Showing 114001 words to 117000 words out of 126208 words
Chapter 39 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf
dauki remote ta qaro gudun
acn,sannan ta kashe qwan wutan ta koma ta kwanta.
Sha biyu saura yaji zaman ya isheshi,duk da yawancin lokutan yakan wuce haka azaune ya
riga daya saba,saiya kashe duka kayan wutar ya tattare komai ya tura qofar dakin ya
shiga,duhu ne ya masa maraba,ya laluba ya kunna wutar,can ya hangota saman gadon nashi a
kwance abinta,ta tattara dukkan filallukan,wani ta dora kanta wani qafafunta,wani ta takore
bayanta kamar mai ciki,duvet din nashi ma hannunta ta dora akai don ba rufe tayi ba,hakanan
ta raba gadon biyu ita bata gefe guda kuma bata tsakiya gaba daya,saiya tattare hannayensa
kawai ya tsaya yana kallonta,yana tunanin ta ina zai kwanta?.
Qarar wayarshi ta katse masa tunani,ya cirota daga aljihunsa ya duba,tsaki yaja ganin
wadda take kiran,saiya maida wayar aljihu,ya qarasa side bed ya dauki remote na ac ya rage
sannan ya nufi bandaki ya daura alwala,sallah yayi raka'a biyu yana saman abun sallah yana
addu'a wayartashi ta sake ruri,tsakin dataji yaja tuni zuciyarta ta gaya mata wacece,gyara
kwanciyarta tayi ta soma gunguni qasa qasa yadda tasan zai iyaji
"Haka kawai a takurawa mutane da waya,sannan a kashewa mutane iska bayan zafi sukeji"
daga kai yayi daga tasbihin da yake qirgawa da yatsun hannayenshi yana kallonta,saidai bai
samu nasarar kallon fuskarta ba,sai bayanta daya hanga wanda rigar baccinta mai sulbi tabi ta
lafe,sake maida kanshi yayi yaci gaba da tasbihinta ba tare daya sake daga kanshi ba,saida ya
kammala komai,ya sanya kayan baccinsa sannan ya tsaya yana tunanin ta inda zai kwanta,ya
jima yana kallonta ta rigar baccin dake jikinta wata kasala na saukar masa,saiya zauna gefan
gadon qafafunsa a qasa,hannu ya sanya ya dan daki gefan filon da take kai,shuru ta masa
kaman batajiba,saida ya sake sannan ta juyo gaba daya a fusace,cikin rashin saniiii wuyan
rigarta yadan zame,saman qirjinta ya fito bata sani ba,idanunsa suka soma kaiwa nan,yayi
hanzarin janye idanunsa,saiya tsuke fuska
"Bafa wai zaki dinga zuwa min da duk shigar da kikaga dama bane,saboda haka ki tashi ki saka
hijabinki" saidata koma arub da cikinta ta juya masa baya sannan tace
"Ina cewa dai duka gidan nan gidana ne ko?,ko bayaga haka ma ni ban saba kwana da hijabi
ba,ban iya ba saidai kayi haquri kam" daga haka bata sake waiwayoshi ko cewa komai
ba,hakanan ya qaraci zamanshi,dole ya kashe wutar ya dawo daga gefe daya kaman wanda ya
roqa ya kwanta,gamida hade hannayenshi yayi matashin mai dasu karon farko tsahon shekarun
da suka wuce dabazai iya tunawa ba.
Qamshinta shine abu na biyu daya ringa takurashi,ya juya baya a banza,yayi kai da qafa
amma banza,saida bacci yayi masa mugun kamu sannan ya samu salama.
Sanda ta bude idonta ta fuskanci bacci yayi awon gaba dashi,saita miqe ta sauka daga
gadon ta koma saman kujera tayi kwanciyarta,abinda bata sani ba shine tunda ta motsa ya
tashi,kusan ya saba kwana shi kadai,ya jima rabonshi daya kwana da wani,hakan ya sanya
tunda suka kwanta yakejin banbarakwai baccin bai sama dai dai yadda ya saba ba.
Cikin duhun taji an sureta gaba daya,ihu take shirin saki taji bakinsa cikin nata,bai ajeta ko
inaba sai saman gadon,qarfinsa ya aza mata,qasa qasa yace da ita
"Tunda kika fara saikin sauke,anan zaki kwana kamar yadda kika tattare min filo da abun rufa"
"Ce maka akai tsoro nikeji?,kawai banda muradin hada gado dakaine"
"Nasan da hakan,kuma saboda sanin baki da muradin yasa na dora mikishi a matsayin
wajibinki" ya fada sanda yake komawa inda ya tashi,saita yunqura zata sake sauka
"Idan kika sauka ban yafe ba" a hankali ta dawo ta kwanta inda ta tashi,jikinta yayi sanyi da
kalmarsa,tasan tabbas idan ta sauka din ba ruwan Allah sai Allah ya isanshi ta bita.
Washegari data sauko tuni har sa'ida ta kusa kammala kintsa gidan,rainon anty usaina na
wasa na,dama ko a gidan duk yalwar gidan nasu babu mai aiki,ita da yaranta suke kula da
gidan,sai masu share can harabar gidan,saita tsaya ta hada breakfast, sunayi suna hirarsu
harta kammala,cikin dakinta ta shiga tayi wanka,ta shirya cikin atamfa riga da skert.
Sama ta sake komawa da zimmar dauko wayarta,ta turo qofar bedroom din ta shiga,saita
sameshi xaune gefan gado tana latsa wayarshi,kai ya daga suka hada idanu,saiya kasa dauke
idanunshi
"Ya salam" ya furta can qasan ranshi,sosai kayan suka fidda kamarta,ta dauke kenta zata
gotashi tana gaidashi,baisan ya akayi ba ya tsinci kansa dakai hannunshi ya fincikota,bata zata
ba saboda haka jikinsa tayo gaba daya cikin tsoro,saiya riqrta gam,ta dinga yunqurin qwatar
kanta amma qoqarinta ya gaza,wani irin abu yakeji yana zagaya jikinsa,idanunsa ya saka cikin
nata cikin qanqanin lokaci ya kashe mata jiki gaba daya,saidai duk da haka bata bari hakan ya
nuna ba,hade ranshi yayi sannan yace
"Bana gaya miki cewa ba kowacce shiga nakeso ba?" Ranta a hade tana sake son qwace kanta
tace
"Nifa gidana ne,kuma sai an kafamin dokar yin dressing?" Girarsa duka ya dage
"Au haka kika ce?,bari na koya miki hankali,gobe idan na hanaki kya sakeyi" daga haka ya
juyata qasanshi ya aza mata dukka qarfinsa,yanayin yadda yake matan saiya soma bata
tsoro,jikinta ya dauki rawa gaba daya ta zaro ido tana kiran sunanshi,harga Allah yasone kawai
ya razanata saboda zuciyarshi da jikinsa ba zasu jure ci gaba da ganinta a haka ba,zaifison taci
gaba da kaikawonta cikin hijabi,don bayason dukka abinda zai dinga daga masa hankali yana
zaman zamanshi,amma sai gashi yana niyyar wuce gona da iri.
Cikin second daya bacin rai ya rufto mishi,saiya mirgina gefe sannan ya tashi ya zauna
yana dafe da kanshi daya sara masa,zuciyarsa ta cunkushe bacin rai ya mamayeshi,fuskar
saurayin ta bayyana muraran,zayaso ya sake ganinsa a rayuwarsa,ba shakka duk randa ya
sake katarin ganinsa baiga abinda zai hanashi daureshi ba,me yasa ya shiga rayuwar
shahida?,me yasa ya haifar da gibi a rayuwarsu da har yau ya kasa cikewa?,saiya miqe kawai
ya nufi bandaki ba tare daya sake waiwayarta ba,cikin tsoro ta tashi ta gyara gashinta ta dauki
dankwalinta da sauri ta fice daga dakin.
Cikin kwanakin duk wata hanya da tasan zatabi ta raunana zuciyar iyayen nata sai data
bi,ta kwantar dakai sosai da kuka da magiya kansu yafe mata,to hausawa sunce tsakanin daa
da iyayensa sai Allah,hakance kuwa ta kasance,suka yafe matan tare da sake jan kunnenta
kanta sake aikata sakarci makamancin wannan,ta kuma nuna musu ta tuba,farinciki sosai ya
cikata ganin ta cimma nasara a matakin farko,saita bijiro musu da magana ta biyu bayan 'yan
kwanaki.
Anan ne kowa yacoge a cikinsu,abban yace sam da kunya a idanunsa bazai nemi anwar ya
dawo ya aureta ba,,ganin abba yaqi saita waiwaya tana hawaye ta dubi mummy
"Mummy don Allah" kaita girgiza
"Wa?,ni?,toba dani ba sa lallen karya,idan anwar ya dawo yau yace zai aureki sai nafi kowa
farinciki saboda sanin nagartarsa,amma a yanzu dai ina bayan mahaifinki,keda kika bata ke
zaki gyara abinki" sosai hankalinta ya sake tashi ganin ga qoshi amma tana neman tayi kwanan
yunwa,anwar kam tun kafin ta tunkari kowa shita soma tunkara amma*_43R_*
*Alqawarin Allah*
43
Wani irin murdawa mararshi tayi wanda hakan ya sanyashi duqawa riqe da cikinsa,ya tako a
haka a hankali zuwa gefan gadon,idanu ta zaro jikinta ya dauki rawa,ta tako ta tsaya daga
bayanshi amma ta kasa cewa komai,da qyar cikin rawar murya tace
"Sannu,baka da lafiya" kallonta kawai da yayi da qwayar idanunsa da suka kada zuwa launin
jaa ya tabbatar mata da bashi da lafiyar kenan,ta juya zata futa da niyyar ta kira anty usaina ta
shaida mata,saiya dakatar da ita
"Jirani na shirya,zanje naga likita".
Hannu likitan ya saka ya cire abun abun awon jini daya sanya a dantsen anwar din yana
kallonshi
"kamar yadda na tsammata ne,jininka yahau sosai,kamarma yahau fiye da kowanne
lokaci,gaskiya anwar bazan boye maka ba,wani lokaci sai naga kamar kana wasa da lafiyarka
ne,bansan meya hanaka kwantar da hankalinka ba ka samu jinin nan ya sauka gaba daya,sai
yayi kaman ya sauka saiya sake hawa,bansan daga inda matsalar take ba" murmushin qarfin
hali yasaki,ya lumshe idanunsa kana ya bude
"Share kawai khalid" likitan mai sunan khalid ya waiwaya ya dubi shahida wadda ke zaune wata
kujerar daban,hannayenta rungume a qirjinta,ta zubawa anwar ido ba tare da yasani ba,kallon
mamaki take masa na bayanan da taji daga bakin dr khalid,wanne irin hawan jini?,yaushe
anwar din yasamu hawan jini?,iya saninta dashi kaf tarayyarsu anwar baida hawan jinin,yaushe
ya gamu da wannan matsalar?
"Madam" ya kirata wanda hakan yaja hankalinta zuwa kanshi
"Bayan hawan jini gaskiya abokina na buqatar kulawa,don Allah ki kulamana dashi,nasan kinfi
kowa sanin mutumin kirki ne,lalurarshi ba zata yiwa mutane da yawa dadi ba" kai ta gyada
likitan ya miqe yana cewa
"Ruwa naso indan saka maka,amma nasan hali ba zaka taba yarda ka zauna ba,bari na rubuta
maka wasu magungunan na bayar a karbo maka,madam sai a kula da bashi akan lokaci" kai ta
sake gyadawa tana duban anwar din,saita kauda kai sanda taga ya waiwayo suna shirin hada
idanu.
Suna tafe a hanya motar ta dauki shuru,kowa da abinda yake saqawa cikin
zuciyarsa,tambayar ta yiwa shahida tsaye a rai na hawan jinin anwar,yayin data gefan anwar
din maganganun dr khalil suka dinga kai kawo a qwaqwalwarsa,tabbas ba shakka shine mutum
na farko da zaifi kowa son rabuwa da cutar,zaifi kowa son ganin ya cire kome cikin ransa,zaiso
ace ya goge kome dake damunsa,amma saidai shi kansa yasan hakan bame yiwuwa
bane,shahida ce,idan da wata macen ce daban ha tabbatar da tuni ya cireta daga rayuwarshi
irin fitar da mai rai kanyi daga duniya wanda har abadan bazai dawo cikinta ba,amma akan
shahidam hakan ya gaza,ya sani cewa koda zai fada a baki koda zai nuna a aikace shahidan
bata dameshi ba yayiwa kanshi qarya,karon farko dayakejin inama inama,inama ace bai kalli
hotunan ba,inama ace ranar baije gidansu zance ba bare yaga abinda ya gani,inama ace
shahidan bata fada halin data fada ba a baya,da wannan tunanin suka isa gida,da kanshi
wannan karon yasha maganin sannan ya shiga bedroom dinsa ya kwanta kozai samu relief.
A kasalance yake shiryawa cikin farar shadda,riga iya gwiwa mai gajeran hannu da dogon
wando,kana ganin yadda yake shiryawar kasan cewa ba wani dadin jikinsa yake ji sosai
ba,yana daura agogon hannunshi ta turo qofar dakin da sallama,hannunta riqe wata butar shayi
me kyau,da mamaki take dan dubanshi saidai bata tanka ba ta aje butar "Ya jikin?" Ta tambaya a taqaice,daga kai yayi ya dubeta yadda ta juya baya ya maida kansa
yaci gaba da daura agogonsa sannan yace
"Alhamdulillah" tadanyi taku biyu sannan ta sake tsaiwa,ya fuskanci akwai magana a bakinta
saiya amsa
"Tun jiya akwai alqawari. Haduwarmu dashi,jiya banjin dadi,so yau nakeson nacika" yana gama
fadi ta taka ta sauka daga saman,dama tanson jin fitar zaiyi amma tanajin nauyin tambaya.
Tun jiya take zuba idanun ganinsa,ta kasa zaune ta kasa tsaye,tun bakwai na dare take
zirya tsakanin harabar gidan,falon abbansu zuwa nasu falon da dakinta ma gaba daya,ganin
goma na dare tayi hankalinta yayi mummunan tashi,Allah yasa abba bai gane ba,Allah yasa
anwar bai kira abba ba ya sanar masa yaji yana nemansa ba abba kuma yace bashi bane,daga
daren zuwa safiyar ranar ji tayi kaman ta zare,duk motsin shiga da fitar mota a gidan yana kan
idanunta,saida dare yayi ta tabbatar babu wani sauran wanda ka iya zuwa a wannan lokacin
sannan ta haqura.
Da safema haka ta dasa abun zama cike da fata da kuma buri,qarfe goma da rabi da minti
takwas aka saki horn mai gadi ya doshi qofar don ya bude,gabanta wani mugun faduwa yake
haka tamiqe tsaye tana duban qofar gidan,kusan shidewa tayi sanda taga fitowarsa daga
motar,idanunta qur akanshi yana sake burgeta duk wani motsi da yayi,tana kallon aka masa iso
cikin falon daddyn,cikin wani mugun hanzari ta diba tayi cikin gida kai tsaye ta wuce
dakinta,hijabi ta lalubo ta zira saman kanta sannanta sake fitowa da hanzari don kada lokaci ya
qwace mata.
Sanda ta shiga mummynta na tare da daddyn,hakan yayi masifar yi mata dadi,sait tayi
qoqarin daidaita nutsuwarta ta taka zuwa cikin falon da sallama.
Dukkaninsu suka amsa mata,ta isa gefan daddyn inda anwar ke zaune qasan carfet
saboda girmamawa suna gaisawa,nan ta duqa kan duka gwiwoyinta,ta saki kuka sosai wanda
ya karade ilahirin falon,duka sakin baki sukayi suna kallonta,mummy ce cikin hade rai tace
"Kewai meye haka?,wanne irin shashancine wannan kawai zaki shigo kisa mutane a gaba da
kuka?" Cikin muryar kuka tace
"Don girman Allah mummy ku yafemin,ku yafemin,ku roqamin ya anwar shima ya yafemin"
"Me ya dawo da wannan maganar data riga tawuce kuma nafi?"
"Gafarar ya anwar nake nema" gaba daya kanshi ya kunce,shi sam.bai dauki abunda tayi a
matsayin wata matsala ko abun bacin rai ba,tuni ya riga daya wuce wajen,tun a lokacin da abun
ya faru shiya tattara komai daya shafi wannan fannin ya ajeshi a gefe,baison zancan yayi tsaho
saboda haka yace "Ya riga ya wuce har abada" ranta taji yayi,wani mugun sanyi,alamun nasara na tabbata kenan
a gareta,saita sake sunkuyar da kanta qasa sosai sannan tace
"Bansan cewa nayi wauta ba kuma nayi kwaba saida na rabu dakai,nakai kukana ga abba da
mummy amma kowannensu yaqi mara min baya ka dawo cikin rayuwata,sunce idan ka amince
suna murna da hakan,saboda sunsan cewa idan sukayi maka magana ko bakaso zakace
eh,gani a gabanka anwar don girman Allah inason ka sake dawowa rayuwata karo na biyu,ka
yiwa iyayena dake shauqin son ganin haka alfarma wanda alkunya da kawaici yasa suka kasa
gaya maka"
"Ke nafi!" Abbanta ya dakatar da ita ta hanyar daka mata tsaw,a,bataji komai ba don idanunta
da zuciyarta sunyi nisa wajen son ganin cikar muradi da burinta,saita daga kai ta dubi abban
sannan ta sake sunkuyarwa
"Abba na fadi masa gaskiyar abinda yake faruwa ne,na tabbatar da zaka iya da kaine xaka
nemi ya aureni karo na biyu....anwar,ka duba wannan alkunya da kara ta iyayena gami da
girman soyayyar da nake maka" baqinciki ya kama mummy na yadda sam halayen nafisan suke
wadansu irin mabanbanta daban,ta kawo mata duka anwar ya dakatar da mummyn cikin sauri "Rabu dani na mata duka,baki da kunya nafisa ko kadan?,a gabanmu kice kin fasa
aurensa,sannan ki dawo a gaban namu dai kice ya aureki?,wace iriyar yarinya ce ke?" Cikin
kuka sosai nafisan tace
"Kuskure ne mummy yanzu kuma na gane kuskuren da nayi,wallahi idan babu anwar rayuwata
ba zata taba dai daita ba,mummy ku tayani bashi baki"
"Ce miki akayi baida zuciya da zaki gujeshi yanzu ki dawo masa saboda rashin ta ido?,kema
kinsan bazai taba yiwuwa ba" mummy ta amsa mata tana jifanta da harara,so take kawai ta
samu dama ta daki bakin nafisan ya fashe ko zata samu sassauci takaicin dake cikata
"Na amince zan aureta" anwar ya furta,lafazin daya girgizasu dukka su ukun,basu taba zata ba
sam ko a mafarki,sunyi tsammanin bazai taba yarda ba,cikin hikima yake karantar yanayin
fuskar alhj abba da munny bilkisu,ko basu fada masa ba ya gama karantar yanayin da
zukatansu suka shiga,alhj abba da mummyn suna da daraja a idanunshi,ya sani cewa tsantsar
kara kawaici da alkunya ne dasu,amma da qauna kowa ya sani suna matuqar qaunar nafisa,me
yasa shi bazai iya musu kara ba ya auri diyar su wanda yasan shine cikon muradinsu,ba shakka
da nafisan diyar wani ce da ya barta kenan har abada,amma ko a lahirama wani yana cin
albarkacin wani bare nan gidan duniya.
"Bazaiyiwu ba anwar,ka tashi kawai kayi tafiyarka" cewar alhj abba,don harga Allah bayason
su xama sila na yiwa anwar din dole,wani tashin hankali ya saukowa nafisan,ya ga qoshi ga
kuma kwanan yunwa tana shirin yi?,me yasa abban nata zaiyi mata haka?,girgixa kai anwar
yayi cikin qarfin hali
"A'ah abba,ba za'ayi haka ba,nafisa qanwa take a gurina idan da kara da kawaici,abinda ya
wuce ya riga daya wuce tunda ta gane kuskurenta,Allah ya yafe mana gaba daya ya kuma
kiyaye gaba" murna farinciki kaman ta taka rawa a gabansu,saidai yanzu ba lokacin hakan
bane,sake kwantar dakai tayi sosai ta sake neman afuwa gamida nuna tsantsar
nadamarta,itakam hajiya bilkisu miqewa tayi ta fice tabar falon,tana jin ciwo cikin zuciyarta sosai
duk lokacin da nafisan ke roqar soyayya,ta rasa wacce irin diya Allah ya bata?,zataso ace
nafisan ta auri wanda shi yake mutuwar sonta ba ita take mutuwar sonshi ba,ta rasa meye
matsalarta meye damuwarta?,ba kalar saurayin da bata dashi wanda kowa neman yardarta kan
ya aureta yake amma sam ita ta qwallafa rayuwarta kan anwar,eh anwar ya isa mutumin da
za'aso a zama mata a gareshi,amma duka hakan a ganin mummyn xaifi kyau idan har shine
yazo da kanshi ya nemi hakan.
Tunaninsa ne ya dinga kasuwa kashi kashi,abinda ya faru yanxu cikin gidan alhj
abban,tabbas shi shaidane kan irin son da nafisan ke masa wanda sautari hakan yakan bashi
mamaki qwarai,karbar aurenta da yayi yasani shi kadaine abunda zaiwa alhj abba ya saka
masa dimbin alkhairin da yayi masa da kyautatawa a rayuwa,da yadda yake kallonshi tamkar
danshi,saidai ko daya zuciyarsa babu nutsuwa ko jin dadin karbar da yayi,bayajin wani daidaito
ko daya kan batun nafisan,duk da agefe guda ya sani yana da buqatar kulawar mace,amma,ta
yaya wata zata sanyo kai cikin rayuwar gidan alhali ga yadda take?,ta yaya zai kawo
gyara?,tuninsa ya sake tafiya kan hotunan dake aje har yanzu suna yankawa gami da qona
zuciyarsa duk daqiqa ko sa'a daya da zata shude,duk lokacin da idanunsa