Showing 84001 words to 87000 words out of 126208 words
Chapter 29 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf
jarunta da mazantaka na jajirtaccen namiji,kai take jinjinawa hawaye na
zuba daga fuskarta sosai yana hadewa da majina,ji take kaman ta cire ranta,ji take kama ta
dauki numfashin shahida da bata tashi dawowa rayuwarta ba sai sanda ta sakankace take saka
ran ta mallaki anwar,tana ganin da tayi faduwar baqar tasa,data shiga ta zama 'yar kallo gwara
ta haqura dashi har abada
"Anwar!...kaje ka auri shahida bazan aureka ba,bazan aureka ba har abada" tana kaiwa nan ta
juya da gudu gudu sauri sauri tayi cikin gida,yayi niyyar dakatar da ita amma sam bata tsaya ta
saurareshi bama bare taji me zai sake fada,saiya furzar da numfashi,kana ya ture kujerar baya
ya miqe yana daukar muqullin motarsa gamida da handkherchief dinsa dake aje saman teburin
ya saka cikin aljihunsa ya nufi qofar fita,sai daya shiga parking space sannan ya dauki motarsa
yayiwa mai gida horn ya bude masa gate ya fice daga gidan cikin nutsatstsen tuqi.
Yana tuqin yana furzar sa iska mai dumi daga bakinsa,wai me yasa mata dukka harkarsu
matsala ce?,don kawai yace mata ba ita daya za'a daurawa aure dashi ba shine xata masa
wannan jinnun?,to xaya zuba ido yaga iya nata gudun ruwan.
Wayarshi dake aje gefe ta dauki rura,yadan juya ya kalleta,ganin number anty usaina ce ya
sanyashi dagawa,ya saka handsfree ya aje gefansa
"Kana wajen ta ina ne?"
"Ina hanya anty"
"To shikenan saika iso"bai amsa ba ya katse kiran ya aje wayar ya maida hankalinsa ga
tuqinsa,duka hannayensa na zube saman sitiyarin,yayin da rabin tunaninsa ya tafi ga abinda
nafisan tayi yanzu,me take tunani?,zaita binta ne yana lallashinta?,ko yace ta taimaka ta
aureshi?.
Yana fitowa daga motar su sa'ida suka shigo gidan,dawowarsu kenan daga makarantar dare
dake can daya bangaren na unguwarsu,ba yadda anwar din baiyi ta qyalesu ba amma tace sam
batason zaman banza,zaman kallon bayan sallar magariba daga waccar tashar a koma
waccar,dukansu suka iso suna masa sannu da zuwa ya amsa ya shiga cikinsu suka shige cikin
gidan.
Qaramin falon anty usaina suka shiga suka bar yaran a babban falo,idanunsa nakan
tauraruwa tv anty usaina ta shigo ta aje masa abinci,kallon abincin yayi
" banajin yunwa anty"tana shirin zama tace
"Kaci a gidan abinci kenan?,gwanda dai kayi auren nan suma sa huta da ganinka" murmushi ya
saki yana shafa kanshi,zama tayi suka gaisa
"Ya za'ayi da kayan lefen?,na ina za'a fara kaiwa?" Tsaki yaja can qasa sannan yace
"Ni kaina ban sani ba,ina tunanin iya nasu za'a kai,don nafisa tace ta fasa" idanu anty usaina ta
fiddo
"Ta fasa kamar yaya?"hannayenshi ya watsa sannan yace
"Oho,na shaida mata kawai su biyu ne dalilin da yasa tace ta fasa kenan" saita sauke ajiyar
zuciya tana dubanshi
"Don tace ta fasa bawai yana nufin ta fasa dinne ba,kishi ne kawai da bacin rai,lokaci qanqani
zata sauko,saboda haka ba za'a fasa shirin komai ba,zuwa gobe ka kirata ka bata baki duk
yadda kukayi saika sanarmin" kai kawai ya gyada yana mita qasan zuciyarshi,yadan jima anan
suna tattaunawa sannan daga bisani yayi mata sallama ya wuce.
A guje nafisa ta shiga falon gidan nasu ta wuce momy dake zaune tana kallo ta haye sama
dakinta,da kallo momyn ta bita harta shige,saita dauke kai tana sauke ajiyar zuciya,dama ta
sani za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya,yadda nafisan ta dora burinta da rayuwarta duka
kan anwar din tasan za'a sha gwagwarmaya duk sanda labarin ya shiga kunnenta,qyaleta tayi
bata bi ta kanta ba,ta barta ta gama kukan zuciyarta ta huce tukunna.
Tamkar zata zauce haka taji,ta kai ta kawo ta kasa zama kamar wadda ta hadiyi
tabarya,wannan wacce iriyar masifaffiyar shahida ce?,wanne irin mayen anwar ne?,ace duk
yadda takai ga rabasu haqanta ya gaza cimma ruwa?,iya abinda ya kamata tayi don rabasu tayi
amma ace bayan shekaru shidda sun sake dawowa sun jone?,idan ma kisa ba batasan me
zatayi don rabasu ba,wayarta ta rarumo ta kira number mima,saidai hartayi quginta ta katse
bata daga ba,haka ta dinga kira ba qaqqautawa amma bata daga ba,cillar da wayar tayi cikin
muryar kuka mai cike da bacin rai da qunan zuciya tace
"Shegiya mahaukaciya,wai ina kika shiga ne?!" Ta qarasa fada cikin qaraji wanda banda sautin
tv dake aiki ba abinda zai hana momyn jiyo sautinta.
Haka ta dinga qaramin hauka ita kadai cikin dakin har sha biyu saura na dare sanda wayarta
tahau kuka,ta daukota da hanzari tana tsammanin mima ce,maimakon mima anwar ne,aje
wayar tayi kawai tana kallonta harta qaraci kukanta ta gama,sai daya kira sau uku bata daga ba
tana zaune da kallon wayar ruwan hawaye na fita daga idanunta,tana ganin hakan da zatayi
kawai shine zaisa anwar din ya janye qudurinsa ya haqura shahidan.
Washegari qarfe goma na safe tana gaban mudubi a zaune tana kallon yadda fuskarta ta
qojale saboda kukan data kwana tana yi wayar ta sake burari,wannan karonma anwar ne a
maimakon mima,bata da mafita tilas ta daga wayar ta sake gaya masa kalaman da zasu
tabbatar masa da cewa ta rabu dashi kp hakan zai tsoratashi ya janye nufinsa "Karka sake kirana matsawar kana kan qudurinka na hada aurena da wata macen daban,na
gaya maka tun jiya nikam nafisa bazan aureka ba anwar muddin kana a matsayin mijin mace
biyu,na haqura dakai har abada" daga haka ta yanke kiran,saiya furzar da numfashi daga
bakinsa ya baiwa banza ajiyarta,ya aje wayarshi yaci gaba da shirinsa,shikam ya yankema
ransa babu sauran wata mace da zata sake bashi wahala,bazai sake son wata ba bare ta gasa
mishi zuciya yadda ya faru dashi a baya,ya saki qaramin murmushi sanda ya tuna cewa da
sonta yake da tuni yanzu yana cikin tashin hankali da dimuwa a sanda tace bata sonshi,yanzun
kam hankalinshi kwance yake jinsa,saidai kuma wani bari na zuciyarsa yana dan jin
damuwa,musamman idan ya tuna da mahaifanta yadda zasu dauki maganar,da wannan
tunanin ya gama shirinsa ko abinci yau bai saurara ba ya dauki muqullinsa ya fito,kafin ya tashi
motarsa ya tsaya ya turawa anty usaina yadda sukayi da nafisan,don baison kiranta ma bare ta
bijiro da wani abun da zai hanashi uzurinsa nayau.
***** ****** ****** *****
"Wannan sakarcin banza ne ai sakarcin wofi,ta isa ta haramta abinda Allah ya halatta?" Alhj
abba mahaifin nafisa ya fada cikin fushi da bacin rai yana duban mummy mahaifiyarta,kai ta
gyada itama,sau tari tana mamakin halayen nafisan,ta rasa inda take debo wasu baqaqen
halayen,abubuwa da yawa ita dai ta sani ba halayyarta bace kota mahaifinta ba "Atoh,nayi mata magana daxun da safe ta nunamin tana kan bakanta" mummy ta baiwa alhj
abba amsa,shikam anwar yana daga gefe kanshi a qasa cikin girmamawa yana
saurarensu,baice komai ba sai a sannan
"Kuyi mata uzuri,duba da yadda zancan ya sameta a qurarren lokacin da bata zata ba,ni kaina
bani da masaniyar abun zai kasance haka sai gab da zanyi tafiya,sai naga yafi kyau idan na
dawo na shaida mata mu fahimci juna,to sai kuma aka samu sabanin fahimta"
"Qarancin hankali da tunani dai,ita zata zauna maka da ita?,ko ita haqqin kula da ita yake
kanta?,bilki....kiramin ita maza" a nutse hajiyan ta miqe ta fice zuwa dakin nafisan.
Kwance take rub da ciki tana aikin kuka,tana son anwar tana tsoron rabuwa dashi,tana
tsoron yaqi janye qudurinsa,don itakam ba abinda zai sata ta sauka daga kan
bakanta,matsawar ta yarda ta aureshi to yaqin da tayi shekara da shekaru tana yi,kudinta data
kashe,lokacinta data fansar duka sun tashi a babin badinuhu bataci riba ba kenan "Kin hadu da aiki kuma kin gama kanki da wahala wallahi,tunda kin daukama kanki aqidar
banza da wofi,ki tashi kije mahaifinki nason ganinki" cewar mummy daga haka bata qara ba ta
juya tayi ficewarta.
Sanda ta isa falon anwar ta soma gani,kishinsa ya sake lullubeta ganin yadda kamar ma
sake kyau da fresh yayi abinsa tsakanin kwanakin da ita take fama da quncin zuciya,gefan
abban nata ta zauna ya dubeta
"Nafi,wanne irin shashanci da sakalci kike shirin aikatawa haka?,saboda Allah ya halatta masa
auren daga daya zuwa hudu saikice ba zaki aureshi ba saboda haka?,zaki sauya hukuncin
Allah kenan?,koke kikayi kanki?to kar naji karna gani,banason wannan shirmen banza,yana da
damarma yace biyu zaiyi kece ata uku" Kuka ta saki sosai "Abba...wallahi bazan aureshi ba,bazan iya zama dashi da wata ba"baki bude alhj abba ya
watsa mata daquwa
"Kinci gidanku,kajimin fitinanniyar yarinya?,to saikin aureshin naga wanda ya isa ya hana"
miqewa tayi cikin kuka
"Wallahi abba zan gudu,zan barku idan aka aura min shi" mummy na shirin kai mata duka
saboda takaici ta fice a guje daga falon.
Shuru ne ya ratsa falon,kunya da takaici na kama alhj abba da hajiya bilkisu,sai suka rasa ta
inda zasu kama zancan,sunsan halin nafisa sarai sai addu'a,karta aikata wani abu da zai zama
musu illa nan gaba,anwar ya fahimci shurunsu saboda haka yace
"Alhj,karka damu,Dukkaninmu ni da kai da mummy bamu da ikon da zamu sauya mata
ra'ayi,sannan duk yadda mukaso abin itace zata zauna,dole saida gamsuwarta sannan komai
zai tafi yadda ake buqata"ajiyar zuciya suka saki dukansu kusan a tare cikin bacin rai da takaici
"Yarone ka haifeshi baka haifi halinsa ba,kayi haquri anwar" cewar alhj abba yana jin babu dadi
har cikin ransa,yana jin kaman ya muzanta
"Haka Allah ya qaddara" anwar din ya furta kanshi a qasa,shima yana jin babu dadi saboda
yadda sukejin laifin kaman a kansu yake.
Tana zaune har yanzu inda ta zauna tana rusar kuka a haka mummy ta tura qofar dakin ta
sameta,da hanzari ta daga kai cikin fargaba da razani tare da taraddin furucin da zai fito daga
bakin mummyn,tana son anwar tana fata ace ya karbi muradinta
"Shikenan ko?,burinki ya cika?,saikije ki samo wani mijin wanda yafi anwar" daga haka ta juya
abinta ta fice tabar mata dakin,cikin tashin hankali ta miqe kaman zata bi bayan mommy don
samun qarin bayani,sai kuma ta dawo da baya qwaqwalwarta na gaya mata ma'anar maganar
mummyn,anwar ya barta?,anwar ya zabi shahida akanta?,wahalarta ta tashi a banza
kenan?,kai ta shiga girgizawa tana fadin bazaiyiwu ba,ta dauki wayarta ta soma kiran layin
mima ba qaqqautawa don tana da buqatarta a yau fiye da kullum,saidai amsar dai daya ce
wayar a kashe take.
A qalla ta kwashi awa kusan biyu a haka,bata da wata mafita ayanzu banda ta kira anwar,ta
soma laluben number dinsa ta kira.
Fitowarsa kenan daga kitchen dauke da cup na coffe wanda ya shiga ya hada da
kansa,cikin mamaki yake duban mai kiran,saiya samu daya daga cikin kujerun falon ya zauna
yana amsa wayar
"Ni zaka yiwa haka anwar?,ni nafisa zaka gujewa saboda wata banzar shahida da bata kama
qafata wajen qaunarka ba?,idan baki sani ba bari yau na fada maka,ni nafisa nice silar duk wani
arzqinka,nice silar duk wani matsayi daka taka a yau,nice silar zamantowa abinda kake a
yanxu,amma sakayyar da zaka yimin kenan?,ka zabi wata akaina?" "Kin gama?" Ya furta a nutse yana saurarenta,jin batace komai ba yasa ya dora
"Na farko ba wani bawa daya isa ya azurta wani bawa dukkaninmu muna cine cikin taskar
ubangiji,abu na biyu banyi zabe ba hakan ban fifita ba,kece wadda kika zabarwa kanki haka,ko
a yanxu kika yarda da abinda nazo dashi,kika amince da cewa qaddararmu ce gaba daya ina
maraba da hakan,saboda haka zabi ya rage game shiga rijiya" daga haka ya datse kiran ya aje
wayar gefanshi,yadda yake tsammanin zai damu ko zaiji ciwo saiyaga duka ba haka bane,abu
daya cikin daruruwan daya sanya ya kasa baiwa nafisa koda digo daya cikin dari na so ko
qauna a zuciyarsa kenan,bata da lafazin magana,bata da tarbiyya yiwa kai waigi a duk sanda
rai ya baci,ya godewa Allah daya sanya ya maida dukkan kudaden da kamfani da kuma alhj
abba ya bashi a wancan lokacin ya zabi yaci gashin kanshi ba tarema da yasan waye yayi silar
zuwanshi wajen ba,saiya dauki coffensa a hankali ya soma kurba ba tare daya ji wata
gagarumar damuwa ba.
Kira ya sake shigowa wayar tashi,ya dauka itace dai sai yaga anty usaina,ya amsa wayar
bayan sun gaisa ga gaya masa komai ya kammala kuma jibi ne zasu miqa lefan
"Shikenam babu damuwa,Allah ya nuna mana,saidai na nafisa ki ajesu wajenki,zan shigo gobe
zamuyi magana"
"Allah ya nuna mana" ta amsa masa.
Wayarsa ya dauka yana duba jerin numbers din dake cikin wayar,kaf wayar babu number
dinta,ba abun mamaki bane don yasan dama da zaman hakan,rabonshi da number dinta ta rabi
wayarshi cikin xamanin da yake amfani da waya keypad,wayar da har yanzu bai rabu da ita
ba,hakanan baisan dalilin qin rabuwa da ita ba,saiya koma neman number wayar
sulaiman,bugu uku ya daga,suka gaisa ya gaya masa ya kaiwa daada wayar,ya shaida masa
yana kusa da ita,sabida haka ya miqa mata wayar,bayan sun gaisa cikin mutunta juna sun dan
taba wasa irin na jika da kaka da suke lokaci zuwa lokaci,don jin anwar din take kamar jikanta
na jini
"Jibi xasu miqa kayan daada,na nemi number dinta ban samu ba,ko zaki nemi wani cikin gidan
a shaida masa"
"Karka damu,sule nada lambar zubaida,yanzu zansa ya kirata ya gaya mata" hira suka dan qra
tabawa kadan yana tsokanarta sannan sukayi sallama.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana kurban coffensa idanunsa saman tv da aka ragewa
volume sosai,tunani nason fisgarsa yana jefashi wata duniya can,zamanin da dukkaninsu shida
shahidan keda buri da fatan mallakar junansu,zamanin da kowannensu yake kwana ya kuma
tashi da marari soyayya da begen dan uwanshi,a sannan dukkan mafarkinsu da fatansu ya
ta'allaqa ne akan lokacin da zasu zama mallakin juna,lokacin da dukansu shida ita quruciyarsu
ta ninka ta yanzj qwarai,bai mantawa wani lokaci daya je hira suna hirar qawar shahida da aka
kaiwa lefe,ganin yadda yake nuna buri da fatan yiwa shahidan lefe mai yawa na kece sa'a yasa
tace
"Nifa yaa anwar,basai ka takura kanka ba,nifa ba wani lefe da zakamin,ni ba kaya nakeso ba..."
"Me kikeso...?" Ya fada yana tsareta da ido cikin wani salon kallo da baisan yana mata ba
saboda shagwabarta data tafi dashi,yasandai cewa sanda yake kallonta din soyayyarta da
qaunarta na narkewa tana sake kwaranya cikin magudanan jininsa,kallon da yake mata ya
sanyata jin kunya harta rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana dariya "Kai nakeso ni"
"Na sani shahida,amma kullum burina shine na daga darajar shahida cikin mata,kullum burina
shahida tafi kowacce mace a duniya,indai ina dashi dole shahidana ta fita daban,kita min addu'a
shahida,idan na tashi zan miki lefe irin wanda kowacce mace xatayi burinsa" idanunta ta zaro
tana kallonshi "Ya anwar?,ranar kuwa zanyi bacci?,ya anwar dina yayimin kaya irin haka ranar kowacce mace
saidai ta biyo bayana"
"Qwarai kuwa,wannan dan qaramin bakinkin ya iya furta kalmomi masu zaqi da tsayawa a rai"
dariya sukayi a tare tana kife fuskarta akan cinyarta.
Yana kawowa nan wani qaramin murmushi da bai shirya ba ya subuce saman
fuskarsa,saiya aje cup din,lokaci guda wani abu yayi kutse cikin farincikin daya tsinci kasa,ya
soma juyawa zuwa bacin rai,da sauri ya soma furta la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu
minazzalimin,saiya miqe ya dauki cup dinsa ya haura sama inda bedroom dinsa yake dashi.
***** ******* *********
"Ina kwana anty" shahida ta fada sanda take sanya kanta cikin kitchen tana daura agogon
hannunta,anty zubaida ta amsa hankalinta na wajen siyayyar da akayi mata tana dubawa,sai
data gama daura agogon sannan ta daga kai,turus tayi yadda taga kitchen din ga kacame da
kayyaki "Anty,wadan nan kayan kuma fa?" Ajiye dan qaramin botikin butter din data duba tayi
"Kayan aikin abincin masu kawo lefe ne" wani mummunar faduwar gaba taji ta ziyarceta,duk
wani dan kuzari data samu ta sauko dashi yau ya soma yin nashi waje,saita dan dafe kujerar
dake kusa da ita
"Lefe kuma?" Kai anty zubaida ta kada tana karantarta
"Eh,jiya da dare daada ta gayamin" sai kawai ta kada kai tana qoqarin hadiye wani abu,ba tare
data ce komai ba ta juya ta fice a kitchen din,ko abincin break dake saman tebur bata saurara
ba ta fice daga gidan,ta samu mai adaidatanta na jiranta ta shiga ta zauna yaja suka bar gidan.
Ko data isa office rufe kanta kawai tayi ba tare data bar kowa ya shigo ba,ta rasa shin kuka
zatayi ko kuwa,idan tayi kuka babu mai sauraren kukanta,idan bore zata ci gaba dayi wanda
zatayiwa borenma bata ganshi ba,wannan wanne irin cin zaline anwar ya shiryawa
rayuwarta?,me yasa zai bibiyi rayuwarta da irin wannan sakamakon na daban,tunda bai
ra'ayinta ya barta tayi rayuwarta cikin salama,irin rayuwar da zata samu nutsuwa mana,saiya
shigo don ya rusata?,ya rusa dukkan walwala da farincikin data jima tana tattalinsu da
rainonsu?.
Kusan haka ta wuni cikin kamfanin babu cikakkiyar madafa ko mafita,don haka suna tashi ta
yanke shawarar zuwa gida,donkarta koma ma ta tadda su anty zubaida na aikin kayan masu
kawo lefe,lefen da takeji kamar ta cinnawa mai lefen da lefan kanshi wuta.*AA*
3️⃣2️⃣
Sallama tayi a tsakar gidansu,khadija dake qofar kitchen tana tankadewa umma dake cikin
kitchen garin tuwo ta amsa,a matuqar kasalance kamar wadda tayi aikin shekara ta tsaya da
qofar kitchen din tana gaida umman,ta waiwayo ta dubeta sannan ta amsa tana karantar
yanayinta,khadija na gaidata ta amsa mata tana shigewa falonsu,jakarta ta aje waje daya
sannan ta cire mayafinta ta dora akai,ta samu daya daga cikin kujerun falon ta kwanta tana
sauke numfashi a hsnkali,saita tashi ta sake qaro gudun fankar