Showing 102001 words to 105000 words out of 126208 words
Chapter 35 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf
burgeta,murmushi shahidan ta kuma
saki
"Ko?" Tace cikin sigar tambaya,kaita kada
"Qwarai kuwa,amma anty,don Allah ki kularmin da uncle dina,wallahi inason uncle anwar,yana
da kirki sosai,yana sonmu shima,yana kula damu sosai da sosai,don Allah anty" saita tsaya
tana sake dubanta kafin ta kuma sakin murmushi,ta dora hannunta saman hannun sa'ida
"Uncle din naki nima zai iya kula dani ne sa'ida?" Dariya ta saki
"Tabdi,sosai kuwa anty,kinsan uncle anwar kuwa?,ai matarshi ta caba" saitayi qasa da murya
"Na zaci fa zai iya aurena harna cewa ummi ina sonshi,ranar saida na daku sosai,ashe babana
ne" dariya ta kubcewa shahida da sa'idan duka,da sauran dariya a fuskar shahidan tace
"Babanki ne sa'ida,amma kita addu'a Allah ya baki wanda ya fishi nagartar halaye"
"Akwai wanda yafi uncle dina kuwa?" Ta fada cikin tantama da tunani,kaita jinjina
"Qwarai kuwa,duk wanda kika gani kome kika gani a duniya akwai wanda ya fishi akwai wanda
baikaishi ba akwai dai dai dashi"
"Tohm shikenan......" Bata qarasa maganar ba suka jiyo taku ana nufowa wajen,saita fiddo
idanu
"Na shiga uku anty,Allah yasa ba ummi bace" riqe hannunta tayi
"Karki damu,zance nina kiraki ki tayani hira" shuru sukayi suna jiran ganin wanda zai shigo din.
Sallamar mutum biyu ce,ummin sai muryar anwar daga bayanta,mummunar faduwar
gaban data sanya shahida maida kanta cikin mayafi ta saukar mata,ummi anty usaina ce a
gaba sai anwar din daga bayanta,idanunta akan sa'ida nashi idanun nakan shahida da kanta ke
sunkuye lullube da mayafi,kama baki tayi "Na shigesu ni usaina,sa'ida...sa'ida ki shiga hankalinki da wannan rawar qafar taki,dama da
akacemin ba'a ganki ba nan kikayo?,to tashi ki wuce ki bama mutane guri" da sauri ta zame
hannunta cikin na shahidan sannan ta miqe,duk da haka da zata gifta anwar din saida tace
"Uncle,kayi kyau sosai yau,amma wallahi in gaya maka gaskiya?,anty shahida ta fika kyau
ashe" anty usaina batasan sanda dariya kubce mata ba,yayin da murmushi ya subuce masa
shima ya bita da kallo harta fice daga dakin,ba ruwanta hakanan take,idan taga gaskiya saita
fada,kusan halayenta suna kamanceceniya dana mahaifiyarsu,duk cikin yaran anty usaina tasu
tafi zuwa daya,kusan sanda aka haifi sa'ida tare sukayi rainonta shida anty usainan tun lokacin
mahaifansu suna raye,idanunsa ya sake saukewa akan shahidan a hankali duk da bai ganin
fuskarta,yana tsaye a wajen har anty usaina ta zauna
"Zauna daga can" ta fada tana masa nuni da inda takeso ya zauna din,kujerar da shahida ke
kaine,duk da cewa mai yalwa ce amma saiya zauna a hannun kujera,cikin hikima da nutsuwa ta
soma magana dasu
"Alhamdulillahi rabbil Aalim,komai na rayuwa a tsare yake zuwa daga wajen ubangiji mai kowa
da komai,basai na tsaya wani tambaye tambaye ba don nasan ba amsa zan samu daga gareku
ba,abunda nakeson na fada shine,wannan auren naku ya isheku dama sauran mutane
ishara,kun rabu da juna kun guji juna ba tare da dayanku ya sake tunani Allah zaiyi ikonsa ku
sake haduwa a wannan bigire ba na aure,wannan kadai ya isa ya nunawa bawa yana tashi ne
Allah yana tasa,ta Allah kuma itace dai dai,saboda haka ku sanyawa zukatanku salama,ku
zauna da juna cikin aminci da bin umarnin mahalicci,kada ku yiwa Allah butulci wanda ya baku
aron rai da lafiya ya kawoku wannan lokacin koda cikin zukatanku bason hakan kuke
ba,dubunku na nan na fatan samun kamar takun,ya sake hadaku a sanda kowannenku
rayuwarsa ta sauya ta samu ci gaba,ta yuwu hikimar rabuwar daku dama don kowanne ya
cimma gacinsa ne,wanda wala'alla idan kuna tare da zaku cimma wannan abun ba,ku kauda
hayaniya da tashin hankali ku ajeshi idanma kun daura azamar hakan,kuyita addu'ar Allah ya
baku mafita ya sanyaya zukatanku" saita waiwaya ta dubi anwar
"Kai kaine babba sannan kaine shugaba,kai keda hankali fiye da mace,sabida haka fiye da
rabin nauyi da yanayin yadda zamanku zai kasance ya ta'allaqa a wuyanka ne,kasan komai
basak na fada maka ba,iyayenmu kafin su rasu makarantace a gareka,ka dauki matarka ku tafi
daga kai sai ita,ina muku fatan alkhairi,shahida...Allah ya bamu alkhairinsa kinji" kasa magana
tayi kunya na kamata,ta fuskanci hakan sabida haka tayi murmushi taga bari kawai ta murje
mata kunyar a wuce wajen
"Ki daina kunyata,don kincemin bakison anwar wallahi banga laifinki ko daya ba,hasalima
burgeni kikayi,donko nice kw abinda zanyi kenan,kawai saika rabu dani tsahon wasu shekaru
ka zagaya ta bayan fage ka aureni haka akeyi?" Ta qarashe maganar tana duban anwar gamida
harararsa "Kuma ka nemi yafiyarta kukan daka sa ta dinga yi da aurenka data yi bayan bata shirya ba
bata amince ba" murmushi ya qwace masa mai dan sauti,itama antyn tana murmushin ta fice ta
barsu.
Shuru ya ratsa dakin na wasu mintina masu dan dama,idonsa akanta da yake
lullube,zuciyarsa na masa bitar wasu shekaru can baya,yasha kwana idanunsa biyu yana
wassafa yaya zai kasance duk randa shahida ta zama mallakinsa,yasha raba dare yana tsara
ranar da irin abubuwan da zasu faru a lokacin,ga komai yazo ga lokacin yazo saidai cikin
bahagon yanayi da dabaibayi,ajiyar zuciya ya saki a bayyane sannan ya furta cikin sanyin
murya
"Tashi mu tafi" yi tayi kaman batajishi ba,yayi tsai yana dubanta,ya tabbatar taji,har tsahon minti
guda sannan yace
"Kin sani sarai tun da can banason musu da taurin kai ko?,indai zaki dauki wannan dabi'ar
zakisha wuya a wajena" daga haka ya miqe yayi gaba,tasan idan ta bari yafice batasan hanya
ba,dole ta miqe itama ta bishi".
Bangaren ajiye motocin gidan suka isa,yasa muqulli ya bude motar ya shiga,saita soma
qoqarin bude gidan baya da zummar zata shiga,lock ya sakawa qofar ba tare daya waiwayo ya
dubeta ba,hakanan ta gaji da tsaiwa ya yunqurin budewar ta matso gidan gaba ta bude,a
hankali ta shiga ta zauna sosai sannan ta kame jikinta waje daya bayan ta sake jan mayafinta ta
rufe fuskarta,karon farko bayan wasu shekaru masu tsayi ta sake hada mazauni dashi cikin
mota,gaba dayansu jinsu suke banbarakwai,kowa yanaji kamar yana tare da baqonsa ne,ya
dage dukka gilasan ya kunna ac dukda sanyin dake dan kadawa a garin,ya tashi motar suka
fice daga gidan.
Wani tuqi yake kaman bazasu gida ba ko kuma yana lallaba kwalta,duk da titin da sukabin
fetal yake babu yawaitar jama'a sai haske fitilun titi tako ina,shuru ya ratsa motar babu me cewa
komai har suka isa wani waje da sukeda saida kayan ciye ciye,kama daga ice cream,burger
shawarma kaza da tsire da sauransu,saida yadanyi gaba kadan inda babu mutane sannan yayi
parking,ya kashe motar ya fita.
Bai jima ba ya dawo hannunsa dauke da leda ya sakata a sit din baya,sannan ya tashi
motar sukayi gaba,hannunsa ya saka ya kunna rediyo freedom wanda minti biyar ya rage su
fara shirin siyasa na kowanne gauta,waqar jarumar matace ta soma plying,waqar tana taba
zuciyarsa sosai,yana son ya kashe amma saiya samu kanshi da barinta tana ci gaba da
tashi,sautin na karade motar yana shiga kunnuwansu cikin sauti madaidaici gami da haifarwa
da kowa yanayi na daban.
Ta gefan ido ya saci kallonta,tayi laqwas cikin sit din motar,idanunta a lumshe,zara zaran
gashin idanunta sun fito sosai,juyawa yayi duka yana kallonta sosai,daidai sanda ta bude nata
idanun,saiyayi hanzarin dauke kanshin ya maida ga titi yaci gaba da tuqa motar cikin nutsuwa
da qwarewa.
_zaku iya jina shuru gobe saboda wani uzuri daya tasomin,amma idan na samu dama zaku jini
in sha Allah_
_kuci gaba dai dayi mana uzuri,kana taka ne Allah na tashi,ta Allah itace dai dai,har kullum
burinmu mu sauke nauyinku dake kanmu,muna godiya_ ?*Alqawarin Allah*
3️⃣8️⃣
Kafin ta sauka qasa ta dan jima a tsaye saman step na kusa da qarshe tana dai daita yanayinta
sannan ta sauka a hankali.
Ana qwala kiran sallahn ya sauko cikin jallabiya mai gajeran hannu fara sol da ita,bisa
dukkan alamu sabuwa ce,jikinsa na tashin qamshin turare mai sanyi kaman wanda yayi wanka
dashi,zuciyarta taso yadan fisgeta ta kalleshi amma tayi ta maza ta dake kaman bata ganshi ba
har ya fice masallacin.
Ba'a jima can da idarwa ba ya dawo,ya zauna saman kujerar falon suna dan taba hira da
anty amina kafin su kammala kintsawa,da suka tashi tafiya saita rasa me zata basu,qarshe data
shiga dakinta wajen akwatunan lefanta ta isa ,karo na farko data budesu ta kuma kalla abinda
ke ciki,guda biyu ne masu dauke kayan sawa taf daqyar aka rufesu don ba abinda aka taba a
ciki,ta dinga daga kayan daya bayan daya tana kalla,kan wata shadda lace ta tsaya,ta kalleta
sosai,tun daga colour har design din choice dinta ne,tasan duk duniya kuma babu wanda yasan
hakan sai anwar,hakan ya saka ta sanya hannu ta cirota,ta kalleta sosai,iya kyau ta mata kyau
qwarai,kuma kana ganinta kasan babbar ce,saidai ba zata iya sanyata a jikinta ba,tasan anwar
ne ya zabeta,ta yanke ta baiwa anty amina ita,sauran manyan su uku ta zaba musu
atamfofi,yan yaran da yan matasan kuma ta diba musu kayan kwalliya,ta zaba kayan gararta da
yawa ta hada musu.
Anwar yana tsaye ta miqawa kowa,ta miqo ledar anty amina yafi kusa da inda take
tsaye,saboda haka ya zira hannu ya karba ya buda yana gani sannan ya rufe,daga kai yayi
tasan ita zai kalla saboda haka ta dauke kai,ilai kuwa itadin ya kalla,haka kawai yaji kyautar ta
masa ciwo,bawai saboda kudin abarba,a'ah,yafi qarfin kudinta hakanan anty amina a wajenta
tafi qarfi wannan,yasan cewa da biyu tayi kyautar itama ta san da hakan,abinda ya bata ranshi
kenan.
Har bakin mota tayi musu rakiya,anwar yace a matse sukazo hala,su ragu wasu su shiga
motarsa ya kaisu,ta musu sallama ta koma cikin gida,harsun gama shiga yace yana zuwa,ya
buda murfin motar ya koma cikin gidan.
Tana tsaka da tattare wajen taji shigowarsa,ta daga kai ta dubeshi saita basar taci gaba da
abinda take kaman bataga shigowarsa ba,bayanta kadan ya tsaya,kaman bazaiyi magana ba
sannan daga bisani yace
"Duk yadda kikeji a zuciyarki game dani kusan nima haka yake koma fiye,amma,karki sake
gangancin da kikayi yau,duk kayan dana siya nasan wa na siyawa shi,idan da buqatar bada
kyautar irinsu a siyo daga waje ba daga cikin akwati ba" idanunta ta watsa masa sannan tace
"Ina ruwan wani?,ina cewa kayana ne ko?"
"Alright,hakane fa,amma keda kayan qasan wa kuke?"
"Oho" tace tana ci gaba da aikinta,shuru yayi yana kallonta,saiya jinjina kai sannan yace
"Zaki gane kurenki" ya juya ya fice saboda tunawa da yayi yabar mutane a mota,tsaki taja taci
gaba da aikinta tana cewa
"Na dade ban gane kuren nawa ba"
A gurguje ta gama duk abinda zatayi ta dauki duk abinda take buqata ta shige
dakinta,wanka ta soma yi sannan taci abinci,ta jawo wayarta ta fara amfani da ita,kama daga
kiran waya,da duba saqonnin wayarta ta watsapp,bataji shigowarsa ba sai wajen qarfe goma na
dare,dai dai sannan ta miqe ta kashe qwanta ta koma gado tayi addu'ar bacci tayi kwanciyarta.
Shika koda ya shigo dakinsa ya wuce abinsa,baibi kota kan abincin dake kan tebur ba.
Washegari ma ta samu baqi ba laifi duk da basu kai na jiya ba,abinda ya debe mata kewa
kenan har wata washegarin,saidai randa ta cika kwana na hudu dif kakeji,duk sai taji gidan
babu dadi,haka ta wuni ita kadai,daga kwanciya sai kallo sai latse latsen waya,har zuwa dare
data kammala abinda take tayi shigewarta daki.
Tunda ta gama yin baqi bai kuma sakata a idanunsa ba,kafin magariba ta gama komai tayi
shigewarta daki,bata fitowa sai washegari shima idan ya fita a gidan,zatayi abincin safe haka na
dare ta aje masa,saidai shima bai bata taba abincin ba,yadda ta jera haka zata kwashe
abinta,kusan hakan na faruwa ne saboda ya koma aikinsa gadan gadan,bai samun damar
dawowa gidan dawuri,hakanan da wuri yake fita.
Sati biyu cur aka suka kwashe a haka,idan ya dawo bai ganinta,hakanan idan zai fita ma
haka.
Zaman taji ya isheta,kadaicin ya mata yawa,tayi kallo har ta gaji,tayi chart ya isheta,saita
yanke shawarar ta sameshi tayi masa magana kan komawarta office don tana da buqatar
hakan.
Sai data idar da sallar magariba yau sannan ta shiga tayi wanka,ta shirya cikin wani cotton
material baqi da aka yiwa adon purple wanda yadan ciza,ta gyara gyara gashinta sannan ta
feshe jikinta da turaruka yadda ta saba,duk da ko batasaka turaren ba qamshi kayan suke
bayarwa na turaren wutar da take turare kayan nata dashi,nan bakin window din dakinta dake
fuskantar harabar gidan ta tsaya,ta yaye labulen tana kallon harabar gidan kawai,duk da babu
kowa sai mai gadi dake zaune can bakin qofar gidan,amma ko ina gauraye yake da haske
tarwai kaman rana,haka gidan yake da wuta 24hrs.
Ta jima tsaye tana saqo tana warwara,har ta soma gajiya da tsaiwar ta saki labulen da niyyar
komawa ta zauna taji horn,saita tsaya tana ci gaba da kallon qofa sanda baaba ya tura gate din
anwar ya sako motarsa cikin gidan,tabi motar da kallo har zuwa harabar da yake ajesu,tana
kallo baban ya qarasa bakin motar bayan ya maida qofar ya rufe,ya tsaya daga bakin window
din da alama magana suke sannan ya juya ya tafi.
Tayi zaton bazai fito daga motar ba jin shuru na wasu mintuna,kana daga bisani taga ya
bude murfin motar ya fito,sanye da mens blazzer ruwan blueblack da baqin takalmi sau
ciki,yanayin takunsa kawai zai gaya maka a gajiye yake,idanunta akanshi har ya bacewa
ganinta sannan ta saki labulen tana sauke ajiyar zuciya,hannunta saman kanta tana son tuna
wani abu tana tursasa zuciyarta kan kada ta tuna mata.
A qalla sai data bada minti talatin kyawawa sannan ta yafa mayafinta ta fito,sam bata ko
sha'awar hawa samansa amma dole ce xata kaita,taso ace yana zama a falo ta cimmasa a can.
Yauma da zata gota table din sai data kalla,komai yana nan akai kamar yadda ta dora,saita
tabe baki tayi gaba cikin zuciyarta tana cewa
"Kai ka jiyo,nidai na sauke haqqina ko".
Yana zaune saman kujera one sitter,sanye da boxer da short sleeve shirt farare
qal,fitowarsa kenan daga wanka,yayi relaxing bayansa a makarin kujerar,idanunsa na lumshe
ya hada yatsun hannanunshi cikin na juna,haka kawai yakejin gidan ya masa shuru tamkar shi
kadaine a cikin gidan,yunwa da gajiya suna damunsa,yana buqatar abubuwa da yawa amma ya
rasa wanne zai fara tunawa cikin zuciyarsa,cikin haka yaji kaman an buda qofar falonsa,da
mamaki ya ware idanunshi da suka dan kada saboda yadda ya jima da rufesu yana kallon
qofar,qwarai yayi mamakin ganinta,amma ya shanye mamakin yana ci gaba da dubanta sanda
take takowa ciki,bazaiyi qarya ba ta masa kyai cikin yadin jikinta,saiyaji wani bangare daya
cunkushe a zuciyarsa yana budewa,tunanin da yakeson yi ya soma dawowa,kwanaki yau kusan
goma sha uku kenan bai sanyata a idanunsa ba,ko motsinta bazai iya fadin yaushe rabon daya
ji ba,tana sake matsowa qamshin jikinta na shiga ta qofofin hancinsa,qamshin daya sanyashi
lumshe idanunsa ya sake budesu a kanta sanda ta samu hannun daya daga cikin kujerun dake
can nesa dashi ta dosana ta zauna kan wuta,shuru ya ratsa dakin bayan sallamar data yi na
wasu daqiqu sannan tace
"Inason magana dakai" idanunshi ya daga ya kalleta na wasu sakanni kafin ya janye duban
nashi daga kanta ya maida idanun nasa ya rufe kaman yadda suke dazu,don shine mafita
kawai a wajensa
"Uhmmm" yace da ita a taqaice
"Inason na koma aiki idan Allah ya kaimu ranar monday" da sauri ya bude idanun nasa ya
zubesu fes a kanta,saitaji ya mata kwarjini saboda haka ta janye idanunta daga kanshi
"Labari kike bani ko umarni?" Ya tambayeta kai tsaye,yanayin tambayar daya mata yasa dole ta
kuma kallonshi,tadan sake tsuke fuska
"Shaida maka nake"sai ya maida idanun nashi ya rufe sannan yace
"Tunda ba umarni bane ba zaki koma ba,kin gama aiki a triple r gem,bama nan ba kawai,kin
gama kowanne aiki ako ina idan ba cikin gidan nan ba" haushi takaici da baqinciki suka
cikata,me yake nufi kenan?,yana nufin ya rabata da aikinta,cikin hasala tace
"Me kakeso kace?,bayan duka qarfa qarfan daka yimin bai isheka ba har saika qara da
wannan?,toni ban yarda ba in gaya maka gaskiya,ai bamuyi haka dakai ba" miqewa tayi tsaye
ta soma tafiya
"Dama na gaya maka ne donkar kazo ka tarar bana nan kace ban shaida maka ba".
Tana dab da fita ta tsinceshi a gabanta,suna hada ido ta kauda kai saboda yadda qwayar
idanunshi ta sauya launi
"Bazan taba lamunta ki fita wani waje mahada jama'a maza da mata ba da sunan aiki,ki
gogayya da maza kiyi magana dasu,ki fita da safe ki dawo da yammaci,idan na barki kika koma
lallai na tabbata wawa,kuma abinda nayi baiyi riba ba,kina nufin komawa office din danaga wani
ya kama yatsarki zai saka miki zobe?,Karki soma gigin aikata kuskure irin wannan,idan ba haka
ba zaki gane baki da wayau,idan kuma baki yarda ba bismillah" daga haka ya kauce daga
hanya ya bata waje yana komawa mazauninsa,da gudu gudu ta fice daga falon ta soma sauka
qasa,tayi nasarar riqe kukanta batayi agabansa ba sai data danga da dakin gadonta,wani irin
tuquqi takeji cikin qirjinta da zuciyarta,sam bazata yarda ba,ba zata lamunci ya sake cin galaba
a kanta ba bayan wadda yaci,idan yayi haka aiya tauyeta da yawa,tayita zama kenan cikin
wannan gidan da zaman cikinsa harya soma gundirarta,zaman da bai mata ma'ana ba
sam?,gobe kam saidai ayi duk wadda za'ayi,idan yaso yace ta wuce gidansu.
Iska yake furzarwa daga bakinsa mai dumi bayan fitarta yana murza tafin hannunshi kan
hannun kujerar da yake kai,yanajin bacin