Showing 60001 words to 63000 words out of 126208 words
Chapter 21 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf
kamata a bata.
Uncle hisham da kanshi ya kaita gidan shugaba kuma mamallakin kamfanin gaba daya don
tayi musu godiya,gida mai dauke da matan aure biyu kuma aminan juna,gida na farko data ji
yanayin rayuwarsu ya burgeta bayan gidan anty zubaida,haduwar farko jininta ya hadu dana
raihana,yanayin rayuwarta nutsuwarta da komai nata,haduwar farko ta karanci yadda ta iya
tattalin miji cikin wani yanayi mai sanyi da kuma mu'amala,rumana uwargida,mace mai fara'a da
saurin sabo itama sunsha hira da ita,wanda daga qarshe ta tattara kan yara tace zasuje siyayya
ne ta barsu da raihana,yaran da shahida ta kasa tantance wanne ne yaran rumana wanne ne
na raihana?.
Cikin qanqanin lokaci ta kama aikinta sosai,ta kama mutuncinta haka nan tsakaninta da
ma'aikatan sai gaisuwar mutunci da girmama juna,ita kanta idan ka kalleta zakaga sauyi mai
yawa tattare da ita sabanin baya,ta sake fresh hakan fatarta ta qara kyau da gogewa,kwanciyar
hankali da nutsuwa sun samu tare da ita,ta soma shimfida sabuwar rayuwa,tayi wancakali da
dukkan wani qalubale da bacin ran rayuwa.
_yanzu aka soma,muje zuwa masu karatu_*Zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don GIRMAN
ALLAH karki sharing,ga mai buqata ki tuntubi wannan numbers din*
07067124863
*ko kuma*
09032345899
*Alqawarin Allah*
2️⃣1️⃣
*BAYAN SHEKARA DAYA*
Komai na duniya baya ga qaddara yana tafe ne da lokaci,wanda wannan lokacin shike
qunshe da komai,yake tattare da faruwar komai,shike bayyana komai hakanan shike haifar da
komai din,cikin shekara guda shaheedan ta samu sauyi da canje canje masu tarin yawa,tayi
qoqarin binne duk wani qalubale data taba samu cikin rayuwarta,ta kaucewa dukkan wani abu
da zai tuna mata dashi fiye da baya,ta fannin rayuwarta kuwa shahidan ta sake zama wata
mace mai aji,irin macen da kana mata kallon farko zakasan ta goge,bawai gogewa ta budewar
ido ba,gogewa ta kyau,gogewa ta iya ado da mu'amala sakamon mu'amala da take da mutane
kala daban daban daga sashe daban daban na qasashen afrika,ta qara wani kyau da
kwarjini,hakanan ta murje,ta gefe guda kuwa a yanzu nuraddeen ya samu kanta babu laifi,aduk
sanda ya kirata zata daga su taba hira,hakanan duk sanda yazo wajenta a gida takanyi qoqarin
fita,wani lokaci ma yakan bita wajen aiki da niyyar daukota,anan ta dakatar dashi,don babu
abinda ta tsana a duniya a yanzu irin shiga motar wani d'a namiji,duk sanda ta saka kai zata
shiga sai abun ya fado mata,wannan moments din ya kasa barin qwaqwalwarta,shine kuma abu
mafi muni cikin dukkan abinda ya faru da ita,tana mamakin me ta yiwa wannan mutumin daya
watsota qofar gidansu cikin cin mutunci da wulaqanci?,me ta yiwa fiddausi wadda har yau bata
bi ta kanta ba ko neman inda take,hasalima bata sake ganinta ba,to me zatayi mata?,me zata
buqata daga gareta?,koma meye tana roqon Allah yayi hukuncin daya dace.
To ko cikin company ma da baqin dakanzo siyayya kamfanin masoyane suka mata
rubdugu,wani lokaci har haushi kan kamata na yadda ba'a cikakken kwananki uku wani bai
ganta yace yana so ba,ta rasa meye a jikinta haka?,me take dashi wanda yake jan
hankalinsu?,da tasan wannan abun ba shakka data cireshi ta jefar kota huta da shegen binbinin
da suke ma rayuwarta
"Kin hadu ne shahida,kina da komai Allah ya miki baiwar komai,ba zaki gane abinda nake nufi
ba shahida,amma kinyi tako ina,ki bani dama don Allah" ta tuno kalaman wani alhj wanda tunda
yazo kamfanin siyawa matarsa sarqoqi gift na birthday dinta ya dafewa shahidan,a sannan ta
sauko zata je cin abinci,baima san ma'aikaciyarsu bace.
Gefe daya ta sake yalwata rayuwar ummanta da qannenta,hakan ta yiwa gidansu gyara ta
sake qawatashi,ita kanta a yanzu jin dadin rayuwarta take,abu daya ne data fuskanci umman
nata ta tsiro dashi shine son shahidan tayi aure,don zancan da ake mubina na ss two ne,kuma
ta samu wanda yake sonta,dama yakeso a bashi yaje can wajen dangin mahaifinsu dake
katsina ya gabatar da kanshi.
Qarfe hudu suka tashi daga aiki yau,cikin sauri saboda kar lokaci ya qwace mata ta shiga
adaidaita sahun da yake nata ne yake kaita aiki ko wata unguwa da takeson zuwa,a sanda
kuma ya ajeta yaje yayi haya dashi.
Saloon din da take zuwa kitso ya sauketa,ta dubeshi
"Ka dan jirani yau ba dadewa zanyi ba"
"To hajiya" ya fadi yana kashe adaidaitan,ta juya cikin takun nutsuwa zuwa bakin saloon din.
Yanayin wajen kaman tsarin ciki da falo aka yi masa,duk da qofar cikin mai fadi ce sai aka
saka labule mai shara shara,falon kuma kujerun zaman custumers ne da kuma kayayyakin
siyarwa na kwalliya kamansu ribbom,man kitso man shamfo,beads da sauransu.
Shagon akwai mutane saidai ba sosai ba,a falon ta tadda mai saloon din tsaye da wasu
mata suna siyan ribboms,cikin fara'a da muntuntawa ta tarbi shahidan,saboda tasan duk sanda
tazo din ba qaramin qaruwa takeyi da ita ba,suka gaisa sannan tace mata
"Kitso nakeso madam,amma manya nakeso yau ayimin ibra nakeso" cikin juyayyar hausarta
tace
"Ohk madam babu damuwa..saidai akwai wasu da za'a wankewa kai,amma bari na soma
sallamarka su sai su jira"
"A'ah madam,aisun rigani zuwa sallamesu tukunna"
"Ohk maa" ta fada tana juyawa ta duba wani waje da take aje magazines ta zubewa shahidan
sannan ta sallami wadanda suke sayen ribbom ta koma ciki inda take wankin kan.
Daya daga cikin kujerun dake wajen shahida ta zauna,ta aje jakarta gefe daya sannan ta
cire glass dinta da take amfani dashi lokaci zuwa lokaci saboda ado ta dorashi saman jakartata
ta bude magazine din ta soma dubawa.
Hayaniya da hirar dake tasowa daga ciki ta cika mata kunne har tasa ta daina fahimtar
abinda take dubawar,sai kawai ta rufe magazine din ta riqeta a hannu,hirar yammatan dake ciki
na shiga cikin kunnenta
"Ya hadu iya haduwa,daa wlh ni bai dameni ba saboda a sannan baida wani abun
burgewa,amma yanzu har wani kishi kishinta nakejin yana kamani wallahi,anya nan gaba kuwa
ba za'ayi juyin mulki ba kuwa?" Dariya suka kece dashi
"Mima baki da kyau,daga daukanki sojan haya saiki fadi haka?"
"Ke qyale shegiya,shekara nawa ina mata bauta?,don tana biya na aiba halitta ta tayi ba" hirar
sam bata wa shahida ma'ana ba,saboda haka ta zaro wayarta kawai tayi kiran ummanta,bayan
sun gaisa tace
"Umma don Allah ki saka mubina ta soyamin wainar fulawa ina nan zuwa,na tsaya yin kitso
ne,ta saka min albasa da yawa,ta manja nakeso"
"Toh shikenan,amma saita saukemin tuwona"
"Eh kafin sannan ma na qaraso"
"Allah ya kawoki lafiya"
"Ameen umma" bayan ta kashe kiran noradden ya shigo,ba yabo ba fallasa ta daga
"Yallabiya kin hanani sukuni sai naji muryarki" murmushi ne ya subuce mata ba tare data sani
ba,ita mamaki ke kamata idan nura na nuna yadda yake tsananin qaunarta
"Dariya ma na baki?,don bakiga yadda na gaji tubus ba saboda tunaninki,shahida har yau kina
daukan son da nake miki da sauqi"
"Ba haka bane,kawai dai haka kai ka fahimta"
"Koma yaya ne dai yanzu kin wuni lafiya?"
"Lafiya qalau,kaifa?" Sosai yaji dadin yadda ta tambayeshin,daga haka ya shiga janta da hira,ta
biye mishi kodan ta ragewa kanta lokacin zaman jiran da takeyi.
Minti ashirin 'yammatan da akewa wankin kan daya ta soma daga labulen ta fito,tana sanye
da riga dinkin straight gown wadda tafitar da duk wata sura tata,shahidan na shirin dauke kai
dayar ta biyo bayanta,itama sak irin dinkin dayar ne a jikinta,har shahida ta dauke kai yadda
taga ta zuba mata ido ya sanya itama ta maida idanunta kanta,da sauri taga ta juya ta koma ciki
tana cewa
"Au...madam na manta qawata tace muyi jiranta a nan"
"Ohkey to babu damuwa" ta bata amsa sanda shahida tayi sallama da nooradden ta maida
wayar jakarta sannan ta cire rolling din kanta,ta zare ribbom dinta ta soma taje kanta.
A gaggauce nafisa tayi parking na motarta a qofar shagon,cikin hanzari da sassarfa ta nufi
qofar shiga wajen kai tsaye.
A sannan anyi rabin kitson da akewa shahida,labulen kawo sukaga an bankado hakan ya
sanya shahida daga kanta ita da madam tawakkaltu dake mata kitson gaba daya,idanunta ne
ya sauka cikin na shahida tana mata kallon fes,itama shahidan kallonta take,tasan
fuskar,fuskace da ba zata taba manceta ba,fuska ce da anwar ya turo mata da hotunansu a tare
yana bayyana mata ita a matsayin masoyiya a gareshi,ta yaya zata manta wannan
fuskar,amma saita dauke idonta ta maida kanta qasa tana ci gaba da danne danne a
wayarta,saidai wani abu yazo ya tsaya mata cak a qahon zuciyarta.
Madam tawakkaltu ce ta amsa mata tana ci gaba da yiwa shahida kitson,saidai idanunta na
akanta tana neman jin abinda ya kawota wajen,don bata santa ba
"Amm,akwai friend dita mima da tazo wankin kai nan ko?" Nafisa tayi qarfin halin furtawa,ranta
da zuciyarta gaba daya a jagule
"Eh sunaa ciki aeke sukee jira" ta amsa mata cikin gurbatacciyar hausa,kafin takai ga isa wajen
mima ta fito da qawarta lima
"Gani...mu wuce ko?" Ta fada tana karantar fuskar nafisan,kaita jinjina yanayin fuskarta na sake
sauyawa yana nuna rudani a ciki qarara,har sukaje bakin qofar da zasu fita tana duban shahida
wadda bata ma san tanayi ba,saidai jikinta ya bata hakan
"Madam ko kinsansu ne?" Tawakkaltu ta tambayeta ganin yadda suke kallonta
"Ba wadda na sani a cikinsu" ta amsa mata a taqaice
"Allaho ya kyauta" ta fada tana mamakin irin kallon da sukewa shahidan su duka.
Duka sai komai ya tsayawa shahidan cak,ba bacin rai takeji ba amma ranta da jikinta sam
babu dadi,wayar ta maida cikin jaka ta ciro carbinta ta maqala a yatsanta ta soma jan
HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL,wansa babu jimawa taji komai na koma mata dai dai.
Dukan sitiyarin motar tayi da qarfin gaske har lima na zaro ido kada fa kan motar ya lalace
"Ba haka nakeso na ganta ba mima,ya akayi na ganta a cikin kyakkyawan yanayi?,so nake ta
dilmiya ta lalace,so nake tayi nisa cikin shan kayan maye karta waiwayo komai nisan kiran da
za'a mata,kudin dana biyaki bai kamata wasan ya tsaya iya nan ba,ya akayi haka?" Ran mima
yadan sosu kadan sabida yadda nafisan koda yaushe taqamarta nakan kudin data bata,amma
abinka da bariki saita danne
"Abinda ya bani mamaki ya girgizani kenan yasa har nayi kiranki" shuru ne ya ratsa motar abun
na kaiwa nafisa ko ina,maganar mima ta katse mata zaren tunaninta
Ba wannan nakeson jiba,meye mafita?" Ajiyar zuciya mima ta sauke
"Toh....a yanzu dai babu batun saka wani kota bar wani ya shiga jikinta,na tabbatar ba zata sake
barin haka ta faru ba a gareta...amma dai duk da haka,ba'a rasa nono a riga,ki fidda
kudi,zansan aikin daya dace muyi a kanta,amma....kece zakiyi rabin aikin,ke kike tare da anwar
kuma zakici gaba da kasancewa tare dashi,dole ki sake cusa masa tsana da qinta cikin
zuciyarsa,kisan yadda zaki ki mamaye tunaninsa ki shiga lungu da saqo"
"Kudi ba damuwa bace,successful aiki shine damuwata"
"Karki samu damuwa,kinsan wace ni,nayi kin gani ai" locker motarta ta bude ta ciro kudi ta irga
ta miqa mata,tasa hannu ta cafesu tana sakin murmushi
"Koma sit dina ki jamu,don bazan iya driving ba a yanzu"
"Ohkey" miman ta fadi,sukayi musanyan seat ta kunna motar ta figeta,wata ta sanya musu
nafisa taja tsaki
"Ina cikin irin wannan mode din zaki kunnan waqa,kashe malama ki barni nayi tunani da kyau"
"Daqiqiya wanne tunani gareki?,bayan duk wani tunaninki nice nake miki" ta fada a zuciyarta
tana cire waqar,yayin da a fili tace
"Am sorry,komai fa zai dai daita".
Qarfe shida ta shiga soron gidansu bakinta dauke da sallama,tsakar gidan nasu babu kowa
sai mubina dake zaune saga qofar kitchen tana suyar wainar fulawarta,fes gidan yake kamar
kullum,cikin gajiya
ta qarasa inda mubina ke zaune
"Sannu da zuwa yayaa"
"Yauwa mubi...ashe kin soma?" Tayi maganar sanda take duqawa ta bude flask din dake gaban
mubina ta gutsiro wainar takai bakinta
"Da tunima na gama ai,maqociyarmu ce ta shigo umma tace a zuba mata shine nake tara miki
wata yanzu"
"Ummmm....amma fa tayi dadi sosai" ta nemi waje kusa da mubinan tana zama ta janyo yaji ta
soma gutsira tana dangwala,mubina na bata labarin bikin wata cousin dinsu dake
matsowa,shirin da akeyi anko da dai sauransu
"Kowa shiri yake yaya sosai,kinsan wanda zata aura din yana da kudi ba laifi" murmushi kawai
shahida ta fitar,wato duk wadda akace yau zata auri me danshi murna ake mata
"Allah yasa abokin zama ne,ya sanya alkhairi"
"Ameen yaya,naga umma ma tasa an kawo mana ankon,amma bandake" harararta tayi
"Ce miki akayi ni cima zaune ce da za'a min anko?" Dariya mubina ta qyaqyace da ita
"Waya isa yace miki cima zaune,hajiya accountat da kanta"sai data ci ta qoshi sosai sannan ta
isa bakin famfo ta wanke hannunta ta daura alwala ta wuce falon umma.
Da sallama ta shiga,su biyu ne zaune suna hira,ita da wata baquwar fuska da batasan wace
ba,saidai kallo daya ta yiwa matar taji gabanta yayi mummunar faduwa,itama matar idanunta
kan shahida,murmushi kan fuskarta tana amsa sallamar tata,dauke idanunta tayi ta samu gefen
kujera ta zauna "Sai yanzu kika shigo?"
"Haba tun daxu umma,na tsaya naci waina ne"
"Ashe takice amma umma ta bamu muka cinyeta" cewar matar cikin fara'a,sai shahida ta juya ta
dubeta itama fuskarta ba yabo ba fallasa tace
"Ina yini?"
"Lafiya qalau,mun yini lpy shahida ko?" Ta amsa gaisuwar gami da jeho mata tambaya daga
qarshe,kai ta gyada tana mamakin yadda akayi matar ta san sunanta,bayan umma bata furta
sunan a gabanta ba
"Tunda nake zuwa ban taba ganinki ba sai yau,Allah dai yayi yau zanga yaya shahida" ta kuma
fada tana murmushi,itama murmushin shahidan ta maidata mata,ganin kaman bata saki jiki ba
ya sanya umma cewa
"Maqociyarmu ce nan gaba kadan gidanta yake,tayi wajen wata shida da tarewa sai yanzu Allah
yayi ta leqo mana,gidan nan da faruq yake gaya miki ana sadaka duk juma'a?" Sai a sannan ta
fahimci gidan da take nufi,kai ta gyada tana sake fadada fara'arta,don mubina tasha bata
labarin kirkin matar,daki ta wuce daga haka tana jiyo hirarsu da umma.
Har ta gama zamanta ta soma shirin tafiya matar tana nan,a nan taci abincin dare tare dasu
umman,mamaki take sosai shahida,a ina suka santa ne?,wace ita?.
A falo tana rataye da jakarta ta dubi mubina
"Cikin kayan da antyn katsina ta kawo miki daukomin na zabi style zankai dinki,yi sauri ki
daukomin,sa'id yayi anguwa mai nisa yace ya barshi basai ya dawo dakata ba tunda kusa da
anguwarsu yake,motar haya zanbi kar dare ya sake yimin"
"Wallahi duka na sakasu yaaya suna wajen wanki" goshinta ta dafe tana jan dan tsaki cikin
rashin jin dadi
"Halinku daya ai indai mubina ce,kowanne kaya da an saka an cire duk kyanshi sai ruwa,saiki
haqura ai har sai ta karbo itama da dan banzan sanabe,ki kama kayanki ki wanke amma saikin
kai wankau" murmushi matar tayi har fararen haqoranta suka bayyana kan idanun
shahida,gabanta ya sake faduwa,matar tana mata kama da wata,kaman ta taba ganin fuskar "Kinga qanwata zo muje ki zabi style wanda kikeso kinji"tayi maganar sanda ta miqe tsaye ta
dauki hijabinta dake aje gefe tana sakawa,kallonta shahida tayi,sai taji tana jin nauyinta
sosai,banda haka ce mata zatayi a'ah ta barshi,amma saita kasa fada,don ita gaba daya ta jima
rabonta da sake amincewa da wani a rayuwarta,duk wata baquwar fuska da zatayi kutsewa
rayuwarta kaffa kaffa take da ita.
"umma...ina kuka samota newai?,ni gaskiya ba wani gidanta da zan bita" shahida ta fada
dai dai saitin kunnen umman cikin nuna rashin yarda
"Babu komai matar sananniya ce,hakanan mun dan jima tare,kije kawai" hakanan jiki ba qwari
ta fito ta sameta bakin famfo tana daura alwala,ta kammala ta yiwa umma sallama suka fice.
Ko a tafiyarma bata yarda sun hada kafada ba,tana gaba ne tana binta a baya,duk da haka
takan juyi jefi jefi ta sako ma shahidan hira,nata eh ko a'ah ne har suka qaraso gate din
gidan,tsaiwa shahidan tayi tana kallon gidan,kaman taso ta taba ganin anwar tsaye bakin gate
din sau daya,saidai bata tabbatar dashi dinne ko bashi bane,kawai dai tun daga ranar ta tsani
kallon qofar gidan ma
"Muje ciki mana shahida saiki zaba a nutse" murmushin yaqe ta saki
"Nan ma ya isa,idan da yara saiki turo su miqo min na wuce,yau nayi dare sosai a waje takwas
ta kusa"
"Yanzu zaki wuce ai,ki shigo ko kuma nace mubina ta fiki kirki dason mutane" murmushi tayi
saita bi bayanta kawai.
Sosai falon ya burge shahida,komai a kammale a tsaftace yana fitar da qamshi
"Zauna gu waje nan shahida" tana nuna mata kujera da hannu,a darare ta zauna din tana bin
falon da kallo mai gwanin sha'awa da burgewa,sanda yake fidda hijabinta wata 'yar budurwa ta
sauko daga sama ta matakalar benan dake falon
"Sannu da zuwa ummi kin dade yau" ta fada tana duban maman tata
"Wallahi sa'ida...yauwa shiga dakina ki bude wardrobe dina,inda na aje dinkunan da aka
kawomin din nan shekaran jiya ki cirosu gaba daya"
"Toh" ta amsa tana shirin juyawa idanunta ya sauka kan shahida,saita sake juyowa da sauri ta
kalleta ta kalli ummin nata,sai kuma ta juya ta sake hayewa saman.
"Ina zuwa shahida kinji" ta fadi tana nufar wata qofa dake nuna alamun kitchen ne,wayarta
dake jaka ta dauki kuka alamun kira ke shigowa,ta cirota tana dubawa,noradden ne,saita latsa
tana karawa a kunnenta
"Ranki