Showing 27001 words to 30000 words out of 126208 words
Chapter 10 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf
son tsafta,bata taba ganin kayanshi babu guga
ba,hakanan bata taba ganinsa da datti ko wani abu makamancin haka ba
"Daure ki fito princess...saiki kallenin da kyau" habawa,wata iriyar kunya ta taso ta lullubeta,bata
taba tsammanin yana kallonta ba,saita sake lafewa ta kasa fitowa,tashi yayi yana murmushi ya
tsaya a qofar soron nasu yana kallon mubina dake gaidashi,ya amsa yana shafa kanta gami da
yi mata wasu tambayoyi tana amsa masa,rabi duk a kan shahidan ne,kunya duk ta sake kamata
ganin yadda mubina ba abinda ya shalleta,komai ya tambayeta gaya mishi take,saida suka
gama hirarsu sannan yace
"ALLAH YA TAIMAKEKI...kona koma ne yau ba za'a samu ganina ba?" Dole ta fito ta saka
musu tabarma daga soron nasu,da yake yana da yalwa sosai masu wucewa ba zasu takurasu
ba.
Gaisheshi ta sakeyi ya amsa yana tambayarta gida kaman ba dazu suka rabu ba,cikin wani
shauqi da yake fusgarsu gaba dayansu.
[7/1, 9:19 AM] يتخا ةصفخ:
https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos
*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI
SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*KO KUMA*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da
sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*
https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos
ALQAWARIN ALLAH 08
Anwar dinne ya soma cewa"Kamar yadda kika sani na gaya miki daxun cikakken suna na
sannan kuma ni maraya ne,na rasa mahaifina da mahaifiyata da qannena guda biyu duka rana
guda" zaro idanu shahida tayi cike da mamaki da tausayi tana duban anwar
"Eh rana daya,sanadiyyar hatsarin mota da sukayi a hanyarsu ta dawowa daga qauyenmu"
"Wayyo....Allahu akhbar" ta fada fuskarta na nuna tsantsar tausayi,qwalla na cika
idanunta,tausayin anwar ya kamata,rayuwa ba uwa ba uba ya zata kasance kenan?
"Mu biyu muka rage a gidanmu,ni da yayata kaman yadda na gaya miki,yayata nada aure tun
kafin rasuwar iyayenmu,yanzu haka tana gidan aurenta ni kadai na rage ina rayuwa a
gidanmu,maganar gaskiya shahida zan gaya miki ba boye boye a tarayyarmu,saboda ina fata
Allah ya shiga lamarinmu,niba mai kudi bane,bani da komai sai abinda Allah ya tsagamin,karki
tsammacin samun rayuwa mai tsada,kyauta mai tsada ko nauyi daga wajena irin wanda samari
sukewa 'yammatansu,indai kina ganin tafiyarmu akwai matsala,duk da tsananin soyayyar da
raina ke miki zan iya haqura na barki da muradinki" kai take girgizawa,sam a batajin zata iya
rabuwa da anwar,qaunarsu dashi daga Allah take,wata qauna ce mai qarfi data kama
dukkaninsu cikin qasa da kwana bakwai,tasan cewa ba qaramin lamari bane a tsakaninsu
"Ni dinma ba wata bace,kaman yadda kake gani rufin asirin Allah ne da dukka bawa yake
qarqashinsa,ina addu'ar yadda muka hadu Allah ya tabbatar damu a haka" sai data fada kuma
taji kunya ta kamata,sun d'an jima kadan suna hira ita dashi,yana bata labarin abinda yake
karanta yanayin makarantar da dai sauransu.
Qarar wayarsa ce ta sa ya dakata da abinda yake gaya mata,ya ciro wayar daga aljihunsa
yana duba mai kiran,gabansa yadan fadi,don sam zuwansa wajen shahidan ya mantar dashi
abinda ya tunkarosa,neman mudin rigestration,hausawa suka ce mai kurmin ido da wuri yake
fara kuka,haka yake duk sanda suka soma exams tun a lokacin yake fara fafutukar neman
kudin,wanda tunda ya soma karatu haka yake,Allah gatan bawa ne,sai yake bashi kafin lokacin
da za'a rufe,saidai wannan karon yana fargaba,saboda ganin yadda rayuwa ta sake
cudewa,fadi tashi ya yiwa mutane yawa,babu ta sake samun gindin zama a rayuwar al'umma.
Saida aka sake kira ya sami ya daga da sauri,don babu ko ficika a layin nashi
"Ina zuwa in sha Allahu" kawai yace ya latse wayar ya maida aljihu,miqewa yayi tsaye
hannayensa cikin aljihun yana duban shahida qasa qasa,ta masa kyau qwarai,bai taba ganin
macen data masa kyau kaman shahida ba,komai nata mai kyaune,tun daga yatsun qafarta har
kanta,dauke kai yayi da sauri yana kwabar kansa daga kallon qurillar da yake mata sanda ta
dago kai tana dubanshi sanda taga ya miqe
"Allah ya taimakeki zan tafi" ya fada yana qawataccen murmushin daya sake fitar da sigar
kyansa,
"Allah ya tsare hanya...na gode"murmushi ya saki
"nine da godiya,yau an shayar dani irin abinda nake ji abokaina na fada....zumar
soyayya.....dama haka take?,haka akeji?" Dora tafin hannayenta tayi saman fuskarta ta rufe
tana murmushin jin kunya,yayin da ya zuba mata idanu yana kallon zara zaran yatsun hannunta
da suka dauki hankalinsa,ya sauke sassanyar ajiyar zuciya cikin ranshi yana roqon Allah daya
sanya yana kammala karatunsa ya shiga cikin sahun daliban da suke samun aiki da wuri,don a
yanzu jikinsa har ya soma sanyi da irin kyan daya lura shahida nashi,irin matan da masu kudi
ke rububin samu su aure,Allah kada ya sanya shahidan ta subuce masa,ubangiji yasa rabonsa
ce,da ya gama dacewa nan gidan duniya,tunanin daya dinga yi kenan har sukayi sallama ya
wuce.
Koda yaje inda ake kiran nasa ma ba wani biyan buqata ya samu ba,kudin da yake nema
bai samu ba,amma sai sam baiji wata damuwa can ba wadda ya saba ji a baya duk sanda yaje
neman kudin registration dinsa bai samu ba,wannan karon darensa cika yayi fal da tunaninta da
begenta,ya dinga juyi saman katifarsa,ya danna wayarsa yana zargin kansa me yasa bai karbi
number wayarta ba?,sai kuma ya saki murmushi daya tuna koya karba dinma ina yaga credit
din kira?,da gaka ya lallashi kansa yana addu'ar Allah ya kaimu gobe lafiya.
Tun daga wannan lokacin wata iriyar soyayya mai qarfi ta shiga tsakanin anwar da
shahida,dukkan tunaninsa nata ne,duk wani motsinsa shahida na ciki,tuni labari ya kai kunnen
anty usaina,kallon anwar din kawao tayi tana mamaki,tunda suke dashi bai taba kawo mata
zancan wata yarinya ba,hasalima koda da tsokana tayi masa zancan budurwa tabe baki yake
sannan yace
"Uhmmmm,anty kenan,anata kai wa yake ta kaya?,yanzu kojin labari kikayi ina kula wata ba
zaki tsawatarmin ba?,a wannan yanayin da muke ciki anty mu tsira da rayuwarmu ma,indai ina
da abun kula budurwa na kasa baki ba shakka bani da wani amfani a rayuwa" tunda har taga
yadda anwar ke muradin shahida sai batace komai ba,tunda haka ta faru tasan cewa soyayya
ce tayi masa mugun kamun da bai zata ba
"Su anwar manya,ashe an fada tarko" dariya yayi yana shafa kansa
"Anty,shahida ta dabance,na soma sonta a sanda babu tsarin soyayya a rayuwata gaba
daya,tana da hankali da kamun kai yarinyar,anty koke na kawowa shahida kika ganta zaki
sota,fatana kawai Allah ya dubeni dana kammala karatun nan na samu aiki,na kula dake anty
na kuma samu damar auren shahida" damuwar qaninta tata ce,su biyu suka ragewa juna a
duniya,anwar irin mutanen nan ne jajurtattu,duk da bashi dashi,duk da shima neman dafawar
wani yake amma indai ya samu ko yaya samun yake saiya tuna da ita,akwai sabo sosai a
tsakaninsu,ba wanda ke iya boyewa wani wani abun,sun zama iyayen juna abokan shawarar
juna
"Kullum fatana kenan anwar,ina maka addu'ar wahalar da kakesha a rayuwarka ta zame maka
alkhairi dajin dadin da har iyayenmu dake kwance a kabari xasu ji dadinsa"
"Allah ya amsa anty"
"Yanzu ya ake ciki da kudin resgistratin dinka?" Ta fada bayan ta aje masa shinkafa kwano guda
da wake rabin kwano,wanda aduk sanda ta samu budi take bashi ya samu ya sauya kalar cimar
da yake ci,duk da itama ahalin ni 'yasun take,amma haka suke raba wuya da dadi tare,kamar
yadda idan shi dinne ma hakanne,duk da yana qoqarin boye mata wasu abubuwa da dama
amma takan fuskanci wani abun koda bai gaya mata ba da bakinsa
"Muci gaba da addu'a,in sha Allahu kafin sannan Allah zai kawo"
"Allah ya dafa mana don isar annabi"
"S A W" ya qarasa mata,daga haka ya miqe,saita kwance bakin zaninta,yasan me take da nufin
yi saboda haka ya dakatar da ita
"Ina da hamsin dina da zan hau mota,bar kudinki" kai ta daga tana kallonshi,tanason karanto
gaskiyarsa ko akasin haka,don ya saba gaya mata haka,qarshe kuma dabawa yake a qafa har
gida duk da tazarar dake tsakaninsu saboda bashi dako sisi,ganin haka saiya juya da sauri
yana mata sallama,bai tsaya saurarenta ba ya fice.
Yana tafe a hanya tunani fal ranshi,shi daya idanunsa sun kada sunyi ja,fatansa da
addu'arsa Allah ya bashi abinda zai sakawa anty usaina dashi,tunanin shahida daya fado masa
a rai shiya dauke duk wani radadi dake ransa,har ya murmusa shi kadai ba tare daya san ma
yayi hakan ba,ya dinga tuna wuninsu na yau,yana zaune daga shagon balarabe kamar yadda
ya saba yana more kallonta,lokaci lokaci sukan hada ido su sakarwa juna murmushi,wani kallo
da yayi mata ya sanya man abincin dake hannunta ya kware duka cikin botikin shinkafar,kunya
ta kamata yayin dashi kuma ya dinga mata dariya,har a hanyar komawarsu gida ya dinga
tsokanarta kan ashe raguwa ce ita bai sani ba?,anya idan anyi aure zata iya dauke soyayyarsa
kuwa?,kunya ta sakata guduwa ta barshi da botikin,sai mubina ce ta shigo dashi,wannan
tunanin na shahida shi ya hanashi jin nisan tafiyar,har ya iso gida,sai yaji kamar baiyi tafiyar
komai ba,bai zauna ba ya kunna risho dinsa ya dora shinkafar,sannan ya tube kayanshi ya
shiga wanka saboda idan ya fito yaji dadin duba karatun jarrabawarsa.
Cikin wasu 'yan qididdigaggun kwanaki qalilan wata iriyar alaqar soyayya mai qarfi ta qullu
tsakanin shahida da anwar,wata iriyar soyayya mai ban mamaki da daure kai,zaka rantse da
Allah sun doshi shekaru masu tsayi tare,kowannansu yayi amanna da d'an uwanshi,kowanne
ya yarda cewa rayuwarshi ta d'an uwanshi ce,baqincikin dan uwanshi nasa ne haka
farincikinsa,wuya da dad'i basujin zasu iya rabasu,qaddara kuwa sun jima dayi mata magiyar
kada ta shiga tsakaninsu,komai nasu ya zama iri guda,tunanin da wannan yake a mafi
yawancin lokutta zaku samu irinsa dan uwanshi yake,tamkar tare aka haliccesu haka
sukeji,tamkar zuciya daya aka halitta musu su biyun kowanne bari daya na cikin jikinsa na
aiki,anwar kullum kwanan duniya shike rakota gida,bayajin an halicci wani uzuri a duniya da zai
iya hanashi rakota gida,yakan xauna a rumfar balarabe yana hangota cike da kishi,duk wani
motsinta yana kan idanunshi,baya samun nutsuwa ko sukuni har sai ta kammala ya tattara
mata kayanta ya kaita gida,da ace yana da iko da tuni ya hanata zuwa wajen,kishi yakanyi
kamar xai halakashi duk sanda take zaune tana rabon abincin,daga bisanima da yaji bazai iya
jurewa ba shike amsa ya zubawa kowa,itama a nata bangaren tanajin shine karsashinta,duk
motsi d'aya idan zatayi saita daga kai ta kalli qwayar idanunshi take samun salama,tana jinsa
har cikin jini da jijiyarta,zata iya sadaukar da komai dominshi,saidai tana mamakin yadda ko sau
d'aya bai taba zuwa ya karbi abincin da take rabawar ba kamar yadda sauran mutane ke amsa.
Bangare guda kuma bai taba gaya mata yanayin wahalar rayuwar da yake fuskanta ba,tadai
san cewa bamai qarfi bane,hakanan yanayinsa ya tabbatar mata da cewa shi din mai wadatar
zuci ne,don bata taba jin wani qorafi daga bakinsa ba,ko nunawa kasawa ko gajiya a fuska da
jikinsa ba gaba daya,hakan kuma ya sake burgeta dashi,ya kuma sake saka mata qaunarsa.
Yau bayan ya rakata sunyi sallama ta amshi botikinta ta juya zata shiga gida taga baquwar
mota qofar gidan nasu,tana kallon motar ta tabbatar da cewa sunyi baqi ne,kuma bata raba
d'ayan biyu uncle hisham ne,wanda shine ya baiwa ummanta kwangilar dafa abincin sadaka da
kullum take kaiwa bakin masallaci a rabar,da farincikinta ta qarasa cikin gidan,don kuwa jininsu
ya hadu qwarai da matarshi aunty zubaida,a tsakar gida ta taddasu,fuskarta washe da fara'a ta
aje botikin nata ta qaraso saman tabarmar da suke zaune anty zubaida na cewa
"Oyoyo 'yammata....sannu da qoqari" tana dariya dariya ta gaidasu,cikin kulawa suka amsa ta
juya tana tambayar yaron anty zubaida na faro farouq yashe sukazo?,
"Sannu da qoqari khadijatu....lallai na yarda ba qaramin qoqari da amana gareki ba.....gaskiya
ali Allah yayi maka baiwa da yarinyar qwarai" cewar uncle hisham,kanta na duqetana murmushi
"Alhamdulillahi kam,Allah ya azurtamu da diyar qwarai,mu kanmu muna alfahari da hakan"
umma ma kai take jinjinawa,don ita kanta zata iya cewa cikin yaranta shahidan ta dabance,wani
irin hankali da nutsuwa gareta,biyayya da kyautata iyaye tana sahun gaba,hakanan take
qaunarsu,dalili kenan dako yaushe itama take ta qoqarin daina biyewa mahaifinta suna raba
gari shahidan na kallo,sunfi kowa sanin cewa abun ba qaramin ciwo yake mata ba a rayuwa
"Nawa ake bina ne kudin kai sadaka khadija?" Uncel hisham ya tambaya yana fiddo kudi daga
aljihunsa,dariya ita abun ma ya bata,wanne irin binsa kudi?,mutum mai tsananin kirki da
kyautatawa a garesu?,ko iya kai abincin ma da take ita ta sani Allah ne kadai yasan ladan da
take samu
"Ba kudin da nake binka uncle....nima ai ina samun ladar kaiwa" kai ya gyada
"Na sani,wannan amma dole na baki haqqinki ne"
"Banda abin shahida aiko kayan kwalliya kya saya ki dinga gogawa idan surukin namu zaizo
ko?" Kunya ta kamata ta dan duqar da kanta qasa tana murmushi,mubina uwar surutu kuwa
tayi caraf
"Kullum sai yazo kuwa mamansu faruqu,yana da kirki kullum saiya kawo mana tsaraba,ko ya
bamu goma goma yace mu siya" kunya tasa shahida kasa zama saita miqe zata gudu,yayin sa
antu xubaida ta soma tsokanarta
"Ah lallai,zanso naga wannan surukin namu,na tabbatar shima yana da kyau da nutsuwa kamar
diyarmu..."
"Rabu dasu shahida....dawo ki xauna muyi lissafi" uncle husham ya tare mata,haka ta dawo
tana sunkui da kai ta zauna
"Mu lissafa kwana nawa akayi ana kaiwa?"
"Allah uncle ka barshi kawai"
"Naqi din" ya fada yana soma irga kudin
"Ki fada kona baki yadda naga dama"dariya ta danyi tana basar da maganar,kudi mai yawa ya
irgo yace
"toh gashi"
"Uncle ka bawa umma ta ajemin"
"A'ah a'ah,ba ruwan umma,wahalarkice karbi kiyi duk yadda kikeso dashi...iyakata in baki
shawarar me zakiyi dashi" cewar umman tana miqews don zuwa kitchen ta hadowa su anty
zubaida abinci,hannu biyu ta saka ta amsa tana masa godiya,a nan ta barsu anty zubaida harta
gama shirin islamiyya suna zaune suna hirarsu,tayi musu sallama ta wuce.
************************
"Malam balarabe ina kayan anwar?" Shahida ta tambayi balarabe mai kanti lokacin da
anwar din ke can yana hada kwanukanta don lokacin komawarta gida yayi
"Gashinan ina aunawa...bari na hada miki harda kwakin"murmushi tayi sanda take amsar ledar
kwakin daga hannunsa
"Anwar...anwar kaina dabanne,ko me zakayi da garin kwaki kuma?"
"Na'am?....ai aikin muhammadu kenan,ba yadda banyi dashi ya dinga sauyawa da wani abun
ba,ya amshi bashi duk sanda Allah ya hore masa ya biyani amma sam sam ya qiya...gaskiyarki
kuwa shi na dabanne,rayuwarsa ma haka,ni tsorona ma kar yayi masa illa yawan cinsa da
yake,bashi da abinda ya wuce gari" sam batasan zancan zucin da take ya fito fili ba saida taji
sharhin malam balarabe fadi ba'a tambayeka ba,saidai maganar tashi ta taba ta,ko a fuska bata
taba ganin wani abu makamancin haka daga wajen anwar ba,hasalima bai taba karbar abincin
da take kawowa wajen ba ko sau daya kuwa,a gabansa take rabarwa har ya qare iyakarsa ya
dauka mata kayanta suje gida ya aje mata ya wuce,a sanyaye take bin ledar garin da
kallo,tausayin anwar din ya kamata,ta yaya mutum zai rayu da cin gari kullum?,tsananin
maraicin ne yasa haka?,amma indai da gaske ne sun zama abu daya mai yasa bai taba gaya
mata ba?,ta yaya tana cin shinkafa kullum anwar yaci gari?,sosai taji haushin boye matan da
yayi,wasu qwalla suka cika mata idanu,saita dauki ledar kawai ta juya ta fice daga kantin ba
tare data ce komai ba.
Sanda ta isa wajen har ya gama hada komai tsaf yana dube duben nemanta,fuskarshi
yadan tsuke kadan
"Ina kuma kika shiga?,banason ki dinga darawa ko ina daga nan fa,kinsan halin mutane da
shegen kallo da sa ido"
"Ba wani waje naje ba,na karbo maka saqonka ne daga wajen malam balarabe"
"Balarabe kuma?"ya tambayeta yana nazartar fuskarta,fes ya fuskanci yanayinta ya
sauya,ganin bata ce komai ba yasa shi daukan botikin ya soma yin gaba,ga tunaninshi zata
biyoshi amma saiyaga bayansa take bi kamar yadda suka fara can watannin baya da suka
shude sanda suke baqin juna.
Cikin jinin jikinsa yaji sauyin yanayin shahidan bai masa ba,ko shakka babu akwai abinda ya
faru shigarta shagon zuwa fitowarta,zuciyarsa yaji ta tsinke sanda ta qyasa masa wani tunani
game da malam balarabe,baisan sanda yaja birki ba,ya waiwayo a sukwane,wanda saura qiris
suyi karo da juna,baya ta danja kadan tana duban qwayar idanunshi da suka sauya launi,saiya
sake matsowa gab da ita,kanta ta girgiza qirjinta na bugawa gana duban hagu da damarta,layin
tsit yake babu kowa,yana daya daga ciki layukan da yake da qarancin zirga zirgar jama'a
" me malam balarabe yayi miki?"ya tambayeta da wata iriyar rikitacciyar murya,tuni qwallar data
cike da idanunta ta soma silalowa,rikicewa yayi jikinsa ya soma rawa,kafin ya sake furta komai
ta bude ledar hannunta garin ciki ya bayyana,kallan garin yayi sannan ya kalleta,tashin hankalin
daya sauko masa yaji ya soma yayewa,hankalinsa ya soma kwanciya ganin ba abinda
zuciyarsa ta raya masa bane,ya saki wata wawuyar ajiyar zuciya wadda ta sanya duk wani qarfi
na jikinsa raguwa,har sai daya jingina da bishiyar da suke tsaye qasanta yana sauke wata
qatuwar ajiyar zuciya
"Me yasa zakamin haka?,wannan abincine yanzu?" Sai yanzu ya sake fahimtar dalilin
sauyawarta,kuka take sosai,saiya amshe ledar ya dora saman botikin daya aje gefansa
"Wannan bai isa ya zama dalilin da zai saka min ke fidda wannan tsadaddun hawayen
ba,wanda duk duniya babu kudin da zasu iya sayen darajarsu a wajena.....ungo nan share
hawayenki" ya fada yana bata qaramin handkherchief dinsa wanda baya rabo dashi saboda
share zufa da yake gwanin zufa ne,hannu ta saka tana goge fuskarta,tsahon minti biyar ya bata
don ta nutsu sannan ya bata damar magana
"Ohk...yanzu fadi duk abinda yake damuwarki"
"Kafi kowa sanin ba haka mukayi alqawarin gina tarayyarmu ba,munyi alqawarin xamu ji dadi da
wuya a tare,kukanka nawa ne,kukana naka ne,haka nan dariyarmu,don me zaka boyen
wannan?" Murmushi mai kyau da qayatarwa ya subuce masa,kullum