Showing 54001 words to 57000 words out of 126208 words
Chapter 19 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf
zuwa hudu ba idanunsa ya sauya launi,jijiyar kanshi ta
motsa ta tashi,sai daya zo dab da ita sannan yace
"Kina nufin a haka zaki baiwa yaran mutane tarbiyya?,a haka kike koyar da yaran jama'a?,na
tambayeki ma me kike koya musu?,uhmmm gayamin,?,yadda zasu....." Sai kuma ya kasa
qarasawa ya kaiwa iska wafta da hannunshi sannan ya dunquleshi tsam kaman zai tatse
dukkan jinin dake cikin hannun nashi gaba daya,dai dai sanda shugaba kula da dukka sashen
makarantar ya iso ganin shuru har yanzu bai iso ba,cikin girmamawa ya rusuna
"Sir....."
"Dakata!" Ya tsaidashi cikin tsawa
"Dama irin wadan nan malaman kuke baiwa yara su koyar?" Cikin mamaki ya dubi shahida da
yake nuna masa,wadda take tsaye qam a wajen kaman an dasata idanunta kan anwar,tana jin
wani fushi na ratsata amma tana ta qoqarin hana hakan tasiri
"Sir.....kodai wani akasi aka samu,amma malama shahida na daya daga cikin malaman da kaf
makarantar nan babu kamarsu a kowanne sashe"
"Sauraramin" ya kuma dakatar dashi wannan karon har yana daga mishi hannu,ya maida
idanunsa cikin nata
"Indai wannan ce malamar da babu kamarta tabbas bakusan abinda kuke ba,babu abinda ta
iya!,bata iya komai ba!,daga yau na koreta!,na koreta cikin malaman makarantar nan.....kar
qafarki ta sake tako mana makaranta,you are fired!" Dukkan wani qwarin gwiwa da taso
tattarowa ya tarwatse da kalmarshi na qarshe saboda yadda sautin ya fito ya bada amsa kuwwa
cikin ajin,qoqarin tattaro abinda zata fada take saidai bakinta ya gaza fidda sautin saboda
karayar da zuciyarta tayi,idanunta suka hada qwalla fal suna shirin ga gangarowa,saiya sake
saka idanunsa cikin nata cikin wani qwarin gwiwa da yake ji yace "Uhmm...kina da wani abun cewa ne?....say it....say it mana!" Ya kuma fada cikin hargagi yana
dan dukan qirjinsa da yatsunshi gaba daya,jakar dake kafadarta ce ta sulmiyo saboda yadda
jikinta ya soma rawa,gaba daya kayan ciki suka tarwatse a wajen ciki harda kwalaben
magungunan huda,a kansu idanunsa suka soma sauka,wani tashin hankali da baisan na meye
ba ya rufto masa,saiya daga kai da sauri yana kallonta,sam ko daya bata da nutsuwar da zata
iya tsaiwa ta tattare kayayyakinta ko ta dauki jakar,hakan yasa ta juya da sauri ta soma
takawa,fatanta da burinta kawai shine tabar makarantar,tabar wajen,tabar inuwar da anwar
yake tsaye a cikinta,burinta shine ta nesanta dashi kawai,ta daina ganinsa ta kuma daina jin
sautinsa
"Ki dawo ki debi wannan kayan zatar naki" maimakon dawowar kamar yadda ya buqata saita
qara sauri kamar wadda aka biyo,don burinta shine ficewa daga makarantar ta tserewa
sautinsa,wannan sautin da ta jima da neman tsari dashi da mamallakinsa.
Titi kawai ta miqa bata ko waiwaye,bata buqatar abun hawa don ji take kaman qafafunta
zasuyi mata aiki fiye da abun hawan,sauri kawai take zubawa wani irin radadi na keta zuciyarta
kamar ana yankarta da reza,anwar dai anwar dai?,tabbas da tasan akwai wata rana da zasu
sake haduwa kaman haka da tuni ta yiwa kanta kandagarki da ita,wannan wace irin baqar rana
ce a wajenta
"Anty shahida...anty shahida" taji ana qwalla mata kira wanda sam bata tsaya ba har sai da
akasha gabanta,shugaban sashe ne riqe da jakarta ya miqa mata
"Don girman Allah kiyi haquri anty shahida,ya dauki hukuncin da dukkanmu bamu isa mu sauya
shi ba"
*zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karkiyi sharing,idan kina buqatar
siya ki tuntubi wadan nan numbers din*
07067124863
*ko kuma*
09032345899
*kuyi subscribing youtube channel dina don samun damar ganin shirye shiryenmu,subscribe
kyauta ne!*
https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos
*Alqawarin Allah*
1️⃣9️⃣
"sabon abune wannan a wajenmu,abinda bamu taba gani yayi ba tunda muke dashi,kowa ya
shaidai wannan kirkin nasa....anty shahida kodai wani abu kika masa?,mutumin qwarai irin haka
canzawarsa...."da sauri ta yanke masa hanzari
"Na gode malam,haka Allah ya qaddara" gaba tayi da sauri don ita kadai tasan me take ji,ita
daya tasan ya take ji,baifi taku biyar ba adaidaita sahu tasha gabanta tana tambayarta ina zata
je?,sai data shiga sannan ta gaya mishi inda zai kaita,duk yadda taso daure zuciyarta ta bari
saita isa gida saita kasa,ta tattakura ta rushe da kuka wanda har sai da dan sahun ya waiwayo "Hajiya...lafiya?,kiyi haquri komai yayi zafi maganinsa Allah" ita dai bata iya tanka masa ba illa
kukanta data ci gaba dayi.
Komao nata ta wurgar tsakar dakinta sannnan ta zauna dirshan tana risgar kuka,tanajin
kaman ranta zai fita ne,duk wata nutsuwarta a yanzu babu ita,anwar dai shi idanunta suka
gani?,anwar shine ya mata wannan tozarcin?,wanne abu tayi mai munin da har zaikai anwar ya
kasa mantawa irin haka ya sake binta da mummunan shaida da wulaqanci?.
Kusan haka ta dauki dogon lokaci,wanda ita din batasan wadanne awanni ta shafe haka
ba,sai tsintar muryoyin anty zubaida tayi da huda,taso qwarai ta tashi amma ta kasa saboda
wani mugun ciwo da kanta yake mata,da qyar take iya motsawa bayaga idanunta da suka zama
tamkar fulawar da aka zubawa yeast,muryar saddiq taji yana cewa "Mummy...tana dakinta" a hankali anty zubaida ta turo qofar tana cewa
"Alhmdlh,shahida kin daga mana hankali,ina kika shiga haka ke kuwa don Allah" ta qarashe
maganar tana qarasowa kanta,zaro ido anty zubaida tayi ganin irin rawar darin da take yi
"Subhanallahi,ashe bakyajin dadi" ta qaraso gefan gadon shahida ta zauna tana qoqarin yaye
rufar da tayi,da qyar da taimakon anty zubaidan ta tashi ta zauna sosai,qarya tayi mata kan
tana shiga makaranta zazzabi ya saukar mata shi yasa ta dawo bata kai ga zuwa dakin hutun
ba ganin yadda duk suka damu daga anty zubaidan har su saddiq,farouq anty zubaida ta saka
ya hada mata ruwan wanka,saddiq ya zubo mata abinci,ita taimaka mata ta shiga bandaki tayi
wanka gami da daura alwalar sallar azahar da magariba da duka bata samu yinsu ba,bata bar
dakin ba sai data ga taci abinci ta kuma sha magani sannan.
Tana daga kwancen amma hawaye take sharcewa masu dumi,duk yadda taso ga kaucewa
anwar da shafe duk wani abu daya shafeshi amma haka yaci tura?,wai sai yaushe?,sai yaushe
zaibar rayuwarta zuciyarta da kuma ruhinta ya huta?wunin ranar gaba daya wani irin wahalallen
yini tayi,ba shakka anwar ya zamewa rayuwarta babban qalubale,har zuwa dare tana cikin
yanayi guda wanda da qyar da sudin goshi ta samu wani wahalallen bacci ya dauketa.
********* **********
A hankali ya daga cup din qarshe na coffe din da yayi saura ya kwankwade wanda shi
kansa baisan kofi nawa yasha ba tsahon awannin daya kwashe zaune a wajen,idanunsa jajur
suke kai kace an badawa idanunsa yaji ne a ciki,saidai yaqi yarda ko kusa ko alama a kira
masa likita ya dubashi,bugu da qari dumin jikinsa ya qaru sosai har kana iya juyo hucinsa idan
ya fidda iska daga bakinsa.
Lumshe idanunsa yayi ya dora hannunsa saman sumarshi mai tauri saidai a gyare take
matuqa yana yamutsata,buri yake inama ya iya kuka idan yana cikin tashin hankali ko
tsanani,inama hawaye zasu fita daga idanunshi ko zai samu sauqin radadin da yake ji?,cikin
sauri ya sake bude idanun shi wanda suka sake kadawa fiye da dazu,ko yaya ya runtsesu
kwalaben da suka zubo daga jakarta yake gani,hakan yana nuna har yau bata bar dabu'arta
ba?,waishin waye ne?,waye ya koya mata wannan dabi'ar?,babu shakka da zaisan waye shida
ita duka saiya hadasu ya hukuntasu,dukan teburin gabansa yayi da hannunsa ko zaiji sauqin
radadin da zuciyarsa ke masa amma a banza.
Knocking katafariyar qofar falon aka somayi wanda yana ji yayi funfurus,saidai ya cika ya
batse saboda koma waye yana son sake birkita masa lissafi ne,bayan kuma ya riga da yaja
kunnen duka ma'aikatan gidan na kada wanda ya sake yako doshi sashensa.
Knociking din jinsa yake har qwaqwalwarsa,hakan ya sanya ya miqe a fusace ya isa qofar
ya budeta ya kuma bude baki don zazzagewa koma waye masifa,muhsin ne bayanshi likita ne
tsaye cikin fararen kayan aiki,dole ya hadiye abinda yaso amayarwa ya saki qofar ya juya zuwa
cikin falon ya zabi wata kujerar sabanin wadda ya tashi daga kai ya zube yana maida
numfashi,kallo daya muhsin yayi masa baice dashi komai ba ya kalli likitan sannan ya maida
idonsa ga anwar din
"Zaka iya aikinka" yace dashi,saiyaka jinjina kai ya soma takawa inda anwar ke zaune ya aje
akwatinshi kana ya bude,ya ciro abun gwada B.P ya daura a hannun anwar ya soma
gwadawa,cikin sakannin da basu wuce goma ba ya warware abun daga dantsensa ya samu
kujerar dake daura dashi ya zauna sosai idanunsa a kanshi "Yallabai....kasan yadda jininka ya sake hawa kuwa?" Ya tambayeshi kanshi tsaye
"Na sani" shima ya bashi amsa bayan ya sake bude dukka idanunshi akan likitan,cikin mamaki
likitan ya maida dubanshi ga muhsin,saiya masa alama daya rubuta magani kawai ya
qyaleshi,hakan kuwa akayi ya rubuta maganin ya baiwa muhsin takardar sannan ya tattara
kayanshi ya yuwa muhsin din sallama ya wuce.
Sai daya tabbatar da fitar likitan sannan ya miqe riqe da takardar maganin ya qaraso inda
anwar din ke zaune,idanu ya zuba masa yana kallonsa wanda hakan ya sanya anwar kau da
kai
"Tsahon shekaru kana fama da wannan damuwar,kaqi gayawa kowa dalilinta,kaqi gayawa kowa
dalilin faruwarta,duk dai amma bazai wuce akan shahida ba,anya kuwa anwar anya?,me yasa
kake shirye shiryen halaka kanka ne babu gaira babu dalili?" Zumbur ya miqe ya soma takawa
don barin gurin "Kar sake cewa dominta ne,na riga dana shafe babinta kamar yadda na shafe babin komai daya
faru dani a baya" qara sauri yayi ya wuce zuwa bedroom dinsa yanason baiwa kansa qwarin
gwiwa don baison ma anty husaina taji cewa baida lafiya,yanzu dukkan tsofaffin matsaloli zasu
taso,magana wata nabin wata har sai yaji kaman kanshi zai tarwatse.
Kwananta goma sha hudu tana qoqarin saisaita kanta da maida kanta cikin yanayin daya
dace,yaqi tayi ba dan qarami ba a kwanakin da kanta,ta rame qwarai saboda jinya tasha
sosai,bata fita ko ina,hakanan hatta da wayarta ma a kashe take,daga daki sai daki,sam anty
zubaida batasan meye ya faru ba,saidai dukkaninsu tattalinta suke har ta soma jin dadin jikinta.
Ranar wata karaba qarfe hudu na yammaci ta fito daga dakinta,gidan yayi mata shuru
haka yayi mata fadi,haka take ji duk sanda su huda suka wuce islamiyya saisu barta daga ita
sai anty zubaida kawai,hakan ya sanyata tunanin samo islamiyya itama da zata dinga zuwa
daukan karatu,don sanda ta fada din anty zubaida dariya ta dinga mata "Ohni zubaida,shahida bansan inda zakikai wannan son karatun naki ba" murmushi kawai tayi
"Anty karatu fa baya yawa,indai ba mutuwa kayi ba ilimi bai yanke maka ba,ba zaka rasa cin
karo da wani abun da baka sanshi ba"
"Gaskiya ne" ta fada cikin nuna gamsuwa.
Sanye take da atampha riga da zani wrapper,sai qaramin mayafi data yane kanta dashi,ta
sake haske haka ta fada,a hankali take takawa har zuwa cikin ainihin falon,babu kowa kaman
yadda ta zata,sabida haka ta juya ta nufi kitchen don tasan a wannan lokacin anty zubaida tana
can.
Da sallama a bakinta ta shiga da dashasshiyar muryarta irin ta marasa lpy,anty zubaida ta
juyo tana amsawa fuskarta qunshe da murmushi
"Patient an taso kenan"
"Wallahi anty...na gaji da kwanciyar nan" ta furta tana jan kujera ta zauna akai
"Ai gwara ki tattaka ko zakiji dadin jikinki" sama sama suke hira ita da anty zubaidan,inda tana
daga zaune ta amshi wasu ayyukan tana tayata,a haka su faruq suka dawo daga islamiyya
suka tarar dasu,zama sukai cikin kitchen din suma,saidai basu bar bakin anty zubaida ya huta
ba,wannan ya buda wancan wannan ya buda wannan wai duka yunwa sukeji,sudai tunda anty
shahida ta soma lalura kawai gidan sai a slow,waiwayowa anty zubaidan tayi
"Kinga shahida...don Allah debe qannenkin nan ku bani waje na yafe taya aikin wallahi" dariya
shahidan ta bushe da ita sannan ta miqe tana duban su huda
"Oya....lets go" ta furta tana kada hannunta,ba musu suka bita a baya suka fice zuwa falon.
Haidar ne ya soma canza tasha zuwa mbc bollywood faruq yace sam shi mbc action xai
kalla,huda kuma ta tubure ita mbc three takeso
"Dalla malama matsa kona kwada miki mari" faruq ya fada yana duban huda gami da zare mata
ido
"A'ah wallahi,dalili dame?,bani remote din gaba dayanku na raba gardama
"please anty" faruq ya fada cikin langwabe kai yana miqa mata remote din,ta gane me yake
nufi,saita basar tana cewa
"Babu wanda za'a kamo zabinsa,zabina kowa zai kalla" gwalo kowa kema dan uwanshi,tana
murmushi ta kamo TVC news kwana biyu tayi missing labarai bata samun kalla,tana jin haidar
na gulmarta
"Miss news" ta waiwaya ta kalleshi
"Zamu hadu anjima" da sauri ya dawo ya fasa hawa saman da yake qoqarin yi
"Sorry my aunty kar aji kanmu,niba dake nake ba,Allah kwana biyu dama da baki da lafiyar nan
duk sanda ustaz zai karbi hadda fecewa nake kar 'yammatan ajinmu su min dariya...ki
taimakeni"
"Saika biya cin hanci"
"Na yarda" ya fadi yana dariya,idnunta a kansu sanda suke wucewa dakunansu don sauya
unifoarm dinsu,saida suka bace mata sannan ta janye idanun nata tana sauke ajiyar zuciya,duk
sai taji kaman ita kadai keda matsala,takura da quncin zuciya,tana son ta rabu dasu amma ta
rasa me yasa qoqarinta ya gaza?.
Ganin cewa suma ba labaran suke ba saita sauya tasha zuwa FASHION TV,sabuwar tasha
ce amma tana tashe kuma ta samu karbuwa wajen al'umma sosai,sukan nuna abubuwa kala
daban daban,kama daga sutturu na zamani,bukukuwa,birthday,engagment da sauransu,wani
lokaci tana son kallon tashar saboda takan debe mata kewa,wasu abubuwan da suke nunawa
na burgeta.
Yauma ta tadda suna hira da wata mai gyaran jiki shuwaarab cikin harshen turanci,shirin ya
qayatar da ita sosai,ta bada dukkan hankalinta akai,sai suka yanke suka tafi talla,tallan farko da
suka sako na engagment din wasu igbo ne,tsaki taja tana gyara zamanta saboda sam bata ji
dadin tafiyarsu hutun ba,cikin ranta tana ganin rashin aikinyi ne kawai da zaka tsaya batawa
kanka lokaci saboda an maka egage da wani,wai itama soyayyar nan gaba daya meye zaqi ko
ribarta?,ta sake jan tsaki sanda aka nunosu suna bayyana yadda suke son juna da farincikinsu
da kuma saqon godiya ga duk wadanda suka halacci bikin engage din nasu,remote ta dauka da
niyyar sauya channel idan sun gama ta dawo,talla na gaba da suka fara haskowa sai yaja
hankalinta matuqa fiye da komai,engage ne na wasu couple da za'ayi musulmai masu cikakken
sunan hausawa,hoton farko na amaryar ne tayi kyau cikin shiga ta alfarma,wanda kallon farko
idan kayi mata zaka tabbatar ta samu gata,hoto na biyu shi ya sanyata jin wani abu ya tsirga
mata,a hankali kanta ya sara,hoton anwar ne a matsayin shine angon da za'a gudanar da bikin
engage din nasu kwanaki goma masu zuwa,sosai ya fito tarwai,ya cika screen din tvn tamkar
yana tsaye ne a gabanta,sanye da wasu shegun suit,daga sama har qasa shigarsa abar
birgewa ce iya kallon mai kallo,miqewa tayi tsaye ba tare data shiryawa hakan ba,wani abu mai
nauyi na danne zuciyarta kamar ana shirin riqe numfashinta ne,remote din taji ya mata kadan ta
kauda fuskarsa daga screen din tvn,saboda haka bata tsaya ba har sai data dangane da socket
din dake jone da kayan kallon ta kasheshi gaba daya,sannan ta juya da sauri don barin falon
zuciyarta na wani irin gudu tamkar wadda taga wani abun tsoro.
Sallamar uncle hisham ita ta tsaidata cak,tasan dole ya ganta bai kyautu kuma ta wuce ba
tare data yi masa barka da zuwa ba,daidaita yanayinta taketa qoqarin yi,kafin afkuwar haka
anty zubaida ta fito daga kitchen din,da sauri ta juya don batason taga fuskarta,ta gwammace ta
fuskanci uncle hisham a haka akan anty zubaida,yanzu zata saka ayar tambaya kan sauyawar
yanayinta lokaci guda bayan ba haka ta baro kitchen ba.
"Sannu da zuwa abbu" ta fada a sanyaye idanunta na kallon qasa saboda tana ji a jikinta
kamar qwayar idanun nata ba dai dai suke ba
"Yauwa rahamatullah(ya kirata da ainihin sunanta),ya jikin naki"
"Da sauqi abbu" ta amsa masa da sauri saboda wani abu dayake qoqarin shaqe mata wuya
"Ma sha Allah" juyawa tayi da zummar barin falon yace
"Shahida" sake juyowa tayi
"Na'am abbu"
"Anjima inason ganinki"
"Toh" ta fada tana sake juyawa zuwa dakinta.
Takai ta kawo tayi hakan yafi sau babu adadi,hawaye keson fita daga idanunta amma ta
hana kanta hakan,tanason lalubowa kanta dalilin da zai sanyata kuka
"Enought is enought shahida,kinyi kuka a rayuwarki da yawa...ya isa haka,ya kamata ki kawo
qarshen komai,ya kamata komai ya qare" take fadawa kanta da kanta bayan ta tsaya gaban
mudubin tana duban qwayar idanunta da kanta gaba daya saika zaci zararriya ce,kallon kanta
da kanta take tana bawa kanta qwarin gwiwa,saidai ina hawaye ba'a masa shamaki,saida daya
ya ziraro mata wanda ya baiwa dukka sauran damar samun hanya,ta fashe da kuka sosai cikin
sassarfa ta isa saman gadonta tayi rub da ciki tana cusa kanta qasan filo tana kokawar hana
kanta ci gaba da kukan.
Kaman ba zata falon ba amma dole ta qarfafa jikinta ko don saboda abbu da yace yanason
ganinta,ta gyra fuskarta gaban mudubi ta zizara kwalli bayan ta shafa powder,batason kowa ya
fuskanci tayi kuka,a kasalance take kawowa har ta iso cikin falon,wanda a al'adar abbun dama
bayan cin abincin dare yana zama ne cikin yaran nashi su taba hira kafin ya tattara ya wuce
dakinshi.
"Rahama,meye ya faru ranar hutun noor international?" Tambayar da abbun ya jefo mata
kenan bayan ta gama dubawa su farouq haddarsu da