Showing 6001 words to 9000 words out of 126208 words

Chapter 3 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf

a hankali zuwa wajen,inda ta janye jikinta ta rabe a
bango,ya durqusa ya dinga daukan kayan d'aya bayan d'aya yana maidasu muhallinsu,duk abu
guda idan ya dauka yana jin kaman yana qarawa zuciyarsa nauyi ne.

Har ya saka wani abu ya sake cirosu ya kalla,suna nan kamar yadda ta bashi su,hatta da
ledarsu itace dai wadda ta qullesu a ciki,d last thing data bashi a tarayyarsu,da hanzari ya
maidasu ya rufe sannan ya sauya lambobin sirrin ya miqe zuwa gaban teburinsa ya amsa
wayar daketa burari,sai daya kammala a nutse sannan ya aje,ya kalli nafisa data tsarki kanta
tare da ala wadai da shegen qwaqwqwafinta da yakeson ya bata mata dukka plan dinta
"Ki wuce gida,saina qaraso" daga haka ya soma diban wasu files,dai dai sanda P.A dinshi ya
shigo suka soma yunqurin barin ofishin,hakan ya sanya dole tabi bayansu jiki a sanyaye,a
wajen elevator suka rabu,su suka hau wadda zata kaisu third floor ita kuma tayi qasa don barin
companyn.

*GA MAI BUQATAR WANNAN LITTAFI ZAI BIYA NAIRA KACAL 200 YA SAMESHI,WANDA
KE BUQATAR DUKKA ZAFAFA BIYAR DUN KUWA ZAI SAMESU NE AKAN FARASHIN NAIRA
500*




*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER
TAREDA TURA MATA SHAIDA_*

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali�_*ZAFAFA BIYAR
NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA
BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da
sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos


***
0️⃣2️⃣


Qarfe biyu na rana suka shigo gidan ita da huda,a falo suka tadda anty zubaida gabanta
plate ne dauke da alala guda uku tana ci
"Wash" kadija ta fada tana zama saman kujerar dake falon,sannan ta zame dankwalin kanta
don tasha iska,dogon gashinta da bashi da cika saboda santsi da tsahonsa ya bayyana
"Ina kuka jima haka yau?" Muskutawa shahida tayi,muryarta dauke da alamun gajiya tace
"Kin manta na gaya miki muna shirye shiryen ziyarar da mai makarantarmu zai kawo mana next
week?"
"Af,na manta haka ne fa....amma da alama ba qaramin shiri kukewa zuwan nasa ba,ga
dalibarku nan ta kasa zaune ta kasa tsaye" inji anty zubaida tana duban huda dake zare safarta
tana dariya,yatsina fuska shahida tayi cike da qosawa
"Nima abun duk ya soma ginsata anty,duk sun d'aga hankalinsu duka malaman
makarantar.....amma hakan qila baya rasa nasaba da halayyarsa,don a yadda kausar ke
gayamin bashi da sauqi sam,kuskure kadan zai gani da bai masa ya dauki mataki,don bai
qaunar abinda zai taba students din,last year yazo lokacin ban soma koyarwa a makarantar ba" "To Allah ya taimaka yayi jagora...kece ma,da kin amshi aikin kamfaninsu abban huda da duk
wannan jigilar kin huta da ita,har mota zasu baki kyauta saboda matakin da aka baki aiki akai

yakai a bakin" murmushin gefan baki kawai tayi,sannan tayunqura ta miqe tana tattara
mayafinta zuwa dankwalinta da jakar makarantarta
"Au....kinga naso na manta...nuraddin ya bada saqo,yayita kiran wayarki wai bai samu ba" cak
shahida ta dakata da abinda take ba kuma tare data juyo ba,fitar furucin daga bakin anty
zubaida zuwa kunnuwanta jinsu take kamar harbin bindiga
"Waima....ina kika aje wayarki?,nayita kira ni dinma ban sameki ba......anya shahida anya?,sai
yaushe zaki saki ki koma dai dai?,saboda nuradden ne kika kashe wayarki?,nuradden kuwa
deeja ya cancanci haka kuwa?" Batasan idanunta sun soma fidda hawayen da suka cikasu ba
sai data ji saukarsu kan hannunta dake cukuikuye da mayafinta,kasa jure tsaiwa tayi saitayi
gaba cikin sassarfa.

Da kallo anty zubaida tabita harta bacewa ganinta sannan ta girgiza kai tana furta
"Allah ya kyauta" bata sake tankawa ba saita maida hankalinta kan alalanta da take ci.

Ganin har huda ta gama komai shahidan bata sake ko leqowa ba,sai anty zubaida ta bawa
hudan saqon tace ta shiga ta kai mata,sannan ta gaya mata ta fito taci abinci.

Qarfe hudu na yammaci ta fito a shirye tsaf cikin doguwar riga abaya wadda ta wadatu da
adon duwatsu,tayi rolling da wadataccen mayafinta,tayi kyau duk da babu ko digon hoda
fuskarta bare akai ga kwalliya,hakanan idanunta tarwai suke babu kwalli ko d'aya a cikinsu.

Ci gaba da kallonta anty zubaida tayi harta kammala tsakurar alalen sannan tace
"Zanje na dubo umma"
"Saikin dawo,Allah ya tsare,bari na baki saqo" ta fada tana miqewa zuwa cikin dakinta,mintina
qalilan ta fito da leda ta miqa mata
"Gashi kikai mata" hannu biyu ta saka ta amsa sannan tayi mata sallama ta fice daga gidan,don
'yar rakiyar tata huda yau akwai islamiyya ta riga data wuce kuma,tilas ta wuce ita d'aya.

A hankali take takawa zuwa bakin titi,jikinta a mace yake kamar yadda take jin zuciyarta sam
babu wani qwarin gwiwa ko karsashi tattare da ita,tun daga can nesa ta hango shigowar
motar,kallo d'aya tayi mata ta gane motar kota wace,hakan yasa ta sake tsananta d'aure girarta
gami da kau da fuskarta tamkar bata ga motar ba.
Ilai kuwa yana zuwa dab da ita ya rage saurin motar,saidai yadda ta dauke kai tare da qara
saurin tafiyarshi ya hanashi damar ce mata komai,tana jinsa ya qara yin gaba,hakan ya nuna
mata reverse zaije yayi ya dawo,don haka ta qara sauri,cikin sa'a ta cimma titi kafin ya juyo ta
samu abun hawa ta shige ko waiwayenshi ma batayi ba bare ta san ya iso ko bai iso ba.
Tsam tayi da ranta cikin abun hawan lokacin da yake sake kusantata da ainihin
unguwarsu,wadda anan komai na rayuwarta ya samo asali,a nan duk wani babu na quncinta ya
bude,anan komai ya wanzu ya kuma wakana cikin shafukan rayuwarta.

Tafiyar mintina talatin suka iso,ya gangara da ita cikin layinsu kamar yadda ta saba aduk

lokacin da tazo unguwar tasu bata sauka a titi saita dangana da qofar gidansu,kanta ta dauke
gefe guda lokacin da sukazo gifta wani katafaren gida,bata maida kanta ga kallon gabanta ba
har sai da suka isa qofar gidansu,sauka tayi ta sallami mai motar tana cusa kai cikin gidan gami
da yin sallama.
Fakadeden tsakar gidan nasu wanda ada can zamanin quruciya takejin babu wajen daya
kaishi dadin xama da dadin yin wasa,kafin wasu murd'addun al'amura su zama silar da zaman
tsakar gidan ya zame mata tamkar zama kusa da ramin maciji,babu kowa a tsakar gidan saidai
a share yake sarai fes cikin tsafta da kulawa,batayi mamakin ganin babu kowa din ba don tasan
a irin wannan lokacin saura qannenta na islamiyya.

Daga falonta ta amsa mata sallama,shahida taci gaba da takawa har zuwa qofar falon ta
sabule takalmanta ta shiga tana sake maimaita sallamarta.

Cikin sanyi ta amsa mata kamar kowanne lokutta,wanda hakan kusan ya zame musu jiki ita
da umman tata
"Yanzu kike tafe?" Umman tata ta fada cikin jin nauyin d'iyartata wanda har yau ya kasa barinta
"Wallahi umma,na manta yaune ranar da nake zuwa sai wajen uku na rana na tuna"
"Da kin bari sai gobe ai,tunda yamma tayi.....mubina ma ta riga da tayi wankin harsun bushe ta
shanya,tunda taga rana ta soma baki zoba tace wataqila yau yaya ba zata samu zuwa ba"
"Me yasa?,da ta jirani ai ina kan hanya" gaida ummantata tayi ta amsa tana tambayarta anty
zubaida huda da mai gidan,ta miqa mata saqon da anty zubaidan ta bata wanda itama batasan
meye a ciki ba,bayan umma ta gama godiyarta ne kuma shuru ya biyo baya,shahida ce ta dinga
qoqarin sako hira jefi jefi,ko kusa a yanzu batason yadda umman take qin sakewa da ita,kaman
ba ummanta ba?,komai ya canza tsakaninsu tun shekarun baya da suka shude.

Qarfe biyar ta shiga kitchen ta soma dorawa ummantata abincin dare da taga tana niyyar
daurawa,ita kuma tana daga tsakar gida zaune kan tabarmar da suka shimfida,duk wani motsin
rahama na kan idanunta,itama rahaman ta ankara da hakan saidai ta nuna bata kula ba,irin
wannan kallon umman tata ta saba binta dashi da dadewa,kallon tausayi,kallon nadama,kallon
kaicon biyewa son rai da son zuciya da sukayi ita da mahaifin rahama shekarun baya da suka
shude,har hakan yaso jefa diyar tasu cikin hallaka,da tuni yanzu bayan shudewar mai gidan ita
daya zata ci gaba da kurbar baqinciki da bacin ran abinda suka aikatawa rayuwar rahaman.

Qarfe shida qannenta nata suka shigo,ta bisu da kallo sanda suke shigowar cikin jin dadi
tare da musu addu'a cikin ranta,koda yaushe tana jin dadi har cikin ranta na yadda rayuwarsu ta
banbanta da tata rayuwar a sanda take da shekaru kamar nasu,kallo daya zakayi musu kasan
suna samun kulawa da tarbiyyar data dace,mubina ke bin rahama(shahida),sai
khadija,faruq,sajid sai qaraminsu nasir.

Dukkansu fuskarsu qunshe da walwala suka iskota,ta jima cikinsu yayin da mubina ta amshi
aikin girkin,tana yi suna hira da yayarta da sauran qannunta.

A nan kan qatuwar tabarmar suka ci gaba da zama,suka gabatar da sallar magariba,sannan
mubina ta zuba abinci cikin babban tray.

Gaba dayansu kowanne ya sanya hannunshi suka soma ci,suna hira lokaci lokaci,har cikin
ranta tana jin dadin kasancewa cikin 'yan uwanta,saidai wannan kallo da duba da umma ke
mata tana qaunar ya gushe daga idanunta,ta manta da faruwar komai,ya zama tarihi kamar ma
bai taba faruwa ba.
Sallamar usman d'an maqotansu shi ya katse hirar tasu,ya gaida ummansu sannan yace
"Ana sallama da anty shahida" hada idanu sukayi da umman,yayin da kowa abinda ke yawo a
zuciyarsa ya tashi daban da na d'an uwanshi,qas da kanta shahida tayi tana kokawar hadiye
lomar tuwon data riga ta saka abakinta,batakai ga hadiyewa ba saqon usman ya shiga
kunnenta,sai taji gaba daya abincin bai mata dadi a bakinta,ya kuma gagara wucewar,hakan ya
sanya ta miqe tsam ta isa bakin rariyarsu ta zubda tuwon sannan ta wuce dakin umman ba tare
data bi takan aiken da akayo mata ba.

Suya kawai qirjinta yake,waye wannan yakeson mata kutse ne cikin rayuwarta a sanda bata
shiryawa hakan ba?,waye shi da zai tunkari rayuwarta a sanda bata da dukkan wani tsari akan
kowanne d'a namiji?.

Shigowar umma dakin shiya katse mata tunaninta,ta yunqura ta miqe ta zauna sosai daga
kasalalliyar kwanciyar da tayi,wani mummunan tashin hankali ya ziyarceta sanda ta dubi idanun
umman taga hawaye na biyo kuncinta,cikin matuqar rudewa da gigita tace
"Um....umma...hawaye fa kike umma meya sameki?,don Allah kibar kukan,kiyi shuru kice wani
abu"
"Dole nayi kuka shahida....bazan daina kuka ba harsai sanda abinda yake damuna ya
gushe,tashin hankalin da kika shiga kadai sanda aka aiko kiranki ya tabbatarmin akwai sauran
rina akaba,kuma hakan ke nunamin cewa dafin da muka zuba a zuciyarki har yau bai gama
wankewa ba" zamowa tayi daga saman kujerar tayi gurfane a gaban umman tata itama hawaye
na sakko mata cikin tashin hankali
"Ko kad'an umma,kufa iyayena ne,kune kukayi silar zuwana duniya,umma....ba tun yauba na
gayamiki ki goge duk wani abu daya faru daga ranki,ki daina alaqanta duk wani yanayi da zaki
gani tattare dani da cewa laifinku ne"
"Indai kinason hakan ta faru shahida ki koma yadda kike....ki amshi wani cikin masu sonki kiyi
aure,anwar bashi kadai bane namiji da don ya miki wani abu zai zama silar da zaki maida kanki
wata aba daban ba,indai ina ci gaba da ganinki a haka baki sauraren kowa bare akai ga batun
aure bazan daina zargar kaina ba har na koma ga mahaliccina,kamar yadda mahaifinki bai
daina zargin kanshi ba har ya koma ga mahaliccin......" Maganar tata saita riqe,kuka sosai ya
qwace mata,tana tuna abubuwa marasa dadi da suka faru a rayuwarsu,tana tuna komai tar
cikin kwanyarta,qaruwar kukanta ya qara dasa tashin hankali a zuciyar shahida,wadda ta miqe
ta figi mayafinta cikin rawar murya tace
"Zanje,zan fita umma indai hakan shi zai sanya farinciki da walwala a cikin zuciyarki" bata qara
second guda ba tayi waje,kai tsaye kuma ba tare da saurarar komai ba ta wuce zuwa qofar

gidansu.*ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH)KARKI
SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*KO KUMA*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don samun shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi
da sabbabi*

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

*AA*
0️⃣4️⃣




Kasa cewa komai tayi,maganar hudan ta cillata tunanin wata duniya can baya,wanda duk yadda
takai ga hana kanta batasan sanda ta fada ba.

Sai data sallami huda sannan taci gaba da sabgar girkinta,batasan me yasa ba sam batajin
yunwa,ko zancan da huda tayi ne ya cushe mata cikinta gaba daya ya sanya har walwalarta ta
ragu.

Tana tsaka da kwashe abincin cikin coolers huda ta shigo da sauri hannunta dauke da
wayar shahida tana fadin
"Anty ana kiranki,zata katse" ta fada tana miqa mata,bata amsa ba ta kalli screen din wayar
dake hannun huda,nuraddeen ne,saita dauke kai taci gaba da juye abincin tana cewa
"Ajiyeta kawai huda,aiki nake" juyawa yarinyar tayi ta fice da wayar zuwa falo da gudu don kada
cartoon din da take kallo ya wuceta.

Tana cikin kintsa wajen sallamar anty zubaida ta karade falon sannan ta taddata cikin
kitchen din
"Sannu da dawowa maman huda"
"Yauwa sannunki shahida,kin ganni sai yanzu ko?,wallahi layi yau na samu....me aka dafa
mana ne yau da yunwa na dawo" nuni shahida tayi mata da food flask din dake jere a wajen,ta
qarasa tana budawa
"Hmmmmm,kice yau na musamman ne abincin,bari wannan sai nayi wanka zan zauna sosai
tukunna na kwashi dabge" qaramin murmushi shahida tayi mai fitar da d'an sauti tana duban
anty zubaidan,har takai bakin qofa ta dawo

"Au....ni kuwa kinsan nuradden na qofar gida zaune cikin mota yana jiranki?" Asanyaye ta daga
kai ta dubi anty zubaidan,sai ta sadda kanta tana goge plates din data wanke zata jerasu a
muhallinsu,hakan da tayi shi ya tabbatarwa anty zubaida ya kira bata daga ba kenan
"Shahida.....wannan wacce irin rayuwa ce kika daukarma ranki?,mai sonka fa ya wuce ka
wulqantashi,laifin wani dama yana shafar wani?" Shuru ta sake zabar tayi,saboda tana ganin
sun gaza fahimtarta ne gaba daya,ta yiwa soyayya hidima,ta yiwa soyayya halacci,ta yiwa
soyayya dukkan wata kara da alkunya,qarshe data tashi ita mai ta bata?,data tashi da wanne
sakamako tazo mata?,sunfi kowa sani saboda haka sunfi kowa amsar dukka tambayoyinta,ko
daya bata tsinci komai cikin soyayya ba face tsantsar butulci mummunan sakamako da kuma
mummunar makoma,shin ta yiwa kanta a dalci kenan idan ta sake cusa kanta a wannan
bigiren?
"Nidai ya roqeni alfarma,saboda haka idan na isa dake ki leqa ko gaisawa ne kuyi" zancan anty
zubaida ya katse tunaninta,daga haka bata sake cewa komai ba ta ida ficewa daga kitchen
din,tana jinta sanda ta kira huda suka haye sama tare,tasan kuma tayi hakanne don sanin
halinta,ba qaramin aikinta bane ta fita ta baro masa huda ta cikashi da surutu wanda idan ya
gaji da zama yake sallamar huda shima ya wuce nashi guri.

Anty zubaidan tafi qarfin komai a wajenta,don haka ta dauraye hannayenta ta wuce
dakinta,ta zari hijabi ta saka ta sanya slipper dinta ta wuce qofar gidan.

Kamar kowanne lokaci yana zaune cikin motar,bayanshi jingine da seat din kujerar dayake
kai,da alama ya jima zaune a wajen,duk da haka ganin fitowarta bai hanashi miqewa ba yana
sakar mata murmushi harta qaraso
"Barka na tunda na samu kin fito" ya fada tamkar wanda baiyi zaman jiranta ba
"Inda kayi aiki da shawarata tun a karon farko da duk bamu kawo wannan matsayin da muke
kai yanzu ba" ta fada kanta tsaye tana dubanshi,kafin daga bisani ta janye idanunta,har ga Allah
wulaqanta dan adam ba dabi'arta bace,zatafi kowa farinciki idan har noraddeen ya janye daga
qudurinsa daga kanta,ga sabanin tunaninta sai taga ya saki murmushi "Bani da damuwa shahida,nasan cewa mahaqurci mawadaci,zan iya jure koma meye indai a
kanki ne shahida" idanunta ta lumshe tana jin kamar jiri zaya kada ta,a rayuwa yanzu babu
abinda ke damunta sama da matsalar nuradden,ya soma shiga jiki da zuciyar
makusantanta,bata da buqatar a yanzu dukkan abinda zai kuma d'aga ma rayuwarta hankali. "Koma meye tabbas mai wucewa ne watan wata rana" furucin nuradden ya sake ratsa dodon
kunnenta,a sanda take kiciniyar dai daita kanta
"Don Allah.....shahida inason ki bani dama,ki saurareni koda wayata ce kadai ki dinga
dagawa,bazan takuraki kan koda yaushe saikin fito na ganki ba,amma ki daga wayata,hakan
kadai ya isarmin....don Allah" ya fada yana hade hannayensa waje d'aya alamar roqo
"Naji ya isa,ka sameni ta wayar" ta fada tana juyawa don ta shige gida kamar wadda take kan
qaya ko wuta
"Tsaya mana shahida....." Yayi hanzarin fada,tsayawa tayi cak kamar yadda ya umarta,saidai
bata waiwayo ba a haka ya cimmata,gabanta yasha,yana murmushi ya miqa mata wata leda
"Ga wannan,ki karba don Allah....." Batason doguwar magana saboda haka ta saka hannu ta
amsa kawai ta shigeshi,kallo ya bita dashi yana jin dad'i cikin ranshi,yau an samu wani ci gaba

da har shahida karo na farko ta amshi abun hannunsa,tabbas watarana yana saka ran komai
zai wuce,bai taba tsammatar tsintar kanshi cikin soyayya makamanciyar wannan ba,saidai
shahida ta cancanci komai,tana da nutsuwa tana da hankali uwa uba kyau,shahidan tayi
masa,tako ina ta amsa sunan irin macen da yakeso,yake da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login