Showing 24001 words to 27000 words out of 126208 words

Chapter 9 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf

kallon yadda suke dagawa juna murya
kamar zasu yagi juna,batasan lokacin da wani hawayen baqinciki ya sauko mata ba,baqinciki
da b'acin rai ya bata dukkan wani farinciki data tsinci kanta a ciki,wannan wacce irin rayuwa
ce?,ina zata je ta daina ganin wannan baqincikin da bacin ran?,tabbas da akwai inda zata ta
qauracewa wannan masifar da tuni ta jima da tafiya,tana son mamarta,hakanan tana son
bananta,duk cikinsu babu wanda take goyon baya a cikinsu,batasan me yasa suka zabi wannan
rayuwar ba bayan ga zuria suna tarawa,hakanan kowa yayi musu shaidar kyakkyawar
mu'amala a waje amma me yasa gidan aurensu ya gurbace haka kamar sansanin yaqi?,haka ta
zauna cikin dakin ita d'aya tana rusar kuka harta gaji da jin sautukansu ta dannan kanta
qarqashin filo tana ci gaba da zubda ruwan hawaye.

Kamar kowanne lokaci yauma ta shirya tsaf cikin atamfa riga da zani,sai hijabi mai hannu
da yasha guga,kasancewar ummanta mai tsafta ce,hakan ya sanya dukka yaranta tun daga kan
shahida zuwa faruqu zaka samesu fes dasu,hakanan ma gidanta da duk abinda ya shafi
gidan,sosai higabi mai madauri purpule colour yayi mata kyau sosai,yau shigar ta musamman
ce ita kanta tana jin hakan a jikinta,yau mai d'aukar matan bai qaraso ba tilas tadan zauna jiran
zuwansa,tun tana jin ba komai harta soma qaguwa,haka kawai taji ra zaqu taje wajen,ta leqo
agogo yafi sau nawa amma shuru yaron bai iso ba,saita kasa zama taci gaba da duba agogo
har ummanta ta fuskanci haka,iya saninta shahida na zuwa kai sadakar abincin nan ne don
kawai tana tsananin jin nauyin uncle isma'il,kusan kullum fuska a hade take tafiya a haka kuma
take dawowa
"Ya akayi ne shahida?,ko tsoron makara islamiyya kike?" Cikin rashin jin dadin ranta ta kada
kanta
"Toko yau zaki zauna kawai idan yazo saiya kai shi?"
"A'ah umma....zan kai bari dai yaxo din" ta fada da hanzari,don bata jin zata iya jurewa rashin
zuwanta wajen
"To ai shikenan" umman tata ta fada tana kwashe shanyar kayan sawarsu da shahidan ta gama
wankewa daxu,ciki harda ba mahaifinta don sam bata da quya ko gandar aiki.

Yana isowa ko zama bata barshi yayi ba ta sakashi ya dauka suka wuce,sai taga kaman

bata sauri,kamar tabar wani yana jiranta,haka dinga ji har suka isa wajen.

Daga nashi bangare shima har ya soma tunanin me ya hanata zuwa har yanzu?,yana daga
zaune cikin shagon bala yana duba agogon wayarshi,sama sama yake amsawa bala hirarsa,ya
daga kai don sake kallon muhallin da take zama din sai yaga isowarta,wata ajiyar zuciya ya
sauke ya zuba mata ido daga inda yake,kaman ance mata ta waiwayo sai suka hada ido,ta
danso ta dirirce amma saita maze,ta samu waje ta zauna yayin da kowa ya soma fitowa da
kwanonshi yana amsa.

Duk motsin da take sai taji kama idanunsa ne a kanta,eh ba kama bane kallon nata yake,a
yau ya hana kansa kallonta,duk da ta kamashi yana kallon nata yafi sau shurin masaki amma
ya gaza dainawa,haka suka dinga hada ido lokaci zuwa lokaci har abincin ya qare,hakanan yau
take jin wani faduwar gaba,ta dinga hada kwanukanta da sauri tana son yau ta bace
masa,saidai burinta bai cika ba,tana gama hadawar ya iso wajen,ya dauki botikin ya soma
takawa,bata da abinyi illa binsa.

Suna isa inda suka saba ta zaci zaiyi yadda ya saba,amma ga sabanin tunaninta wannan
karon sai yaja ya tsaya tsam yana riqe da botikin
"Baki da kirki" taji ya ambata,ba shiri ta dago suka hada ido,qwayar idonta cikin nasa,yayi.mata
wani kallo fuskarsa dauke da murmushin da yasa gudun zuciyarta qaruwa,cikin hanzari ta
sadda kanta jin yadda yake shirin karya lagonta cikin qaramin lokaci
"Nima na san haka ko baka fada ba....kayi haquri.....na gode da karamcin daka yimin harna
tsahon kwana hudu,Allah ya saka maka da alkhairi"
"Amin...amma bawai kyauta nayimiki ba,nayi miki ne donki biyani" ya fada cikin salon tsokana,a
nata bangaren ta zata da gaske yake,take mummunan tunani ya darsu a ranta game
dashi,baya ta danja kadan sannan tace
"Ni bani da kudin biyanka,tun farko ma bansan biyanka kakeso nayiba da nace ka barshi" kai
yake girgixawa dariya nason subuce masa,dariyar data qara masa kyau har tasa adam apple
dinsa ya dinga motsawa
"Ba kudi nakeso ba 'yammata....zuciyarki kawai nakeso ki mallaka min" ya tsinci kansa da
fada,don ya shagalta da kallonta har baisan maganar da yake qasan zuciyarshi ya bayyana
ba,a bazata taji maganar,don bata taba tsayawa ga da ga wani namiji ya gaya mata hakan ba
ita dashi baki da baki sai wannan karon,ganin ta riga dataji me yake fada ya sanyashi kada
kanshi yana ci gaba da jifanta da murmushi
"Eh zuciyarki nakeso" cikin mintina qalilan kwanyarta ta hakaito mata abinda yake nufi,wata
iriyar kunya da nauyi suka kamata,ta rasa tudun dafaww,saboda haka saita juya gudu gudu
sauri sauri ta shige gida,yana tsaya mana amma ina ba zata iya ba,bata taba zaton a
shekarunta sha biyar akwai saurayin da zai gaya mata wai yana sonta ba,kalmar tayi mata
nauyi da yawa.

Murmushin jin dadi ya saki,ya zauna dakalin dake daura da gidansu,abinka da d'an
makaranta ba'a rabashi da takarda,sai ya ciro qaramar jotter din dake aljihun wandonshi wanda
ya gama duba wani karatu da ita yayi rubutu da basu wuce layi goma ba ya jefa cikin botikin,ya

kira yaro ya bashi botikin shi kuma ya wuce.


*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI
SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*KO KUMA*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da
sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*


https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos[7/1, 9:18 AM] يتخا
ةصفخ: *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI
SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*KO KUMA*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da
sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*


https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos


*Alqawarin Allah*
0️⃣7️⃣

Saida umma ta dinga qwala mata kira kan ta fito ta wanke kwanukan ta dauki abincinta taci
kada lokacin islamiyya ya wuce sannan ta taso daga rub da cikin da tayi saman katifarta,ta
harhada kwanukan ta kada ruwan kumfa ta soma sabesu,tanayi tana tunanin kalmar daya furta
mata,ashe kalma ce mai nauyu da dadi haka,lokaci lokaci ta dinga sakin murmushi ita
daya,harta zubawa botikin ruwa ta zubda ruwan sai taga takardar,ta tsame hannunta cikin
kumfar ta dauki takardar sannan ta bude.

Soma fahimta da tayi takardar meye yasa tayi sauri ta shige dakinta,ta samu kebantaccen
waje ta budeta inda zata sha iska ta bushe sosai sannan ta dawo taci gaba da wanke
wankenta.

Kafin ta kammala shirin islamiyyarta saiga qawarta zunnurah ta iso cikin unifoarm din
islamiyya
"Yauwa,dama banason cin abincin nan ni kadai,don Allah bari na dauko ki tayani" cewar
shahida tana nufar kitchen ta fito da kwanon abincinta ta aje a qasa ta zauna dirshan
"Sauko malama muci"
"Ke nifa a qoshe nake wallahi ba abincin da zan iya ci"
"Ni zakima wulaqanci ko?,zaki sake cewa naci abinci a gidanku" tq fada tana saka hannu tayi
bismillah ta soma ci zunnurah na mata dariya,wai ita zata cewa tana cin abincin gidansu,matar
da nata abincin ma sai ya huce bata ci ba,hira suke jifa jifa shahida nacin abincin tana kuma
duba lokaci kada a fito saga sallah a shiga aji basu tafi ba,saidai rabi da rabin hankalinta nakan
takardarta dake shan iska
"Yauwa shahida....wai waye wanda yake rakoki ne kullum daga wajen sadaka" tsaida lomar da
zata saka a bakinta tayi tana duban zunnuran
"Au har kin samu labari kema?" Harara ta watsa mata
"Uwar labari na samu,waye baya ganinku a tare wai kwana hudu kenan,tunda ansan baki kula
kowa...."
"K'nnnn...nima ban sanshi ba wallahi zunnurah,acan nake ganinsa" dariya zunnurah ta saki
"Qawata nasan halinki sarai,duk yadda akai wannan din na dabanne tunda har kika kasa gwada
masa halinki" murmushi ta saka,ita kanta tasan na daban dinne nasai zunnurah ta fada ba,tun
kallon farko taji yakai mata ko ina,ganin farko taji wani qaqqarfan lamari dangane dashi,takan
iya raba dare tana tunaninsa,kowanne second nata da tunaninsa take rayuwa "Amma fa kinsan shaik hafiz zai shiga wani hali?" Dagowa tayi tana duban zunnurah kafin ta
galla mata harara
"Kamar yaya?,sonshi nake?,ko ce miki yayi yana sona" nan ta zauna tsaf ta kwashe mata
yadda dukkan dalibai suka lura da soyayyar da yake mata,baki ta tabe tana miqewa daga
gaban kwanon,don ita dai tasan ko doguwar magana bata hadata dashi bare kuma wani abu
daban can,fita tayi ta wanke hannunta ta dawo tana ware gogaggen hijabinta "Qawata baki da mutunci fa,shaik ke kanki kinsan yammatan makaranta rububinsa suke,kuma
kema kanki qaryarki kice baki san yana sonki ba,maimakon kiyi murna sainaga ke ko a jikinki
labarin bai faranta miki ba ko d'aya"
"Don Allah zunnurah ki qyaleni da zancansa,sai....." Maganar tata ta katse jin sallamar
fiddausi,yarinyar da tsakanin gidansu shahida da nasu gidan layi biyu ne,tun zuwanta
islamiyyarsu shahida takeson qawance da ita,tun shahidan na janyewa harta saki jiki da
ita,saboda ta lura yarinyar itama nada hankali,yawan shuru shuru da rashin son hayaniya.
Tuni zunnurah ta hade rai,hakanan a duniya taji sam fiddausi bata yi mata ba,ko kadan
jininsu ya kasa haduwa,shahida ta rasa dalili,tun tana sharewa har tazo tanawa zunnurah fadan
ta daina haka,wulaqanta dan adam babu kyau,yarinyar na sonsu hakanan bata da wata matsala
meye abun sha mata qamshi da take

"Hakanan wallahi nidai naji batayimin ba" amsar da zunnurah ta baiwa shahida kenan.

A tsakar gida fiddausi ta duqa ta gaida umma cikin ladabi,ta amsa ba tare data tsaya ta mata
wani cikakken kallo ba taci gaba da sabgoginta(babban kuskure na biyu da ummanta ta sake
tafkawa bayan fada da miji gaban 'ya'ya),fiddausi ta shige dakin shahida,cikin fara'a suka gaisa
ita da shahida,yayin da xunnurah ta kauda kai ta amsawa fiddausin sama sama,dif zunnurah
tayi sai shahidan da fiddausi dake hira sama sama,har shahida ta gama shiryawa suka fice
daga gidan.

Suna gab da shiga gate din makarantar xunnurah ta kamo hannun shahida tayi baya da
ita,duk sai suka tsaya ta hade gira tace da fiddausi
"Me kike jira?,magana zamuyi da ita" sum sum fiddausi ta juya ta wuce ciki
"Wai me yasa kikeson koyon halin daba naki ba zunnurah me fiddausi tayi miki?"
"Shahida,ba haka kawai naji banson yarinyar nan ba,an bani labari fiddausi tana taba shaye
shaye..." Rufe bakinta shahida tayi da hannu tana kallon zunnurah gami da zaro ido
"Haba zunnurah,haba,zato fa ance zunubi ne,ya zaki jefeta da wannan mummunan kalmar don
kawai tana son mu'amala damu?"
"Da gaske nake miki shahida,daga bakin namiji na samu wannan labarin,kinsan kuwa su basu
fiye munafunci kosa ido ba bare kice,sannan kuma idan zaki lura da kyau zaki ga yanayin
fiddausi ba irin namu bane,yawan bacci da kasala kawai alamune na mutum yana taba shaye
shaye,zaman kadaici rashin so magana da yawa" zame hannunta shahida tayi daga na
zunnurah,don sosai taji babu dadi ta kuma ji ranta ya baci
"Duk abinda kika fada zunnurah baki da tabbaci a kanshi,karki fadi abinda zaki jawo a tsaidaki a
miki hisabi ran gobe qiyama,ni fiddausi ta gayamin bata da cikakkiyar lafiya,tana da sicklier shi
yasa take yawan bacci" kada kai zunnurah tayi
"Shikenan shahida tunda baki yadda dani ba,kinfi kowa amma sanin halina,nidai ina baki
shawara kibi a hankali,don bazanso abinda zai cutar dake ba"
"Babu abinda zai faru in sha Allahu" daga wannan suka rankaya suka shige cikin makarantar.

Washegari da wuri taje wajen bada sadaka ba kamar yadda ta saba zuwa ba,hakanan
takejin wani nauyi da kunya tunda ta karanta kalaman da yarubuta mata jikin takarda,niyyarta
tayi da wuri ta koma gida ba tare daya sameta ba,saidai abinda bata sani ba tuni ya rugata ma
zuwa,saboda gaba daya ya rasa nutsuwarshi Allah Allah yake gari ya waye yamma tayi yaje ya
ganta,bai taba tsintar kansa cikin irin wannan yanayin ba,duk yanayin rayuwa da yake ciki
hakan bai hanashi bacci ba,sai gashi a karon farko saboda ita ya kasa bacci daren ranar gaba
daya,duk juyin da zaiyi itace cikin ranshi.

Yana biye da ita bata sani ba,baiyi mata magana ba saida suka gota wajen suka shiga wani
layi
"Yanzu yau kuma haramiyar ladan rakiyar za'a yimin?,wanne irin laifi nayi haka?" Cak ta
tsaya,farinciki da kuma faduwar gaba na cakuduwa cikin ranta,idanunta a waje har ya iso
gabanta yasa hannu ya amshi botikin,ya jera kafada da ita
"Muje" ya fada cikin sassanyar muryarta da kullum take mamakin dad'in muryar da Allah ya

bashi,idan yana magana dole sound dinshi yaja hankalin duk mai sauraro,yau saitakejin nauyin
tafiya dashi,ta kasa yin gaba,ya sake dubanta
"Waiko amsar tambayata itace a'ah akemin irin hakane" wani wal tayi da ido,saiya dafe qirjinsa
da hannunsa daya
"Kiyi haquri karki qarasa tarwatsamin zuciya,wannan zuciyar mai rauni ce akanki"

Fuskarta ta qunshe cikin hijabinta tana dariya qasa qasa,wawiyar ajiyar zuciya ya saki
"Wai Allah na,alhmdlh,ko iya haka aka tsaya na tabbatar da cewa ina da nasara...amma dai a
gayamin ana sona?" Kai ta kada cike da tsananin kunyarsa,wani dan tsalle ya saka sannan
yace
"Alhmdlh,alhmdlh" yana rungume da hannayensa.

A hankali suka ci gaba da takawa shida ita,saidai ita gaba daya nauyinsa takeji,yayin da shi
kuma yake janta da hira jefi jefi,yau duk masu binsu da kallo mutanen cikin unguwarsu basu
dameta ba,har sai taji ma batason su isa gida yace zai wuce.

"Kina son wanda bakisan sunanshi ba hakanan bakisan waye shi ba" ya fada bayan ya
miqa mata botikinta,ita sam bata damu da wayeshi ba,sonsa takeji irin wanda bata taba zata ko
tsammatar akwai irinsa ba a duniya,tanajin koma wayeshi yayi mata hakan
"Ni sunana muhammad anwar aminu,haifaffen kano ne kuma dan kusa da unguwarku ne
ni,maraya ne ni bani da uwa bani da uba,sai 'yar uwata d'aya data ragemin anty usaina,ina
karatu ne a fce kano...kefa?,shahida ko?" Murmushi ta saki tana dubanshi cikin tausayi jin cewa
maraya ne,kai ta kada sannan tace "Khadija amma shahida,nice ta farko wajen umma da abbana,ina da qanne hudu,nan ne
gidanmu a nan aka haifeni,ina SS 2 yanzu" kai ya kada sannan yace
"Idan nazo anjima za'a barni na ganki" kai ta gyada da sauri,don tasan yadda zatawa ummanta
bayani yadda zata fahimta
"Shikenan zanzo anjima in sha Allahu,inason mu soma mu'amala cikin fahimtar juna gaskiya da
amana...ki shiga gida lokacin islamiyya ya kusa ko?"
"Na gode" ta furta cikin siririyar muryarta data dauki hankalinsa,kai kawai ya iya gyadawa ya
bita da kallo harta shige.

"Waye a waje kuke tsaye dashi?" Tambayar da ummanta ta soma jefo mata kenan sanda ta
aje botikin tana shirin zama,kunya ta d'anji ta kamata,saita kasa amsa mata da wuri har sai data
maimaita
"Ba kowa umm,yadai taba rakoni gida sanda su ahmadi suka fasamin botiki,shine...shine...."
Saita kasa qarasawa,murmushi kadan ummantata tayi,saboda burinta bai wuce su aurar da
shahida ba da zarar ta kammala secondry schl,ita kanta tasan basa kyauta mata yadda koda
yaushe suke cikin fada da juna suna sakata kuka qunci da baqinciki "Shine me?" Ta sake tambayarta tana tura mata kwanon da tayi kwadon zogale ta rage mata
saboda tasan tana sonshi,sai data sadda kai sannan tace
"Shine yace wai anjima zaizo idan za'a barni na fita"
"Allah ya kaimu" ta fada tana miqewa don ta wanko hannunta,cikin farinciki taja kwanon ta soma

cin zogalenta,wanda tana gamawa ta shige bandaki ta sake watsa ruwa saboda ranar da
ake,fitowarta kenan daga bandaki dauke kwandon wanka zunnurah ta iso,tana shiryawa tace
"Zunnu...akwai labari fa yau"bakin zunnnura a washe tace
" ta samu kenan?"kidai muje na baki kisha,ta fada tana zura plate shoes dinta,ta dauki jakarta
suka leqa suka yiwa umma sallama suka wuce.

A hanya ta labartawa zunnurah komai,dariya ta dinga
"Kai amma wannan gayen yayi addu'a tuquru kafin yazo,shahida da babu wanda ya isheta
kallo?,da kinga wata da saurayi ma zakice wannan ai iskamci ne dududu shekarunmu
nawa?,ashe harkin girma" dundu ta dumawa zunnurah
"Banason iskanci qawa,wallahi nayi mamaki nima sosai,dama haka abun yake?,kinji kuwa
yadda nakejinsa a raina?,har banason mu rabu,idan yana kallona wlh zunnurah ni kadai nasan
me nake ji a zuciyata,ban taba tsammanin akwai wani da zanji haka a kansa ba" dariya
zunnurah taketa tiqawa "Na shiga uku ni zunnu,sati daya kacal amma shine kika zare haka?,Allah yasa to nan gaba kar
ya haukatamin qawa ya cuceni"
"Ba komai idan ya haukataninma zunnu" ta fada tana tayata dariyar,gab da zasu shiga
makarantar sukayi kacibus da fiddausi,da fara'arta take musu magana amma shahida ce kawai
ta amsa suka rankaya suka shige makarantar tare.

Tunda ta dawo daga islamiyya ta kasa zaune ta kasa tsaye,qiyasta da qimanta yadda
haduwarsu zata kasance take,wannan ne karon farko data soma son wani a rayuwarta,kuma
karon farko da zata fara tsayawa zance da wani.

Tuni ummanta ta yiwa babanta bayani,bai kuma ce komai ba,illa ya kirata ya masa
tambayoyi game da shi,ta bashi amsa gwargwadon abinda ta sani game dashi,yace ta kula
kuma idan sun fahimci juna zaiyi magana da yaron.

Ba wani kwalliya tayi ba,tadai saka kayanta masu kyau atamfa riga da skert,ta kuma yafa
wadataccen mayafinta,sanda ya aiko kiranta tare da mubina suka fita,yana zaune saman
yalwataccen dakalin qofar gidansu,daga soron ta tsaya tana qare masa kallo,yayi kyau sosai
fiye da dazun cikin qananun kaya,iya kwanakin kadai da tayi tana ganinsa ya tabbatar da cewa
shi din dan gayune kuma mutum mai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login