Showing 33001 words to 36000 words out of 126208 words
Chapter 12 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf
a kunne sun haskeshi sosai kaman yadda
suka haskesu,idanunta cikin nashi saiya ja da baya ya juya ya soma barin wajen.
Wani tashin hankali ya ziyarceta,da wanne baki zata yi masa bayani?,ganin yadda
hankalinta ya wajen ya sanya saurayin shima juyawa yana kallon wajen saidai baiga komai
ba,bata sake bi ta kanshi ba ta shige gida da hanzari,wayarta ta laluba ta soma kiran layin
anwar din,saidai harta qaraci ringing dinta ta gama bai daga ba,hakan ba qaramin daga mata
hankali yayi ba,ba zata manta ba shekaran jiya suna hira yake ce mata
"Shahida tsoro nakeji,gani nake kaman zan rasaki,kaman kinfi qarfina" cikin mamaki tace
"Me kake fada anwar?" Murmushi yayi saidai ya taba har zuciyarsa
"Shahida...kina kallon kanki a mudubi kuwa?,irinki ba qananun mutane ke aurenki ba....ina
tsoron kada wani mai motar yasha gaba na" sosai taji haushi harma ta shige gida ta barshi ko
sallama basuyi ba,da qyar yasha kanta ya waya,to jiya bai samu zuwa ba kasancewar ya samu
dan wani aiki yana kulawa wani da provision dinsa cikin anguwarsu,ladan da yake bashi ba
wani mai yawa bane kasancewar kanti ba wani girma gareshi ba,amma ya karba yana yi
saboda ba mutum ne shi mai raina sana'a ba komai qanqantarta.
Kusan ranar kwana tayi tana kiran layin nashi amma ko sau daya bai daga ba,daga nashi
bangaren hankalinsa a tashe yake,hakanan zuciyarsa ke wani irin tafasa,kishi ne ki cinsa
sosai,fargaba ta lullubeshi,fargabar kada ace zancansa ne zai tabbata zai rasa shahidansa,duk
sanda ta kirashin bai daga ba sai yaji wani qunci na sake ziyartar zuciyarsa,bai iya daurewa
yana jin kiranta na shigowa amma ya kasa dagawa,daga bisani tilas ya kashe wayar duka yana
fatar ta haqura tayi bacci.
Kwana biyu ba anwar din ba dalilinsa,hakan ya daga hankalinta don har wajen kai sadaka
bata ganinsa,da yammacin kwana na ukun bayan ta dawo daga kai abinci wanda yanzu ajewa
kawai take wajen baba ado dake wajen ya raba a aiko da botikin don fir anwar yace ta daina
kaiwa,shiryawa tayi ta tadda ummanta zaune tana jan carbi bayan ta idar sallar la'asar
"Umma....zanje gidan anty amina"kai ta daga ta dubeta sannan ta shafa addu'arta
"gidan amina kuma?,makarantar fa?"kanta tadan sunkuyar tana wasa da farcenta
"hadda ake karba,kuma ni na bada tawa tun jiya" dan jim tayi sannan tace
"Shikenan,ki gaisheta....yauwa....kice mata yaushe za'a fitar da ankon umaiman,ki gaya mata
lokaci yana qurewa fa"
"Tohm umma....saina dawo"
"Zan rakaki yayaa" cewar mubina wada ke shirin islamiyya ta fada bayan ta watsar da hijabinta
wajen
"Babu inda zaki,makaranta zakije" cewar ummanta,tana jiyo ihunta ta saka kai zata fice tana
dariyar rikici irin na mubinan,dai dai lokacin abbanta ya shigo,saita koma da baya tana masa
sannu da zuwa yayin da yake tambayar abinda aka yiwa mubinan
"Wai gidan anty amina tace zata bini,kuma islamiyya zata"
"Ke ina taki islamiyyar?"
"Hadda ake amsa abba kuma na bada tawa tuni..."
"To ma sha Allahu,dama inason ganinki"
"To abba gani" ta dawo tana dawowa saman kujera 'yar tsuguno ta zauna,
"Shahida....ina fatan ba wani abune ya shiga tsakaninki da yaron nan ba anwar?"
"Abba meka gani?" Ta tambaya a sanyaye
"Kwana biyu bana ganinsa yana zuwa" shuru tayi tana tunanin amsar da zata bashi,dukkaninsu
ummanta da abbanta wani irinso sukewa anwar din,halayen anwar abun sone,nagarta gareshi
wadda ta zama tilas ko waye kai ya burgeka
"Uhmmm...bakice komai ba"
"Abba in gaya maka?" Mubina dake goge hawayenta ta fada,harararta shahida tayi amma
hakan baisa ta fasa magana ba
"Wanine mai mota yazo...umma tace taje ta sallameshi,shine yaya anwar ya ganshi ya tafi"
"Ubanki mai shegiyar magana" umman ta fada tana kai mata duka
"A'ah hadiza barta ta fada....kice kawai kin soma shanshano wani ne....ke shahida tashi ki
tafi,kema zamu gamu dake"
"Duk abinda kaga dama ka fada,tunda dai ba zuciyata ka shiga ka hangi haka ba shikenan na
gode Allah" tun kan ta fice daga soron nasu ranta ya soma baci,saboda taji suna gab da
kaurewa da halayyar tasu da suka saba,saitayi maza maza ta ficema don kada ta jiyo abinda
wunin yau zai sa ta kasa walwala,sam bata iya daurewa duk sanda wani sabani ya hasu tafi
kowa jin zafin abun,tqfi kowa shiga qunci,ta rasa me yasa dukkansu basu haquri da juna,kowa
kaman jiran kowa yake,kamar wadanda aka sakawa hannu cikin mu'amalarsu.
Ba dadewa ta isa gidan anty amina,ta taddata tana wanki ta saka mata hannu suka gama
tare,tanata tambayarta anwar kwana biyu bai leqo ba batace komai ba,har sai da suka gama
suka zauna dakinta suna ninke wasu kayan da suka soma bushewa
"Anty....nifa zuwa nayi ki mana sasanci da anwar"
"Sasanci kuma,me ya hadaku kenan?,yau kwana uku kuwa da zuwanshi ya gaidani"ana ya
gobe abun zai faru kenan?,shahida ta raya a ranta,batasan ma yazo din ba,jininsu ya hadu da
anty amina,gashi kuma ba wani nisa sosai tsakanin gidanta dana anty usaina,don har zumunci
ma suke yanzu ta sanadinsu,tsaf ta kwashe komai ta gayawa anty aminan,a take tasa shahidan
ta kirashi,saidai harta gama ringing bai daga ba
"kin gani ko anty?"shahidan ta fada idanunta na cikowa da qwalla
"Bari na kirashi da wayata" anty amina ta fada tana daukan wayarta,ringin biyu ya daga cikin
girmamawa
"Anty amina...da kanki?" Ya fara fada cikin girmamawa
"To ya zanyi?,diyata ta dagamin hankali?"dariya ya danyi
"Shahida ko?"
"Ita mana"
"Karki qona katinki anty bari nazo"
"Da kuwa ka taimakeni karta fashemin gata nan ta cika fam" da haka sukayi sallama tana duban
shahidan
"Shima a muryarshi kadai ya isa kasan cewa yana cikin damuwa da kewarki,wanne irin so
kukewa juna shahida?" Kunyace ta kamata saita soma sinne kai.
Ba'ayi minti talatin ba cikakke d'aya daga cikin yaran anty amina suka shigo suna cewa ga
uncle da yake haka suke kiranshi,anty amina ta saka hijabinta tace suce mishi ya
shigo.https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos
*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI
SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*KO KUMA*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da
sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARINGν ½νΉν ΌνΏ½*
ν ½ν±ν ΌνΏ½ν ½ν±ν ΌνΏ½ν ½ν±ν ΌνΏ½ν ½ν±ν ΌνΏ½ν ½ν±ν ΌνΏ½ν ½ν±ν ΌνΏ½ν ½ν±ν ΌνΏ½
https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos
*Alqawarin Allah*
1οΈβ£0οΈβ£
A nutse cikin sallama ya shigo ta daga kai a hankali ta kalleshi saboda ita kadai tasan yadda
tayi missing dinshi,shi dinma idanunshi na bisa kanta ji yake kamar ya shekara dari bai ganta
ba,amma duk da haka saiya gintse saboda tuno ganinta da yayi da wani,daya daga kujerun
falon ya samu ya zauna suka gaisa da anty amina sannan ta soma tambayarsa "Wai me ya hadaka da shahida?,duk ka firgitamin diya?"
"Ta firgitani dai anty...bakiga har rama nayi ba?" Murmushi anty aminan ta saki,yadda sukeson
junan nasu na bata sha'awa,bai boye komai ba ya gaya mata sannan ya dora da cewa
"Wallahi anty wani irin kishine dani,ina da matuqar kishi kan abinda nakeso,ranar dana ganta
wallahi anty ban iya bacci ba"
"To kayi haquri mr kishi....bari kaji me ya faru" ta shaida masa kamar yadda shahidan ta gaya
mata,nannauyar ajiyar zuciya ya saki yana jin kaman an sauke masa qaton dutse daga
zuciyarsa,sai a sannan ya sami salama
"A rude nake anty,shahida ba ruwanmu bace mu talakawa,hankalina a tashe yake kada wani ya
qwace min ita"dariya ya baiwa anty amina sosai har sai data dara
"karka damu anwar,shahida taka ce in sha Allah,yo shahida muka bata wani bakaiba ai inajin
fiya fiya zata sha ta mutum" sosai anty amina ta baiwa shahidan kunya,har sai data diba a guje
ta shige dakin anty aminan,shima ya miqe ya fice yana dariya.
A dakin ta taddata ta dubeta
"To laila majnun,saikije ku sameshi tunda na kashe case din,saiki kula a gaba"
"Na gode anty amina ta"
"Eh kyace haka mana tunda na dawo miki da hasken rayuwarki ko?" Dariya ta tuntsire dashi
sannan ta miqe ta zura hijabinta ta fice.
Yana tsaye a soron gidan amma qofar fita yake kallo,tadan tsaya kadan a bayanshi,a jikinsa
yaji tana wajen saiya juyo a hankali idanunsa zube fes a kanta,takowa yayi har sai daya rage
tazarar dake tsakaninsu sannan ya tsaya,a hankali cikin wata murya dake cike da mayen so
yace "Nayi kewar wannan kyakkyawar fuskar,wannan ruhin ya hana ruhina samun barci bare ya
samu salama,na cika da fargabar cewa na rasa hasken idaniyata,ashe abun duka ba haka
bane" sosai kalamanshi suka sanyaya mata rai cikin daqiqu kadan,tayi qas da kanta tana fidda
murmushi "A'ah dago kanki sosai don na samu qwarin gwiwar fada miki albishir din danaso yi miki tun
rannan mai mota ya korani"
"Don Allah ka daina zancan mai motar nan honey haba"
"Na daina" ya fada yana murmushi
"Na samu aikin kamfani Allah ya taimakeki...wani maqocinmu ne ya sama min,kwana goma sha
biyar zan dinga aikin kwana,kwana goma sha biyar aikin wuni,zasu dinga biyana albashi duk
wata dubu sha biyar" sosai fuskarta ta washe da fara'a tana jin farinciki na ratsata,tana jin
burinsu ya soma daukar hanyar cika,rasa inda tsoma ranta zatayi har sai daya tsaya yana
kallonta cikin mamaki,sun jima a soron gidan anty aminan kafin ya sanyata ta tattaro kayanta
tazo su wuce gida,napep ya tsaida musu har qofar gida,sanda suka sauka ta zaro kudi zata
biya ya harareta ya ciro daga aljihunsa ya biya,dariya kawai tayi,ko yaya idan yana da kudi ko
iyakarsu kenan jikinsa baya yarda tayi masa hidima da kudinta,nan ma sun dan jima kafin suyi
sallama ta wuce gida shima ya wuce.
Cikin taimakon Allah ya soma zuwa aikinsa,saidai babban qalubalen daya soma fuskanta
shine na rashin kudin mota,tafiya ce mai nisa tsakanin unguwarsu zuwa kamfanin haka yake
niqar gari ya tafi,duk da cewa ya saba tun sanda yana makaranta amma tafiyar bata kai ta
makaranta nisa ba,sai kuma abincin da zaici shima saiya dawo zai jiqa kwakinsa yasha
musamman idan aikin dare yayi zai dawo da safe,duka wannan bai dameshi ba tunda yasan
cewa komao lokacine,hakanan bai yarda shahida ko anty usaina sun sani ba saboda baiga
dalilin da yana namiji zai dinga daura nauyi wa mata ba,a haka ya cinye watanshi guda,saidai
kafin cikar watan ya fada yayi baqi,hakan ya sanya shahida ta sanya ayar tambaya a kanshi.
Ranar daya amso albashinsa yazo da daddare,duka ya zube mata albashin nasa yana
dubanta
"Me zanyi dashi honey?" Ta fada bayan ta gama saka musu albarka
"Inason ki dauki iya abinda ranki yayi miki,a matsayin albashin mijinki na farko" kai ta girgiza
tasan ko tace masa a'ah cewa zaiyi bata isa ba saiya dauka,saboda haka tasan maganinsa.
Da fari ta ware wasu kudaden tace wannan kudin kayan abinci da zai siyo ya dinga dafawa
yana tafiya dashi kamfani,ta sake ware wasu tace ya sake dinka kaya kala guda duk wata zai
dinka kala daya,ta sake ware wasu tace ya riqe ya kashewa ne,sannan ta cire wani abu a ciki
tace wannan ya kaiwa anty usaina ita yafi cancanta ta sanya albarka,next month kuma idan ya
sake amsa to ya fara ajiya saboda lalurorin yau da kullum,duk sai data gama kasafin ya cakude
kudaden waje daya sannan yace
"Qurun qus kin gama tatsuniyar taki?,toni ba haka nakeso ayi ba,da safe me mike ci idan zaki
makaranta?"baki tadan cuno
"Kome meye ya samu"
"Good" ya fada yana cire wasu kudi ya aje
"Indomie da qwai nakeson ki koma ci" idanu ta zaro tana kallonshi baki bude
"Honey...me kake fada ne?"
"Abunda kunnuwanki suka jiyr miki.....wannan kuma kudin kashewarki na wata gud....."
"Kaga...don Allah ka tsaya ka daina wannan lissafin mana" nan sa'insa ta kaure tsakaninsu,da
qyar ya yadda da nata lissafin bayan ta masa alqawarin wata na gaba ta yadda za'a sata cikin
kasafin,saidai duk da haka yayi cancel kudin kashewarsa ya bata dole ta amsa saboda ya kafa
mata sharadi.
Koda ya kaiwa anty usaina ma itama cewa tayi ba zata soma amsa yanzu ba,ya aje
wajensa zata masa magana idan lokacin daya dace yayi,haka ya dawo dasu ya miqawa
shahida
"Shikenan...zan saya banki na dinga tara maka,duk sanda kake da buqata saika amsa"
washegari kuwa ta sayi bankin ta zuba masa harda kudin daya bata,ta nuna masa sannan ta
roqeshi
"Don qaunar da kakemin kada kace a'ah,za'a tara ne ka siya abun hawa ko keke ne,ko baka
fadimin ba nasan tafiyar qafa kake" da qyar ya amince da shawararta,donshi a son ranta tayi
hidimar gabanta kawai dasu.
Wata hudu cif da fara aikinsa komai ya soma tafiya babu laifi,ta wanni fannin abubuwa da
dama sun soma sauqi,cikin godiyar Allah da yadda da cewa komai lokaci ne.
Cikin haka aka fitar da ankon bikin umaima,wadda take cousin ce a wajenta,ranar data
kawo musu ankon wuni tayi a gidansu,har dare tana nan,sanda ta tashi tafiya anwar yazo
shahidan na wajensa,mubina ce ta rakota tana nanata mata idan ta tashi dawowa ta kawo mata
alawarta,qarasawa tayi wajensu shahidan tana mata sallama daga bisani tace "Ina zuba ido saikinzo siyan ankon,kuma wlh baki isa ba ba wani daya da zaki duka biyun
zakiyi"
"To ummata" ta fada tana hararta,don batason ta tada zancan a gaban anwar din,sun riga da
sun gama maganar su tun cikin gida,da haka sukayi sallama umaima ta wuce.
"Wai ina bankin nan kuwa?"
"Yana cikin gida"
"Idan yana kusa daukomin shi idan yana kusa" bata ce komai ba ta shige gidan ta fito
dashi,bankin qasa ne ya amsa saiya sakeshi ya fadi take ya fashe kudin ciki ya bayyana,baki ta
bude tana zaton itace bata bashi dai dai ba ya riqe ya fadi haka,sai taji yace
"Yauwa yayi dai dai,tayani qirgawa" cikin mamaki ta duqa ta soma tayashi hada kudin,bayan
sun gama hadawa ya miqa mata yace ta irga,cikin murna da mamaki tace
"Da gaske ne kudi wawayene....ban zaci zasu kai haka ba wallahi" murmushi shima ya
saki,walwalar da take kawai ta isheshi farinciki
"Kije ki sayi ankon ko kala nawa ne,saura kiyi dinki,idan ba zasu isa ba kiyimin magana" ranta ta
ba'ta sannan tace
"Me kake fada ne?,kudin keken naka zaka bani kace nayi anko bayan sunkai kudin keke sabo
harda canji?,kuma ma tuni umma tace zatamin daya abba guda daya"
"Duk bansan wannan ba....abinda kawai na sani shahidana zata saka kaya kamar yadda
kowacce mace zata saka...kada kice zakimin musu indai baso kike raina ya baci" kaita duqar
"Allah ya baka haquri" dole ta fidda kudin ta sayi ankon kala biyu mayafi da abun daurawa,cikin
sati uku suka shiga hidimar biki amma hakan bai hanata ganin anwar ba,shima hakan ya masa
dama tunaninsa rashin ganinta.
Ranar da za'ayi dinner tun safe suna gidan kwalliya,qarfe biyar da rabi na yammaci ya kirata
yazo ganinta tana ina,itama yana ranta don jiya basu samu ganin juna ba basa unguwar kwata
kwata suna can aikin snacks,ta kwatanta masa gidan kwalliyar,ya gane gidan saboda cikin
anguwarsu ne.
Sanda ya iso tuni an gama mata tata,zata wuce kuma gidan bikin ta saka kayanta kafin a
soma dibansu zuwa wajen da za'a gudanar da shagalin.
Dan kwalinta a hannu ta fito soron gidan don kada ya bata mata kwalliyarta,dubansa tayi
yadda yayi mata kyau cikin wani sabon yadi blue black,wanda aka yiwa dinki irin na matasan
zamani,bata mancewa da ita yayi shawara kafin ya sayi yadin ta kuma zabar masa dinkin
qarshen wata sanda aka biya salary ya cira a ciki yayi,anwar nada wata baiwa ta daban,idan
yayi dressing kai kace shi din wani ne,daga kai yayi daga danna wayarsa da yake yana
dubanta,subhanallah ya fada a sarari,wani azababben kyau yaga ta qara masa,kai kace ba
shahidarsa bace,sai yayi sak yana ci gaba da dubanta,abun ba qaramin dariya ya baiwa
shahida ba har sai data d'an dara
"Yaya anwar wucewa zanyi fa ana jirana.....tun daxun kake kallona sannan kuma kai baka ce
komai ba" ta fada a shagwabe tana langabe wuya,ajiyar zuciya ya sauke sannan ya dubeta
"Ba inda zan barki ki fita a haka shahida....gaskiya zuciyata ba zata iya jurewa wasu su kalleki a
haka ba a filin Allah wajen bikin dake cakude da maza da mata"
"To a yaya kakeso na fita?" Ta fada tana cuno baki wanda hakan ya sake tafiya da imaninsa,dan
qaramin bakinta mai dauke da pink din labba yasha maroon din jambaki
"Mafita kawai ki wanke fuskarki" idanu ta zaro tana dubanshi
"Haba yaa anwar....haba don Allah" ta fada kaman zatayi kuka tana dan buga qafarta,fuskarsa
ya hade sosai,harga Allah yana da wani irin kishi akan shahidan,yana jin kaman zai mutu idan
wani ya zuba mata idanu bare akai ga batun furta yana sonta
"Ashe kuwa zaki shekara a soron nan,don na rantse ba zaki matsa ko inaba indai fuskarki da
wannan kwalliyar" tasan cewa da gaske yake saita rasa ya zata masa,hakan yasa ta juya ciki ta
yiwa amarya umaima magana,ita tazo ta roqa mata alfarma wanda daga qarshe yace saidai ta
cire eye lashes din da aka qara mata don nata ma ya isheta,sannan kuma a goge wasu
abubuwan da aka sa mata a fuska,saida akayi hakan sannan ya qyaleta,duk da haka a gaba ya
sakata tana gaba yana bayanta,sai faman sakin ajiyar zuciya yake,duk da an rage kwalliyar
gani yake kowa ma kallonta yake,adaidaita ya tare mata bai barta ba sai daya rakata har qofar
gidan bikin,yana mata sallama zai juya itama ta tubure kan dole yaje wajen bikin,yasan da biyu
tayi hakan don bai fiya zuwa wajen fate fate ba,to amma abinda bata sani ba gata tayi
masa,don har yanzu hankalinsa bai aminta ba da zuwanta wajen ita kadai,gani yake tafi
kowacce mace kyau,hakanan idanun kowanne namiji yana akanta
"Zanje na dawo,idan kun gama shiryawa kimin magana" tana masa dariyar cin galaba ta shige
ciki.
Qarfe shida aka soma