Showing 48001 words to 51000 words out of 126208 words
Chapter 17 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf
kanshi da wuri ne,to kinyi kuskure idan ma zaki
zage damtse kiyi kaman kinayi to" ta jima tana juya zantukan miman a kwanyarta,inda daga
qarshe ta zage damtsen kaman yadda ta bata shawara,saidai gogan ko a jikinsa wai an mintsini
kakkausa,yadda ya saba mu'amala da ita haka yake babu abinda ya canza,naci kuwa babu
kalar wanda batayi masa ba,inda daga qarshe ma ta matsawa dadynta ya bata gurbin aiki a
kamfanin,ya bata din saidai tace matsayin secretary din anwar takeso,babu musu ya bata
kasancewarta diya mace diya tilo dake gareshi,anwar din bashi da bakin cewa don me?,haka
ya amsheta saidai kusan ba wani aikin kirki take ba,cikin qaramin lokaci kowa ya fahimci yadda
nafisan ke bala'in so da qaunar anwar din,wannan labarin shi yakai har kunnen umminta,take ta
saka abban nafisan ya karbe gurbin aikin daya bata aka maida shi da wani,fada ta dinga ma
nafisan kan wautar da take nunawa na nunawa namiji irin wannan zallar son bayan shi baisan
tana yi ba,kuka ta dinga duk da ta bata tausayi amma sam bata nuna ba,don tana sone idan
anwar zasiso nafisan ya sota don karan kanshi,ya kuma sota da datajarta ba tare data zubda
qimartata ba wajen neman soyayyarshi ba a matsayinta na diya mace.
Wannan karbe aikin ya bata ran nafisa matuqa,tana ganin kaman ummin nata bata sonta
ne,banda haka meye aibu a nunuwa anwar soyayya da take,hakan ya sanya ta sake maida
akalar shawararta dai wajen mima,inda ta bata wasu shawarwari da take ganin anwar din bai
isa ya tsallakesu ba dole ya furta mata soyayya da kuma kula koda ba haka bane har
zuciyarshi.
Cikin sa'a kuwa a lokacin aka maka wani gagrumin ruwan sama daya sanya gidan anwar
rushewa,dama yana dab da soma aikinsa ne,dalili kenan daya sanya alhj abba ya sake
nemanshi ya dawo gidanshi da zama har zuwa sanda zai kammala gyara nashin,tofa,abun
nema ya samu wajen nafisa,nan ta zage damtse ta shiga shigewa anwar din haiqan,har
abunma yana wuce gona da iri,don takan iya zamanta bangarenshi da sunan tayashi hira har
tara ko goma na dare,duk wadda kuwa akayi katari cikin yammatan dake damunshi da kira ta
kira nafisan ta samu nasarar dauka hara zata dauka ranar suyi kace kace da sunan matarshi
ce,hakan ya sanya ya qaranta dawowa gida da wuri,ya qirqirarma kanshi guraren zuwa saiya
daida daici sanda tayi bacci,wani bin ya dace wani bin kuma ya taddata dai tana zaman jiranshi.
Ganin abun yaqi ci yaqi cinyewa tamkar cin qwan makauniya yasanyata amfani da shawarar
mima,inda ta kwanta ciwo sosai suka hada baki da wani likita aka kaita can,ya dubata ya kuma
ce lallai tana cikin damuwa ne,kuma tilas a sama mata abinda takeso idan ba haka ba za'a iya
rasata.
Randa ta farfado daga suman qaryarta anwar na dakin shida alhj abba da mahaifiyar
nafisan,a sannan yana gefan daya gadon da babu kowa a kai yana charting da wani abokin
kasuwanci da suka fara shirin saka hannun jari shi da shi su tashi nasu kamfanin,sunanshi ta
soma kira wanda yaja hankalin dukkaninsu,saiya daga kai yana dubanta bayan ya amsa,ta wani
lumshe idanu kaman gaske tana kallonshi,nauyin idanun alhj abba da mahifiyarta ya sanyashi
barin abinda yake ya taso zuwa kusa da ita,sai ummanta tabar kujerar da take kai wanda ke
gaban gadon ta masa nuni daya zauna ba musu ya zauna.
Ba kunya ta kama hannunshi cikin dabara ya zame,saita saki kukan qarya
"Don Allah anwar kace kana sona kaji" mummunar faduwar gaba ce ta sameshi yayi shuru yana
jin yadda qirjinsa ke bugawa
"Ina sonki" yayi qundun balar fada saboda ganin yadda take kuka gaban iyayenta
"Zaka aureni?" Ta sake jefa masa tambayar data kusan sa jininsa hawa a take,tanason daureshi
ne wato da jijiyoyin jikinsa.*zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karki
sharing,ga mai buqata saita tuntubi wadan nan numbers*
07067124863
*ko kuma*
09032345899
*kuyi subscribing youtube channel dina don samun damar ganin shirye shiryenmu,subscribe
kyauta ne!*
https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos
*Alqawarin Allah*
1️⃣8️⃣
Kanshi yaji yayi masa nauyi kaman an dora masa dutse,kafin ya ankara nafisa ta saki kuka tana
roqonshi,dukkansu ya tabbatar hankulansu da kunnuwansu na wajen,haka yake,don dukansu
fata yace ya amince,don sun yarda da hankali da nutsuwar anwar,sun tabbatar idan ya auri
diyarsu ta fada hannun dako bayan ransu basa kokwanto ko shakka,saidai ta bangarin
mamanta magiyar da take ta taba ranta ta kuma bata takaici
"Meye haka kikeyi ne?,baki da hankali?" Cewar mamarta data matso kusa da gadon a fusace,ta
rasa meye matsalar diyartata,kullum kwanan duniya cikin dorata hanya da gyara mata
kurakurenta take amma a banza wai an tsikari kakkausa,cikin sauri anwar ya dakatar da
maman,ko mutuwa ma tana kunyar idanun mahaifi,hakanan kara da alkunya ma wani abu
ne,kuma shi alkhairi danqo ne baya faduwa qasa banza,nafisa diyarsu ce kuma fadinma suna
sonta bata baki ne,saidai su wasu irin mutane ne masu kunya kara da kawaici,wanda soyayyar
dansu bata hanasu ganin gaskiya
"Qyaleta mama" hakan shi ya tsaida hajiya ta koma da baya tana sauke numfashi,duban
nafisan yayi sosai sannan yace
"To kuma meye na kukan?,ya isa kiyi shuru kinga ba cikakkiyar lafiya ce dake ba"
"Indai kanason shuru na saika yarda kanasona zaka aureni ya anwar" alhj abba ne ya soma
takawa don barin dakin ganin rashin kunyar nafisan na qara gaba
"Zan aureki in sha Allah ki shuru" ajiyar zuciya dukkansu suka sauke wanda su kansu basu san
ta fito sarari ba saida suka hada ido da juna suka tabbatar anwar din yaji sai kuma sukaji
kunya,hakan shi ya tabbatarwa da anwar suma zancan na ransu,basason tararsa ko tauyeshi
ko tilastashi kan abinda bashi da niyya ko ra'ayi.
Wannan abun daya faru sai ya zama kamar wani lasisi nafisa ta samu na nuwa anwar
soyayya ko a gaban waye,wanda hakan ya sanya babu shiri ya qara qaimi wajen gyaran
gidansa,don yana ganin matyqar yaci gaba da zama a gidansu akwai matsala,don nafisan
kaman ta soma fitsare sawayenta,duk da yadda hajiya bilkisu ke taka mata burki amma sam
bataji,hudubar mima gani take itace dai dai don itace dai dai da ra'ayinta.
Ta dage sosai wajen farauto zuciyarsa,da yake Allah shike sanya soyayya cikin zukatan
bayinsa duk irin kulawa da kyautatawar da take masa bai taba jin wani abu mai kama da
qaunarta ba cikin zuciyarsa,yana mata kallon qanwa tana kuma da qima a idanunsa darajar
mahaifanta da yadda suke sonshi.
Shekara biyu cur rayuwar anwar ta sauya,kai baka ce shine wannan anwar din ba,kamanni
yanayin rayuwa da komai nashi,saida zuciyar nan na nan,zuciyar dai itace babu wani abu daya
sauyata,a sannan alhj abba ya shirya bikin yaye wasu daga ma'aikatansa wanda su suka
buqaci haka don suci gashin kansu,ciki harda anwar wanda tun dacan dama bai sha'awar zama
qarqashin wani,yafison duk wahala yaci gashin kansa,a lokacin da alhj abba ya yayesu ya
danqawa kowanne kudin sallama,saidai kudin anwar yafi na kowa yawa,ya zauna da alhj abban
ya gaya masa zai amsa ya qara cikin kudadensa,amma in sha Allahu zai dawo da dukka kudin
da aka bashi,aljh abba yace sam wannan kudin kyautane kawai saboda bauta da wahalar da
suka yiwa kamfani, a nutse anwar ya fahimtar dashi manufarsa,shidai yace yaje kawai ya kafa
kanshi din.
Komai na rayuwa wato yana da lokacinsa,hakanan rabon kwado bai hawa sama,anwar ya
tsaya tsayin daka,babu dare ba rana,babu lokacin bacci bana hutu sai daya tabbatar ya kafu,ya
fidda kudin alhj abba ya maida masa,shi kansa alhj abban yayi mamakin yadda anwar din yayi
kafuwar da aqalla kayi shekara goma sha bakayi irinta ba,saidai yasan komai yassarewace ta
ubangiji,shi kansa anwar yasan cewa qarfin addu'ar iyaye tsayawa kai da fata kan gaskiya da
riqe Allah da yayi shi ya kaishi fa wannan matakin,tuni ya tamfatsawa anty usaina gida,saidai a
sanda yace ta zabi unguwa saita zabi unguwarsu shahida,farkon layinsu wasu gidaje da suka
tashi suka saida,daya tambayeta dalili tace ba ruwansa,ba yadda ya iya haka yayi mata yadda
tace tana so,saidai har aka kammala ginin bai taba taka qafarshi unguwar ba,data koma kuma
sai zuwan ya zame masa dan zani shima,sai daya sanya aka sake fasa qofa ta bayan layinsu
yake shiga ta nan.
Ganin lokaci yana ja anwar yaqi soma maganar aurensu babban burin daya rage mata a
duniya yasa ta soma masa shagube,qwarai ya fahimta saidai har yanzu baiji nutsuwar zama da
nafisa a matsayin matar aurensa ba,duk da ya sani tunda ya furta dole ya cika amma har yanzu
zuciyarsa taqi karban hakan,abinda yaketa yaqi akai kenan,ita kuma tasan cewa iyayenta ba
zasu taba yi masa batun ba,mutum daya ce nan duniya zata ce yayi ya zame masa dole yayi
anty husaina,dalili kenan da yasa ta wanki qafa bisa shawarar mima taje mata da batun,wanda
a yanzu haka akan qadamin da suke kai kenan yanzu haka(idan baku manta ba a baya kunji
inda anty usainan ke masa maganar kar suji kunya kan nafisan).
Ta bangaren shahida ma kwanaki watanni zuwa shekaru sun soma tafiya,tuni ta kammala
degree dinta wanda ta samu gamasu da qananun shekarun da kowa ya kalleta sai yayi
mamaki,hakanan ta dora da masters shima Allah ya taimaketa ta kammalashi cike da nasara
mai tarin yawa,a sanda sakamakonta ya fito uncle hisham yaso ta amshi tayin lacturing da
jami'o'i suka yi mata tace sam bata ra'ayi,ya tura takardunta kamfanoni da dama ta samu aiki
daga wajensu nanma tace ba zatayi ba ciki harda kamfaninsu,ba yadda ya iya hakanan ya
qyaleta.
Sanda tazo masa da zancan koyarwa a *NOOR INTERNATIONAL* sai daya cire gilashinsa
ya kalleta don ya tabbatar da wasa take koda gaske,hakanan taji kawai bata da burin daya
wuce itama yaran talaka su amfana da karatu ilimi da baiwar da Allah ya bata,ba haka yaso ba
sam,saboda tayi karatu kai kyai wanda ya dace ta tsaya ta moreshi tayi amfani dashi ta hanyar
yin aiki a gurbi da kuma bigiren daya dace,hanatayi kai tsaye yace maida kai baya ne,ta nace ta
dage wansa ya sanyashi dole ya amince,amma bisa wasu sharudan.
Duk sanda suka mata wani abu da bai gamsheshi ba to ba shakka ta gama koyarwa a
makatantar,kai tsaye ta amince don bata ga ma abinda zai gamota dasu ba bare wani abun ya
faru,kan wannan sharadin ta soma koyarwa cikin makarantar,ta kuma samu karbuwa daga
wajen dalibai har malamai,zama cikin makarantar kuma yayi mata,hakanan yana mata dadi
qwarai.
Wannan shine labarin taurarinmu guda biyu da abinda ya zama sanadiyyar rabuwarsu ba
tare dakowannensu yasan cewa MAQARQASHIYA CE ba.
Zaman bitar rayuwarsu ita da anwar din data tsaya yi daren jiya ba qaramin taba zuciya ruhi
da kuma gangar jikinta yayi ba,tayi kuka irin wanda ta jima ta jefashi kwandon shara tare da
yiwa kanta alqawarin ta daina har abada,dalilin daya sanyata makara kenan bata kwanta da
wuri ba,hakan ya sanyata bata tashi farkawa ba sai qarfe bakwai na safe,ko sallar asuba ta
qwace mata kenan,cikin hanzari ta sauko daga saman gadonta duk da yadda jikinta yake a
matuqar mace,hakanan ya mata nauyi tun daga gangar jikinta zuwa kanta.
Tana idar da sallar da ake binta tana cikin yin azkar dinta na safiya huda tayi knocking ta
turo qofar,ta shirya tsaf cikin wankakku kuma gogaggun unifoarm dinta,kai kace yau ne zata
soma zuwa makarantar,fuskarta qunshe fal da walwala da farinciki,saidai tana ganin alamun
shahidan bata shirya ba ta turo baki kaman zatayi kuka "Anty...bakishirya ba,yaune fa?" Murmushi ta saki tana qarashe salatin annbi guda goma da
takeyi ta shafa sannan tace
"Banajin dadine yau huda"
"Amman zaki ko?" Ta tambayeta da sauri cikin fargabar kada tace ba zata samu zuwan ba
"Zanje huda...amma inajin zamu makara da yawa fa" qafa ta soma bubbugawa shahidan ta
gane me take nufi
"Kinga...ki shirya a soma kaiki,idan yaso in ya dawo daga kaiki ni saiya kaini,saimu hadu a hall
din hakan yayi?" Kaita kada tana murmushi
"Bari naje naci abinci to" ta fadi tana juyawa a guje ta fita a dakin,sai data bacewa ganinta
sannan ta dauke kanta tana sauke nannauyar ajiyar zuciya,tanajin inama ace itace
hudan,quruciya abu ne mai dadi,baka da matsala baka da damuwa,dukka ka tsere musu.
A nutse ta cire kayanta ta shige bandaki ta tara ruwan dumi ta soma wanka,saboda yanayin
jikin nata da batajin dadinsa yasa komai nata ma cikin nawaa take yinsa,hakan ya sanya ta
kashe kusan awa guda a wanka da shiryawa.
Ta jima gaban mudubi tana kallon fuskarta kaman yadda ta saba koda yaushe,dukda
idanunta sun dan sauya saboda kukan da tayi daren jiya amma sai taga fuskarta tayi
wasai,farar affaya mai taushi data nade jikinta ta amsheta qwarai,akwai adon golden
jikinta,hakanan taji kaman ta cireta,me yasa ma tayi shigar ne?,batason dukkan wani abu da zai
mata kyau a yanzu har yaja hankalin wani zuwa gareta,ta saka hannu ta soma cire lullubin
laffayar dake kanta anty zubaida ta turo qofar ta shigo,wanda hakan ya tarwatsa abinda tayi
niya
"Me kike haka?,yau lafiyanku kuwa shahida?"koda ta boyewa antyn yadda take qare mata kallo
tasan saita fahimceta,jin tayi shuru saita girgiza kai tana tabe baki
" damuwa dai damuwa dai?,ina zakikai damuwa shahida?,wannan kuma da kike niyyar cireta
fa?,don ta miki kyau?"dole yadda anty zubaidan tayi maganar ya baka daroya,saita murmusa
tana maida lullubin gami da zarar jakarta
"Ina kwana anty?"
"Lafiya lau ni zan fita inason idan ya saukeni saiya wuce dake makarantar basai ya sake
dawowa ya dauki wani ba"
"Tohm anty" tare suka fito daga dakin shahida ta wuce saman dining ta soma tsakurar
abinci,anty zubaida kuma ta koma dakinta don dauko mayafi da jakarta.
Sam abincin ji take bazai ciwu ba,don haka ta hada tea kawai tasha anty zubaidan na fitowa
suke fice tare.
Sun dan sake bata lokaci a hanya saboda cunkoson ababen hawa da suja tarar a hanya
wanda shahidan ta rasa na meye,titi ne da yake da wuya ka samu cunkuso akanshi,ita kanta
data dubi agogonta sai da taga makarar tayi yawa,da qyar suka samu hanya suka wuce,ta
sauke ajiyar zuciya sanda suka isa bakin katafaren ginin makarantar noor international
academy
"Yau ina tunanin zamu iya kaiwa biyu,saboda yaune hutu,idan mun tashi zan maka waya in
sanar maka"
"To babu matsala" ya fada yana tashin adaidaitan,tana tsaye kaman wadda aka dasa har
adaidaitan data sauketan tabar gurin,sannan ta soma takawa a hankali kaman mai sanda zuwa
cikin makarantar,haka kawai taji zuciyarta tayi mata nauyi,qafafunta kuwa kaman an sare
su,bugun zuciyarta na daduwa duk sanda ta qara wani taku guda da zai kusantar da ita da cikin
makarantar.
Harabar makarantar fetal,sai ababen hawan wasu daga cikin malamai da kuma wasu baqin
motoci guda uku da take kyautata zaton na baqonsu ne,shuru makarantar take,hakan ke nuna
mata cewa duk an tafi zuwa hall din da za'a gudanar da taron da kuma hutun dalibai,ta dan
tsaya tana shawarar ta soma kaiwa huda maganinta tasha kota bari sai sun hadu a dakin taron? "Malama shahida ya akayi haka?" Taji muryar kausar wadda ta fito daga can wani sashe wanda
zai sadaka da dakin taron,murmushin yaqe shahida tabi kausar dashi saboda yadda takejin
jikinta ba qwari haka kawai
"An sallami kowanne aji saura naki,yau tsarin na daban ne,inviglating ya yiwa kowanne aji saiya
gama dubaka sannan sai ku wuce kai da dalibanka dakin taron" murya qasa qasa tace
"Yana naki ajin yanzu ku kawai ake jira a soma,kiyi sauri ki riskeshi donma yana da kirki,nima
amakare na iso amma ina bashi uzuri ya karba" kai kawai shahida ta kada mata sannan ta
soma takawa zuwa sashen azuzuwa.
Bayanshi take iya hangowa saboda qofa da ya baiwa baya,tsaye yake gaban blackboard
sanye da suits ash da suka zauna das a jikinsa,fuskanshi na kallon 'yan ajin da alama wani abu
yake saurara daga garesu.
Sautin fitar murmushinsa shi ya soma dukan kunnenta,bisa alama wani cikin daliban ya
fadi abinda ya bashi dariya
"To shikenan...next question....who is the best teacher in dis school?"
"Anty rahama...aunty rahama!" Suka hada baki dukkansu suna fada,abinda ya sake sashi
dariya qwarai,irin dariyar daya jima baiyi irinta ba,baisan wanne irinso yaran kewa malamar tasu
ba,komai anty rahama anty rahama,wai wace anty rahama nan
"Auntyyy" wasu daga cikin yaran da suka hango tsaiwarta bakin ajin suka fada cikin shauqi da
nuna qauna tamkar sunji tambayar da yakewa kanshi,duban yaran yayi sannan a hankali ya
waiwaya yana son yaga wace.
Shahida....shahida ce dai tsaye cikin shigar kamala ta lafaya,jakarta rataye a kafadarta
idanunta saye da farin gilashin daya zamto yana taimaka mata wajen gani,sakamakon matsalar
idanu da taso gamuwa dashi tun shekarun baya saboda yawaita kukan da take,wani irin abu
yaji yana zagayawa saman kanshi,tsigar jikinsa gaba daya ta zuba,zuciyarsa ta kasu kashi
biyu,kowanne sashe na zuciyar tasa da abinda take ayyanawa.
Gaba daya jin jikinta tayi tamkar an zare dukkan wata laka data yi saura,,nutsuwa tayi
qaura daga jikinta a take,idanunta cikin nashi a hankali taga yana juye mata daga anwar data
sani zuwa wani mutum daban,matashin saurayi mai kyau kwarjini kamala da haiba,matashin
saurayi daya jiqu da hutu da naira,matashin saurayi mai cikar zati,tsayayyen namiji wanda
tambarin ilimi nutsuwa da wata qasaita ta daban ta bayyana muraran kan fuskarshi,dukkan wani
abu daya gani tattare da ita shekarun baya suka soma dawowa