Showing 117001 words to 120000 words out of 126208 words
Chapter 40 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf
suka kai kai,yaha
shahidan tsirara tare da wani sai yaji kaman mai shirin haukacewa,duk sanda ya kallo hoton
yaga shahidan rungume qirjin daya daga cikin masu saida kayan maye sai yaji dama makaho
ne shi,Allah ne kadai da qarfin addu'a suka sashi ya rayu har yakai bigiren da yake kai a yanzu.
Sassanyar ajiyar zuciya ya saki sanda yake kashe motar shi,ya daga hannunsa ya kira
maigadin,cikin girmamawa ya qaraso
"Baqi indai ba 'yan uwa bane na jiki duk wanda yazo kace musa bama nan"ya qarashe maganar
cikin muryar dake nuna jiki da zuciyarsa duka babu qwari
"To ranka ya dade" ya wuce ya koma bakin qofa yayin da shi kuma ya fito,ya dinga takawa a
hankali zuwa cikin falon.
Shuru yake kaman koda yaushe,saidai ya hangi abinci a shirye saman dining,hakanan yayi
sha'awar xama a falon,idonsa kan wata tasha da suke nuno fasahar zamani da qere qere,suna
wani shirin kan na'ura mai qwaqwalwa,tsohon mintuna idanunsa nakan allon talabijin din,wani
bayani da baqon nasu yakeyi ya dauki hankalinsa matuqa,yadda ci gaban xamani yazo da
sauye sauye,yadda za'a qirqiri abu a idanunka kaga haka yake,amma da za'a sanyashi a na'ura
sai kaga abun ba haka yake ba,tsahon minti ashirin yana bayanin wanda yayi matuqar daukan
hankalinsa.
A hankali tunaninsa ya karkata ga abunda zuciyarsa keson tuna masa tun daxun,saiya miqe
da hanzari ya soma haurawa saman cikin sassarfa,bai tsaya ko inaba sai bakin safe din
nashi,cikin sauri ya tsugunna,ya soma saka lambobin sirrin ya budeshi,envalope din ya ciro
kaman ko yaushe ya zazzage hotunan ciki duka suka fado
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ya furta kaman yadda ya saba sanda yake binsu da kallo daya
bayan daya,duk sanda zai gansu yakanji kaman duniyarshi sama ta kona qasa ne,kullum
yanajin kamar ranar ya soma ganinsu,saiya zauna sosai zuciyarsa na fata da kuma burin
samun mafita,xuciyarsa ta cika da fatan dama ace ba haka bane,dama ace ba ita bace,dama
ace ba shahida bace a jiki shine bai ganin dai dai duk sanda zai kalla,saiya sake gyara
zamanshi sosai,ta ina zai fara?,bashi da wani qarfin sani ta wannan fannin,idan kuma yi masa
za'ayi duk duniya bayajin akwao wani mahaluki da zai iya bari yaga hotunan,koda mahaifiyarshi
data haifeshi ce inda tana raye.
Sake miqewa yayi da sauri saboda tunawa da yayi da makarantar computer da sa'ida ta
mishi xancan ummi ta musu register xasu fara zuwa,idan bai manta ba ta gaya mishi akwai
online classes da special classes da za'azo har gida a koya maka,system yayi nufin
kunnawa,sai yaga kamar ba zata masa sauri ba,ya ciro wayarshi daga aljihunsa ya kunna data
sannan ha fada google ya soma rubuta sunan makarantar,bai manta sunanta ba saboda kusan
ma'abocin siyayya ne a shagonsu na yanar gizo wato www.rahamalls.com,bakin gado ya koma
sannan ya rubuta sunan makarantar *RAHA COMPUTER INSTITUTE* ,cikin qaramin lokaci ya
samu dukkan bayanai,kuma tsarin ya gamsar dashi,ya dauki number dake cikin bayanan ya
kira.
Cikin sanin daraja da mutuntaka tadan adam ya sake samun bayanan da yake buqata,cikin
abinda bai gaza awa guda ba yayi register dasu da komai da komai,ajiyar zuciya ya sauke
sanda komai ya kammala,ya duba agogo yaga lokacin daya kwashe,ya miqe a hankali yana
fidda kayan jikinsa,ya sauya wasu marasa nauyi,wando iya gwiwa sai jallabiyya daya fitar ganin
lokacin sallah ya kusa,ya shiga bandaki ya daura alwala,sanda ya fito wayarshi na ruri,gab da
zai isa gareta ta katse,saiya duba mai kiran,nafisa ce,miscal na shida kenan daga sanda ta fara
kiransa zuwa yanzu,sai a sannan ma zancan ya dawo masa,ya duba saqon data tura masa
wanda na godiya ne da kuma ya yaje gida,aje wayar yayi ya isa inda magungunansa suke ya
cira yasha,sannan ya fesa turare ya qarasa bakin gado ya dauki jallabiyyarsa ya saka,hakanan
yakejin kaman wani nauyi ya ragu daga zuciyarsa.
Cikin mamaki ta dubi table din sanda ta fito daga dakinta,taji kaman ya shigo amma bataga
alamun hakan ba,kaman zata share sai kuma taba hakan bai dace ba,kodon jikinsa takega ya
kamata ta duba,idan lafiya lau shikenan babu buqatar sake damuwa ko saka ido.
Zai fita ita kuma zata shigo,kusan lokaci daya suka murda handle din,baya tadanja kadan
bayan ta dubeshi ta dauke idanunta,sai taga kaman ya fada kadan daga jiya zuwa yau da kuma
fitar daya sakeyi da dawowarsa,ganin alamun fita zaiyi sallah saita juya ta soma sauka tana
cewa "Sannu da zuwa"
"Yauwa" ya amsa yana tsaye cak yana dubanta sanda take sauka din,yanajin kaman ya rintse
ido ya bude yaga duk abinda ya farun da wanda ke faruwa a mafarkine,bai taba kwana ya
kwatanta a ranshi ko sau daya rayuwar zata iya zuwa musu da wannan salon ba,dai gashi
lokaci daya komai ya canza,komai ya tabarbare,komai yazo da cikin wani bahagon yanayi.
Karon farko tun bayan rabuwarsu dayaji wani abu mai kama da tausayi tausayi akanta
saboda tuna cewa nan gaba kadan nafisa xata shigo gidan a matsayin kishiya a wajenya,ya
tuna yadda mata ke komawa duk sanda zance makamancin haka ya shiga kunnensu yatuna
yadda nafisa ta birkice a sanda labarin wanzuwarta qarqashin inuwa guda ya shiga kunnenta,a
sannanma bata zama qarqashin ikonsa na,basu taba kwana qasan rufi guda ba,inaga ita?,duk
da bashi da tabbacin cewa zataji wani abu ko zata damu,saboda dukkan dalilin dake sawa
mace tayi hakan babushi tattare da ita.
"Kidan samu kifi ki dafaminshi idan ba damuwa,zanje sallah na dawo" ya fada cikin laushin
murya wanda har hakan yaso bata mamaki,saita juyo tana kallonshi,suka hada idanu ta sake
dauke kai ganin yadda ya kafa mata idanu,taji kallon nata har cikin jikinta,sai taba baiken kanta
data sanya kaya irin wannan ta zauna haka ko mayafi babu bare hijabi,amsa masa tayi da to
tana ci gaba da sauka daga benan,har sai dayaga bacewarta sannan ya sauko shima yawuce
masallacin.
Sai data soma shiga daki ta samu dan qaramin hijabi ta saka sannnan ta wuce kitchen din
har yanzu tana mamakin irin salon da yayi mata magana dashi,ta ciro kifi ta gyarashi,ta kauda
wancan tunanin na farko ta fada tunanin yadda zata sarrafashi ta yadda zai dace da
yanayinsa,wani gashi ta tuno mai kama da romo romo da takanga anty xubaida bayi,ba bata
lokaci ta soma hadashi,wanda cikin mintuna qalilan ta kammala,qamshi kuwa ya cika gidan ko
ina,ta gyara komai a kitchen din ta gogeshi sosai yadda ta saba sannan ta fito don barin kitchen
din.
Tunda ya dawo yana falon a zaune yana shaqar qamshin kifin har cikin zuciyarsa,da
mamaki tadan dubi sashen da yake din,don iya zamanta a gidan batace ga sanda ta ganshi
zaune haka sosao cikin falon ba,kamar yasan da tsaiwarta shima ya waiwaya yana
dubanta,yabi hijabin jikinta da kallo,shima hakan yayi masa don tamkar gata tayi masa,baisan
me yasa takeson ta zame masa tamkar wani maganadisu ba ko mayen qarfe aduk sanda ya
ganta?,baisan me yakeson sauyashi haka ba,bayan a baya yasan bai damu da dukka shigarta
ba,amma cikin abinda bai gaza sati biyu ba yanason sauyawa gaba daya?.*Alqawarin Allah*
44
Komawa tayi da baya kitchen din ta shirya komai ta dauko kan tray sannan ta sake fitowa
"A'ina za'a aje maka?" Nuni yayi kata da gabanshi,ta qaraso nan ta aje ta shirya komai ta dauko
sauran na wajen dining shima ta shirya masa,tayi sarving dinsa sannan ta yunqura zata miqe
saiya dakatar da ita yace ta zauna,ba musu ta koma ta zauna din,saidai duka bata jinta dai
dai,baiyi magana ba harya qare cin abincin sannan ya soma da cewa "Da can kafin aurenki ina tare da wata yarinya nafisa wadda har an saka mana rana lokacin biki
ya rage saura sati uku,to wasu abubuwa suka biyo baya wanda ya zama silar fasa auren namu
a wancan lokacin,a yanzu maganar ta dawo wanda ina tunanin duka ba za'a wuce sati uku ba
nan gaba" bata taba tunanin zataji irin abinda taji a zuciyarta ba'a yanzu,tunda ya ambaci sunan
zuciyarta da idanunta suka haska mata ita,saita dinga binsa da kallo kawai sanda yake
bayanansa,gaba daya saita daina fahimtarsa,duka bayanan da yake kawai tana ganin yana
yine saboda radin kanshi,yarinyar daya aiko mata da hotunanta sanda take tsaka da radadin
rashin mahaifinta?,yarinyar daya turo mata da fuskarta sanda take tsaka da jimami da alhinin
rabuwa dashi?,yarinyar daya kawo mata hotonta ta gani cewa ya samu wadda ta fita?,ya sauya
wata a madadinta,a yanzu ita zai aura ya kawo gidan?,shine yake wani rufa rufa dason yiwa
zancan kwaskwarima?,tana ganin abu mafi sauqi kawai ya fito ya gaya mata zai cika muradi da
burinsa ne,yanzune manufar da yasa ya aureta zai bayyan muraran baro baro,me yayi
saura?,me xata xauna taji daga bakinsa,ai komai ya qare hakanan komai ya fito fili,sai kawai ta
miqe sanda yake tsaka da bayanin nashi,binta yayi da kallo ganin ta soma tafiya zuwa hanyar
dakinta ba tare data ko waiwayeshi ba,kiran sunanta ya soma yi abinda ya jima rabonshi dayin
hakan,saidai ko daya bata saurareshi ba bare taji me yake fada,da hanzari ya miqe ya bi
baya,taji takun tafiyarsa,saboda haka tana shiga dakin ta saka key,ta samu gefan gadonta ta
xauna ba tare datasan me zata tuna ba,wani kuka ne mai sautu ya qwace mata wanda ta kasa
tsaidashi,hannunsa saman kanshi yana yamutsawa jin sautin kukanta dake ratso har inda yake
tsaye
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ya furta yana kallon qofar dakin da yayi juyin duniya ta bude
taqi,bai taba xato ko tunanin xata damu ba ko sau daya,me yasa ta damu?,me yasa ranta yw
baci?,bayan ta gaya mishi cewa bata qaunarshi ko kadan?.
"Me yasa kike kuka shahida?,kukan me kike?,kins kukane saboda mutumin da kika dainaso
xai qara aure?,ko kina kuka ne saboda mutumin daya daina sonki xai auro wadda
yakeso?,muradin zuciyarsa?,haske rayuwarshi?,meye abun damuwa a ciki shahida?,har yanzu
anwar na cikin zuciyarki ko kuwa?" Tambayoyin da zuciyarta ta dinga mata kenan wanda yasa
ta soma tuhumar kanta da kanta.
Duban nafisan mima takeyi sosai da wani irin banzan kallo,cikin ranta ji take kaman ta tashi
ta shaqe nafisan,cikin ranta tana ala wadai da sakacin da tayi har ta bari tunanin nafisa yakai
gata nemi anwar karo na biyu,tabbas da tasan da irin wannan ranar da tunu ta saka almakashi
ta datse alaqar da tayi saura tsakanin anwar din da nafisan,koda yake a yanzu ma bata baci
ba,saidai kuma ba haka taso ba,dole ya saka taka tsantsan da nutsuwa dinta wargaza
tsakaninsu,don a yanzu bata da burin daya wuce ta ganta itama gidan anwar din a matsayin
matarsa,sake duban nafisan tayi a karo na biyu yadda taketa faman fara'a,bakinta kamar zai
hade da kunnenta,irin kallon da miman ke mata yasanya jikinta yadan soma sanyi
"Ko bayi dai dai bane hajjaju?,bafa zan iya haqura da anwar ba matuqar ina raye shima yana
raye" baki miman ta tabe tana ci gaba da dubanta
"Dama aida kin jira ni nidin xan miki wannan aikin,abinda yasa kika ji shuru ba'a kai gabar
bane,naso mu gasashine harsai ya kawo kanshi da kanshi ta yadda koda kin shiga saikinfi
daraja da qima a idanunsa,amma a yanzun yadda kikayi wallahi qimarki ta zube qasa
warwas,kuma haki da wata fuffuka da xakiyi idan kin shiga gidan,hasalima ba baiyi matsuwar
shigowarki gidan ba kinga baki da abun cewa sawa ko hanawa koda kin shiga gidan" sai jikinta
ya danyi sanyi,taji maganar mima tabbas tana kan hanya,shigen maganar da mummynta ta
gaya mata kenan,ita kuwa a rayuwa yanzu burinta na gaba shine ta shiga gidan anwar ta zama
ita ke fada aji,ita zata sa ayi ta hana kuma a hanu,wanda daga qarshe take fatan shahidan ta
fita tabar mata gidan gaba daya taci gaba dayin yadda takeso.
"Gaskiyar magana mima banason nayi rayuwar da bani zance ayi ba cikin wannan gida,saboda
har yau ina tsoro kuma ina shakkar soyayyar dake tsakanin anwar da wannan mayyar yarinyar"
abun nema ya samu wajen mima,hanyar da zata wargaza rayuwar auren nafisan cikin
sauqi,duk da haka saita sake tsuke fuska ta kuma gum da bakinta harsai da nafisan ta sake
magantuwa cikin mitar tayi mata shuru,fuska ta yatsina
"In sake shiga sabgarki ki watsamin qasa a ido?,ina qoqarin fiddo miki da daraja da martabarki
amma ke baki gani,gwara kawao na qyaleki kici gaba da samawa kanki mafita" harara ta
watsawa miman
"Banason wulaqanci wallahi mima,haba don Allah,sau daya dai don nayi amfani da shawarar
kaina saiya zama matsala?" Sai data gama shan qamshinta sannan tace
"Shikenan,zaki samu yadda kikeso,zaki mulka anwar ki kuma juyashi shida waccar yadda
kikeso matuqar zaki jure ki kuma bi doka da qa'ida,zan dawo next week randa kikacemin zaki
fara rabon IV zakiji sauran qarin bayani" kamar ta goya mima haka nafisa taji,kudade masu
yawa ta baiwa miman sannan ta rakata.
Dariya mima ta saki bayan ta gama irga kudaden,mota takeson sauyawa,kuma ba shakka
lokacin da zata sauya motar da takeso din yayi,a jikin nafisan zata hada kudinta tsaf,daga
qarshe kuma ta tashi a tutar babu,ba anwar din ba kuma kudinta,daga haka ta tada motarta taci
gaba da tafiya tanabin waqar dake tashi cikin motar cikin nishadi gami da tsara yadda zata
mallaki anwar ita kadai bayan ta fitar da shahida da nafisan ma daga gidan dukkansu.
Kaman a mafarki take jiyo sallamar anty xubaida cikin falon nasu,da sauri ta sauko daga
gadon wanda ta maidashi wajen rayuwarta,idan kaga ta fito tota tabbatar anwar ya fita baya
gidan sannan zata fito tayi aikace aikacenta a gaggauce ta koma,sam bata qaunar haduwa
dashi ko daya,Suna shirin yiwa kansu mazauni ta fito fuskarta a washe "Anty yau a gida na?,ashe xakixo?"
"Kamawa ai take,gashi ta kama shahida naxo" cikin walwala da farinciki ta tarbesu.
,sun jima sosai ranar,sunata hira dasu huda,duk sai yaji kewar gida ta sake kamata,kaman
ta koma gidan haka takeji.
Saida suka dan kebe sannan anty zubaidan ta gaya mata abinda ya kawota,zancan auren
anwar,kebe fuska shahidan tayi cikin nuna halin ko in kula,saidai can qasan ranta wani abu ke
tsinkulinta,maganganu sosai anty zubaidan tayi mata,gami da jan hankalinta,suna gama cin
abincin rana tace zasu koma,kaman shahidan tayi kuka amma hakan ta haqura,taso sosai
antyn tabar mata hudan amma qememe taqi,haka suka tattara tanaji tana gani suka tafi.
Zuwan antyn yasa tadan sake ranta,ta koma sabgoginta kamar baya,saidai ta sake janye
sosai daga anwar din,sati biyu da faruwar hakan anwar ya shigoda set din manyan akwatina
guda hudu,da farko tayi burus amma daga bisani tayi tunani kada ya tsammaci kishinsa take
saita karba ta masa godiya,yayin daya bita da kallon mamaki,da gaske bata jin kishinsa? Hakan
na nufin bata sonshi?.
Cikin kwanakin ka'in da na'in ya maida hankalinsa ga koyon abinda yasa gaba daga raha
computer instute,ya ware lokaci har gida yake iskeshi malamin,baisan me yasa abun ya tsaya
masa a rai ba,bai san me yasa ya maida hankali fiye da yadda ya xata ba,wanda yake da
tabbacin cewa cikin wata uku ya cimma abinda yakeso ya cimma din,ta bangare guda guda
kuwa yayi qoqarin kawo sauyi ko yaya yake tsakaninsa da shahidan,don ko kusa baida burin
nafisa taxo ta fuskanci komai dangane da zamansu,duk da qoqarin nasa sau da yawa yakan
cimma tasgaro,saboda rashin samun cikakken hadin kai daga shahidan.
Ta bangaren amarya nafisa kuwa shirye shirye sun kankama ka'in da na'in,dukkan wani abu
da aka sani na bidi'ar biki ba wanda bata tsara xatayi ba,harda ma wanda ba' saba gani ba,ko
sauraren abinda anwar din zai bayar batayi,sha'aninta kawai take.
Qarfe shida saura malamin da suke karatu tare ya tafi,yarage saura shi kadai a dakin,ya
shiga cumputer din sosai yayi shige da fice wanda ya tabbatar masa lallai ya soma
nisa,hakanan yana cimma abinda ya nufa din,saiya kasheta yana sakin murmushi wanda yayi
dai dai da shigowar kira a wayarshi,duban wayar yayi sai yaga nafisa ce,ya manta shaf cikin
satin zasuxo jeran kaya,bai daga ba harta katse,saiya janyo wayar yana laluba inda ya aje
numberta,cikin sauyin da aka fara samu wanda ada bashi da ita.
Har tayi ringing sau biyu tana katsewa ba amsa,sai ana ukun sannan ta daga,shuru tayi
tana sauraren muryarsa wadda ko mutuwa tayi ta dawo ba zata kasa gane muryar waye ba
"Bakisan ina cikin gidan bane?" Ya tambayeta ganin tsahon zamansu baiji motsinta ko
gilmawarta ba,shuru babu amsa saboda haka ya kautar da wancan zancan
"Ki sameni a dakin karatuna....am yana nan daga baya kaman zaki shiga qofar kitchen ta baya"
ya sake mata bayani don ya sani bata sani ba,tunda bata taba zuwa ba.
Wayar ta sauke tana jin wani haushinsa na kamata,tome zaiyi mata,kiran me kuma yake
mata?.
Har sai daya zaci ba zata zo ba yaci gaba da aikinsa sannan yaji an murda murfin qofar,ya
daga kai yana kallon bakin qofar,itace cikin jar doguwar riga wadda ta yane kanta da qaramin
mayafinta,idonsa ya dauke wani abu na tsirga masa,ba kwalliya a fuskarta amma tayi masifar
amsarta rigar wanda ya kasa kubuta daga qyasata da zuciyarsa tayi.
Daga sallama bata sake cewa komai ba,ta samu gefansa ta zauna,saiya kashe wayar tashi
da yake dannawa,ya juyo gaba daya suna fuskantar juna sosai yatsunshi sarqafe da juna
idanunshi cikin nata,fuskarsa na nuna zancan da zaiyi mai muhimmanci ne,sai taji kallon da
yamata nauyi,ta kauda kanta gefe guda "Gobe jibi