Showing 9001 words to 12000 words out of 126208 words
Chapter 4 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf
burin mallaka,macen da cikin dubu
sai an duba.
Tana shiga a nan falo ta ajewa huda ledar,tace ta dauka ta bata,tana jin huda na tsallen
murna da kacaniyar bude ledar tawuce dakinta ta hau sabgar gabanta,duk don ta yakice
komai,wanka ta soma yi,sannan ta jawo plate din abincin data shigo dashi daxu sanda zata fita
wajen nuraddeen din ta soma tsakurar abincin ciki,ci take kawai,amma ko za'a rutsata da
bindiga batasan wanne taste ke ga abincin ba,tana cusa wa ne kawai maganin yunwa,duk
sanda taji irin wannan yanayin tattare da ita tasan cewa can cikin zuciyarta ba lafiya qalau take
ba,ta hanata kanta dukkan wani tunani,ta bude jakar makarantarta ta dauko exams din
dalibanta ta shiga marking tana shigarwa cikin paper din dake dauke da sunayensu.
Tana tsaka da haka wayarta dake aje can gefe ta soma haske,don dama abadan wayarta a
silent take,batason wani qwaqwwaran motsi da xai dameta,daga kai ta dubeta,kamar ba zata
daga ba saita miqe tsam tace ta duba,anty amina sunan dake yawo saman screen din
kenan,dan qaramin murmushi ta saki wanda bai bayyana ba koda saman fuskarta ba bare
mutum ya gane,saida ta bari wayar ta katse da kanta sannan tabi kiran
"Ranki ya dade yallabiya,don naga alama kin xama hukuma saida lallashi,kinbar rayuwar kowa
bare ki nemeshi ko?" Wani murmushin ta kuma saki wanda yafi ja daxu armashi fa bayyana,sai
data koma ta zauna inda ta tashi sannan tace
"Ni na isa,ta yaya zan manta da anty amina ta?" Ta fada tana tura hular kanta zuwa baya,hakan
saiya qara fidda kyanta,sakamakon gashinta mai santsi daya bayyana
"Gashi kuwa?,kin d'aura aniyar mantawa dani din?,anya duniya da amana kuwa shahida?" Duk
sai komai ya tsaye mata cak,duk da cewa gaskiya anty aminan ta fada,abinda bata sani ba tana
gujewa kiranta ko haduwa da itane,saboda tana daga cikin abubuwan dake tuna mata
baya,wanda take ra yaqi shafe komai shekara da shekaru "Yanzu dai ayimin afuww,inayini anty amina mun yini lpy?"ta fadi tana kada biron dake hannunta
hagu da dama
"Lpy alhmdlh....ya gida?"
"Lpy qalau muke,ina yarana?"
"Yaranki duka sunyi fushi" murmushi ta sake saki
"Suyimin afuwa,ina nan zuwa,zuwan ba zata"
"Haka dai,kullum maganar kenan,fafur kin qimu kin gujemu,na rasa ma LAIFIN NA WAYE?" jin
anty aminar nason fadawa wani bigiren na daban ya sanyata soko wata hirar don kauda waccar
maganar
"Zan baku mamaki anty amina,kedai ki sharen hanya"
"Yo sharar hanya kuma ta nawa,na share na share har na gaji,kedai sai an ganki kawai" sai ta
miqawa yaran nata wayar suka shiga gaisawa d'ai d'ai da d'ai,su dinma bikonta sukeyi duk tace
musu tana nan zuwa susha kuruminsu,daga bisani suka miqawa mamarsu wayar suka dan
sake tattaunawa sannan sukayi sallama da juna.
Tana shirin aje wayar wani kiran ya sake shigowa,anty zubaida ce take kiranta
"Ki sameni a falo" ta fada kawai ta yanke kiran,saita sauke wayar daga kunnenta tana miqewa
tsaye ta gyara daurin zaninta,tana zura hijabinta wayar ta sake haske,nuradden ne ke kira saita
dauke kai ta qarasa saita hijabin nata ta fice a falon.
Abbi anty zubaida da huda ne zaune gaban kwanukan abincin,kamar yadda al'adar abbi
take bai hawa dining saidai a sauke masa abinci a qasa a shimfida masa table mat,yanzun ma
abincin suke ci,ta qarasa cikin nutsuwa ta zauna gefan huda tana gida abbun,ya amsa mata
fuska a sake kamar kullum yana tambayarta dalibai,murmushi tayi ta sani sarai baison koyarwar
da take ko kad'an,amma ya haqura ya bata damarta don baison ya tauyeta ko ya hanata abinda
ta zabawa kanta,duk da cewa tana koyarwa ne bisa wani sharadi da bata tunanin ma akwai
randa sharadin zai gindaya yayi sababin afkuwar barinta makarantar
"Wannan kayan da kika baiwa huda fa?" Cewar anty zubaida tana nuna ledar da baki,waiwaya
tayi yana duban ledar don sam ta mance ma tayi kyautarta,kunya ce ta dan kamata ganin kayan
da suke ciki,katuna ne masu dauke da kalaman soyayya sai sauran tarkacen kaya da suka
shafi masoya,idan ma akwai abinda ya shafi huda a ciki bai wuce choculet masu tsada dake ciki
ba,dan satar kallon uncle abbu tayi taga shi sam hankalinshi ma ba'a kansu yake ba,saita
maida wajen antyn
"Ki cire mata choculets din saiki ajemin sauran kayan"
"Eh da yake ni aka bawa ko?,to tattara kayanki ki bar wajen dasu tun ban gayawa abbu abinda
kike yi ba" da hanzari ta miqe tana miqawa anty zubaidan ban haquri da ido,haka ta tattare
kayan tana jin kamar ta watsar dasu a wajen
"Yaushe zakuyi hutu ne khadija?,inason wannan karon kuje kankia kuyiwa su dada hutu,tanata
qorafin kin yada su gaba daya bakya ta tasu"
"Kwana uku ya rage,donma sun tsaya jiran zuwan mai makarantar ne"
"Na qagu abbu ranar tazo wallahi...." Cewar huda cikin zumudi,waiwaya shahida tayi tana
duban hudan,batasan me yasa take yawan zumudi da zuwan mutumin da kowa yake masa
shaidar baida sauqi ko rangwame ba,kamar anty zubaida tasan tadin me take a ranta tace
"Oh hudaaaa...irin wannan zumudi kullum zancanki kenan?"
"Ummi....yana da kirki wallahi,yanasonmu,idan yazo kowa sai an bashi chaculets masu dadi da
biscuits manya manya"
"Sarkin kwadayi...." Abbu ya fada yana lakuce mata baki,dariya sukayi gaba daya
"Ina tunanin randa zakuyi hutu ranar su faruq zasu dawo suma" abbu ya fadi yana zuba lemo a
cup,shahida dake niyyar barin falon ta dakata,fuskarta qunshe da murmushin data kan jima
bata yi ba,tayi kewarsu sosai,duk sanda suka koma makaranta gidan baya mata dadi,tace
"Abbu amma baka gaya mana ba sai yau?" Dubanta yayi,yana mamakin shaquwarsu
"Eh,saiku hanamu sakat da shirin zuwansu,kaman su kadai ne mutane a gidan" ya qarashe
zancan nasa yana duban anty zubaida,tasan sarai su yake tsokana ita da shahida,don haka ta
dauke kai kaman bata jishi ba,murmushi mai sanyi shahida ta saki ta juya tana ci gaba da tafiya
"Allah ya dawo dasu lafiya"
"Amin" ya amsa,huda kam ta kasa zaune ta kasa tsaye,yayun nata kamar qawaye suke a
wajenta,ita daya ce mace banda zuwan shahida gidan itama idan suka koma makarantar ita
kadai ke watangaririya a gidan,saidai idan ta gaji ta gudu gidan kakanninta na wajen uwa.
ν ΌνΌΊν ΌνΌΊν ΌνΌΊν ΌνΌΊν ΌνΌΊν ΌνΌΊν ΌνΌΊν ΌνΌΊν ΌνΌΊν ΌνΌΊ
A nutse yake kai abincin bakinsa,yayin da rabin hankalinsa ke kan wayarsa dake aje gefan
plate dim abincin,zaune take kan kujerar dake fuskantar tasa,tasha kwalliya iyaka,kai kace zata
je wajen wata dinner dinne,cikin dinkin lace riga da skert take,hannayenta gaba daya biyun ta
tallafe kumatunta dasu,yayin data zuba masa idanunta,duk wani wani motsinsa yana yinsa ne
kan idanunta,batasan wanne kalarso take masa ba arayuwa,saidai koma meye tasan cewa son
da take masa wani bangarene mai girma a rayuwarta.
Kanshi ya daga daga wayar yana sake kai wani spoon din abincin bakinsa,sai a sannan ya
lura da irin kallon da take masa
"Hey!" Ya fada yana murza yatsunsa,hannayen ta sauke tana dan qaramin murmushi bayan ta
sauke ajiyar zuciya
"Kallon fa?" Ya tambayeta a taqaice,muryarta cikin rauni da nuna fargaba wanda ya wanzu har
saman fuskarta tace
"Ina tsoron kar na rasaka anwar,ina jin kamar watan watarana zan rasaka" ta fada can qasan
ranta tana jin kishinta na cin zuciyarta,tana jin kamar zata dawo rayuwarshi ta rabasu,ta san
cewa a yanzu sun yiwa rayuwar juna nisa saidai ta kasa samun nutsuwa da kwanciyar hankali
duk da haqarta ta cimma ruwa,aje cup din da yayi niyyar kaiwa bakinsa yayi,ya hade
hannayenshi waje guda gami da saka yatsunsa cikin na juna
"Meye abun jin tsoro a ciki?" Kai ta kada tana gyara zamanta bayan ta goya hannayanta a qirji
"Kai din kalar namijin da kowacce mace keso da buri ne,don me bazanji tsoron kar a rabani
dakai ba?" Bai bata amsa ba sai kofin daya aje dazun yanzu ya sake dauka,yana mamakin
yadda take daukar abubuwan da suka shafe shi da girma haka,saidai har yanzun baya jin wani
feeling na daban ko na musamman tattare da ita,yana dorata ne kawai bisa mizanin wasu
abubuwa da martabarta ke alaqantuwa dasu
"Shine dalilin kenan da kikai qorafi wajen anty hasana?" Ya jefo mata tambayar yana kafeta da
ido,gefe guda kuma yana karantarta a fakaice
"Aure kikeso?" Kai tsaye ta gyada masa kai a sanyaye tana mai fata da addu'ar cikar
burinta,shuru ya ratsa na tsahon minti daya ba tare da wani daga cikinsu yace komai ko yayi
wani qwaqwaqwaran motsi ba,ture kujerar da yake kai yayi baya sannan ya miqe tsaye yana
kwashe wayarshi da muqullin motarsa "Zamuyi magana later" ya fada yana sauka daga step din da dining din yake kai,da hanzari ta
biyoshi a baya tana son tace wani abu,kacibus sukayi da hajiya bilkisu mahaifa ga nafisa,dan
dakatawa yayi kadan cikin girmamawa
"Au harka kammala kenan?"
"Eh zan wuce office ne ana jirana"
"To ko saika dawo din?,da akwai maganar da da nakeso muyi"
"To ba damuwa" ya fada yana ja da baya,ta wuce yabi bayanta zuwa cikin falon.
"Alhaji ne yace na tuntubeka,me zai hana ka dawo cikin gidan nan kaci gaba da zama damu
kamar yadda ake a baya?" Nafisa dake lafe kusa da hajiya bilkisu ta daga kai a hankali tana
satar kallonshi,addu'a take a ranta Allah yasa ya amince da hakan,da tafi kowa jin dadi a
duniya,koda yaushe bata da burin daya wuce ta ganta kusa dashi
"Ayima alhj godiya na gode sosai,saidai yanayin aikina bazai bani damar hakan ba,hakan ma
alhmdlh babu wata a matsala" dan shuru tayi sannan ta jijijjiga kai
"Toh shikenan...babu damuwa Allah ya dafa...."
"Don Allah ya an....." Nafisa tayi hanzarin fada don ba hukuncin dataso anwar din ya yanke
kenan ba,harara hajiya bilkisu ta jefa mata wanda shine silar yankewar sauran maganar
tata,miqewa yayi yayi mata sallama kana ya fice daga falon gaba daya zuwa inda ya aje
motarshi.
"Ke wace iriyar yarinya ce ne nafisa?,bakiji gargadin da nake miki koda yaushe akan ki
dinga kama kanki gaban anwar?,a haka kike tunanin zaki samu qima da daraja wajenshi?"
Langabe kai tayi cikin sigar tausayi tace
"Afwa mom...." Bata sake ce mata komai ba ta gyara zamantabta dauki wayarta ta shiga danne
danne,hakan ya sanya nafisan itama miqewa ta haura sama inda dakinta yake.
Kai tsaye gaban mudubi ta isa ta tsaya sosai tana qarewa kanta kallo,har yau cikin zuciyarta
bata jin ta mallaki anwar yadda takeso,tanaji a jikinta har yau zuciyar anwar ba tata bace,meta
rasa?,meye bata shi?,ta fita komai,ta kere mata a komai,tun daga kyau,kudi zuwa matakin
karatu,amma tana jin har yau kamar ta kashe maciji ne bata sare kanshi ba.
Da hanzari ta koma da baya ta lalubi wayarta dake aje gefan pillow dinta,sai data fara tura
mishi saqo dake qunshe da kalaman soyayya sannan ta lalubi number mema ta kira,bugu hudu
ta d'aga
"Yayinki ake" mema ta fada cikin daga murya mai cakude da dariya dariya,murmushi nafisa ta
saki tana shaf fuskarta zuwa wuyanta,yayin da take sake qarewa kanta kallo a madubi,wannan
kalma na mata dadi,amma gaba daya kaman bata aiki akan anwar,duk da cewa bata da wata
qwaqwqwarar hujja da zata nuna cewa babu sonta cikin zuciyarshi,saidai ita din bata gamsu da
yadda mu'amalarsu ke gudana ba har zuwa yau
"Wannan kalma mema taqi amfani akan anwar har yau"
"Kai haba?,wane mutum?,shi ya isa?,me ya fiki dashi da zai...."
"Dakata mema....kice komai a kaina amma banda akan anwar....mema,ina tunanin mun kashe
maciji ne amma bamu sare kanshi ba,zuciyata da ruhina har yau basu gamsu ba,ta yaya zan
sake binneta da ranta?,ta yaya zan sake b'atar da ita daga duniyarshi?,inason haskena shi
kadai ya wanzu a cikin ruhi da rayuwarshi" "Yanzu me kike tunani?,me kike gani?"
"Ke zanwa wannan tambayar" shuru mema tayi na wasu 'yan sakanni sannan tace
"Alright ina da wadansu 'yan dabaru da shawarwari,amma yanzu bana qasar,ina benin
republic...."
"Ubanme kike jeyi can?,ke mema???" Nafisa ta katse meman cikin zabura,tun kafin ta gama
bayanin nata,dariya mema ta saki sannan tace
"Share kawai"
"Ohk....ya zama dole ki dawo to"
"Saboda me?" Ta fada a dan tsiwace
"Saboda matsalata,kin sani sarai bana son jira?"
"Haba hajiyata....kinsan me ya kawoni nan din?,asara kikeson janyomin kenan"
"Har ta nawa?" Ta tambayeta kai tsaye
"Dubu dari ce ba yawa"
"Zan biya....ki tabbatar gobe kin dawo,wajen yammaci mu hadu a indomie joint"
"Allah ya barmin hajiyata,karkiji komai,bari na fara hada kayana" ta katse wayar yana fadawa
saman katifar dakinta,ba wani benin da taje,ba nisa tayi ba,don a yanzu haka ma tana cikin
katsina.
Aje wayar nafisa tayi,sannan ta juya ta shige bandaki.
Jujjuya wayar yake a hannunshi bayan ya kammala karanta saqon nafisan,sau tari bai fiya
maida mata amsa ba,har hakan ya zame mata jiki bata fiya damuwa ba,har zuciyarshi yake
hakan bawai da gayya bane,bayajin wani abu dangane da duk wata kalma da zata fito daga
bakinta ko ta saqon waya,maida wayar yayi aljihunsa sannan ya fito daga motar tashi ya kashe
ya tunkari ginin kamfanin.*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN
ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*KO KUMA*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da
sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARINGν ½νΉν ΌνΏ½*
ν ½ν±ν ΌνΏ½ν ½ν±ν ΌνΏ½ν ½ν±ν ΌνΏ½ν ½ν±ν ΌνΏ½ν ½ν±ν ΌνΏ½ν ½ν±ν ΌνΏ½ν ½ν±ν ΌνΏ½
https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos
*AA*
0οΈβ£5οΈβ£
Qarfe sha biyu na rana ta duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunta,siririn tsaki taha
qasa qasa,tun daxun ake maimaita magana d'aya taqi ta qare,da d'ai da d'ai d'ai take qarewa
malaman dake zaune a office din shugaban makarantar ana tattauna taron da gobe ne za'a
gabatar a kuma rufe makarantar don tafiya hutun azumi,don tsarin makarantar ne basa karatu
cikin azumi,suna rufe makaranta ne azumi saura sati daya ,su dawo karatu bayan sallah da sati
biyu,caraf idanunsu suka hadu,saita janye tata qwayar idanun taja tsakin a sanda yake jifanta
da murmushi,malam musbahu kenan,mutum daya tak daya takura rayuwarta cikin makarantar
fiye da kowacce halitta,itakam shi da nuraddeen batasan wanda yafi wani naci ba,harma gwara
nuran yakan d'aga mata qafa lokaci zuwa lokaci,tun dazun take jinta not comportable ashe
shike kallonta.
Sake duban agogon nata tayi sannan ta miqe lokaci guda,ta kuma nemi izinin tafiya kan
tana da wani uzuri,babu musu shugabannin sashen secondry dana primary suka bata izini
"Bamuso tafiyarki ba ayanzu miss shahida,saboda yanayin gudunmawar da kike badawa ta
bambanta data kowa" malam musbahu ya fada yana dubanta qasa qasa,bata amsashi ba har
sai data kammala hada takardunta sannan tace
"Ba wanda nafi a nan,kuma duk wata gudunmawa data dace na riga dana bada ita" a nutse ta
juya ta fice bayan tana yunqurin ciro wayarta daga jaka.
Sai data kira anty zubaida ta shaida mata ta wuce gidan anty amina sannan ta tsaida abun
hawa,don idan azumi ya kama bata fita ko ina sai an kammala,in bata jewa anty aminan ba
batasan lokacin zuwanta ba,hakan yasa ta daure zuciyarta ta yanke shawarar gwara taje din
kawai.
Tafiyar minti arba'in kacal daga makarantar zuwa gidan anty aminan,da sallama ta shiga
gidan,saidai hayaniyar yara bai bari anji ba saidata sake wata sallamar,hamida ita ta soma ji,ta
nufi shahida da gudu tana mata oyoyo,kafin kace meye wannan sun lullubeta,qarin tashin
hayaniyarsu shiya ankatar da anty amina dake kitchen tana shirya musu abincin rana saboda
lokacin tafiya islamiyya ya gabato,ta leqo cikin mamaki tana duban shahidan,bata taba
tsammatar ganinta ba,yadda ta saki baki ya bawa shahida dariya,saita murmusa sanda take
ciro alewa daga jakarta tana barewa qaramin yaron anty aminan faisal
"Ku qarasa ciki ina zuwa" ta fada tana komawa kitchen din,da haka suka qarasa falon anty
aminan suka zube kowa na murnan ganinta,sun kasa qarasa shiryawa ma zuwa islamiyyar.
Duk sai data raba musu abinda ta ruqo sannan sukaci gaba da hirar kowa tana biye
dashi,ta jima rabonta da walwala irin haka,tunda can maison yara ce dama ita,hakan yasa taji
wani sukuni na musamman na shiga cikin ranta.
"Yayaa,ina uncle kuwa?,yayimin alqawarin sweet har yau bai dawo ya kawomin ba" sadiq
yaron anty amina ya fada yana saka rigar islamiyyarshi,dai dai sanda anty aminan ta shigo da
plates din abinci,cak shahida taji komai ya tsaya mata,ta kasa hadiye biscuit din data farke cikin
wanda ta kawo musu ta d'an soma ci saboda hamida data takura mata cewa da dad'i,yadda ta
tsaya cak haka anty aminan ta tsaya tana dubanta,don tasan saddiq ya b'arota,yayin da sauran
yaran duk suka zuba mata idanu suna sauraren amsarta,don gaba dayansu suna da buqatar
sanin dalilin daina ganinsa dare d'aya lokaci daya kuma gaba d'aya
"Ya mutu" furucin ya fito daga bakinta kamar mai ciwon baki,idanunta kan saddiq wanda ya
kasa qarasa saka rigar tashi jin abinda shahidan ta fada,harga Allah tana daukarshi tamkar
matacce ne a ruhi da zuciyarta,duk da dama ya dade da mutuwa a cikin tata zuciyar
"Ya mutu yayaa?"saddiqa ta fada tana zaro idanu,alhini da mamaki ya bayyana qarara kan
fuskar yaran gaba daya
"Kai banason dogon surutu,ke hamida dauki abincinku ki kai muku dakinku kuci a can ku shirya
maza ku fice ku bani waje" cewar anty amina tana musu wuta wuta,don tasan tabbas ba
qaramin furuci bane wannan a wajensu,duba da yanayin sabo dake tsakaninsu dashi,c gaba fa
maganar kuma dai dai yake da hargitsa lissafin shahida da dukkan walwalar data samu cikin
gidan,hakanan yaran suka dinga fita daga dakin jikinsu a matuqar sanyaye.
Sai da suka gama fita gaba daya sannan anty amina ta qarasa kusa da shahida ta aje
kwanon abincin idanunta na kan shahida data sauke kanta qasa
"Har sai yaushe shahida zakici gaba da rayuwarki kamar kowa?,sai yaushe zaki maida abinda
ya faru kaman bai faru ba?,yaushe zaki rufe wannan tarihin daga babin rayuwarki?,me yasa
wannan lamarin