Showing 36001 words to 39000 words out of 126208 words
Chapter 13 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf
daukan 'yammatan,a sannan tuni ta yiwa anwar waya,shida da rabi
ya kirata yace ta fito yazo,su biyu ne ita da 'yar anty umma yayar ummanta,ga mamakinta yana
jingine jikin wata qaramar mota mai kyau qirar kia,ya sauya shigar jikinsa,wannan dinma yadine
wanda tare ya siyesu da wancan,saidai wannan ruwan madara ne lallausa,shima bamai tsada
bane amma sai taga kaf mazan wajen ba wanda ya kamoshi a kyau duk dacewa jayan jikinsu
yafi nashi tsada nesa ba kusa ba.
Shi dinma gaba daya saiya daina ganin 'yammatan dake kai kawo a wajen,ita kadai take
gani cikin dinkin ankon da ya amshi fatarta fiye da zato,kowa idonsa cikin na dan uwanshi a
haka ta qaraso,baice mata komai na sai gaban motar daya bude mata ta shige,shima ya bude
sit din driver ya zauna bayan kubra 'yar anty umma ta shiga gidan baya ya tada motar.
Saitake jinsu yau kaman rana ta musamman ce a wajensu,wani farinciki taji yana ratsata,ta
samu kanta da addu'ar Allah ya shiga lamarinsu ya buda ma anwar din,motar tayi masa kyau
qwarai da gaske kaman tashi
"Wani abokina ne ya dage lallai lallai yau sai na amsheta na dana,tun tana sabuwa yamin tayi
ban taba danawa ba,kinga kuma bai kamata naqi ba karya dauka wani abun ne na daban
kuma" kai ta gyada yayin daya dinga satar kallonta lokaci zuwa lokaci,har bintu ta fahimta ta
d'an masa tsiya,kunya ta sanya shahida daukan wani plate data gani ta saka jikin redion
motar,tadan qaro volume sanda taji batajin me yake fita daga cd din,waqa ce ta hamisu breaker
waqar jarumar mata,sautin waqar ya ratsa motar,kidanta ya fita sosai ta speakers din motar ya
karade ko ina,har ta saka hannu zata kashe anwar ya daga mata hannu alamar ta barshi,shuru
ya ratsa motar saidai gaba dayansu waqar na ratsasu ne,ji suke kaman su suke rerawa
junansu,shurun yaci gaba da yi musu jagora har zuwa inda za'a gabatar da bikin.
Sai daya rakata har ciki yayi mata mazauni,ya kuma gaya mata bai yadda da shiga rawa ba
sannan ya fito ya dawo cikin motar ya zauna,wanda ya faka ne a bakin titi,sai yabar murfin
motar a bude iska na shigowa qafarsa daya a waje.
Awa guda da fara gabatar da bikin yana zaune yasa sauraren redio
"Yauwa ga wani can....salamu alaikum" yaji an ambata,kanshi ya dago yana dubanta sannan ya
amsa,matashiyar budurwa ce wadda a qalla ta doshi shekara ashirin da d'aya,sanye cikin
doguwar riga da siririn mayafi,fuskarta saye da tafkeken glass,gabanta ne yayi mummunar
faduwa saboda cika mata idanu da kwarjini da yayi mata,uwa uba kyau data jima bata ganshi
tattare da wani d'a namiji ba,da qyar ta tattaro miyan bakinta tace
"Don Allah bawan Allah ko zaka taimaka ka duba mana motarmu?" Tayi maganar tana qare
masa kallo ta cikin glass dinta,sai daya kashe redion sannan yace
"Me ya sameta?"yarfar da hannu tayi cikin yauqi
"toh wlh ban sani ba,ina cikin driving ta soma slow sai kuma ta tsaya gaba daya" dan jim yayi
kafin ya jinjina kai ya fito daga motar ya rufeta sannan yayi gaba zuwa inda motar tata take.
Tsahon wani lokaci yana qoqarin ganin ya gyara saita tashi saita sake mutuwa,saboda haka
ya dago yana goge hannunsa da tsumma
"Gaskiya dole sai bakanike yazo"ya fadiwa nafisa dake gefe tsaye suna qare masa kallo ita da
qawarta mima
"Ya salam...bari na kirashi Allah yasa yana kusa" ta ciro tsadaddar wayarta ta soma
nemanshi,cikin sa'a yace yana kusa ta bashi adress din inda motar take
"Idan ba damuwa ko zamu dan zauna cikin motarka kafin ya iso saboda zama a wajen ba dadi"
nafisa ta fada sanda anwar ke komawa zuwa cikin tashi motar,tsayawa yayi ya waiwayo,kaman
yace a'ah sai yaga mata ne bai kamata ya barsu tsaye ba,tunda motar tasu ba zasu iya zama
cikinta ba,shi kuwa diya mace ako ina take yana da kishi da qoqarin kare mutunci da martabarta
bakin gwargwado koda bai santa ba
"Ba damuwa" ya fada yana sake yin gaba,idanu suka hada da mima ta kashe mata ido gami da
sakin murmushi suka bi bayansa.
Ya tsammaci duka baya zasu shiga,sai yaga mima ce kawai ta shiga bayan,nafisa ta shiga
kujera mai zaman banza,sai data zauna sosai sannan ta waiwayo ta dubeshi tana murmushi
"Suna na nafisa....kaifa?"
"Muhammad anwar" ya bata amsa a taqaice,idanu ta lumshe
"Nice name...sunan ya dace da maishi" saiya waiwayo ya dubeta kafin ya dauke kai,murmushi
ta sake saki
"Dan wanne anguwa ne kai?,Allah yasa ban matsanta maka ba da tambaya" kai ya jinjina
sannan ya gaya mata unguwar da yake
"Kai ai bamu da nisa sosai" itama tasu unguwar ta fada masa,kusan duk unguwannin nasu
maqotan juna ne,shuru ne ya sake ratsa tsakani yayin data lula duniyar tunanin yadda zata sha
kan anwar,don ba zata cuci kanta ba kallon farko taji anwar yayi mata,infact ma zata iya cewa ta
kamu da sonshi ne kai tsaye.
Isowar mechanic din shi ya katse duk wani tunaninta,hanya daya ta rage mata saboda haka
ta miqa mishi wayarta
"Idan ba zaka damu ba ka sakamin numberka mana,saboda nayi maka godiya" kai ya girgiza
"Basai kinmin godiyar komai ba" kai ta langabe
"Ya zama dole na gode maka,saboda alkhairi kayi min" baison jan zancan saboda ya gaji da
surutunta,saboda haka ya amshi wayar daidai sanda shahida ke takowa zuwa inda motar
take,tana iya hango komai saboda akwai haske cikin motar,mummunar faduwar gaba ta
samu,saidai ta kasa hana kanta qarasawa wajen,saitaci gaba da takawa harta isa bakin
motar,daidai sanda ya gama saka mata number din ta amsa tana murmushi tace
"Na gode,sai gani na gaba" ja baya shahida tayi a hankali sanda nafisa ke fitowa daga gaban
motar,idanunsu suka hadu dana juna,kallon kallon suka yiwa juna kafin nafisan tayi gaba mima
ta rufa mata baya,binsu shahida tayi da kallo har suka bacewa ganinta cikin duhuwar wajen
sannan ta dawo da dubanta ga anwar wanda sai sannan ya lura da tsaiwarta a wajen.*ZAFAFA
BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA
BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da
sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*
https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos
*Alqawarin Allah*
1️⃣1️⃣
"Wacece?,me takeyi a nan wajen?" Ta tambaya tana daga tsaye ba tare data shigo cikin motar
ba
"Motarsu ce ta lalace nayi qoqarin gyara musu,bata ma gyarun ba sai data kira bakinikensu"
"Shine tazo kusa da kai ta zauna?,har kana amsar wayarta tana jifanka da murmushi?"
"Shigo tukunna sai muyi maganar" ya fadi yana bude mata murfin motar sosai,kaita girgixa sai
kawai ta juya tabar wajen idanunta cike fal da qwalla,cikin hanzari ya fito don ya cimmata saidai
ina tuni ta kutsa cikin mutane ta bace masa bat,haka ya qaraci nemanta bai ganta ba,dole ya
dawo gaban motar ya dinga jera mata kira amma bata daga ba.
A hankali wajen ya soma yoyewa,ya sake shiga ya dubata amma kome kama da ita bai gani
ba bare ita
"Ya salam shahida....ya salam" ya dinga furtawa a jejjere sanda yake tuqa motar zuwa hanyar
gidansu amaryan,ba qaramin tashi hankalinsa yayi ba,bai samu 'yar nutsuwa ba sai daya isa
gidan yasa aka shiga aka binciko masa aka tabbatar masa ta dawo gidan nan sannan ya saki
ajiyar zuciya,nan kuma ya shiga jera aiken kiranta,saidai mirsis taqi zuwa,ganin dare ya soma yi
ya sanyashi haqura kan tilas yaja motar yabar unguwar,bai je gida ba sai daya soma kaiwa
abokinsa matar,yace daya barta ma sai sun gama bikin don tafiya ma zaiyi ta sati
guda,murmushi ya saki wanda kusan na yaqe ne,donshi kusan sam baiji dadin hawa motar
ba,yana ganin kaman itace silar faruwar komai,inda ace a motar haya suka tafi shikenan nafisa
ba zata ganshi ba,da amotar haya suka tafi nafisa ba zata rabi wurinsa ba saidai wajen
wani,don bashi da gurin da zata roqi alfarmar zama har shahida ta gansu tare,da a motar haya
ne da tuni tare zasu dawo da shahidanshi su rabu cikin farinciki sa walwala.
Ta gefan shahida kuwa hankalinta a tashe,gani take kaman za'ayi mata qwacen anwar
din,duk kwanan duniya idan ta kalli anwar din sai taji fargaba ta cikata,anwar nada kyau kwarjini
da cikar zatin da zai zama abun kwadayin mallakar kowacce mace,kallo daya ta yiwa nafisa ta
tabbatar 'yar masu dashi ce,idan hakan yayi nasarar janye hankalin anwar fa tayi yaya?,da sauri
ta kori wannan tunanin daga ranta,don fatan dorewar hakan,a ranar da qyar ta sami bacci duk
da wayarta na silent tana da yaqinin ta tara miscal na anwar din.
Itama kusan tubure masa tayi yadda ya mata kwanaki,qarshe dai saida suka dangana da
anty amina tayi sasanci kamar yadda ta saba,zuwa lokacin ba qaramin jigata yayi ba,wanda
hakan ya faranta ran shahida ta wani gefe,tunda ko babu komai ta sake sanin mizanin da zata
dora soyayyar da yake matan.
A haka rayuwar wannan masoya take ta kuma ci gaba da gudana,kowanne cike yake da
tsananin so qauna da kuma kishin dan uwanshi,kowannensu cike yake da buri da fatan
farantawa dan uwanshi,har zuwa sanda shahida suka soma shirye shiryen yin candy,a boye ba
tare da saninta ba don yasan zata iya hanashi anwar yasa akayi mata jaka da memo,yace
bazaiyi calender ba bare wani qato ya rataye a dakinsa ya dinga kalle masa mata,ko memo
dinma babu hoto a jiki,yayi mata key walder hakanan ya soya kayan da zata saka ran walima
complete,dukka yayi hakanne bada saninta ba don yanason mata suprise ne.
_*TAURARUWA MAI WUTSIYA*_
Tsaye take a hamshaqin falonta gaban window,wanda yaji komai da komai na kayan alatun
more ruwa,falone dan qarami saidai ya wadatu da dukkan wani abun buqata domin hutawa da
nutsuwar ruhi,tana sanye da riga da skert wanda iyakar skert din qaurinta
"Ina jinki mema....na zaqu naji daga gareki,wallahi tun ranar dana soma ganinshi har yau ban
sake samun nutsuwa cikin rayuwata ba....duk iya qoqarina na ganin na samu zuciyarsa abun
yaci tura,yana da wata izza kaman d'an wani,kwarjininsa shike sake dakusar dani,inajin sonshi
ya kaimin ko ina cikin jiki da ruhina" tayi maganar duka tana tsaye jikin window din ba tare data
juyo ba,idanunta na farfajiyar gidan data wadata da korayen tsirrai.
Tabe baki mima tayi,ita duka mamaki ya cikata,ta yadda feena ta fada qaunar talaka
matsiyaci kaman anwar din,ta kuma fita hayyacinta lokaci guda,haka kawai tana tsaka da more
rayuwarta,to amma ita nata yi mata aiki ta kuma biyata,indai zata biyata din ai shikenan
"Ba haka kawai kika kasa samo kanshi ba ai feena" meman wadda ke zaune kan daya daga
cikin kujerun falon qafarta daya kan daya tana karkada takardar hannunta ta fada,da hanzari
nafisa ta baro inda take ta qataso gaban feena sannan ta yiwa kanta mazauni kan wata kujerar
daban tana duban feena idanu bude "Kaman yaya?,meye dalili?" Wani shu'umin murmushi ta saka tana qiyasta kudin da zata tatsa
wajen feena a yau sanadin wannan zazzafar jaridar da zata saida mata
"Zaki iya tuna yarinyar da kukayi kallon kallon da ita ranar da muka zauna motarshi" yatsanta
manuni ta daga sama da sauri kaman maishirin bada amsa cikin aji
"Exactly....na tunata,tun ranar yarinyar na tsaye cikin raina...na rasa wacece mai shegen kyau
da izza haka,da farko nayi tunanin qanwarsa ce saikima naga basuyi kama ba tako ina"
"Right....budurwarsa ce" gaban feena ya fadi ta zaro idanu
"Wait....da saura fa" mima ta fada tana dariya qasa qasa sannan ta gyara zamanta
"Idan kin taba karanta labarin soyayyar romio da Juliet wannan sun wuce haka,qauna ce irin
wadda zata bawa bahaushen mutum mamaki,son junansu suke kaman tare aka haliccesu,daya
baya komai saida shawarar daya,daya baya iya tafiyat da komai saida daya,bari dai na baki a
taqaice a dunqule,sun narke sun zama abu daya...." "Dole su rabu su zama abu biyu kuwa...na fahimta,wato saboda itane na kasa cimma burina
kenan?" Ta tambayi mima kai tsaye,kai ta jinjina tana lumshe idanu sannan ta bude
"Qwarai kuwa....amma saidai karki damu akwai mafita" ta ambata tana warware takardar
hannunta,daki daki ta soma karanta mata abinda shahida tafiso da wanda bataso har sai da
nafisa ta gaji daji ta daga hannu tana dakatar da ita
"Jin wannan abun dame zai qare ni?,qara qonamin rai kikeson yi mima"
"Kina da gajen haquri inda matsalarki take kenan....amma tunda kina ganin haka shikenan bari
na wuce" ta fada tana ninke takardarta,caraf ta kama hannunta
"Mtsweeww,banason ko jin sunanta ne wlh,zauna mu qarasa" bata wani jaa ba ta zauna din don
tana lissafin abinda zata samu ne,taci gaba da karanto mata inda gabar qarshe take dauke da
"Ta tsani cin amana,ta tsani munafurci,ta tsani ta zauna dakai zuciya daya kai kuma ashe da
zuciya biyu kake tare da ita" tana kaiwa nan ta daga kai tana duban shahida sannan taci gaba
da karatunta,fagen anwar ta shiga,abinda yakeso da wanda bayaso inda shima tashi gabar
qarshe ta zama "Ya tsani mace mara kamun kai,ya tsani macen dake bin maza,sannan yayi masifar tsanar
mace 'yar shaye shaye" ta sake yin shuru tana duban feena,dan jim tayi sannan ta gyada kai
tana sakin murmushi sosai tana nuna mema
"Shegiya mima,sai yanzu na gane...ko shahidan yana tsoron kaidinki qarashe bayaninki" sosai
taji dadin yadda take sake samun karbuwa wajen feena koda yaushe,ta ninke takardar sannan
ta sake tattara nutsuwarta
"Yarinyar tana da ciwo tana da matsala cikin rayuwarta,duk da har yanzu ba'a gano wace
damuwa gareta ba,amma zamuyi amfani da wannan damar mu sanyata ta zama 'yar
maye,kinga mun samu matakin farko na rabasu,zai zama matakin farko ne saboda wanna kadai
bai isa ya rabasu ba bayan bai kamata da wani laifi ba bayan wannan,itama bata kamashi
ba,bayan ta zaba tantiriyar mashayiya zamu qara mata da sharrin bin maza...wannan kuma
aikin wadanda suka san kan na'ura mai qwaqwalwa ne,zamu saka mata cewa baya sonta ita
kuma yana tare da wata,duk zan kula da yadda komai zai kasance,naki kawai ki saki kudi ki
zuba idanu" murmushin nasara ya subucewa feena,ji take kaman ta samu anwar ta gama,dukka
kudin da yayi saura a jakarta ta zazzagewa mima,ta kuma yi mata alqawarin wasu
"Ya...zaki dinner dinsu mu'az dinne" idanu ta fiddo
"Me zai hana?,ai har na shirya qaryar da zanwa momy ta barni na fita,kedai jirani na shirya"
cikin mintina qalilan ta fito cikin wasu matsiyatan riga da wando,hannunta riqe da burmemen
hijab da take qoqarin sakawa mima na zaune na sheqa dariya,ta zuba duk kayan makeup dinta
cikin haka ta maqaleta cikin hijabin sannan ta dubi mima "Mu hadu a bakin gate,don da mun shiga tare ta ganki zata saka ayar tambaya" haka kuwa
akayi,ta isa wajen momy ta shirya mata qarya ta yadda ba yadda za'ayi ta ganota sannan ta fice
suka hadu da mima,tun a cikin motar ta cillar da hijabinta tahau tsara kwalliyarta yayin da mima
ke driving.
Cikin nasara da taimakon ubangiji ta kammala rubuta jarabawarta kaf,wanda a ranar sukayi
bankwana da dalibai da sauran malamai 'yan uwansu,a daren ranar anwar yayi shiga ta
musamman yazo don tayata murna,ya kuma bata duk wani gift daya tanada saboda ita,sai data
shiga dakinta tana dubawa abun ya sake burgeta,duk da anwar ba wani mai hali bane amma
Allah ya hore masa tsari da iya siyayya,komai daya bata ya burgeta,ta jima tana kallon wani
zobe,duk dana azurfane amma an qawatashi qwarai dole ya burgeka,zanen heart ne a jiki
amma heart din rabi ne,murmushi ta saki tana sakashi cikin yatsunta,yayi masifar yi mata
kyau,saita tattara kayan ta kaiwa ummanta wanda ita kanta ta yaba da qoqarinsa kaman yadda
abbanta ya yaba,hakan ya mata dadi qwarai,ya kuma bata tabbacin kenan bata da matsala
bata da wani shamaki da zai hanata mallakar anwar,tuna haka cikin jin dadi ya sanyata
qanqame filon da take kai tana hango kanta da anwar dinta a matsayin ango da amarya
qarqashin inuwa guda.
Cikin farinciki da walwala ta gabatar da walimarta,komai ya tafi lpy ya kuna qayatar sai jiran
sakamako,a sannan komai na tafiyar mata lpy,rayuwar tana hangen nan gaba kadan zata yi
mata kyau,komai zai qarasa dai daita musu,anwar ma an masa qarin albashi wanda hakan
dukka su biyun ya musu dadi.
*SANADIYYA*
Ana tsaka da haka gagarumin tashin hankali da yayi sanadiyyar lalacewa komai,ya zama
silar tabuwar rayuwar mutane da dama,yayi sanadin wargajewar wannan iyali,ya kuma silar
tarwatsa rayuwar shahidan...ya zama wani sanadi na dasa baqinciki mai tarin daci da zafi a
rayuwarta ta faru.
Rayuwa tsakanin mahaifinta da mahaifiyarta rayuwa ce ta rashin haquri,dauke kai yafiya da
juriya da akasan dukkan ma'aurata da yiwa junansu,fada gaban yaransu wannan ba wani sabon
abu bane tun tasowar shahidan,wanda hakan ya sanya bayan girmanta abun ya zame mata
wani ciwo da duk sanda ya taso mata yake mata zafi da quna a zuciya,dukkan wani mataki da
take ganin ya dace ta dauka a matsayinta na diya mai qarancin iko da abun fada ta dauka
harma wanda ya zarta huruminta amma babu abinda ya sauya,duk da alqawari da qoqarin
sauyawar da suke.
Kwatsam dare guda mahaifinta ya jijjigo maganar qarin aure suna tsaka da rayuwarsu cikin
rufin asirin Allah,wanda hakan ya sanya mahaifiyarta tayi tsalle ta dire tace batasan wannan
zance ba,dalilin daya janyo tashin tashina da fadan da bata taba gani ya wanzu tsakaninsu
ba,hakan ya sanya walwalarta da duk wani kuzari nata ya ragu,anwar ne mutum na farko
dayafu kusanci da ita a sannan shiya soma gane tana cikin damuww,amma baisan dalili ba,taqi
kuma sanar masa,ta yaya