Showing 72001 words to 75000 words out of 126208 words

Chapter 25 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf

da gaske daada da wannan karamci,amma inason kimin wata alfarma guda
daya"
"Ba zata gagara ba insha Allahu anwaru"sassauta muryarsa yayi
"mun samu sabani da shahida wanda shi ya zama silar rabuwarmu na wadan nan shekaru,na
dawowa shahida saidai yadda ta dauki zafi fiye dani ta tabbatarmin ba zata taba karbata a
matsayin miji ba..." Yadan dakata a ranshi yana istigfari kan qaryarda yayi
"Inason don Allah dada a boyewa shahida gaskiyar wanda ke neman aurenta,inason na gaya
mata da kaina mu sasanta kuma kanmu ba tare da kowa ya shigo ciki ba" qanqan da ido daada
tayi cikin masifa tace
"Wato ja'ira tasan komai shi yasa ko zaka kwana tambayarta saita dinke bakinta ko?,yoni aida
ka barni da ita don dakalin qofar gidansu mu gauraya da ita,ja'ira tana tafe kaman daben
masallaci kai kace ba ita bace..." Duk yadda yake jin ransa saida fadan dadan ya bashi
dariya,ya danne yana cewa "Ki haquri daada karki tasarmin ballina"qwafa taja
"Don dai kace haka ne amma da goben zan gaya mata da kaina,idan yaso ta iskoni katsina ta
hukunta ni" daada na tsaka da fadan dake baiwa anwar dariya yake kuma sakashi nishadi
sabida nasarar daya samu sulaimanu ya dawo da damammiyar fura mai sanyi data sha
suger,sosai anwar ya sake ya dinga sha suna hira da dadan tana bashi labarai wanda anan yaji
labarin rasuwar abban shahidan,sosai jikinsa yayi sanyi qwarai,ya dinga jin babu dadi har cikin
ransa,ya dinga tuno abubuwa da dama tsakaninsa dashi,yana qaunarshi sosai hakanan yana
ganin girmansa,kaman dan cikinsa ya daukeshi ba suruki ba,yayiwa daada ta'aziyya sosai.

Bata barshi ya tafi ba saida tayi masa irin danwaken da yakeso,wanda ta taba yi masa
zuwansa ziyara wajenta na farko,baici da yawa can ba saboda tuna wani lokaci da yayi a
baya,hakan yasa yaji cikinsa ya cushe,sai bayan la'asar sannan yayi mata sallama ya wuce.

Daga nan gidan wani abokinsa ya wuce,bashi ya baro wajensa ba shima sai gab da
magariba,koda ga koma unguwar kakannin nasa yana aje motarsa ya wuce sallah
masallaci,acan suka gamu da kawu modu suka rankayo gida bayan an idar.

Inna na zaune cikin rumfarta iskar fankar solar da anwar ya hada duka gidan na kaiwa da
kawowa a falon,bata qure fankar can ba hakanan batayi qasa da yawa ba,hakan ya sanya iskar
ke kadawa dai dai
"Ina ka tsaya haka daga cewa yanzu zaka ka dawo?" Sosai yakejin gajiya da kasala yadan
motsa fuska
"Wallahi inna..nima ban zaci zan dade haka ba" dauke kai tayi ta kalli jijarta bushira dake xaune
tana kallo falon inna tace ta miqawa anwar tuwon darenshi da mamarsu ta aje masa,cikin
sabbin fulasai kaman da plates masu kyau harda ruwan sha a jug kaman yadda suka saba
masa duk sanda yazo.
Qasa ya sauko ya soma zubawa da kanshi duk da cewa ba wata yunwa yakeji sosai

ba,amma saboda innar kar tava dazu baici ba yanzun ma haka taji ba dadi
"Naje gidan daada ne,kakar shah....." Saiya kasa qarasa fadin sunan
"Rahama" ya qarashe fada da ainihin sunanta,wanda baya jin tsahon zamanin da yayi da
saninta ya taba ambatar ainihin sunanta
"Wacece haka?"
"Yarinyar da zan aura..na taba baki labarinta shekara shida baya,wadda ta kasa zuwa
gaidaku?" Murmushi inna ta saki
"Shahida wai?,yarinyar da usaina ke bamu labari wadda ta damu kan rabuwarku?" Kai ya gyada
yana ci gaba da ci tuwon
"Ma sha Allah,amma saidai wani hanzari ba gudu ba,ina maganar yarinyar can nafisa 'yar wajen
alhajin nan?,ina cewa duka duka watanni aurenku ya rage?,don dama zuwan naka nake jira naji
ainihin sati nawa ya rage"
"Maganar nafisa tana nan,kuma watanni uku suka rage"
"Anya anwar?,kana nufin auren mata biyu lokaci guda?" Inna ta fada tana kallonshi,kai ua
gyada
"In sha Allah inna,tunda Allah ya hore saidai a tayamu addu'a" shuru ta danyi kadan kafin daga
bisani tace
"Shikenan...Allah yayi jagora,ubangiji ya kore abinqi"
"Ameen"sai daya hadiye lomar bakinsa sannan ya sake cewa
"Na shaidama kakartata gobe su kawu zasu je su tambayamin izini a wajensu,to gashi ban
samu na sanarwa kawun ba,kuma a goben nakeson na koma saboda na baro ayyuka,ban
tsammaci ma yau din zan kwana ba"
"Aiba wata matsala bace,ai ado kawai za'a yiwa waya(qaninta kenan)a sanarwa,shehu da
dahiru suna kan hanya yanzu muka gama waya,sunje duba ta'annabi,idan suka shigo sai kuyi
maganar".

Bashi yabar gidan ba sai qarfe goma na dare,sai daya tabbatar komai ya kammala ya kuma
tsaru sannan ya nufi masauki,yana fitowa daga wanka yana shirin kwanciya wayar nafisa ta
shigo,ya gaji tubus duk da yaga tarin miscal dinta niyyarsa saida safe zaya kirata saboda bacci
yake da buqatar yi,dole ya daga bayan ya kwanta sosai saman gadonshi "dear,ina ka tafi ne?,muhsin yace min baka gari"
"Katsina"
"Me kuma kajeyi can dear?"
"Kin manta ina da dangi ne a can?,naje gaida su inna,sannan kuma na gabatar da wani dan
aiki"
"Au haka ne,me yasa baka hadani da ita ba na gaidata?"
"Idan kin matsu kina iya karbar lambarta tunda tana da waya,da can baki gaidata ba saida nazo
zakice na baki?" A shagwabe tace
"Am so sorry dear,ka turomin number din nata saina kirata"
"Saidai gobe idan Allah ya kaimu,yanzun kam na gaji bacci nakeson nayi" da haka ya samu ya
sallameta ya aje wayar tunani nakai kawo cikin ranshi,kenan yanzu idan lamarin ya tabbata
mata biyu zai aure kenan?,juya lamarin yayi cikin zuciyarsa,koda wasa bai taba kawowa kanshi
xai auri mata biyu ba,sai kuma tunaninsa ya juya kan shahida da nuradden,zayaso yaga fuskar

kowannensu a sanda labari ya isa kunnensa,murmushin mugunta ya saki yana mirginawa
hannun damanshi ya soma karanto addu'ar bacci bayan ya kunna suratul baqara cikin wayarshi
ya rage mata sauti sosai.


*ga mai buqatar littafin da zan soma bayan kammala rubutun alqawarin Allah,zaije youtube yayi
searching SAUTIN HIKIMA,akwai jan rubutu na SUBSCRIBE daga qasa,zaka dannan sau daya
zai koma baqi,sai kiyi screenshoot ki turawa wannan number da zataso daga qasa,za'a sakaki a
group din littafin da yardar Allah*
07038670166*zafafa biyar na kudi ne,idan kika gansu don GIRMAN ALLAH karki sharing,idan
kina da buqata ki tuntubi wannan numbers din*

07067124863

*ko kuma*

09032345899

*Alqawarin Allah*
2️⃣6️⃣






Washegari qarfe tara na safiya ya gama shirinsa tsaf cikin yadinsa na maza mai kyau da
tsada,yayi masifar kyau yadda hularshi ta zauna kanshi sosai kawai ya isa ya gaya maka ya
hada jini da kanawa,hakanan yake jinsa wani sawai kuma fayau dashi,ya qarasa reception yayi
maida musu key din dakinsu ya sallamesu ya wuce zuwa gidan inna.
Falon inna ya wuce kai tsaye bayan ya isa gidan,ya tadda kawu dahiru da kawu modu suna
rumfar innar suna hira da alama anan sukari karin safe tare,cikin girmamawa ya gaida inna
sannan ya gaidasu yana zama daura da ita,ita ta yunqura da kanta ta hada masa lafiyayyen
kunun tsamiya da sukayi da wainar gero,cikin marmari yake ci suna ci gaba da hira dasu kawu
dahirun,yana kammalawa kawu shehu ya iso,basu wani jima ba suka miqe gaba daya zuwa
gidan daada,shi yaja motar,kawu shehu da yake shine babbansu yana gaba,kawu dahiru da
kawu modu kuma suna baya.

Sanda suka isa gidan sha daya na safe har ta dan gota,hakan yasa suka tadda kawun nan
shahida sun riga da sun iso,sulaiman shi ya musu jagora kamar ko yaushe zuwa cikin gidan
"A'ah....shehu,kardai kacemin yaron dake neman shahida dan wajenka ne?" Kawu ummaru

wanda yake yaya ne ga mahaifin shahida ya fada yana dariya sanda sukayi musabaha da kawu
shehu
"Yaro na ne,dan wajen qanina ne mai rasuwa"
"
"Kai ma sha Allah,amma naji dadin abun nan qwarai,to ai abunma duk na gida ne,ita kanta
daadan ma bata sani ba,inaga basai anje anata kaiwa da kawowa ba,ayi komai kawai a gama
lokaci guda"
"Kana ganin babu wata damuwa ko matsala?"
"Haba shehu,kaine fa,babu wata damuwa wallahi,dama meye burinmu banda muga yaranmu
sunata aurensu".

A ranar gaba daya kawu ummaru suka amshi kudin auren shahida harda sadaki,aka kuma
tsaida lokacin biki ko ince daurin aure a wajen maza watanni uku masu zuww,wanda yayi dai
dai da watannin da aka tsaida a farko na daurin aurenshi da nafisa.

Yana tsaye jikin motarshi qafafunshi amatuqar sanyaye,irin wannan lokaci ya jima yana
mafarkin zuwanshi shekara shida baya,ya qiyasta yanayin farinciki da zai samu kansa a duk
sanda Allah ya tabbatar masa a wancan lokaci har baisan sau naya ya qiyasta din ba,sai gashi
abun yazo a bahagon yanayi,yanayin daya kasa tantance wani iri ne,farinciki ne ko
baqinciki?,kansa ya daga a hankali sanda ya soma jiyo muryoyin su kawu dahiru da alama suna
sallama ne dasu kawu ummaru.

Ranar kasa shiga yayi wajen daada duk da yaso suyi sallama,haka ya sake dibansu kawu
shehu ya sauke kowanne a gidansa sannan suka wuce wajen inna shida kawu modu.

Murmushi ne kawai ke fita a fuskar daada sanda 'ya'yan nata ke gaya mata yadda komai ya
kasance
"haba,ba banza ba nutsuwar yaron ta yimin,naji ya shiga raina sosai,ashe jinin gidan malam
usman ne(sunyi zama na maqotaka ne tun iyayensu da kakanni,zaman da sukaji
dadinsa,kunsan mutanen daa akwai riqo da zumunci da kuma girmama alaqa da dangantaka
komai qanqantarta),na godewa Allah,Allah yasa albarka ya kuma tabbatar da alkhairi" "Amin daada" dukkansu suka amsa suna jin dadin hadin
"Yanzu daada za'a sanar dasu kenan?"kai ta girgiza
"qwarai kuwa,ka shaida ma ita uwartata,sannan kuma ka kira can gidan hishamun a shaida
musu,duk da cewa shi ya sani amma sai a gaya masa an karba harda kudin auren da
sadaki,gobe idan ka dawo kai ummaru ka kiramin rahamar ka hadani da ita"
"To shikenan daada" ya fada yana lalubar wayarshi dake aljihun rigarsa.


*_GUDUN QADDARA guzurin taddata....._*


Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke wadda ta fito tun daga zuciyarta,ta sauke idanunta kan

tafin hannunta tana bitar maganganun nuradden daya gama furta mata ayanzu,dauta dauko na
anty zubaida data gama gaya mata jiya,kusan maganganun nasu sunyi kamanceceniya da
juna,a yanzu bata da wata mafita bata da wani uzuri kaman yadda anty zubaida tace
mata,imma dai ta baiwa nuradden dama wa imma ta sallameshi hakanan ya daina wahala,ko
ga ummanta madai wannan karon ta matsa qwarai kan ya kamata ta tsaida manemi tayi
aure,tunda dai abinda ya farun da ita bawai qarshen rayuwarta ya kawo ba,saima sabon babin
rayuwa daya sake bude mata,idan ta sallami nuradden bata jin akwai wani qwaya daya cikin
samari dama masu auren dake kara kaina akanta da zata iya kwatanta rayuwarta ta wanzu tare
da tashi
"Na amince nuradden....Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi" hannayensa gaba daya ya
hada ya rungume a qirjinsa yana lumshe idanunsa,wani farinciki da baisan a wanne mizani zai
dorashi ba ya shiga dawainiya dashi,sai kawai ya zame saman gwiwoyinsa a gabanta
"Shahida,ki fadamin me kikeso na baki ladan wannan kyakkyawan albishir din naki?" Kai ta
kada kawai qwalla na taruwa a idanunta,murmushi mai cakude da alamun son yin kuka na
kubcewa saman fuskarta
"Babu abinda zaka bani face nace kayi qoqari karka sa na sake yin nadama da dana sani a
rayuwata karo na biyu"
"Koda baki roqi haka ba wannan duty na ne" da ido kawai ta dinga bishi yadda ya rasa inda zai
tsoma ranshi ya dinga bata mamaki,harta daina mamaki ma abun ya soma bata dariya,sai daya
tabbatar ta dan saki ranta sannan yace
"Yanzu yaushe za'a kai maganata katsina?,shine abu daya da zai sake sawa in samu nutsuwa
a raina,in kuma tabbatar na yiwa duk wani dake da buri ko hanqoran mallakarki na masa
fintikau din da dole ya haqura" murmushi ya qwace mata,tasan cewa burinsu daada kenan,tana
da tabbacin indai nuradden ya isa katsina to magana ta qare,don ba wani lokaci zasu ja ba ba
tare da sun bashi ita ba
"Karka damu duka abun bana sauri bane,next month za'a dauki azumi,sai kayi haquri mu barwa
salla" fuska yadan bata
"Gaskiya yayimin nisa,saidai idan har kin yarda ne ni zan kaiki,qafarki qafata"hannu ta daga
tana murmushi
"Shikenan naji,sai kuma me?"
"Aikin gama min komai nikam,yau nafi kowanne namiji dake fadin duniyar nan sa'a" yayi furucin
a sanda yake kallon sararin samaniya cikin madaukakin farinciki.

Qarfe tara ta shiga gida don bata wuce hakan a waje,duk da dama ba fita take wajen kowa
ba,kusan nuradden din ne kawaima yaci qwallo da har take fita ta saurareshi,ga mamakinta
saita tadda anty zubaida zaune saman kujerar falon hannunta daya tallafe da kanta,gwiwar
hannunta saman hannun kujera,ba kowa falon sai ita kadai,kallon wani series da suke haskowa
a mbc take,sallamar shahidan ya sakata dagowa da sauri tana dubanta
"Anty,yau yana sameki a nan?" Qoqarin daidaita kanta tayi
"To ya zanyi,uncle dinki yace lallai lallai naga shigowarki na tura masa ke" murmushi tayi tana
zama hannun daya kujerar dake daura da anty xubaidan
"Hala anty kinkai masa qarata ne kan nuradden?,to kisha kuruminki,na riga na baiwa nuradden
dama,zuwa nan da qaramar sallah xai isa gasu daada in sha Allahu" ta qarashe tana duban

anty zubaida,don tasan ta gama mata abinda ranta keso kenan,sai taga ta murmusa kadan
"Ya za'ayi nakai qararki?,koda nakai dinma ai Allah abinda ya hukunta dole shi zai faru
ko?,yanzu dai kije yana falonshi yana jiranki" sai data miqe sannan tace
"Anty muje tare mana don Allah"
"Ba ruwan zubaida" ta fada da hanzari,dariya ta baiwa shahidan yadda tayi maganar kamar
wata baquwar uncle hisham din,saita juya ta wuce tana cewa
"Ai shikenan anty".

"barka da dare uncle"shahida ta furta sanda ta nutsu a gaban uncle hisham,ya sauke
takardar da yake dubawa ya kalleta
"barka kadai shahida,sai yaushene zakuyi hutun naku kamfanin?"
"Eh to uncle gaskiya ina zaton sai sai dab da sallah,saboda wannan season ne na yawaita da
kuma cunkoson custumers" kai ya jinjina sannan ya danyi shuru kamar mai nazari kafin daga
bisani yace
"Daada ce keda buqatar kije,to ban sani ba ko xaki samu ko weekend ne kije kiji kiran nata na
meye?"
"Shikenan uncle babu damuwa,yau alhamis ranar juma'a tunda da wuri muke barin kamfani
saina shirya naje,idan yaso ran lahadi da yamma saina dawo"
"Hakan yayi,shikenan dama kiran"
"To uncle saida safe" ta fada tana miqewa
"Allah ya bamu alkhairi".

A inda tabar anty xubaida nan ta taras da ita,saita daga kai tana kallon shahidan,ganin babu
sauyin fuska tattare da ita ya tabbatar mata uncle din bai gaya mata komai ba,zai turata ne
kaman yadda dada ta buqata,sallama anty zubaidan tayi mata ta wuce wajen uncle din,tabar
shahidan na sake sabon xaman ganin maimaicin wani shiri,tana mitar baccin wuri da yau su
faruqu sukayi suka barta ita daya,don bata jin dadin zaman falon ita kadai.

A nutse yake murza motarsa tamkar wanda baison barin titin har zuwa sanda ya isa
unguwarsu anty usaina,cikin nutsuwa ya faka motar sannan ya kasheta ya fito,cikin wani irin
karsashi yake takawa zuwa cikin gidan,haka kawai yake jinsa kaman mai yawo cikin farin
gajimare wanda shi kansa baisan dalilin haka ba,yana shirin saka qafarsa kan step qwaya daya
da zai sadashi da falon gidan ya jiyo muryar sa'ida na kiranshi,a nutse ya waiwaya,sai ya tsaya
hannayensa zube a aljihun wandonsa yana dakon qarasowarta.

Aladabce ta rusuna tana gaidashi ya amsa yana dubanta
"Daga ina kike?" Sai data dan waiwaya sannan ta dawo da dubanta wajensa
"Uncle....gidansu anty shahida,ummi ta aikeni na amso mata saqo?,kasan me uncle?" Kai ya
girgiza yana dubanta
"Na ganta mafa tazo wajen mamansu,uncle kaganta kuwa kaman ba ita ba...."takun data jiyo ya
sanyata tsuke bakinta,cikin minti daya anty usaina ta bayyana,akwai 'yar tazara tsakaninsu
kadan,ya juya ya dubi sa'idan
"Wuce kafin tazo ta fara miki jajayen idanuwa" maganar ta baiwa sa'ida dariya har sai data

qyalqyale da dariya sannan ta soma takawa don wucewa ciki
"Wato kin dawo shine kika samu waje kika tsaya kina masa wannan dan banzan surutun naki
ko?"kai ta gyada
" a'ah ummi,nima fa yanzu na shigo"harararta tayi cikin ranta tana qissima lallai ya zama dole ta
kwabi sa'ida,donta fuskanci kanta yana rawa tanason ta lalata mata plan
"Wuce,saura kuma naga qafarki a wajen" da hanzari sa'idan ta wuce,anty usaina ta bita da kallo
harsai data shige sannan ta dauke idanunta,dai dai sanda anwar yake tsaye daga inda yake,a
nutse yana karantar duk wani motsi na anty usaina,murmushi ya kubce masa,ya gama ganeta
tsaf,ya gama karantar tsoronta,ya kuma gane me take boye masa,saidai baisan nata shirin
ba,koma meye nata shirin shi zai mata ba zatan da bata tsammata ba,idonta ta sauke a
kanshi,tana tsaye har ya isketa
"Yaushe kai kuma ka dawo?,daga wuni daya sai kwana har biyu?"
"Tun jiya na dawo,wasu sabgogi ne suka riqeni,duk yadda naso in shigo baiyiwu ba" bata ce
komai ba ta bude qofar falon ta shiga yabi bayanta.

Bayan sun gama gaisawa suka shiga hirar mutanen garin daya baro ya gaya mata kowa
lafiya sannan yace
"Kin tambayeni lafiya na tashi zuwa katsina ba yadda na saba ba" ya fada yana duban anty
usainan dake yankan farcenta
"Eh ai dole,koma waye daya sanka yadda kaqi jinin zuwa katsina dole yayi mamakin tafiyar
taka"
"Neman aure naje,na nema kuma sun bani" saita dakata da abinda take tana kallonshi
sosai,saidai bata ga alamun wasa tattare dashi ba,hakan ya sanya ta gyara zamanta
"Auren wa kuma anwar"
"Shahida" ya fada kai tsaye kuma a taqaice,wani abu taji ya tsarga mata gaba daya ilahirin
jikinta,saita aje rezar gefanta ta zauna sosai tana kallon anwar,tana jin wani farinciki na
ratsata,da gaske ko mafarki take,shahidan da take tayi masa farautarta?,sun shirya kansu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login