan saman dardumar.
******* **** ********
Qarfe takwas na safiya ta kammala shirinta tsaf,tsaye tayi kawai tayi gaban mudubin tana
qarewa kanta kallo,tayi kyau iya kyau,irin kyan nan mai sanyi,saidai wasu abubuwa da suka
soma mata yawo akai take suka d'auke duk wata sauran walwala da taketa yunqurin d'orawa
fuskarta,qarar kira daya shigo wayarta yaso janye hankalinta,saita zubawa wayar dake gefan
mudubin ido tana kallonta ba tare data tabata ba gudun zuciyarta na qaruwa,bata kuma da
niyyar hakan ma gaba daya,har ta qaraci b'urarinta ta katse,tamkar mai jira kiran ya katse din
kuwa tayi gaggawar surar wayar ta kasheta gaba daya sannan ta jawo locker din madubin ta
jefata ta maidata ta rufe.
Cikin kasala kamar wadda tayi wani babban aiki ta koma da baya ta zauna gefan gadonta
tana ci gaba da kallon fuskarta cikin mudubi,ko kad'an bata qaunar ta raba wani abu ajikinta da
zai sata tayi kyau,don dai kawai bata k'aunar bata ran anty zubaida ne,amma da bata ga dalili
ko alfanun kasancewarta a haka ba.
"Auntyyyyy...." Muryar huda ce ta ratsa kunnenta,firgigit tayi tana dubanta kafin ta samu
qaqaro murmushi wa fuskarta
"Anty ina kwana"
"Lafiya huda ta,kin shirya kenan?" Ta furta tana janyo yarinyar kusa da ita tana gyara mata
daurin jelar rigar makarantar dake jikinta
"Ummi tace ki fito karmu makara"
"Muje na gama ai,fitowa kawai xanyi" ta fada tana miqewa,ta qarasa ma'ajiyar jakankunanta ta
ciro daya daga ciki da zata dace da shigarta,sannan ta dauko wata daban ta zuge,ta fiddo da
tarkacen ciki ta maida wadda zata fitan da ita sannan ta kama hannun huda suka fice.
A kitchen suka tadda anty zubaida tsaye tana shirya lunch box din huda,sanye take da
rigar bacci da qaramin hijabi,kallo daya anty zubaidan tayi mata ta karanci yanayin data
shiga,don haka bayan sun gama gaisawa ta shigar da qorafinta
"Yauma kinyi halin ne?" Murmushi kawai tayi wanda ya fito da ciwo tun daga zuciyarta zuwa
labbanta,maimakon ta amsata saita shigo da wata maganar
"Yanzu anty dan Allah ta yaya zanci gaba da kwanciya kina tashi kina girki bayan kula da uncle
aby da kike?"
"In kinason komawa kitchen sai kiyo qoqarin maida mode dinki yadda yake....." Cikin seriouse
ness ta waiwayo tana dubanta
"Cikin shekaru biyu mun soma yin nasara shahida....saidai bansan meke neman tarwatsa
nasarar da muka samu muka yi ta tsahon shekara biyun ba" ta fada cikin nuna damuwa,shuru
shahida tayi tana k'okarin kokawa da damuwar data taso mata,tun lokacin data san cewa suna
rayuwa ne ashe cikin gari d'aya da anwar bata sake samun peace of mind ba,murmushin yaqe
kawai ta jefi anty zubaida dashi,don bata son dukkan abinda zai sake jagula nutsuwar da take
ta yunqurin samarwa kanta,shuru ne ya ratsa tsakani,ganin bata da niyyar magana anty
zubaidan ta saki hannayenta tana dauko lunch boxs din huda ta miqa mata gami da cewa
"Shikenan,ku wuce ku karya karku makara,amma dai.....kota halin qaqa karki bari abinda ya
riga ya gabata a rayuwarki ya bata future dinki,koda anwar ko babu ki baiwa kanki qwarin
gwiwar xaki rayu,rayuwa mai inganci...."
"Zan rayu babu shi ne anty rayuwa mai inganci,babu batunshi ma cikin babin rayuwata" ta fada
wani radadi na tasowa tun daga cikin zuciyarta har saman fuskarta,murmushin da ita kadai
tasan ma'anarsa anty zubaida ta sako,shahida mutum ce me confidence,tana da qwarin gwiwa
saidai har zuwa yau kaman hakan yaqi tasiri ga wannan lamarin,duk da koda yaushe tana
yunquri da fadi tashin baiwa kanta wannan qwarin gwiwar,da idanu ta bisu har suka fice daga
kitchen din ita da huda sannan ta saki ajiyar zuciya tana yiwa deejan addu'a a fili da zuciyarta.
Suna gama karyawar abby ya fito,sanye yake da jallabiyya,mutum d'an kimanin shekara
arba'in da takwas,mai cikar kamala da fara'a,cikin girmamawa shahida ta gaidashi,ya amsa
fuskarsa qunshe da fara'a yana fadin
"Teacher uban karatu....baku wuce ba kenan?,hala yau keda dalibar taki tare zakusha bulalar
latti" murmushi ta fidda,tana mamakin abbyn sau da dama,wuta ne shi a wasu lokutan,amma
wani lokacin yafi xuma dad'i
"Yanzun nan zamu wuce abby" ta fadi tana sab'a jakarta
"Gwara kam,don qila hadi(mai adaidaitan dake kaisu makaranta)yana waje yana jiranku na
sanshi da himma" dai dai sanda anty zubaida ta fito daga kitchen din sukayi mata sallama suka
wuce.
A bakin k'aton gate din *NOOR INTERNATIONAL ACADEMY* ya saukesu
"Daganan zan kai adaidaitan wajen gyara....amma zanyi qoqari in sha Allahu na dawo na
d'aukeku"
"Karka damu,yauma muna shirye shiryen wasu abubuwa da za'a gudanar a makarantar,ina
zaton ma zamu d'ara lokacin tashi,zamu bi ta haya mu koma"
"To na gode,amma du da haka idan na gama akan lokaci zanzo" bata sake ce masa komai ba
ta kama hannun huda suka ratsa gate din makarantar zuwa ciki.
Dukansu ita da hudan sashen 'yan nursery da primary suka nufa,saboda a nan ne deejan
ta zabama kanta ta koyar,duk da tarin ilimi da Allah ya bata,wanda tana da cikakkiyar damar da
zatayi lacturing amma bisa wani dalili nata ta zabi koyarwa a qaramin mataki na 'yan nursery da
primary,tun daga bakin section din yara ke gaidata cikin nuna qauna da soyayya,yayin da ita
kuma take amsa musu cikin fara'a da jansu a jiki,sai da zata shiga staffroom sannan suka rabu
da yaran,suka wuce azuzuwansu ita kuma ta shiga ofishin malamai.
Office ne madaidaici mai girma da tsari,duk da girman office din su uku ne kacal a
ciki,makaranta ce da kallon farko.idan kayi mata zakayi tsammanin private ce irin mai tsadar
nan,saidai sam ba haka abun yake ba,makaranta ce da wani shahararren d'an kasuwa ya
ginata saidai akwai sa'ido da kulawar gwamanti akanta,duk da cewa shike dauke da duk wani
nauyi na makarantar,kama daga school unifoarm,littafan karatu,abincin da yaran zasuci na
break da dai sauran dukkan wasu lalurori,aqidarshi ce haka,yakan gina makarantar a duk inda
yaga hakan ya dace,ya kuma hada hannu da gwamnatin garin donta tayashi lura da
makarantar,bawai lura na su bada wani abu ba,a'ah,tsarin gudanarwa tsaro da sauran
abubuwan da ya kamata,kusan kowacce qasa dake africa ya gina makarantu d'aya,saidai a
inda makarantun suka fi yawa a nigeria ne yankin arewa,duk dalibin dake karatu cikinta yana
farinciki haka iyayensa farinciki da kasancewar dansu a cikinta,saboda ta tsaru da tsari mai
kyau,hakanan tana da dukkan wani qualities da akeson makaranta dashi.
Hidaya kawai ta samu cikin office din tana hada littafan dalibai da tayi marking,da alama
tana da ajine qarfe takwas,murmushi suka yiwa junansu
"Kinso makara yau malama shahida"
"Yau da gobe hidaya...." Ta fada tana zaman kan kujerar teburinta.
"Sai Allah..." Hidayan ta qarasa mata kana ta gyara yafen mayafinta
"Mun tashi lpy...."cewar hidaya
"alhmdlh....mun godewa Allah"
"Ma sha Allah....zan wuce aji don Allah idan kausar ta iso kice mata ga kayan nan ta duba"
"Babu damuwa" cewar shahida,tana kallon hidaya ta bude office din ta fice sannan ta maida
qofar ta rufe musu,saita maida kanta a hankali ta kwantar saman teburin dake gabanta,idanunta
a lumshe,batason tuna komai,batason tunanin komai,tanason ta saita kanta kafin lokacin
shigarta aji yayi,don nan da minti goma sha biyar periode dinta zai shiga.
***********************
"Dukkanin takardun na cikin wannan file din,sauran takardun da za'ayi amfani dasu a d'akin
taron ma gab suke da kammala,na shiga dakin buga takardun na musu magana sunce nan da
mintina goma da izinin Allah....engine ne yaso basu matsala" mutumin d'an kimanin shekara
arba'in dake zaune saman d'aya daga cikin qawatattun kujerun dake shirye a qayataccen office
din ya fada,yana bayanin ne ga dogo kuma tsayayyen matashin dake tsaye tsakiyar office din
yana kai kawo a hankali,hannunshi riqe da dan madaidaicin glass cup,yayin da d'aya hannun
nasa yake riqe da wata zungureriyar takarda yana dubawa,sanye yake da suit masu azabar
kyau da d'aukar idanu,wankan tarwada ne shi,dogo wanda ke tafe da tsaho da kuma 'yar qiba
kadan,wadda kai tsaye ba zaka kirata da qiba ta zahiri ba saidai ace murjewar jiki,doguwar
fuska gareshi wadda take cikakka,lumsassun idanu mai kama da wanda kejin bacci,saidai da
girmansu idan ya budesu sosai aduk sanda yaso hakan,bashi da cikar gashin gira can,saidai
gashin idanunshi a cike suke,siraran labba masu taushi,da qawataccen qasumba da aka
gyarata aka rage mata yawa da fadi,ta zagaya ta hade da habarsa da kuma qasan
hancinsa,kanshi saisaye ne wanda ya qawata fuskarshi saboda gyaran fuska da aka yi
masa,kana kallonshi kasan tsafta hutu da iya dressing sun kama gida a wajensa,kana kallonshi
kasan ba ma'abocin fara'a bane,sosai ya bada hankalinsa kacokam kan takardar hannunsa da
gani kasan abune mai muhimmanci yake dubawa,yayin da ta wani b'angaren daban ya bada
hankalinsa ga wanda ke masa bayanin
"Ina imran?"
"Yana sashen aje tsaffi da sabbin qarafa" kai ya gyada yana ci gaba da takawa sannu a
hankali,har yanzu hankalinsa na kan takardar hannunsa
"Amma ba tuni na bada umarnin a cire wancan a sanya sabon da mukayo order ba?"
"Sorry sir.....engineer din ake dako,yaudai yayi alqawarin zuwa ya hada" ya fada cikin nuna
tsantsar ladabi,bai sake cewa komai ba har na tsahon wasu mintina,sannan ya isa gaban
teburinshi ya aje kofin hannunsa,ya taka zuwa gaban matashin dake zaune ya bude files din
dake gabansa ya sanya takardar ciki ya rufe,sai a sannan ya dubeshi
"Karku wuce qarfe biyu ba'a gama kammala komai ba,bana son delay...."kafin ya gama fada
qofar office din nashi dake aiki da lantarki ta bude da kanta,wanda hakan ke nuna muhimmin
mutum ne zai shigo ciki,don ba kasafai take budewar da kanta ba sai bayan sakatariyarshi ta
sanar masa ya bada umarni sannan ta bude din.
Dukkansu maida idonsu sukayi kan qofar,tun kafin ta qarasa shigowa ya fahimci
wacece,hakan ya sanya ya maida idanunsa kan yaqub,don bashi da tabbacin yanayin da zata
shigo dashi,don haka ya sallameshi
"shikenan....zaka iya tafiya" a bakin qofar sukayi clashing da ita tana shigowa,cike da
girmamawa ya rusuna yana miqa mata gaisuwa,kaman yadda aka saba haka ta amsa a
daqile,cike da izza,shan qamshi taqama da isa,yaqub ya wuce ita kuma taci gaba da takowa
cikin office din.
Fuskarta qunshe da murmushi,hakanan idanunta na kan fuskarshi,taku take d'ai d'ai harta
kusa cimmasa,yayin da shi kuma yake kallonta yana nazarin shigarta,babu laifi shigar tata
tayau,doguwar riga ce mai wrapper,saidai kuma gajeran hannu ce,tayi rolling mayafi qarami a
kanta,high hill ta saka a qafafunta,hannunta ba komai daga waya sai key din motarta "It seems kamar bakayi farinciki da ganina ba M.A" ta fada a shagwabe tana kallonshi
"Uhummm....who told you?"
"Ba kowa....kawai yau nayi missing ganin cute face dinka,ka fita tun da sassafe ban samu
ganinka ba,me yasa baka yi break fast ba yau a gida?" Takawa yayi zuwa d'aya daga cikin
kujerun wajen yayiwa kanshi mazauni,itama yayi mata nuni da yatsa yana nufin ta zauna,sai
data zauna sannan yace "Me yasa zaki fito a irin wannan lokacin?" Farrr tayi da ido,tana jin wani dad'i na ratsata,a duk
sanda ya nuna kulawa a gareta takanji babu ya ita a fadin duniya,sai data saki murmushi
sannan tace
"Kai kadai na fito don na gani,kasan bazan iya wuni ban ganka ba" shuru yayi yana dubanta,can
qasan ranshi yana jinjina wanne irin so nafisa ke masa?,kalamanta sunyi shigen kama da na
wata,wadda ya soma qoqari da kokawar badda ta daga ranshi a yanzun da takeson taso
mishi,don ko kusa bashi da sha'awar hakan,itama kallonshi take,tasan cewa wannan plan din
nata ya d'anu,tanason dukkan wasu kalamai nata da yanayin kulawa yayi kama dana waccar da
tasan ta taba wanzuwa cikin rayuwarshi,duk da tana baqinciki da cewa kwaikwayonta shine zai
sama mata wani gurbi data dauki tsahon lokaci tana neman samu a zuciyarsa,duk da irin baqin
fenti da qin jini da yayyabe tarihinta a zuciyarsa,amma duk da haka kishinta take fiye da komai
a rayuwarta
"Naso na iso tun dazun sai aka samu akasi" ta katse kallon kallon da sukema juna,dan
muskutawa yayi kadan,cikin muryarshi dake nuna halayyarshi yace
"Akasi?,name fa?" Sai data d'an jaa fasali sannan ta sake cewa
"Wallahi wasu 'yammata ne suka so yiwa motata b'arna..."
"Me ya gamoki dasu?" Ya tambayeta kai tsaye yana ci gaba da dubanta,kafad'a ta daga sannan
tace
"No,karka damu,na musu uzuri saboda a make suke,kana ganinsu kasan sunsan sirrin shan
syrup,har zan hadasu da police sai kuma na wuce don bai kamata na b'ata lokacina akansu ba"
sexy eyes dinshi ya lumshe gaba dayansu,yana jin wani abu mai ciwo na sauka saman
zuciyarshi kamar ana d'iga masa wuta,wani boyayyen murmushi ta saki sannan cikin shagwaba
tace
"Karka damu nawan....ba abinda ya faru dani,am safe..." Bude idanun nasa yayi kaman zai
kalleta saiya kalli wani sashe na daban,yana sauke ajiyar zuciya a boye,a duk sanda yaji ko
yaga labari irin wannan babu wadda yake tunawa sai ita,hakanan haushi tsana da qyamarta
yakan sake ninkuwa a ransa.
"Yaya" ta kirashi tana son kauda damuwar data ziyarceshi,tunda haqarta ta cimma ruwa
"Yaune fa zamuje yaya?,don Allah karki sake cewa kana da wani uzurin"
"Saura minti goma sha biyar mu shiga meeting....saidai bayan mun kammala kuma" ya fada
yana miqewa a hankali kai tsaye ya wuce bandakin dake cikin office din nashi ta bishi da idanu
tana tantamarsa.
A hankali ya tura qofar bandakin sannan ya maidata ya kulle,gaban dan fanfon dake maqale
a bango mai hade da madubi dake manne a samanshi ya isa,yasa dukka hannayenshi ya dafe
sink din tangaran dake qasan famfon,qirjinsa na zafi haka zuciyarshi,ya jima a haka kanshi a
duqe yana kokawar maida yanayinsa yadda yake sannan ya dago yana duban kanshi a
madubin kamar baisan halittar kansa ba saiyau,maganganu yake da zuciyarshi,magana yake
gayawa kansa wanda shi kadai yasan meke kai kawo a ranshi harna tsahon wasu lokutta
sannan ya zare 'yar samam suit dinshi ya daura alwala bayan ya tattare dogon hannun ta
ciki,sai daya saka dan qaramin towel ya tsane ruwan jikinsa sannan ya maida rigar ya fito.
Da sauri ta jiyo a firgice suka hada idanu dashi,tana tsaye gaban wani dan qaramin
akwatinsa da ake budeshi da lambobin sirri,wanda ta budeshi ta kuma soma fiddo wasu
kayayyaki dake ciki,dauke idonsa yayi daga kallonta ya maida kan d'an akwatin dake zaune
dirshan daga can wani saqo na office din,baya taja cikin rawar murya muryarta can qasa tace "Am sorry" baice mata uffan ya taka a hankali zuwa wajen,inda ta janye jikinta ta rabe a
bango,ya durqusa ya dinga daukan kayan d'aya bayan d'aya yana maidasu muhallinsu,duk abu
guda idan ya dauka yana jin kaman yana qarawa zuciyarsa nauyi ne.
Har ya saka wani abu ya sake cirosu ya kalla,suna nan kamar yadda ta bashi su,hatta da
ledarsu itace dai wadda ta qullesu a ciki,d last thing data bashi a tarayyarsu,da hanzari ya
maidasu ya rufe sannan ya sauya lambobin sirrin ya miqe zuwa gaban teburinsa ya amsa
wayar daketa burari,sai daya kammala a nutse sannan ya aje,ya kalli nafisa data tsarki kanta
tare da ala wadai da shegen qwaqwqwafinta da yakeson ya bata mata