Showing 90001 words to 93000 words out of 126208 words

Chapter 31 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf

faru ba,a hankali ta
motsa labbanta sannan tace
"Kawai bana sonshi,shima kuma baya sona,hasalima mun rabu dashi a qalla shekara shida
kenan,ba wanda keda muradin wani" shuru anty usaina tayi tana nazarin kalamanta,ba shakka
akwai wani abu,amma dukkansu amsa kusan guda ce,jiya jiya ta titsiye anwar din kan meye
sanadin rabuwarsu da shahida amma ya kasa bata amsa daya qwaqwqwara,kowannensu
bayason fallasa asirin dan uwanshi,hakan na nufin akwai ragowar wani abu da yayi saura game
da zukatansu qarqashin zukatansu kenan koda su basusan da hakan ba?
"Amma shahida....ya akayi kikasan baya sonki?,kuma dama an taba rabuwa hakanan babu
wani dalili?"tambayar taso kaita maqura saboda rashin amsa
"Miji da mata ma kan iya rabuwa haka kawai ya saketa badon ta masa komai ba,saidon
qarewar wa'adin zamansu da Allah ya qaddara musu" saitayi shuru tana hadiyar zuciya tana
neman amsa ta biyu da zata bata wadda zata gamsar da ita,da qyar ta iya hada abun fadi
bayan anty usainan tace "Uhmmm,ya akayi kikasan baya sonki?"
"Duk wani abu na nuna kulawa ko xiyara da zai nuna saurayi yana son budurwa babu shi tattare
dashi,sau daya ya taba zuwa wajena,shima bamuyi ganawar dadi dashi ba,ta yaya zance yana
sona?" Ta qarasa maganar badon abinda ta fada ya dameta koya dadata da qasa ba,a'ah,ta
fada ne kawai donta riqeshi hujjar da anty usaina zata taimaka mata ta rana wannan auren da
take kallonsa a matsayin qarfen qafa mai wuyar kwantuwa a gareta.

Lallai ya zama dole ta shiga alaqar shahida da anwar,tana fata nan gaba dukkansu suyi

dariya,tana fatan ko meye silar shiga tsakaninsu nan gaba ya zama tarihi,rayuwarsu ta koma
kamar yadda take a baya
"Naji dadi da kika kasance yarinya mai biyayya wa iyayenta,ina mai miki kyakkyawan fatan ba
zaki toxarta ba in sha Allahu,biyayyarki zata kai miki da ixinin ubangiji" da wannan kalaman
sukayi sallama,ta fice daga gidan bayan ta samu umma ta roqeta kan karta gaya mata
dangantakarta da anwar,donta tabbatar hakan zai baiwa shahidan kunya.
Tun a kan hanya ta soma gwada number anwar din,saidai bata sami wayarshi ba akashe
take,da alama yana muhimmin wani abune,dole ta katse kiran ta isa gida,saidai lokaci lokaci
tana gwada number tashi ko xata dace ta shiga.

Tana idar da sallar magariba ta soma shirin barin gidan,umma ta dubeta
"Amma da kin dan jinkirta tafiyar tukunna,saboda garin a dinke yake da hadari ga iska ta soma
kadawa"
"Idan ya sauko bansan ranar da zai dauke ba,anty zubaida kuma zataji shurun yayi yawa,don
ban gaya mata ma ina nan ba"
"Shikenan,Allah yayi miki albarka,yasa albarka a rayuwarku"
"Ameen" ta amsa tana maida qwallar dakeson fitowa,haka ta baro gidan tana tafiya kamar
wadda batason taka qasa,wanda bai sani ba sai ya zaci salo ne ko tana sane,amma ba komai
bane sai tsabar damuwa dake cinta a rai,tana jin yadda hadarin ya taso sosai sanda takai
tsakiyar layin nasu,iska ta dinga kadawa tana ratsa jikinta,saidai sam bata damu ba,bata damu
da ruwan ya sauko ya daketa ba,hakanan bata damu data koma gida donta samu mafaka ba.

Daidai lokacin da motarsa ke tsaye qofar gidan anty usaina wadda ta buqaci ganinsa a yau
basai gobe ba,yana zaune cikin motar baikai ga yiwa mai gadi horn ba bare ya bude masa,ya
tsaya ne amsa waya,dukka gilasansa a rufe suke ruf kamar yadda al'adarsa take yawanci idan
yana cikin mota,bugu da qari kuma ma sabida iskar dayaga ta taso sosai,wanda yasan ba za'a
rasa qura ba cikinta,gefansa ya kalla kamar wanda aka fisgi hankalinsa,sai yaga kaman itace ta
wuce,yaci gaba da amsa wayar yana kallon bayanta,tabbas ita dince,amma me take har war
haka duhun magariba ya mamaye gari bata koma gida ba,idanunsa suka ci gaba da kallonta
har lokacin data dan bada tazara daga inda yake,yana shirin janye idanunsa yaga yayyafi ya
soma sauka ta gilashin motarsa,yaso ya dake yaso ya dauke kai ya saka motarsa cikin gidan
anty usaina amma saiyaji kaman umarni,a zafafe yace
"Oh god" yana zare belt din jikinsa,cikin zafin nama da kuma jin haushin kansa da kansa ya
bude murfin motar ya fice.

Yana kuzari da halittar ba daya bace,hakan ya sanya cikin qididdgaggun taku ya cimmata
"Daga ina kike haka?" A nutse ta waiwayo tana dubansa sanda take gab da qarasa bakin
titi,saita juya da niyyar ci gaba da takawa ba tare data amsa shi ba
"Wai sanda zaki fita ma kin tambayeni ne?,saboda tsabar rinton zunubi?" Kalaman sun mata
ciwo,wato tun yanzu yake nufin xai mulkata kenan?,hakan yasa ta tsaida tafiyar tata ta juyo ta
dubeshi
"Kai waye da don zan fita saina tambayeka?"

"Kinfi kowa sanin ni waye ai ba buqatar na maimaita miki,banason dogon zance wuce muje na
taimaka miki na saukeki,amma kafin sannan idan kina da niqab ki saka a fuskarki kar mutanen
unguwa su ganmu tare su zaci nima dan harka ne" ya kai qarshen zancan yana dage girarsa
duka biyun,wanda hakan ya masa kyau ainun duk da fuskarshi a murtuke take,sosai kalaman
suka fusatata wanda hakan ya sanyata ta juyo gaba daya ta watsa masa idanunta da suka sake
budewa saboda bacin rai,hakan ya tilasta masa dan qanqance nashi idanun gami da damqe
hannayensa dake zube a aljihu
"To hell with your taimako...Allah suturu buqui,har abada bana son taimakonka,sannan kuma
aikin banza kake harara a duhu,da kake gudun kar a ganmu tare me ya kaika neman dauramin
igiyarka,idan da gaske kake qyamata aiya kamata ka gujeni da gaske ta yadda ko qasa daya ba
zaka hada dani ba bare inuwa daya,indai ka cika kai anwar ne ka aikata hakan" qaramin
murmushi ya saki daya sake fitar da kyansa,ya dage dukka kafadunsa
"Ba zaki taba samun yadda kikeso ba,niba qaramin yaro bane bare kalamanki su tunzurani nayi
miki yadda kikeso,abu daya kawai na sani shine,na riga dana biya sadakinki,saboda haka ina
da power a kanki ko kinqi ko kinso...saboda haka ki wuce muje" dogon tsaki taja wanda ya ratsa
kunnuwansa,sannan ta watsa masa harara ta juya taci gaba da tafiya,bai fasa binta ba shima
har suka isa titi.

Adaidaitan farko data tsaida ya sallameshi da dubu daya yace yane abinsa,na biyu ma
haka,na uku kuwa da yame dattijone yace masa baba kaje matata ce yaji takeson yi,na bata
haquri taki haqura,nan yasa bawan Allahn ya tsaya yana mata nasiha,inda daga qarshe ya
sallameshi da dubu uku ya amsa yana godiya,ta hudu kuwa ya samu sauayi maiji da tashen
girma yaso masa gardama.kan saiya dauketa tunda itama tana son shiga
"Kana sha'awar xaman gidan kaso kenan?" Harya karkata baki zai masa diban albarka saiya
nutsu ya qarewa shigarsa kallo,tun daga takalminsa,kayan jikinsa zuwa agogonsa,aibabu shiri
yaja abun hawansa ya fece,bacin rai ya taru ya rufeta ruf sanda ta kalli titin ta ganshi fayau ba
wani sauran abun hawa na haya kuma nan kusa,ta waiwayo zata gasa masa magana ko xataji
sanyi,kadan ya rage fuskarsu ta gwaru,sam batasan yana bayanta ba a tsaye,da alama kuma
duk tsahon lokacin kallonta yake,baya yaja yana bata fuska
"Ke baki da kunya ne?,akan titi kike neman ki rungumeni?,toki maida qwalamarki,ni ba naki
bane" kawai saita fashe da kuka ba tare data shirya ba,saboda ya gama cutarta,bata ga wani
kalma da zata fada masa ba wadda zata rama abinda ya gaya mata,minti biyu kacal ruwan
sama ya soma sauka,ya kalli sama sannan ya kalleta "A karo na qarshe nake gaya miki ki wuce mu tafi" baya taja saman wasu tayoyi da masu faci
suka tashi suka barsu a wajen ta zauna,ta gwammace ruwan yayi mata koma meye data bishi
kota shiga motarshi,ganin ta zauna dafa'an ya sanyashi juyawa ya koma cikin layin don dauko
motartashi zuwa nan bakin titin dukda yadda ruwa yake dukansa.
Yana isowa wajen yaga tashinta cikin adaidaita sahu,qaramin murmushi ya sube masa,wato
dama tana da taurin kai kenan?,saiya sake baiwa motar wuta harsai daya je daya side din na
adaidaitan,ya tabbatar ta ganshi sannan ya barsu suka wuceshi,a baya yaci gaba da binsu har
xuwa sanda yaga shigarta gida sannan ya karya kan motar ya koma gidan anty usaina.

Sanda ta shiga gida baqinciki da takaici ya sake cikata ganin yadda gidan har baqi yadan
samu,hakanan ga kayan amsar lefe a kammale gobe kawai suke jira,hasina ma ba'a barta a
baya ba,ganun zata saka mata ciwon kai da tsokanarta yasa tayi zarcewarta daki ko tsayawa a
wajen batayi ba bare ta zauna,gaban mudubinta ta tsaya tana kallon yadda ta jiqe gaba
dayanta,haushinsa ya sake cikata,taji kaman ta sake fashewa da wani kukan,duk shi yaja
mata,da ta shiga adaidatan a lokacin daya dace da duk hakan bata faru da ita ba,haka ta ringa
cire kayanta daya bayan daya ta daura babban towel ta shige bandakinta ta hada ruwa mai zafi
tayi wanka.*Alqawarin Allah*https://youtu.be/alR4jOvvQUc

*Alqawarin Allah*
3️⃣3️⃣



Washegari da wuri tabar gidan fiye da yadda ta saba fita,ko a kamfaninma masu gadi kawai ta
taras,ta bude office dinta ta shiga ta zaun donko mai maita shara ma bata iso ba.

Sanda aka tashi ta tsaya tunanin inda zata,don tasan wala'alla dai dai lokacinne ma gidan
yake a cike,yankewa kawai tayi ta tafi gidan oga rayyan,ba bata lokaci ta gayawa mai
adaidaitanta ya wuce can da ita.

Sosai taji dadin zuwa gidan,a rayuwa gidan yana burgeta qwarai,yanayin mu'amalar
jama'an gidan,nan wajen raihana ta zauna suka sha hira sosai,sai bayan sallar magariba
sannan tayi haramar tafiya,nan ta cikata da turaruka tana cewa
"Gashi amarya,naji oga yace kin kusa shiga daga ciki,ki fara amfani da wadan nan kafin lokacin
xan kawo miki na amare"
"Hmmm" kawai tace tana dan fitar da murmushin da baikai zuci ba daga fuskarta.

Tun daga harabar gidan zaka san cewa ansha baqi a gidan,bata yarda tabi ta qofar falo ba
saita bi ta qofar baya tayi shigewarta dakinta,kayan hannunta ta aje ta rage kayan jikinta ta
shiga wanka,bayan ta fito ta murza manta mai qamshi ta saka riga mara nauyi,ta ciro wayarta
daga jaka kenan taga miscal din zunnurah,sai fuskarta ta washe da fara'a,ba bata lokaci tabi
kiran,bugu biyu ta daga,abu na farko data fara shine guda ta sakar mata,bacin rai ya bijirowa
shahidan,wato kiranta tayi donta tsokaneta kenan?,sai kawai ta yanke kiran,ta nufi gadonta ta
hau ta kwanta rub da ciki tana lumshe idanunta,dai dai nan hasina ta turo qofar
"Au yaushe kika shigo?" Banza tayi da ita kamar bata ji ba,hakanan taqi bude idanunta,don
tasan qarshenta itama tention xata qara mata kawai
"Shahida" hasina ta sake fada tana matsowa dab da gadon,ta dora hannunta saman filon tadan
daka,sai a sannan ta ware idanunta tana dubanta
"Bacci nakeji,don Allah ki barni na huta" murmushi hasina ta saki
"Amma na miki jaje da zaki kwana bakiga kayanki ba wallahi,kallo ya barki" qur ta mata da
idanu kafin taja qaramin tsaki ta maida kanta daya barin tana rufe idanunta,dariya ta sheqe
sosai da ita sannan ta juya ta fice tana waqar amarya.

Da sauri ta diro daga saman gadon ta isa bakin qofar ta saka key ta kulle sannan ta sake
dawowa ta kwanta,tana gyara kwanciyar tata tana mita ita daya gami da jan tsaki lokaci
lokaci,rigingine ta kwanta tana kallon roofing din dakin,idanunta a kulle gam tanason tilasta
kanta tayi bacci.
Haka aka dinga mata knocking tana ji ta share,donko hasina yau saidai ta kwana wani dakin
amma ba nata ba,kadaitaka kawai yau take da buqata.

Sai sha daya da wani abu na dare sannan bacci ya soma fisgarta,qarar wayarta yasa ta
bude idanunta ahankali kan wayar dake aje saman cikinta,ta daga wayar tana dubawa,lambace
babu suna,kaman ba zata daga ba sai kuma ta daga kana ta kara a kunneta gamida yin
sallama,can qasa taji an amsa sallamar har bata tantance muryar waye,shuru ya ratsa da wasu
sakanni
"Nuradden" ta canki sunan
"Shahida,na rasa ta ina zan fara koyawa kaina haquri dake" idanunta ta lumshe tana jin bacin
rai na ratsata
"Kayi haquri noradden,duk ni na jawo mana komai,da ace banyi jinkirin hanaka zuwa gidanmu
ba da guni hakan duka bata faru ba"
"Ki tayani addu'a kawai,Allah ya yayemin,don ba lallai bane na daina sonki" daga haka wayar ta
katse,a sanyaye ta ajiye wayar ta mirgina daya barin nata,harga Allah bata tausayin kanta
kamar yadda take tausayin nuradden din,ya riga ya fada da yawa,ta kuma son ciwo da radadin
soyayya,musamman a sanda ka rasa abinda kake tsananin so ka kuma saka ranka dashi,a
hankali kalamanshi suka fado mata,baya neman yaradarta,bata cancani ta rayu cikin farinciki ba
ta zabi wanda takeso,zai aureta ne don ya nuna mata ya isa,lebanta na qasa ta cije tana
rarrabe maganar da abinda yake nufi,auren manufa zaiyi da ita kenan?,zaiyi ne don cimma
wani boyayyen nufi nashi?,lallai zata nuna masa yayi ganganci,akwai banbanci tsakanin da da
yanzu,ta jima ahaka tana saqa abubuwa da yawa tare da tunawa da al'amura masu yawa kafin
bacci yayi nasarar saceta.

Washegarima kusan fitar wuri tayi,tana tsaye a kitchen tana shan ruwan dumi anty zubaida
ta taras da ita
"Ba zakiga kayan ba kenan zaki fita" agogonta ta kalla sannan ta sauke hannu
"Sauri nake anty"
"Hakan yasanya jiya nace a tasoki ki gani ai" baki ta tabe a fakaice tana tuna haushin da hasina
taso tura mata ajiyan da yadda ta matsanta mata,kayan da bataga abinda anwar zai zuba a ciki
da zasu burgeta ba
"Idan na dawo na gani,saina dawo anty" ta fada cikin hanzari bayan ta dauki jakarta data aje ta
rataya tana ficewa da hanzari,kasa cewa komai anty zubaida tayi sai binta da kallo kawai da
tayi harta fice sannan ta girgiza kanta tana tadi ita da zuciyarta,ko ba'a fada ba tasan ganin
kayanne bata sonyi.
Kwana uku tana cewa anty zubaidan zata gani amma bata yarda taje inda sukebama bare ta

gani,dole ta gaji ta zuba mata idanu,a haka har akaci kwana goma sha biyu,ga tsammanin anty
zubaida shahidan zata dauki hutu wajen aiki,saidai taga ko ajikinta bata fasa fita aikin na,sake
qara mata kwana biyu tayi taga ko zata dakata da fitar,saidai ranar daya rage biki saura kwana
bakwai cif da safe anty zubaida ta sameta a falo tana karyawa ta gama shiryawa tsaf,kallonta
sosai take taga da gaske take fita aiki zatayi?,kallon harya sanya shahidan itama yin sak tana
kallon anty zubaidan,saidata soma dan tsuke fuska sannan tace
"Ina zaki haka da safe?" Tambayar tadan baiwa shahida mamaki,ko maqota sunsan inda taje
zuwa daga safiya zuwa yammaci bare anty zubaidan,don ita bata kawo tambayar tata nada
alaqa da aurenta ba
"Office mana anty" ta fada cikin son gamsar da ita,kai anty zubaida ta girgiza
"Bakisan aurenki saura kwanaki bakwai ba ko lissafi ne ya qwace miki?,ko kuma duka kina
sane saboda kinha na zuba miki ido ne?"wani abu ya taba zuciyar shahidan,ba zancan data
tsana a yanzu irin zancan aurenta,tana sane saura kwanaki bakwai su qullashi to amma ita
meye nata a ciki?,me zata zauna gida tayi " to anty,ni menene nawa a ciki?,me zan zauna nayi a gida?"
"Eh babu komai naki a ciki tunda zubaida ce zatayi aure,so kike duniya ta zagemu ko?,tunda
kike kin taba ganin amarya budurwar da aka aurar salin alin?,to banason sakarci,babu ruwana
da wani abu daya taba gittawa tsakaninki da anwar ni aikina zanyi kawai,rawata zan
taka,saboda haka ki koma ciki daga yau zansa abban huda ya dauka miki excuse,su baki hutun
sati uku" kaman ta zunduma ihu haka taji sanda anty zubaida ke maganar,abinda ta dauka
wasa ne gashi yana neman tabbata,ba damar musu da ita saboda yadda ta tsare gida
sosai,haka shahidan ta soma takawa don komawa dakinta
"Eheennn...jimana" anty zubaida ta sake fada,saita tsaya gami da waiwayowa tana dubanta,sai
data kallo agogo sannan tace da ita
"Qarfe sha daya na rana zamu fita dake,ki zauna cikin shirin" kai ta gyada kamar kazar da qwai
ya fashewa cikin cikinta,haka ta dinga tafiya harta isa daki,ta watsar da duka kayanta kanta na
daukar zafi,me yasa anwar yake son ya soma da nasara da sa'a a kanta?,me yasa anwar ya
dawo cikin rayuwarta bayan bata da buqatarsa?,haka ta dinga yiwa kanta tambaya ranta na
zafi.

Sha dayan da 'yan mintina suka fita ita da anty zubaidan kawai,bata tambayeta ina zasuje
ba har saida suka isa gidan sannan ta fahimci wajen gyaran jiki ta kawota,tamkar wata doluwa
haka ta dinga bin anty zubaida da kallo har suka gama gaisawa da matar da gabatar da
shahida wajen matar a matsayin amaryar da za'a yiwa bikin "Kai tubarkalla masha Allah,wannan badon hausawa suna cewa idan kana da kyau ka qara da
wanka ba ai bata buqatar komai,saida nasan gyaran ba qaramin hawanta zaiba zubaida" tana
jinsu harta gama surutunta ta soma hada kayayyakin gyaran jikin ta buqaci shahida ta sauya
wani zani na daban data dauko.mata,fuska ta bata tana duban anty zubaida ranta na baci ta
wani gefan,yanzu saboda anwar ne aka kawota nan wajen
"Anty,don Allah abar abunnan,batamin kaya kawai zaiyi" dago idonta tayi daga wayarta da take
dannawa ta watsawa shahidan harara,hakanan tana ji tana gani ta sauya zanin aka shiga mata
gyaran,bakinta gum tana bin matar da kallo kaman ta mangareta saboda yadda takebin fatarta
da kayyakin tana shafeta dasu.

Tana ganin kawai bata lokaci da bata kudi ne.

A qalla sun kusa kashe awa biyu cur ana abu daya,bin jikin nata take da kallo yadda ya
soma wani santsi sulbi da sheqi na musamman,tabe bakinta tayi data tuna saboda me akayi
mata,sai taji gyaran sam bai burgeta ba,tana maida kayanta wani qamshi na tashi daga jikinta
duk sanda ta motsa,turarukan qarshe da aka murje mata jikinta dasu.
Basu jima ba suka isa gida,a falonta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login