Showing 39001 words to 42000 words out of 126208 words

Chapter 14 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf

zata gaya masa wannan murdaddeb zance?,tun baya baisan halin da
gidan nasu ke ciki ba saboda kare martaba da qimar iyayenta,duk sanda ta fuskanci akwai
rashin jituwa tsakanin iyayen nata bata taba yin zance a gidansu,a gidan anty amina take
zancanta,toko yanzu ma da lamarin gidan nasu ya lalace can take tafiya ya sameta anan,don
ba zataso wataran wani mummunan abun ya faru a gabansa ba duk da yana musu kallon
iyayensa amma asirin ciki sai hanji.



*MAFARI*


Cikin tashin hankalin da bata taba tsintar kanta a ciki ba ta fito daga gidan nasu tana
hawaye,yau a gidansu a gaban idanunta ake doki in doka tsakanin ummanta da
abbanta?,wanne irin iyaye gareta?,ya ilahi ji take kaman zuciyarta zata fashe,ji takae bugawa
zuciyarta zatayi,ita kadai tasan yadda takeji tana jin kaman zuciyarta ta kumbura ne ta cika
qirjinta,zataso ace zunnurah na nan saidai ina,gidan anty amina takeson zuwa amma babu ko
nutsuwar daukan kudin mota a wajenta,ba tare da tuna nisa da tazarar dake tsakaninsu ba ta

hau tafiya cikin fitar hayyaci da tashin hanakali bacin rai da baqinciki.

Dawowarta kenan daga inda taje ta sauka a abun hawa,tana yunqurjn shigowa layin nasu
ta hangi kaman shahidan,tayi mamaki don shahidan bata taba zuwa gidansu ba,hakanan bata
yowa layinsu don asalan ita bamai yawo bace,sauri ta qara donta cimmata,sai taga itace dince
kuwa,amma a binda ya bata mamaki hawayen data gani shabe shabe a i fuskarta,hannu tasa ta
kamota tana cewa
"Shahida,meye haka kuka kike fa akan hanya" sai a sannan ta kula da fiddausin,sake fashewa
da kukan tayi,ita koma waye ta gani zata iya fada masa abinda ke damunta ko zataji sassauci a
zuciyarta,abun ya mata yawa,wannan damuwar bata shekara daya bace ko biyu,ganin haka sai
fiddausin ta janye shahidan zuwa gidansu,ta tura gate din gidan suka shige sannan suka nufi
dakinta ta qofar baya,sau tari takan iya shigowa ba tare da an sani ba saboda gidan nada girma
babu laifi.

Kuka take sosai tana cewa
"Na gaji fiddausi....na gaji da wannan bacin ran,ina zanje naji dadi,me zanyi na samu sassauci?"
Murmushi fiddausin ta saki,duk da shahidan bata gaya mata damuwarta ba amma tana ganin
sara ne yazo kan gaba
"Ina da maganin damuwa shahida,maganin da zai dauke duk wata damuwa da kike ciki komai
qarfi da girmanta,zaki jiki fresh kaman yau aka haifeki,nauyi da zuciyarki keji ya sauka kaman
bai taba faruwa ba" idanunta dake jiqe da hawaye ta daga tana kallon fiddausi
"Don girman Allah ki bani kona daina jin suyar da qirjina yakemin"
"Kwantar da hankalinki basai kin hadani da girman Allah ba" ta fada tana zuge jakar data shigo
da ita,kwalabe ta fito dasu ta hada abubuwan ciki ta gauraya sannan ta miqawa shahida
"Daga kanki ki shanye nina daga wajen likita nake shi ya rubutamin shi yace maganin damuwa
ne" ba tare da kowanne tunani yazo kanta ba,ba tare da tayi lissafin komai ba,ba tare da ta
jinkirta ba ta daga kai ta shanye duka din kamar yadda fiddausin tace mata,cikin wasu qananun
mintina ta soma jin dummm,ta soma ji kamar ana sauyata daga tata duniyar zuwa wata
daban,ta soma daina gane komai,take a nan ta zube saman gadon fiddausin,lokaci qanqani
nannauyan bacci yayi awon gaba da ita,dariya fiddausin ta saki tana rufe kwalabenta tare da
maidasu haka tana cewa
"WASA FARIN GIRKI YARINYA".


*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI
SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da
sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*
https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videoshttps://youtu.be/T9a10
h1Apqs


*zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani DON GIRMAN ALLAH karki sharing,idan kina da buqata
ki tuntubi wadan nan numbers din*

07067124863

*ko kuma*

09032345899


*Alqawarin Allah*
1️⃣2️⃣


A hankali ta farka tana mutstsuka idanunta da taji sun mata nauyi,sam ta mance inda take
saida tayi dan tunani sannan ta tuna,da hanzari ta tashi ta zauna ganin gari yayi duhu sabanin
sanda suka shigo gidan akwai hasken rana,agogon bango ta kalla sai taga qarfe takwas,hakan
yana nuna kenan ta rasa sallar la'asar magariba dama isha'i.
Da hanzari tayi nufin tashi saidai gaba daya jikinta a mace yake babu qwari,daidai lokacin da
fiddausi ta shigo dakin dauke da plate din abinci,cikin murmushi take duban shahida
"Sannu kin tashi?,ya kike jin kanki yanzu fresh ko?" Eh to,lokacin da tayi baccin ta mance
komai,saidai yanzu bayan ta farka komai ya sake dawo mata,saidai baccin da tayi din ya rage
mata bacin rai kadan,amma duka ba wannan ba,sallolin data rasa lokacin da take bacci su
sukafi damunta,saboda haka tace "Banyi sallah uku ba fiddausi,nunan bandaki na daura alwala"ta fada tana jin babu dadi har cikin
ranta,wannan wanne irin bacci ne?,bata taba irinsa ba,hakanan koda bata da lafiya bata taba
hada salloli ba.

Qofa ta nuna mata wadda take cikin dakin gadon nata,nan shahida ta shiga ta daura
alwala,ta fito sannu sannu saboda yadda takejin jikinta sam.babu qwari,gagara yin sallar tayi a
tsaye saboda yadda takejin qafafunta kamar lagwani tilas ta zauna ta yita a zaune.

Tana gamawa ta miqe don hankalinta yayi gida kuma,don bata taba tsayawa a waje har
wannan lokacin ba bata koma gidan ba
"Ki tsaya kici abinci saiki sake samun qarfin jikinki"

"A'ah fiddausi gwara na wuce gidan,ba wanda yasan inda naje"
"Shikenan....bari na baki wannan duk sanda kike cikin bacin rai kina sha zaki baccinki ki manta
da kowa" sam a cikin ranta batajin zata sake sha,saboda bata taba bacci irin haka ba,bugu da
qari ita babu wani raguwar bacin rai data ji,don kada ta gwasaleta kawai ta amsa
"Maganin damuwa ne,zaki samu relief,kin ganni nan,ko bacci ne yaqi daukata saboda wani
bacin rai dana sha zanyi baccina hankali kwance" kai kawa i ta gyada,fiddausi ta rakota har
qofar gida ta wuce ita kuma ta koma cikin saurin don ta labartawa mima komai da yadda
abubuwa suka gudaba,sannan ra fara da turo mata kudin data alqawarta mata,don syrup dinta
dama ya qare tana buqatar siyan wasu ta aje.

Tsakar gidan nasu babu wadatar hasje sosai kasancewar babu wutar nepa,bata nemi kowa
ba don bacin rai ke sake taso mata na yadda tabar gidan nasu dazu,uwa uba kuma wani sabon
baccin take ji,gqba daya jikibta jibsa take kaman an tsoma lagwani a ruwa.

Kan katifarra ta fada rub da ciki tana lumshe idanu tanajin yadda gabobinta sukayi
rauni,idanun nata na arufe taji wayarta na ruri,sam baki daya ta mance da ita,ta miqe cikin
kasala ta daukota daga saman akwatin kayanta,anwar ne yake kira,take ta dannan ta kara a
kunneta "Ina kika shiga haka shahida?,nazo gida ana nemanki sama da qasa ba'a ganki ba?,na kira
wayarki ya kusa sau hamsin ba'a daga ba" sai data lumshe ido sannan tace
"Babu inda naje fa,ina gidansu fiddausi,wayar kuma na manta ta ne cikin akwatin kayana,koka
kira babu lallai aji sautinta" ajiyar zuciya ya sauke yana jin tashun hankalin da yaji dazu na
sauka
"Karki sake irin wannan fitar,hankalin umma ya tashi sosai"
"In sha Allahu" ta fada amma cikin zuciyarta tana fadin koma meye sune suka ja
"Ya naji muryarki haka?,lafiya kike?" Saidata gyara kwanciyarta saboda baccin dake fisgarta
tace
"Lafiya qalau....kawai...bacci ne yakeson saceni"
"Bacci yau kuma?" Ya tambaya cikin mamaki,sabida yasan a qalla suna kaiwa sha daya suna
waya,a hakama shike datsewa yace tayi bacci,sam bata iya baccin wuri ba
"Wallahi" ta fada a gajarce,saiya raya a ransa jiki da jinine kawai don haka yace
"Alright,asuba ta gari to,tunda yau anmin ruwa gani da jin muryarki" murmushi ta saki a
kasalance tace masa na gode ta datse wayar ta cillar gefe tana maida kanta saman filo hadi da
sake lumshe idanunta.

Mubina ce ta dago labulen dakin ta shigo
"Yaya kizo inji umma...ashe kin dawo tun dazu ake nemanki" juyar da kanta tayi daya side din
cikin muryar jin bacci tace
"Saida safe...kice mata nayi bacci" yau ba 'yan maganar bane akan mubinan don haka ta fita ta
shaidawa umman tasu saqon shahida,sai gata ra taso da kanta
"Ke shahida....ina kika je tun dazu?"
"Gidansu fiddausi" ta bata amsa ba tare data juyo fuskarta inda umman tata ke tsaye ba
"Tashi ki dauko abincinki a kitchen kici"

"Ba qoshi" ta sake fada cikin muryar bacci,sam umman tata bata lura da sauyin dake tattare da
ita ba,ga tunaninta fushi tayi kaman yadda ra saba a duk sanda wani abu ya gilma tsakaninta
da mahaifinta,saboda haka ta tabe baki
"Indai ba zaki sawa ranki haquru da kauda da kai ba zakita ganin bacin rai,kije ki hadu da
hawan jini a banza,babanku baida haquri kuma baida adalci,ni kuwa bazan tsaya ya tauyen
haqqina ba atoh" tana gama fada ta juya ta fice,sama sama take jin abinda umman ke cewa,ga
mamakin kanta da kanta,maimakon ta sake jin haushi yadda ta saba sai taji sam maganganun
basu d'a d'ata da qasa ba,baccinta ya fiye mata komai,idanu ta sake rintsewa ba jimawa kuwa
wani nannuyan bacci ya kwasheta.

Kwana biyu tsakani suka ci gaba daga inda suka tsaya,a lokacin tana daki zaune tana
turawa anwar tex,tun tana daure zuciyarta harta kasa,ta toshe kunneta duk a banza,takai ta
kawo cikin dakin ita kadai saita fita,haquri ta soma basu tana kuka kowa idanunshi ya rufe ba
wanda ya saurareta bare yayi shuru ya ragawa dan uwanshi,dare yaui ba damar ta fice daga
gidan ta huta,sai kawai maganin da fiddausi ta bata ya fado mata ta juya da sauri ta koma dakin
ta rufo qofar don sautin tartsatsin fadan ya ragu,ta duba saman madubinta yana aje ta dauka ta
bide ta shanye gaba daya,ta koma gefan gadon ta zauna tana kuja gamida addu'ar Allah yasa
yayi mata aiki,Allah yasa baccin yazo da wuri ya dauketa kota huta dajin meke faruwa cikin
gidan.

Cikin mintina qalilan bacci ya soma zuwa mata,kafin kace ta sheme a wajen,ba ita ta farka
ba sao washegari da safe bayan gari yayi tarwai rana ta take,da hanzari ta miqe tana tariyo
abinda ya farun,sosai taji dadi har ranta da Allah baisa taji qarshen masifar ba,don haka
batasan ya aka qarke ba,ta bude sakatar dakinta ta fita tsakar gidan nasu,a share yaje fes
saidai gidan nasu yayi tsit alamun ba kowa ko duka yaran basa nan,tasan da hakan don lokacin
tafiya makaranta yayi,saita tari ruwa ta shiga bandaki,wanka tayi don tafijin qwarin jikinta
sannan ta hado da alwala ta fito ta shiga dakinta ta sauya kaya ta tada sallar asuba da bata
samu tayi ba,bayan ta kammala ta wuce dakin ummanta,ta sameta a zaune a falonta tana
tsintar shinkafa,ta dago suka hafa idanu,kallo daya zaka mata kasan ranta a masifar bace
yake,wanda tasan hakan bai rasa nasaba da kace nacen da sukayi jiya da babanta,gaidata tayi
ta amsa sama sama
"Wato don wulaqanci da iskanci da asuba kina ji ana bugun qofarki ki tashi kiyi sallar asuba
kikaqi ko?" Ita sam batasan anyi hakan ba,batasanma yaushe aka buga qofar tata ba,amma
kawai sai tace
"Kiyi haquri umma,bacci ne yaci qarfina"
"Oho ke kika sani,naga alama kin fara goyawa mahaifinki baya,to wallahi kikace haka zakiyi
wahala zakisha" ko kadan ranta bai baci ba sai tace
"Kiyi haquri" banza tayi da ita,sai bayan mintina wajen goma sha biyar sannan tace da ita
"Saikije ki dauki abun karyawarki a kitcheni,idan kin gama ki kunnan wuta na dora shinkafar
nan"
"Toh" ta fada tana miqewa zuwa madafa.

Tana cin abincin tana tunanin abinda ya farun jiya,gaskiya baqaramin rage mata radadi

maganin yayi ba,ko banza batasan qarshen abun ba,hakanan bata ji wani bacin rai ba,saita
yanke kawai yau ta sake zuwa gidansu fiddausi ta gaya mata inda ake saida abun ta siya,duk
sanda suka soma balahirarsu tasha ta samu bacci ta qyalesu.

To tun daga lokacin shahida ta shiga ruwa tsundum,batasan illa da giraman abinda takeyi
ba,batasan yadda take rushe rayuwarta ba,kawai ita ta bada amanna ne tana shan maganin
matsalarta,batasan tana sake qarawa rayuwarta matsala bane,tana tunanin maganin bacci
kawai takesha,batasan ta fada shaye shaye bane tsundum,wanda ba wanda ya kula da
sauyawarta banda anwar,lokaci zuwa lokaci idan yazo fira wajenta da zarar sun fara zata soma
gyangyadi,haka zai mata sallama ya tafi,ya nazarceta sosai baiga wani abu daya sauya
dangane da ita dinba bayaga yawan jin baccin,hakan ya sanya yayi tunanin ko shawara ce da
ita?,baiyi qasa a gwiwa ba ya amso mata magungunan gargajiya harda na sanyi,ta amsa dai
kawai ta jibge taci gaba da sha'aninta.

Zuwa sannan sam abinda ke faruwa tsakanin mamanta da bbanta ya daina damunta,wani
lokaci takan iya shigowa gidan ma ta taddasu sunayi tayi wucewarta daki ta kwanta abinta
tahau baccinta,dukkan wadan nan sauye sauyen basu ganshi ba,ga ummanta kawai tayi mata
shaidar ta koyi nunqufurci tana goyon bayan babanta,yayin da abban nata yake ganin hankali
tayi ta daina damuwa da al'amarin dake faruwa.

Ta bangaren fiddausi kuwa da akayi amfani da ita don cusa shahida cikin wannan harkar
nasara ce a wajenta,don duk yadda aka tsara abun ya tafi dai dai,hakan yayi sanadiyyar samun
kudade mai yawa daga wajen nafisa,plan dinsu na gaba shine cusa samari masu kudi 'yan
duniya rayuwar shahidan,saidai duk yadda sukaso ga ganin hakan ya yiwu abun bai kasance
ba,saboda sam shahidan tun asali a jininta yake,bata da kule kule,haka suka qaraci shirya plan
din nasu suka gaji,hakan ya sanya suka sauya dabara,suka sake sabon shiri sabon taku da
sabon tsari,wanda suke fatan shine mataki na qarshe da zai tarwatsa mu'amalar dake tsakanin
anwar da shahida komai qarfinta.

*_SHARRI KAYAN KWALBA_*



Kusan a yanzu babu wata qawa kuma aminiya da shahida ke da ita data wuce
fiddausi,kusan koda wanne lokaci suna tare,hudubar farko data soma yiwa shahida shine anwar
ba son shahidan yake ba,yasha fada cewa mai zaiyi da yarinyar da iyayenta suka kasance
tamkar karnuka saboda fada,sosai xancan ya daki shahida,saidai iya saninta anwar baisan
badaqalar dake faruwa a gidansu ba,don tuni ta yanke yin zance dashi a gidansu bama gidansu
kawai ba unguwar baki d'aya,yanzu kacokam gidan anty amina take tafiya su hadu a can,saidai
kuma akace yau da gobe tafi qarfin wasa,sai maganar ta dinga tsayewa shahidan aranta,duk da
cewa ko daya bata yarda ba bata gasgata ba,hakanan ba abinda ya ragu game da son anwar
daga zuciyarta,duk sanda taso yin wani dogon nazari kan maganar fiddausi na kadar da
hankalinta ta bata wani abun mayen sai zancan yasha ruwa.

Ta gefan anwar gaba daya hankalinsa ya ta'allaqa ne kan nemawa shahida gurbin karatu
cikin daya daga cikin makarantun gaba da secondry dake jahar kano tunda aka yi musu qarin
albashi,bai gaya mata ba saboda yana sonne yayi mata ba zata,yaci wahala ya kashe kudi kafin
komai ya kammala.
Ana ya gobe zai shaida mata yana gurinta,ranar sun jima tare suna hira,sunyi hirar da suka
jima basuyi irinta ba,kowanne yan jaddadawa d'an uwanshi yadda yake jinsa cikin jikinsa da
zuciyarsa,sun tsokani juna sunyi raha wasa da dariya sosai,har anwar ta saka ranakun cikin
daya daga cikin kundin ranakun farincikinsa da bazai taba mantawa dasu ba,ta bashi hotunan
data dauka musamman sabodashi wanda ba qaramin kyau tayi cikin hotunan ba,kyanta ya fita
muraran,ya qurawa hotunan idanu yaga kada kai
"Wannan hotunan bazan iya maidasu enlargment ba" dubansa tayi tana narke ido tana
dubanshi
"Saboda banyi kyau ba ko?" Dariya ya saki yana cewa
"Dama akwai wani lokaci da zaki qiyin kyau a idanuna koda wankan kashi kikayi?" Dariya sosai
ya bata har shima ya tayata darawa
"Dama ana wankan kashi ya anwar?" Girarsa ya dage
"Eh waikoda ace anayi din...kyan da kikayi ne shahida yayi yawa,ina kishin mai aikin
budawarma ya ganki" baki ta bude tana dubanshi
"Ya anwar"
"Shahida....kaman har yau kina kokwanton yadda nake sonki da kishinki ko?" Kai ta girgiza tana
dariya
"Xaki fahimta,sai ranar da aka kawoki dakina a matsayin matata" kunya ta sata sadda kai tana
qiyasta ranar a ranta,gata ita dashi a matsayin miji da mata.

Daya tashi tafiya saita miqo masa dari biyar bayan wata baqar leda,wadda daya bude links
ne da agogo guda biyu masu matuqar kyau irin wanda tasan yana masifar so,kallonta yayi
itama shi take kallo
"Kada kacemin komai,na fuskanci yau miskini kake baka dako sisi(ta furta cikin sigar
zolaya)"murmushi ya saki,gaskiya ta fada,don duka albashinsa ma na wajen wata uku ya qare
ne wajen sama mata admission,dan abinda yaje riqewa bamai yawa bane,kudi ya dinga
badawa don ta samu gurbin karatun,don yasan cikar burinta kenan shida ita,hakan bai dameshi
ba ko kadan,yana jin zaiwa shahidan fiye da hakanma indai ita dince
" har saika fada?"ta katse masa tunaninsa
"Ina iya karantar zuciyarka ba tare daka furta abinda ke cikinta ba" ta fada cikin sanyi da
taushi,sun riga da sun zama daya,sai ya saka hannu ya amsa yana murmushi
"Na gode matata" kalmar data yi mata dadi sosai,cikin farinciki walwala da qaunar juna suka
rabu,yana tafe yana tariyar dukka kalamanta,saiyakejin kyautar data masa tayau din daban
take,hakan ya sanya ya kasa fasa kudin ya hau mota,ya taka har zuwa gida da qafa yana juya
ledar data bashi gift din a ciki,gift din data bashine da sunan tayashi murnar xagayowar ranar
haihuwarsa,wanda sam shi ya mance ma da yaune ranar haihuwarsa.



Qarfe biyar na yammaci da 'yan mintuna ta sauke wayar daga kunneta tana sakin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login