Showing 21001 words to 24000 words out of 126208 words

Chapter 8 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf

har sai data tabbatar ya bace daga layin
gana daya sannan ta sanya hannu ta dauki botikin nata,sai kuma taji haushin kanta ya
kamata,ko banza ya cancanci ta bude baki tayi masa godiya saboda taimakon da yayi mata ba
tare daya santa ko yasan daga ina ta fito ba,yanzun haka babu lallai ta sake ganinsa bare tayi
masa godiya,da wannan tunanin ta qarasa qofar gidansu,sai kuma fargabarta ta dawo sabuwa
sanda ta soma jiyo tashin murya daga cikin gidan nasu,dai dai sanda qanwarta mubina ta fito
hannunta dauke da 'yar tsana da kayan wasa na qasa wanda suka sha fentin pink da green,har
zata wuce abinta da gudu shahida ta cafko rigarta,saita tsaya tana duban shahidan
"Baba ya dawo?" Ta tambayeta tana fatan tace mata a'a,amma saita amsa mata da
"Eh ya dawo,yana qofar dakinsa ma suna fada da umma" ta bata amsa tana zame rigarta ta
sake sheqawa da gudu ta shige cikin yara 'yan uwanta ko a jikinta.

Jingina bayanta tayi a soron gidan nasu tana jin munanan lafuzan dake fitowa daga bakin
mahaifinta da mahaifiyarta suna jifan junansu dashi,wani qataton tashin hankali da take tsintar
kanta a ciki duk sanda ta riskesu a wannan halin ya rufto mata,saita sulale ta duqa a soron
tanajin ruwan bala'in dake tashi cikin gidan,wanda ta tabbatar zuwa yanzu dukka maqota kowa
ya kasa kunne ya diban rahoto,ta rasa wannan wacce irin masifa ce?,ta rasa meke haifar da irin
wannan gagarumin yaqi kulli yaumin tsakamin mahaifanta,basa kwana uku cur cikin jituwa da
juna,basa sati cikin salama da walwala,tunda ta taso tayi hankali haka ta rsiki rayuwarsu,babu
ragayya ko kad'an ga junansu,ba wanda ke ganin wani da gashi a tsakaninsu.

A qalla sun kusa awa guda suna wannan dauki ba dadin a tsakaninsu,wanda har zuwa
sannan hawaye baibar zuba a idanun shahida ba,tilas ta miqe da niyyar shiga ciki ko Allah

zaisa tayi nasarar dakatar dasu,duk da tasan cewa da wuya wai gurguwa da auren nesa,don
idan irin hakan ta faru dukkansu idanunsu rufewa yake basa ji basa gani.

Ilai kuwa yana zaune bakin rijiya yayin da da umman tata ke cikin kitchen,har ta qaraci
sallamarta babu wanda ya jita a cikinsu,hakan ya sanya ta dirr botikin ta durfafi dakinta ta bude
ta shige sannannta rufe qofar ruf waiko zata daina jin tashin munanan furucinsu,saidai bata
sauya zani ba,haka tq zame ta zquna gefan katifarta ta hade gwiwarta ta qanqame tana ci gaba
da kukanta.

Basu saurara ba har sai da khadija qanwar shahida ta biyu ta dawo daga gidan kitson da
umman ta turata da yunwa,tace umma yunwa amma bata bi ta kanta ba,hakam yasa ta watsar
da takalmanta ta zube dirshan wajen tahau ihun kuka,katsam sai farouq mai binta ya farka daga
baccin da yake shima ya hau tsala nashi kukan jin ba'a daukeshi ba akan kari,tilas baban nasu
ya suri takalminsa ya fice fuu badon sun gama ba,ita kuma tahau hidimar yaran tana yi tana
mita da alamun itama bata huce ba.

"Au,ita kuma wannan yaushe ta shigo tazo ta yasarwa da mutane botiki kan hanya salon
wani yaci karo dashi ya fadi,inama sauran botikan?" Jin hakan ya sanya shahida komawa
saman katifa ta kwanta luf tamkar mai bacci tana sauke ajiyar zuciya,hakan ya sanya koda
khadija da umman ta aikota tazo ta dubo shahidan tazo saita koma tace mata umma bacci take "Bacci?,bacci kuma da wannan yammacin?,k'nnnnn,to Allah yasa ba zazzabinne kuma ya dawo
ba" ta fada tana ci gaba da baiwa faruqu nono.

Takunta ne kawai ke kai kawo a idanunsa sanda yake komawa daga inda ya
rakota,idanunsa ya dinga lumshewa hakanan yanayinta da yanayin tafiyarta yaji ya
burgeshi,sanyinta,yanayin maganarta,da haka har ya qarasa wajen da suka baro dazun,yanzun
babu kowa,har malam isuhu ma ya wuce,kai tsaye ya wuce shagon balarabe mai saida kayan
provision,wanda dama tun asali wajensa yazo.

Hannu ya bawa bala sukayi musabaha,sannan ya zauna kan bencin dake aje daga cikin
shagon saboda custumers daya tarar yana sallama
"Ai na hangoka kaida wadan can yaran marasa kunya,yarinyar da babu sawa ba fitarwa,ina
Allah Allah naje na musu magana naga kaje,ai yarinyar kirkir ce,ba qaramin taimakon masu
sana'a a nan wajen take ba,kowa na yabonta"balarabe mai kanti yaci gaba da baiwa anwar
labarin zamanta a wajen duk da ba tambayarsa yayi ba,hakanan shima ya samu kansa da
saurarensa,duk da cewa bai tofa komai ba cikin zancan,har sai da balarabe ya gama
b'ab'atunsa yayi shuru
"Kana nufin kullum sai tazo nan kenan?" Anwar ya tambaya yana miqawa balarabe naira dari
biyu,yasa hannu yana amsa
"Qwarai kuwa,kullum tana zuwa daga qarfe uku na rana zuwa hudu,hudu tanayi ta gana
rabarwa ta hada kayanta sai tayi gida" baice uffan ba saiya maida akalar tunaninsa kan me xai
saya da d'ari biyun wanda zai riqeshi zuwa sanda zai sake samun wani kudin
"Me dame za'a baka malam anwaru" d'an tsaki yaja kad'an na alamun dawowa daga tunani

yana murza goshinsa
"Bani kwaki da suger"
"Kuma dai?" Kafadarsa ya dage yadan mari cinyarsa da tafin hannunsa
"To yq za'ayi,rayuwar kenan ai,wataran sai labari in sha Allah"
"Baka yarda ne anwaru....ni na yarda da amincinka,na yarda ka zabi abinda kakeso cikin
shagon na baka bashi kaje idan ka samu ka kawomin amma ka qiya" balarabe ya fada sanda
yake auna masa kwakin a baqar leda,dan miskilin murmushi anwar ya saki
"Idan ka bani naje na samo na kawo maka naji dadi gobe sake karba zanyi,idan kuma yauna
samu abun biyanka gobe fa ina dashi?"
"Ni a wajena ba wata matsala" kai ya kad'a
"A'ah,Allah ne kad'ai baya gajiyawa,amma yau da gobe dole dan adam ya gajiya" kai malam
balarabe yake kadawa,ya jima rabon da yaga matashi mai kishin kai kamar anwar din,matashin
daya dogara da kanshi bai rabu da kowa ba,ya yarda shi din ba kowa bane,ya kuma yarda da
talaucinsa ya kame kansa,yana gama auna masan ya miqa masa ya karba yayi masa sallama
ya wuce.

Muqulli ya ciro cikin aljihunsa ya saka ya bude qofar gidan,ya tura ya shiga,babu kowa cikin
gidan dama bai tsammaci ganin kowa din ba tunda yasan shi d'aya yake rayuwa a cikin
gidan,saidai ga mamakinsa gaba daya dakinsa daya fita ya barshi a akillace an bibbincike
masa,ya saba ganin hakan,yasan kuma bazai wuce samarin unguwa bane da suka kafa masa
qahon zuqa haka kawai ba,yasan baibar wani abu mai amfani da za'a dauka ba cikin
kayan,bama cikin kayan ba cikin gidanma gaba daya,aje ledar garinsa yayi ya duba agogon
dake maqale a bango,saura minti ashirin asha ruwa,yasan zai isheshi ya gyara wajen,mutum ne
da bayason qazanta ko kadan,a nutse ya gyara komai ya maida muhallinsa,sannan ya wuce
kitchen ya bude robar da yake aje plate da kofi ya dauko ya jiqa garin sannan ya sake fita ya
siyo pure water guda d'aya da naira goman data rage masa,yana shigowa soro aka sha ruwa,a
nan ya balle ya shanye,ya qarasa bakin fanfo ya daura alwala ya wuce masallaci.



*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI
SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*KO KUMA*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da
sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*


https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos
*AA*
0️⃣6️⃣





Saida gari ya danyi duhu kadan sannan ya dawo cikin gidan,ya duba garinsa yayi laushi,ya
zuba suger dai dai gwargwado ya zauna gefan 'yar katifarsa ya soma sha,inda ya kunna redio
da wayarsa qarama keypad samfutin tecno yana sauraren labarai.

Kafin ya kammala an kirayi isha'i,sake miqewa yayi ya fice zuwa masallaci,don sam baya
wasa da sallar cikin jam'i,koda aka idar nan majalisar dake kusa da gidanshi yadan xauna aka
taba hira,bai jima can da yawa yayi sallama dasu,kasancewar yana da masaniyar gobe yana da
lacture ta qarfe tara,kuma dama bai fiya zama cikinsu ba ba dabi'arsa bace wannan,hakan
yasanya wasu kejin haushinsa tare da yi masa kallon mai girman kai,yakan zauna lokaci zuwa
lokaci saboda kauda wannan zargin daga ransu,bugu da qari ya sani dole kuwa ya fita tun
bakwai,don kuwa da qafarshi yake takawa har zuwa makarantar,zuwanshi mota a abun hawa
abune mai matuqar sa'a,imma wani aikin qarfin ya samu yayi ya samu kudi,ko idan anty usaina
ta d'anyi samuwa ta kirashi ta bashi wani abun,ko Allah ya hadashi da d'aya daga cikin 'yan
makarantarsu ya rage masa hanya.

Allah ya taimakeshi yau cikinsu ba wanda ya shigo masa gida,saboda haka ya kulle ko ina
yayi nafilfilunsa kamar yadda ya saba,ya roqawa iyayensa da 'yan uwanshi gafara sannan ya
kwanta bayan ya sake kunna rediyon yana sauraren shirye shiryen da sukeyi.

Sannu a hankali tunaninta ya kutso cikin kaiwa da kawowar da qwaqwalwarsa keyi tun
dazu,ya dan saki murmushi yana wassafo kamanninta,yanayinta tsarinta da tafiyarta,da ganinta
zatayi hankali,da ganinta akwai nutsuwa tattare da ita,da ganinta ba maison hayaniya bace
"Duk taya akayi kasan hakan?" Ya tambayi kansa da kansa,saiya sakarwa kansa murmushi
yana girgixa kai gami da runtse idanunsa,shima baisan ya akayi ya tsinci kansa da fadawa
wannan bigiren ba,saiya juya zuwa daya barin yana son maoda hankalinsa kan programe din
da ake gudanarwa a gidan redio a sannan.
Tun bayan sallar magariba ummantata keta sintirin aiken qannen nata kan ta fito taci
abinci,saidai sam ta qiya,tayi kwanciyarta abinta,ranta ne kawai ke mata suya,a duk sanda irin
wannan balahirar ta faru a gidansu idan da safe ne wuni take cikin qunci da damuwa,hakanan
idan da yammaci ne koda dare kwana take cikin qunci shima da damuwa,wani lokacin takance
inama kurma Allah ya halicceta?,inama makauniya ce ita ta huta da ganin wannan baqon
lamari,wanda ya zama tambarin gidansu,ya kuma zama abinda jama'ar unguwa ke goranta
musu dashi,don babu wanda baisan irin rayuwar da ake tsakanin uammansu da babansu
ba,tayi kuka har sau babu adadi,tabi hanyoyin gyara bila adadin amma babu alamun ma sauyi

bare akai ga gyaran gaba daya,tayi tunani iri daban daban masu kyau da marasa kyau amma
bata samu hanya mai bullewa ba,tayi yaji tabar gidan batasan adadin sau nawa ba amma sun
bita sun dawo da ita kan alqawarin komai ya wuce zasu gyara amma babu alamun sauyawar
lamuran,ta tambayesu me yasa suke hakan amma su kansu basu san amsa ba,abu d'aya ta
sani shine,dukkaninsu tsakanin ummanta da babanta babu wani mai haquri acikinsu,ummanta
bata da haquri ko kad'an kamar yadda mahaifinta yake,bata raga masa ko daya,idan ya mata
taga bai mata dai dai ba take zata rama,shi kuma yaga ta rainashi kenan haka zai biye mata
suyita yi.

Basu san ciwon da hakan ke mata a qirjinta ba,basu san illar dahakan ke haifarwa ga
tarbiyya yara da tunaninsu da ginuwar hankalinsu,iyayenka a wannan bigiren na fada da juna
kulli yaumin har sauran jama'a su shaida hakan kai me yayi saura a rayuwarka?.

Saida umman taga da gaske take bazataci abincin ba kamar yadda ta saba a duk sanda ta
samesu suna cecekuceb da suka saba,saita dire faruqu ta nufi dakin nata,ta yaye labulen tana
tsaye daga dokin qofa tace
"Tunda sai abinda kikaga dama zakiyi bismillah,dadin abun cikinki ne ba nawa ba,yunwa kuwa
dai dai take dake matsalarki ce wannan,ki tashi ki gayamin ya akayi sauran botikaina sabbi
suka fashe haka?" Da qyar ta juya daga kwancen da take ta d'aga kai ta dubeta
"Wasune garin wawaso suka fasa su"
"Botikan duka?" Kai ta gyada mata
"K'nnnn,ai shikenan,Allah ya kyauta" ta fada tana sakin labulen,maida kanta tayi ta
kwantar,inama ace haka takewa mahaifinsu a duk sanda wani abu ya hadosu?,ta tabbatar da
shine tsautsayi irin haka ya faru da yau Allah ne kadai yasan qarshen fadansu.

Mubina ce ta shigo da kwananon abincin ta dire mata ta juya ta fice,bata dai kallesu ba tana
ci gaba da kwanciyar
"Idan baki tashi kin kama abinci kinci ba na shigo sai nayi mugun saba miki" ta jiyo muryar
umman daga tsakar gida tana gaya mata,hakanan badon son ranta ba ta sauko ta tanqwashe
qafa ta dinga cusa abincin har sai dataji kaman zatayi amai sannan ta maida murfin ta rufe ta
sake kwanciya.
Runtse idanunta tayi tana fatar bacci ya dauketa,sai taga wata fuska data sanyata saurin
sake bude idanunta,dawo mata yayi tar a kwanyarta,bacin ran da take ciki yasa bata sake
tunowa dashi ba sai yanzu,saita gyara kwanciyarta tana kallon bango,ta dinga tuno fuskarsa da
yadda tafiyarsu ta kasance daga bakin masallaci har zuwa gida,hakanan taji nauyi da bacin ran
zuciyarta ya ragu sosai,ta shagala da tunanin daya d'auketa zuwa bacci mai nauyi.

Qarfe biyu na rana gaba ya tsinci kansa hankalinsa ya tafi bakin masallaci gurin da ba wajen
zuwansa bane idan ba shagin balarabe zashi ba ko wani babban uzurin ya kamashi na zuwa
wajen,sai ya sake tsintar kansa da sake yin wanka bayan ya gama hutawa duk da kusan
dabi'arsa ce a duk sanda ya dawo daga makaranta,amma wannan karon saiya laluba kayanshi
har ya zaro zai saka ya maida ya sauya wasu,abinda bai taba yi ba,bai taba damuwa da suturar

da zai saka,kawai dai yasan dukka kayan sawarshi a tsaftace suke kullum,hakanan basa rabo
da guga,duk da cewa ba wasu masu shegen kyau da tsada bane,Allah dai yayi masa wata
baiwa ta duk kayan daya saka jikinsa na dauka,hakan yasa matasan anguwar da dama ya
tsone musu ido,wanda yawancinsu dukka sunfishi gata rufin asiri da komai da komai,tsaftarsa
tasa baka gane kaashinsa.

"Ki kulamin da botikai na,karki sake bari su fasamim botiki,kai jamilu idan ka aje mata ka
dawo ka kaimin shara" cewar ummanta wadda take rufe botikin abincin data gama zubawa
almajirin ya qaraso wajen ya dora a kanshi suka fice tanawa umman sallama.

Har sunje soron gidan hakanan taja ta tsaya,saita juya da hanzari ta koma ciki
"A'ah,lafiyarki kuwa?" Umman tata da taga wucewarta ciki ta fada
"Lafiya umma ina zuwa" kai tsaye ta dauko dan kwandon kayan kwalliyarta dake saman akwatin
kayanta,ta ciro ruwan madubi mai fadi dake soke a ciki ta kalli fuskarta
"Hoda na miki kyau wallahi shahida,don Allah ki dinga d'an shafawa mana" ta tuna maganar da
qawarta ta gaya mata daxu a makarantar boko,saita samu kanta da ciro hodar ta bude ta
shafa,data sake kallon fuskarta sai taga ta canza din kuwa,sosai hodar tayi mata kyau ta sake
fidda kyau da qyallin fuskarta,murmushi ta saki ta aje mudubin ta juya ta fice da sauri.
Yana zaune daga shagon balarabe yana kallon duk wani motsinta dake bayyanar da
hankali da nutsuwarta da kuma ainihin ita wace,duk surutu da hirar da balaraben yake masa
baya gane abinda yake fada sam,shi kuma bai fahimta ba bare yaja bakinsa yayi shuru ya
barshi.
Haka ta dinga raba abincin kamar yadda ta saba,saidai tanata dube duben kadan kadan da
batasan meye dalili ba,harta kammala tsaf ta hada kwanukanta waje daya,haka kawai saitaji
ranta ya baci lokacin data gama shirin komawa gida,duqawa tayi don daukar botikan taga an
sako hannu an dauka,da hanzari ta dago don ganin waye?,ta tsammaci ma su ahmadi ne ma
basu gargadin da aka musu jiya ba yau suka dawo,saidai ga mamakinta saurayin jiya ne,gaba
yayi abinsa sai tabi bayansa sukaci gaba da tafiya ba tare da kowa yace da d'an uwansa wani
sbu ba.

Basuyi wani nisa ba ya janye ta koma ita ce a gaba shi yana baya,bata kawo komai a ranta
ba ta tsammaci bazai gane gidan nasu ba shi yasa yayi hakan,kamar tafiyar jiya har suka je
inda ya dakata a jiya ya aje mata botikin,saidai yau din ta daga ido ta kalleshi,akaci sa'a shima
ya kalleta a sannan,wani irin zallar kyau da kwarjini idanunta suka gani,sai taji wani abu tun
daga qwaqwalwarta har tafin qafarta,mazewa tayi gami da d'auke kai tana jin izzarta ta diya
mace na motsawa,a nashi bangaren ma wani abu mai qarfi yaji yana janshi game da ita tamkar
maganadisu da mayen qarfe,sai bakinsa yayi nauyi,bai furta mata komai ba ya juya ya soma
takawa don barin wajen,daga manyan idanunta tayi tana bin bayanshi da kallo har sai daya
bacewa ganinta,batasan me yasa ba bakuma tasan sanda ta saki murmushi ba ta daukin
botikin nata ta fada gida.

Tsahon kwana uku irin hakan na faruwa tsakaninsu,ba wata magana data taba shiga
tsakaninsu,duk sanda tayi yunqurin yin wata magana saita kasa sabida kwarjinin da yake
mata,tana son tace ya daina rakota saboda ganin yadda idon sa'idinawan unguwa ya soma
dawowa kansu saidai ta kasa furta masa hakan,cikin ranta takejin nishadi a duk sanda suke
wannan tafiyar ta kurame tun daga masallaci zuwa qofar gidansu,ko sunanshi bata sani ba,sai
taga meye nata na tambayar sunansa ma,aishi ya kamata ya soma tambayarta sunanta,wani
sashe na zuciyarta ya qalubalanceta da a'ah ba haka ake ba,ke yakewa alkhairi,ko godiya baki
taba yi masa ba kan rakokin da yake,ta jinjina kai tana tabbatarwa da kanta rashin
kyautawarta,ta kuma quduri aniyar a gobe zata masa godiya ta kuma tambayi sunanshi,kai ta
girgiza kuma tana sake sakin murmushi,batasan dalilin daya sanya take yawan tunashi
ba,batasan me yasa takejin wani baqon yanayi game dashi ba tun ranar data soma dora
idanunta a kanshi,bata da amsa,tilas ta aje tunaninta a gefe sanda ta jiyo muryar babanta sun
soma rabon halin nasu shi da ummanta,saita miqe a hankali ta isa bakin windon dakinta,ta yaye
dan labulen net din dake maqale jikin window din tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login