Showing 42001 words to 45000 words out of 126208 words

Chapter 15 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf

ajiyar
zuciya,itakam har cikin zuciyarta sam batajin zuwa ko ina,haka kawai taji batason
fita.https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/video

*Alqawarin Allah*
1️⃣4️⃣


Ta bangaren shahida kuwa mahaifinta ne ya turo qofa ya tsinceta cikin wannan halin,wanda
hakan ba qaramin kadashi yayi ba,bai gane a cikin maye take ba sai daya kamata zuwa cikin
gida yaji tana surutai irin na wanda yasha wani abu ya bugu,saiya saketa suka zuba mata idanu
shida ummanta suna kallonta,kasa tsaiwa tayi saita fadi luuu ta zube nata ci gaba da
surutanta,wanda a nata tunanin anwar take kira ya tsaya tayi masa bayani,kuka umma ta fashe
dashi yayin da abbanta cikin tashin hankali yace
"Ina kika barmin 'yata taje mariya?"
"Ina kuwa zan barta taje abba?,gaisuwar mutuwa suka je ita da qawarta" ta fada cikin tsananin
tashin hankali da kuma kuka
"Wallahi wallahi ki tabbatar da cewa indai wani mummunan abu ya samu 'yata toki kuka da
kanki" ya fada cikin hargagi yana nunata da yatsa,a ranar dai umma babu bakin magana ta
diyarta take,salati kawai take tana duba jikin shahida daya lalace da jini,bandaki ta kaita tayi
mata wanka wanda shiya sanya bacci ya kwasheta bayan ta dawo da ita daki.



Da salati ta farka tana qarewa dakin kallo,ko ba'a fada ba tasan dakin ummanta ne,a hankali
ta soma tuna me ya faru da ita,tun daga barinsu inda sukaje zuwa gidan qawar
fiddausi,sauketa da saurayin yayi a qofar gidansu,daga nan zaren tunanin nata ya yanke,tayi
tayi ta sake tuno abinda ya faru ta kasa,zuciyarta na gaya mata taga anwar,wata zuciyar tana
ce mata bashi bane.

Muryar umma ta jiyo tana kiranta cikin kakkausar murya wadda tasa hanjin cikinta kadawa
"Shahida....ina kikaje jiya?" Saita kasa amsa mata,indai har a wannan yanayin ta shigo gidansu
to tabbas bata da bakin kare kanta,kafin ta sake cewa wani abu umman ta zube dukka
kwalaben da suka fado a jakarta wanda tuni ta gama karantawa ta kuma fahimci kayan shaye
shaye ne a ciki,idanun umman jajur tace mata "Meye wannan shahida?" Kasa hada ido tayi da umman,hankalinta yayi qololuwar
tashi,lafiyayyen mari umman ta sauke mata wanda ya gigitata,sannan yayi dai dai da shigowar
abbanta dakin,wanda tunda ya fita sallar asuba daya daga cikin maqotansa ya masa jajen anga
shahida an kawota qofar gida an yasar me ya sameta bai sake samun sukuni ba,yasan tabbas
maganar akayita tattaunawa a jiya ana kuma sauya mata kamanni,yasan halin anguwar da 'yan

unguwar kaf.

"Ai kibar dukanta bari na gaya miki mariya,koma meye shahida ta zama laifinki ne,kin zaki
baki kin kasa bawa diyata tarbiyya shine yanzu zaki zo kina wani hargagin banza da wofi?"
Cikin bacin rai da shiga zafi biyu ta maida masa amsa
"Indai shahida ta lalace ne kaima akwai laifinka,tunda kaima ubane ai ba'a dauke nauyin haqqin
kula da ita daga kanka ba"
"Au haka ma zaki ce?"
"Eh na fada din,dame kakeso naji ne iye?"
"To mariya nidai tsakanina dake saidai nace Allah ya isa ban yafe ba..." Cikin qaraji gana zubda
hawaye tace
"Nima Allah...." Qarar da shahida ta saki ita ta katse sauran magabar da umman tata taso
furtawa,kuka take sosai hawaye wani yana bin wani
"Ku dainawa juna Allah ya isa kune sila....dukanku ku kuka zama silar koma meye na koma a
yau...ku ku kaini ga afkawa halin da nake ciki a yau,wannan abun da kukeyi shiya janyo
komai,duk d'a na halak bazaiso yaga rana guda tak data zama ranar da mahaifansa sukai
cecekuce ko jayayya ba a gabanshi,sai gashi ni nawa mahaifan a gabana suke xagin juna,a
gabana suke aibata juna,a gabana suke debewa juna albarka,a gabana suke fada da
junansu,duk yadda naso da ganin gyaruwar al'amarin hakan ya gaza,duk habyar da nabi ta
ganin kun gyaru ba wadda ta bulle min,zafi da radadin haka yasa na nemowa kaina
gurbatacciyar mafita,nake shan abinda ni a nawa tunanin bacci kawai zao sanyi ni,ban sani ba
cewa ya shiga cikin abinda annabi ya haramta tunda zai gusar da hankali,zai saka maye,idan
zanyi kuka bazanyi da d'aya saga cikinku ba,zanyi kuka ne sa dukkaninku,kun kasa fahimtata a
sansa ya dace,kun kasa gane illar abinda kuke aikatawa a gabamu mu 'ya'yanku"daga haka ta
miqe ta miqe jiri da kuma rashin qwarin jiki ya sanya ta dinga layi,amma bata dakata ba har sai
data fice daga dakin zuwa nata dakin.

Dukkaninsu sai jikinsu yayi sanyi,kowannensu ya shiga nazari da dogon tunani,bai sake
cewa komai ba abban ya fice daga dakin,saiya zura takalmansa ma da niyyar ficewa daga
gidan gaba daya.

Yana sanya qafarsa a waje yaci karo da mutum uku cikin maqotansa
"Yauwa malam nuraini...dama yanzu muke neman yaron da zai mana sallama dakai" qoqarin
dai daita fuskarshi yayi ya basu hannu suka gaisa
"Ashe haka abu ya faru?,wallahi sam bamuji dadi ba,yarinyar da kowa ke mata kallon hankali
da nutsuwa" daya daga cikin maqotan nashi da ake kira da malam sallau ya fada
"Wallahi kuwa malam sallau,amma nidai ina kyautata zaton sharrin qawaye ne tunda kowa ya
shaidi nutsuwar yarinyar....amma cire ciki aiba qaramin abu bane,sanda haruna ke gayan
qaryatashi nayi saida yatabbatar min da kunnensa yaji saurayin yana fada" a hautsine abban
shahida ya dago yana musu wani bahagon kallo,kusan bai fahimci me suke fada ba gaba daya "Yata shahida ce tayi ciki harta cire?" Sai suka koma kallon kallo tsakaninsu,malam sallau ya
dubi abban
"Errrhmmm malam nuraini kodai mata sun maka irin halin nasu ne an boye maka bakasa me

yake faruwa cikin gidanka ba?,banda haka wannan zancan ai ya karade unguwarnan daga
daren jiya zuwa safiyar yau"
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" ya dinga maimaitawa yana dafe da kanshi,me yayi jama'ar
unguwarsu haka sa cikin qanqanin lokaci zasu jefi diyar cikinsa da wannan sharrin,kansa ya
dafe da yaji ya soma juya mishi sai kawai ya juya zuwa cikin gida
"Allah ya tsare gaba ya kiyaye" ya juyo malam sallau yana fada cikin daga murya,dai dai sanda
shahida data fito don shiga bayi ta kama ruwa ta saki butar hannunta cikin tsananin tashin
hankali ta koma dakinta,dukka jikinta rawa yake,tana tariyar kalaman da saurayin ya dinga fada
bayan ya saketa a qofar gidan,kenan duk abinda ya fada sun yarda dashi?,kenan yanzu kallon
da kowa zai dinga mata?,innalillahi wa'inna ilaihir raji'un,Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifni
khairan minha"shine abinda ta dinga maimaitawa kenan.

Cikin kwana biyu kacal ta rame ta fige ta fita a hayyacinta,bata taba tunanin akwai tashin
hankalin daya wuce na fadan iyayenta ba saiga wanda ya ninkashi ya risketa,duk ta silar
kaucewa wancan bacin ran ashe zata fada wanda yafi wancan tsanani rusa farinciki dama
ruguza rayuwa gaba daya.
Ba ita kadaiba gidanma gaba daya ya zama shuru,baya ga abinda ya faru abbanta ya
kwanta ciwo sosai tun randa su sallau sukazo masa jaje,wanda ba komai bane ya taba ranshi
irin maganar da suka furta,qarshe da aka aunashi jininsa ne yayi mugun hawa,hakan ya saga
hankalin ummanta itama ta shiga wani sabon tashin hankalin da firgici.
Kwana uku amma shahidar jinta take akwai ya babu,gata nan dai kawai amma komai ya fice
mata aka,ranar kwana na ukun da yammaci wani yaro yayi sallama tsakar gidan nasu dauke da
takarda wanda yace gashi a baiwa shahidan.

Mubina ce ta bita har cikin daki a sannan tana kwance saman abun sallah ta miqa mata,saita
saka hannu kawai ta amsa ta aje saman kanta tana ci gaba da lazuminta,wanda kusa fiye da
rabi istigfari take da salatin annabi.

Sai data idar sannan ta dauko envalope din,tana daga kwance ta farketa,takarda ce qwaya
daya a cikinta ta fado,sai wata azurfarta guda biyu data siya ta baiwa anwar ajiya,da sauri
tasoma warware takardar tana zumudin jin daga gareshi,don tunda abun ya faru taji dif daga
bangarensa,tana zaton wala'alla yazo ance mishi bata da lafiya,don bata da maraba da mai
lalurar,ita kuma wani kunya da nauyin kiranshi take,gani take kaman daga muryarta zai karanci
komai,zai karanci halin data fada,wasiqace cikin rubutun anwar din mai tsari

_Basai nayi miki sallama ba don baki cancanceta ba,saqo nake son isar miki dama ba wani mai
tsaho ko yawa ba,shahida,sam baki dace dani ba,kuma sam bakiyi dai dai da rayuwata
ba,tuntuni ina zaune dake ne kawai don bani da abinyi kuma bani da wata qwaqwaqwarar
sana'a,gashi ina da buqatar macen da zan di ga rage dare a wajenta,to zuwa yanzu al'amura
son suma yimin kyau,bana jin zan iya ci gaba da zama dake,ki sani ni muhammad anwar ban
taba sonki ko qaunarki ba,na miki alfarma ne kawai a baya,kuma ki saka a ranki cewa baki taba

soyayya da wani mai kama dani ko suna na bar har qarshen rayuwarki,wasiqar na tafe da
guzurin sabuwar masoyiyita wadda nake da tabbacin ta fiki komai,idan nace komai ina nufin
komai da komai da kikasan diya mace na mallaka_

Cikin rawar jiki ta miqe zaune dungurgur,sannan ta jawo envalope din ta sake lalubawa
ciki,saiga hotuna guda shida rigis sun fado,dukkaninsu anwar ne cikin hotunan da wata
matashiyar budurwa cikin kyakkyawar shiga ta alfarma,kana musu kallon farko zaka tabbatarwa
kanka lallai masoya ne da sukayi zurfin cikin qaunar juna,saboda yadda kowanne ke kallon
danuwanshi cikin fara'a da shauqi,sosai ta tsurawa fuskar yarinyar ido zuciyarta na wani qara
gudu tamkar zata faso qirjinta,suya zuciyar tata take mata tanason yin kuka amma bataji koda
alamarsa ba bare yazo,nazarin fuskar yarinyar take take ta tuno inda ta santa,ranar bikin
umaima,ranar bikin umma zaune gaban motar daya amso don ya kaita ya daukota,saita saki
hoton tana girgiza kai tare da laluben wayarta duka lokaci daya,tamkar tababba take zancan a
fili ita kadai
"Nasan wasa kake min ya anwar ba zamu taba rabuwa....nasan wani ya kaima labarin abinda
ya faru dani,ranka ya baci ka furta min wannan kalaman saboda kishina da kake" maganar tata
ta katse sanda wayar ta shiga ta soma ringing.

Wata murya daban ta dauka,cikin matuqar sauri da zaquwa tace
"Don girman Allah ka taimakeni ka bawa anwar" dan jimmm yayi cikin tunani,don a yanzun
bayajin anwar din zai iya wata dogon magana,tunda Allah yasa suka miqashi asibiti yayi
kwanaki biyunsa cur ya farfado yace a dawo dashi gida yazo ya dauke wata envalope dashi
kansa muhsin baisan meye a ciki ba ya adana yake zaune waje daya,kana kallon yanayin
fuskarsa kasan ya dulmiya cikin wani qunci,iein quncin dake kama zukata ya riqe tamau ya
dinga yankarta a hankali yana saka rudani damuwa da baqinciki mai yawa a rayuwa,irin
baqincikin dake tasiri kadan kadan daga ruhi zuwa gangar jiki ya illata mutum ta farat daya ba
tare da an ankara ba.

Miqa masa wayar yayi,sai daya daga idanunsa da suke nuna alamun gajiyawa da damuwa
ya dubi muhsin sannan ya maida kan wayar,hannu ya saka a hankali ya masa,muhsin ya sakar
masa yana tashi gami da cewa
"Bari naje gida na dauko wayata na barta a chargy" kai kawai ya iya gyada masa yana kara
wayar a kunnensa.

Abu na farko da tayi kuka ta sakar masa,wanda yake bayyana rauninta qarara,gajiyawa da
rashin samun madafa,idanunsa ya runtse yana jin zuciyarsa cikin wani inji ana hautsinata sama
da qasa ko zata faso qirjinsa ta fito.

*zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani DON GIRMAN ALLAH karki sharing,idan kina buqatar
siya ki tuntubi wannan number*

07067124863

*ko kuma*

09032345899https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos


*Alqawarin Allah*
1️⃣6️⃣


Daga kai tayi ta dubi anty zubaidan maimakon yadda ta saba yi mata a baya duk sanda ta
ganta,takan tashu cikin farinciki tana mata sannu da zuwa dama tambayarta yaushe ta iso,hadi
da tambayarta su faruqu,a nutse anty zubaida itama take qare mata kallo bayan ta zauna dab
da ita,cikin mintina qalilan ta gama karantarta "Shahida" ta soma kiran sunanta a sanyaye,sake tada kai tayi ta dubeta saita sake
saukewa,shawarar da zuciyarta ta bata tabbas itace mafita,dole ne saita fara tayar mata da
mikin dake zuciyarta don da ala zuciyarta ta riga data daskare,dab take da rasa feelings,dole ta
sata tayi kuka ta rage radadin da yake damun zuciyarta wannan shine hanya daya na farkar da
zuciyar tata,dole ta sakata da kan kanta ta nuna akwai ciwo a zuciyarta wanda ta wannan
hanyar ne kawai zata dawo da feelings da emotion dinta na fushi,sannan asan yadda gyara zai
iya yiwuwa,tana son maida zuciyarta ne matacciya idan ba'ayi gaggawar gyarawa al'amarin ba
"Shahida!" Ta kirata wannan karon da mugun tsawar data taba zuciyar shahidan,ta kuma
sanyata dago kai tana duban anty zubaida gami da zuba mata idanu,yadda ta kafeta da idanu
shi ya sanya itama tsaiwa tana kallonta
"Shahida bansan ke shashasha bace,ban kuma san ke wawiya bace sai yau,ban raina wayonki
ba sai yau,ashe ke banza ce?!" Shuru tayi kaman wata sokuwa tana duban anty
zubaida,qwaqwalwarta nason tariyo mata meta aikata haka?,ganin yanayinta ya baiwa anty
zubaida qwarin gwiwa "Shahida....saboda namiji kikeson maida rayuwarki haka?,saboda wani da dacan baki sanshi
ba?saboda wani daya nuna bai damu da rayuwarki ba?,wace iriyar shashasha ce ke wadda
batasan ciwon kanta ba,shi din banza?...waye shi?,kina da 'yan uwa,kina da
mahaifiya...mahaifinki ya rasu,waishin shi da mahaifinki wanne ne yafi miki muhimmanci,kin
rasa mahaifinki ma ya tafi kuma har abada,kun rabu kenan da wanda yayi silar kawoki
duniya,inaga wanda ya tsinceki rana tsaka da girmanki,shahida!....kisan me kikeyi,ki shiga
taitayinki!" A hankali ta soma girgiza kanta,yayin da hawaye ya cika idanunta,zuciyarta ta soma
motsawa,mikin dake danqare ciki ya tashi,kuka ta saka mai sauti qwarai wanda hatta mutumin
dake tsakar gida zai iya jiyo gunjinta,sai anty zubaidan ta matso da ita jikinta,ba musu ta
kwantar da kanta saman cinyar anty zubaidan taci gaba da gursheqen kukanta,bata ce mata
komai ba hakanan bata hanata ba,shuru tayi tana sauraron yadda kukan nata yake fita,ta sani
duk sanda hawaye daya ya sauka yana sauka ne da wani radadi daga cikin radadin dake
danqare cikin zuciyarta,hannu anty zubaida ta dora saman kan shahidan ta dinga shafawa a
hankali a hankali tana tayata jin radadin.

Aqalla sun shafe awa guda cur a haka,harsai da kukan ya soma sassauta ta soma rage sauti

ya koma sai hawaye,mintina talatin ta sake qara mata zuwa sannan hawayen ya sake raguwa
"Me ya faru shahida?,garin yaya haka ta kasance?" Bata boyewa anty zubaida komai ba kanta
na saman cinyarta ta warware mata dukkan yadda akayi ta soma shan wani abu da niyyar rage
baqinciki da bacin ran dake damunta,sannan ta zarce da rabuwarta da anwar sannan ta dora da
cewa "Baqinciki na shi ya kashe abbana anty,shaye shaye yabarmin tabon da har na mutu dashi zan
mutu,na kashe abbana da takaicina!" wanda hakan ya sake bude sabon shafin kukanta,kai anty
zubaida take girgizawa
"Kuskurenki na farki shahida shine da kika saki Allah,kika manta da cewa babu wani babban
abu dake yaye qunci da baqincikin a zuciyar bawa ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali irin
kusanta kai da Allah,babu wani abu da zai kawo miki farinciki da walwala irin karatun
qur'ani,shan wani abu a wajen dan adam domin gusar da baqinciki bacin rai ko kuma damuwa
bashi da wani tasiri a gareshi,baya haifarwa da bawa komai face sake sanyashi cikin
damuwar,baya yaye damuwa ta har abada face ya sake sanyaka cikin wasu sabbin
matsalolin,ya haifar maka da ciwuka masu kai d'an adam ga kushewa,Daga kai tayi ta dubi anty
zubaidan maimakon yadda ta saba yi mata a baya duk sanda ta ganta,takan tashu cikin farinciki
tana mata sannu da zuwa dama tambayarta yaushe ta iso,hadi da tambayarta su faruqu,a nutse
anty zubaida itama take qare mata kallo bayan ta zauna dab da ita,cikin mintina qalilan ta gama
karantarta
"Shahida" ta soma kiran sunanta a sanyaye,sake tada kai tayi ta dubeta saita sake
saukewa,shawarar da zuciyarta ta bata tabbas itace mafita,dole ne saita fara tayar mata da
mikin dake zuciyarta don da ala zuciyarta ta riga data daskare,dab take da rasa feelings,dole ta
sata tayi kuka ta rage radadin da yake damun zuciyarta wannan shine hanya daya na farkar da
zuciyar tata,dole ta sakata da kan kanta ta nuna akwai ciwo a zuciyarta wanda ta wannan
hanyar ne kawai zata dawo da feelings da emotion dinta na fushi,sannan asan yadda gyara zai
iya yiwuwa,tana son maida zuciyarta ne matacciya idan ba'ayi gaggawar gyarawa al'amarin ba
"Shahida!" Ta kirata wannan karon da mugun tsawar data taba zuciyar shahidan,ta kuma
sanyata dago kai tana duban anty zubaida gami da zuba mata idanu,yadda ta kafeta da idanu
shi ya sanya itama tsaiwa tana kallonta
"Shahida bansan ke shashasha bace,ban kuma san ke wawiya bace sai yau,ban raina wayonki
ba sai yau,ashe ke banza ce?!" Shuru tayi kaman wata sokuwa tana duban anty
zubaida,qwaqwalwarta nason tariyo mata meta aikata haka?,ganin yanayinta ya baiwa anty
zubaida qwarin gwiwa "Shahida....saboda namiji kikeson maida rayuwarki haka?,saboda wani da dacan baki sanshi
ba?saboda wani daya nuna bai damu da rayuwarki ba?,wace iriyar shashasha ce ke wadda
batasan ciwon kanta ba,shi din banza?...waye shi?,kina da 'yan uwa,kina da
mahaifiya...mahaifinki ya rasu,waishin shi da mahaifinki wanne ne yafi miki muhimmanci,kin
rasa mahaifinki ma ya tafi kuma har abada,kun rabu kenan da wanda yayi silar kawoki
duniya,inaga wanda ya tsinceki rana tsaka da girmanki,shahida!....kisan me kikeyi,ki shiga
taitayinki!" A hankali ta soma girgiza kanta,yayin da hawaye ya cika idanunta,zuciyarta ta soma
motsawa,mikin dake danqare ciki ya tashi,kuka ta saka mai sauti qwarai wanda hatta mutumin
dake tsakar gida zai iya jiyo gunjinta,sai anty zubaidan ta matso da ita jikinta,ba musu ta
kwantar da kanta saman cinyar anty zubaidan taci gaba da gursheqen kukanta,bata ce mata

komai ba hakanan bata hanata ba,shuru tayi tana sauraron yadda kukan nata yake fita,ta sani
duk sanda hawaye daya ya sauka yana sauka ne da wani radadi daga cikin radadin dake
danqare cikin zuciyarta,hannu anty zubaida ta dora saman kan shahidan ta dinga shafawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login