Showing 1 words to 3000 words out of 92754 words

Chapter 1 - YAYI SAKE COMPLETE BY A'ISHA A MUHD-1.pdf

10 Jul 2025

2453

[13/11, 2:03 p.m.] Aysher Muhd Writr: ν ΌνΌ² *YAYI SAKE*ν ΌνΌ²



*written by*

Aishat A muh'd

β™» *E.W.F*



*BISSMILLAHIR RAHMANUR RAHIM*
( _Da sunan Allah mai rahma mai jin k'ai_).




*Page 1*



K'was K'was K'was k'arar takalmin ta ya karad'e cikin babban hall di'n da suke d'aukan lecture's, tun
Kafin ta k'araso cikin hall di'n k'amshin turaren jikin ta ya cika cikin ajin, gaba d'aya kusan ilahirin
student's di'n suka d'ago kansu tare da mayar da hankalin su kan mai Shigowar malamin da yake musu
lecturing di'n shi kanshi jiran wacce mara kunyar ce take kok'arin shigo mishi aji bayan ya kafa dokar hana
shiga cikin ajin indai ya riga d'aya daga cikin student d'in shiga.

Kusan second biyar wata kyakykyawar yarinya ta bayyana cikin ajin kunnen ta mak'ale da waya tana
faman tauna chewing gum a bakin ta tana amsa wayar, tana sanye cikin wani less cotton milk colour da
touch d'in pink a jiki anyi mishi wani shegen d'inki riga da siket ta yafa wani k'aramin mayafi da takalmin
ta hill dashi tasha heavy makeup kamar wata aljana, ta had'u iya had'u wa *MUFIDAH EL HUSSEIN*
kenan, ko kallon inda malamin yake bata yi ba ta nufi inda ta sa ba xama cikin wata kakkausar murya taji
ance
" hey you get out!"
Yanda ya buga tsawa shi yasa hankalin sauran d'aliban ya dawo kan malamin gaba d'ayan su a tsorace
suke, wadda aka buga wa tsawar bata ma san me yake cewa ba sai da k'awar ta nabeelah ta xungure ta
tare da yi mata alama da hannu, wani irin juyi tayi tare da bin shi da wani matsiyacin kallo.

Shima cikin kallon wulakanci yake bin ta dashi tare da sake furta " i said get out don't west my time"

Cikin muryar ta mai shegen dad'i da yanayin shagwa6a a cikin muryar tace "Ohh! dani kake wai? "

Wata harara ya xabga mata tare da yi mata nuni da hannu kan ta fita don ya k'ulu iya k'ulu wa da yarinyar
sosai ya fusata da abin da tayi mishi tuni fuskar shi ta yi ja saboda tsantsar 6acin rai, cikin isgili tace
"sorry sir "
Ta fad'i tana wani langa6e kai gefe tana Mishi irin wani kallo na raini, shi ma a wulakanci ya kalle ta tare
da fad'in
"idan baki fita wlh xan miki rashin mutunci "

Hura hanci ta fara alamar kaxo gidan Indai rashin mutunci ne ta iya shi, ajin dai yayi tsit kamar ba mutane
d'aliban sai faman raba ido suke tsakanin junan su da kuma mufidah da malam suna jiran ganin K'arshen
dramar nan.

Had'a ido mufidah tayi da nabeelah tayi mata alamar don Allah ta fita d'an hararar ta tayi kafin kuma ta
fara tafiya alamar xata fita daga ajin, ta gaban shi ta shige tana tafiar kasaita bak'in ciki ya gama rufe shi

ganin wannan K'aramar yarinyar tana kok'arin wulak'anta shi a gaban d'aliban shi da suke ganin
mutuncin shi wani mtswww yaja wani uban tsaki tare da bin ta da harara kamar idon shi ya fad'o k'asa.

Bayan fitar ta ya ma kasa cigaba da lecturing di'n saboda ranshi a matuk'ar 6ace yake, wani d'an tunani
yayi na tsayin second uku take ya saki wani shegen murmishin mugunta nan ya rubuta musu test, nan
cikin d'aliban ya d'uri ruwa don wlh basu xaci xai musu test yanxu ba, kowa jiki a sanyaye ya xaro paper
da biro, yayin da nabilah ta d'ora hannu akai Shikenan yanxu wannan test d'in ta shige mufidah gashi
tana bala'in tsoron malamin balle tayi mata hka jiki a sanyaye ta fara rubuta text d'in.

Cikin mintuna talatin ya tattara test d'in yayi gaba a fusace fuskar nan babu alamar fara'a a cikin ta.

Ta gaban mufidah ya shige da take xaune kan mota tana mak'ale da headphone tana sauraren wak'ar
Justin Bieber ta love me love me har wani gid'a kai take saboda son wak'ar da take bata ma kula da
shigewar shi ba idanun ta a lumshe suke.

Tana cikin hka taji an doke ta a cinya da sauri ta bud'e idon tare da furta "wash Allah na nabilah me nayi
miki? ", ta fad'i tana kallon nabilah da take hararar ta
"baki da kirki k'awata yanxu kin kyauta abin da kika yi? "Cewar nabilah
Mtswww mufidah ta saki tsaki tare da cewa "Wannan ke ya dama ba abin da ya dame ni "

"baki da kyau k'awata ai kuwa kin fusata shi, gashi yayi test wlh "

D'aga kafad'a mufidah tayi alamar ko ajikin ta Kafin tace "ae Allah sai na dai dai ta mishi sahu a skul d'in
nan "

Dariya suka tuntsire da ita tare da tafawa can mufidah ta sakko daga saman motar tare da cewa "mu
ware koh nabilah? "
"yes kamar Kinsan a gajiye nake "

Daga hka suka shiga motar mufidah ta yiwa motar key suka fice daga skul d'in suna faman hira har sai da
ta sauke nabila a gidan su tukunna ta shige nasu gidan.

Tun Kafin ta k'araso dai dai get d'in take faman xuba uban horn don ta tsani jira, ai kuwa mai gadi cikin
rawar jiki ya bud'e mata get d'in ta danna hancin motar xuwa cikin k'ayataccen gidan parking tayi sannan
ta nufi cikin gidan.

Belt door di'n gidan ta danna da sauri house girl din gidan taxo ta bud'e tare da russuna wa tace "Barka
da dawo wa aunty "
Cikin d'an murmishi tace "Yawwa saudat ki kawo min hollandian milk mai sauk'in sanyi "
Cikin girmama wa saudat mai aiki tace "toh aunty "

Sannan ta shige da sauri ta nufi kitchen, yayin da mufidah ta K'arasa cikin falon umman ta ta gani xaune
tana kallon sunnah tv da sauri taje ta rungume ta tana cewa "i miss u umma nah "
Cikin jin dad'i umma tace " i miss u too my sweetheart, ya skul?"
"lau ummah "

"Yayi kyau ina nabila" umma tace cikin murmishi, cikin murmishi ita ma mufidah tace "yanxu na sauke ta
a gida tana gaida ke "
"ina amsawa "

A dai dai lokacin saudat ta kawo wa mufidah hollandian di'n sai da ta xuba mata tare da mik'a mata
sannan ta bar wajen, tana sha suna cigaba da hira da umman tah............

Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:03 p.m.] Aysher Muhd Writr: ν ΌνΌ² *YAYI SAKE*ν ΌνΌ²



*written by*
Aishat A muh'd

β™» *E.W.F*



_wannan shafin sadaukarwa ce ga en exclusive writers forum Allah ya k'ara had'e kan mu ya k'ara mana
basirah tare da dukka marubatan mu Ameeen_


*Page 2*



A fusace ya tura kofar shiga palon gidan ko sallama a ciki ciki yayi ta ba lallai ma a ji ba ko kula da
wad'anda suke xaune a falon bai yi ba ya fara hawa upstairs ya taka mattatakala ta biyu yaji ance
"my bro wane ya ta6a min kai yau? "
Cikin sauri ya jiyo aikuwa suka had'a ido da Yah sadeeq ai kuwa da sauri ya taho har da d'an had'a wa da
gudu ya rungume yayan nashi wanda yau kusan tsayin Sati biyu rabon da su ga juna sai dai waya cikin
tsananin murna yace
"Yah sadeeq xuwan yaushe? "

"xuwan shi kenan tun da ganin yayan na ka ka mance dani " Cewar mumyn su kenan da take xaune, sosa
kai yayi cikin shagwa6a yace "Haba mumy taya xan manta da ke just ina farincikin ganin brother ne"

Nan kuma suka 6arke da hira a tsakanin su irin ta yaya da k'anin shi xuciyoyin su cike da tarin farinciki duk
da shi ranshi a 6ace yake game da abin da yarinyar nan tayi mishi, kuma ya d'auki alk'awarin sai ya
wulak'anta ta.



_Bayan k'wana biyu_

Yammaci sosai wajen misalin karfe 5 na yamma mufidah da nabilah suka yi parking a wani had'ad'd'an
restaurant wanda yawancin suke cin kayan mak'ulashe a wajen don akwai su da shegen kwad'ayi, gashi
restaurant ba irin abincin da babu shi anan shi yasa suke samun costumers ta ko'ina.

Bayan sun xauna suna er hirar su har aka kawo musu abin da suke son ci bayan sun gama ci ne mufidah
ta Kalli nabilah tace

"yanxu karfe nawa ne don Allah? "
"tabbb Kya tambaye ni bayan duk wayar namu na cikin mota "Cewar nabila
Dafe goshi mufidah tayi tare da cewa "oh my god gashi ko watch bamu d'aura ba, don Allah kije ki d'auko
mana "

Hararar ta nabila tayi tare da cewa " lallai ma yarinyar nan ni zaki aika, idan kin matsu da ganin time d'in
kije ki d'auko ko kuma mu tafi ae mun gama komai "

D'an murgud'a baki mufidah tayi tare da cewa "kada ki d'auko di'n, kuma banyi ra'ayin tafiya yanxu ba "

"toh ae shikenan daman ke kika matsu da ganin lokacin "fad'ar nabila tana kur6ar sansanyan juice di'n
pineapple da yake gabanta cikin glass cup.

Yayin da mufidah ta fara wurwurga idanun ta kan mutanen wajen, karaf idanun ta suka sauka kan wani
kyakykyawan guy ya sunkuyar da kanshi yana kallon k'asa yana sanye cikin blue d'in jeans da red d'in
T-shirt mai dogon hannu sosai guy d'in ya had'u ba k'arya duk da bata ga fuskar shi ba idanun tane ya
sauka akan wayar dake hannun shi yana lallatsa wa ganin hka yasa mufidah mik'e wa tsaye tare da cewa
"nabila bari naje wajen wancan guy d'in naga time Kinsan 5:40 nake son mu bar nan "

Kafin nabila ta bata amsa tayi gaba kawai sai ta bita da kallo watak'ila tsokana xata yi Indai tsokana ce
mufidah ta K'ware a wajen.

K'arasa wa tayi wurin ba sallama ko irin excuse di'n nan kawai tasa hannu ta kar6i wayar daga hannun
mutumin kamar ta tace bata kalli fuskar shi ba ta mayar da hankalin ta kan wayar don ganin time d'in.

Shi kuwa wanda aka kar6ar wa waya cikin tsananin mamaki ya d'ago kanshi don ganin mai k'arfin halin
nan ae kuwa idanun shi suka sauka a kan mufidah tuni ranshi ya 6aci sosai har wani rawa jikin shi yake,
ko nabila dake xaune gefe ta tsorata da ganin yanayin yanda ya koma lokaci d'aya da yake idanun ta suna
kan mufidah don ganin wa gurin wa xata.

Kawai kafe ta yayi da ido wad'anda suka canja launi xuwa ja saboda 6acin rai *MUSADDIQ ABUBAKAR*
kenan, tana gama duba time taga 5:35 kenan sauran mintuna biyar su tafi ta d'an yatsine fuska tukunna
ta mik'a mishi wayar tare da kallon mutumin mai wayar ae kuwa suka had'a ido da malamin nasu wato
musaddiq tuni hantar cikin mufidah ta kad'a amman ta d'aure tace
"sorry sir ashe kai........."
Kafin ta K'arasa fad'i taji saukar wani gigitaccen mari a kuncin ta dama da hagu wani k'ara ta saki lokaci
d'aya don ba'a ta6a yi mata irin wannan axabbaben marin ba tuni hankalin mutanen wajen yayi kansu da
sauri nabila ta K'arasa wajen ta rik'e mufidah cikin girmama wa tace
"malam don Allah kayi hak'uri batasan kai ne ba please "

Cikin tsawa yace "Kad'an ma kika gani tun da ke baki da tarbiyya xan koya miki ita stupid girl"

Gama fad'in hka yayi gaba kallon Inda suke bai k'ara yi ba don baxai iya sake kai mata wani marin ba
K'arshe ma ya fice daga wajen gaba d'aya.

Nabila taja hannun mufidah suka fice daga wurin in ban da kuka babu abin da mufidah take fuskar nan
taji jawur da ita hka ma idanun ta wad'anda suka kumbura saboda kuka don ba k'aramin maru wa tayi
hannun musaddiq ba, rarrashin ta take yi nabila kan tayi hak'uri tayi shiru cikin tsananin takaici ta d'ago
kanta ta kalli nabila tace

"hak'uri kika ce fah nayi toh wlh sai na rama ko bata hanyar mari ba ni nasan abin da xan mishi "
Cikin mamaki nabila tace "oh yanxu baxa ki hak'uri ba da ganin guy d'in nan bashi da kirki fa"
Juyar da kai mufidah tayi bata k'ara magana ba hka ita ma nabila sai da ta sauke nabila a gida kamar
kullum sannan taja motar xuwa gida yau duk ma'aikatan gidan sun fuskanci an ta6a er lelen Abba da
Mumy ganin duk Sannun da xuwan da suke mata bata kalli su ba balle susa ran amsa musu, wata ajiyar
xuciya ta saki lokacin da ta shiga falon taga umma bata nan d'akin ta ta wuce da sauri tana xuwa kan
gado ta fad'a sai lokacin ma wani kukan ya xo mata xuciyar ta tana ingixa ta kan me yasa bata rama marin
ba har ta barshi ya tafi nan ta fara sak'e sak'en yanda xata rama abin da musaddiq yayi mata.

_Washe gari_

Karfe 10 na safe ta gama shirin ta tsaf na tafiya skul wata swiss atampha kalar bak'i da blue ta sanya
d'inkin doguwar riga ce ba k'aramin kar6ar kayan jikin ta yayi ba sai tayi light make up bata d'aura
d'ankwalin ba don ita ba ma'abociyar son d'ankwali bace sai ta samu veil blue tayi rolling d'in kanta da
shi sannan ta fesa different perfumes a jikin ta sannan ta d'auki bag d'in ta wanda yta xuba tarkacen
hand out a ciki sai wayar ta da key di'n mota a hannun ta, palo ta fito ta tarar da umma tana xaune tana
karanta jarida rungume ta tayi tare da bata peck a kumatu tana cewa "Gud morning umma nah"
"morning dota kin tashi lafia?"
"Qlau umma nah, ina Abba nah kuma? "
"ya fita yanxu "

Cikin shagwa6a tace "shine ya fita bai tsaya mun gaisa ba"
Dariya umma tayi tare da cewa "kiran gaggawa akayi mishi amman ya lek'a bedroom d'in naki ya tarar sai
bacci kike "
D'an murmishi tayi tare da cewa "Allah sarki abbana Allah ya barmin ku"
"Ameeen "

Cikin sauri ta kammala breakfast d'in sannan tayi wa umma sallama ta tafi skul duk jikin ta ba dad'i
sakamakon nabila da ta kirawo ta baxa ta samu damar xuwa skul d'in ba bata jin dad'in jikin ta, hka ta
K'arasa skul d'in bayan ta gama d'aukan lecture's ta fito tana xaune a saman motar ta suna waya da
abban ta adai dai lokacin musaddiq yake kok'arin shiga motar shi kunnen shi mak'ale da waya alamar
waya yake da yake taxarar su da inda suka yi parking ba nisa sai taji yana cewa
"kada ka damu gani nan xuwa brother "
Mufidah ta fara tunanin ko ta bishi ta rama abin da yayi mata bata ankara ba taji ya tashi motar tare da
yin gaba da sauri ta dira daga motar ta shige ta ta ita ma ta bishi a baya.

Wani shegen murmishin mugunta ta saki ganin wannan restaurant d'in da ya mare ta jiya yayi parking ita
ma parking tayi tare da shigewa ciki amman sai bayan ya shige, cikin mamaki tnake bin mufidah da kallo
maimakon naga ta wuce ta samu waje ta xauna sai naga ta nufi wajen masu ba da abinci taja wani gefe
cikin harshen turanci take ce mishi ya fad'a mata kalolin abincin Chinese food nan kuwa ya dunga fad'a
mata su a ciki ta xa6i wani kalar abincin tace mishi
"ka ga wancan mai ash d'in t-shirt di'n xaka kai mishi"
Cikin rashin yarda yace "ae bai fad'a mana abin da xamu kai mishi ba? "
er dariya mufidah tayi tare da xaro kud'i wajen 10k tace "idan har ka kai mishi abincin nan to wannan
kud'in ya xama naka "
Nan take cikin rawar jiki ya amince ae kuwa ta damk'a mishi kud'in cikin rawar jiki yaje ya had'o abincin
ya kawo wa mufidah don ta gani da sauri ta juyar da kanta ganin abincin har sai da taji xuciyar ta na tashi
da sauri tayi mishi alama da ya kai mishi ai kuwa ya rufe ya doshi table d'in da musaddiq da yah sadeeq
suke xaune suna hirar su cikin kwanciyar hankali.

Ajiye abincin yayi kuwa a gaban musaddiq sannan ya tafi ganin ya bud'e plate di'n abincin yasa spoon a
cikin abincin yana kok'arin sa spoon di'n acikin bakin shi hankalin shi gaba d'aya yana kan waya yaxo dai
dai bakin shi xai xuba ya d'ago don ganin kalar ma abincin da aka kawo mishi ganin abin da yake kok'arin

sawa a baki ne yasa shi sakin ihu tare da wurgar da spoon di'n ya fara kakarin amai, da sauri Yah sadeeq
ya juyo da kallon shi kan musaddiq ganin abin da ke faruwa yasa shi furta "subhannallah musaddiq me
yake faru wa "
ganin yanda ya ke kakarin amai yana rik'e da cikin shi...............





Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:03 p.m.] Aysher Muhd Writr: ν ΌνΌ² *YAYI SAKE*ν ΌνΌ²



*written by*
Aishat A muh'd

β™» *E.W.F*




_A gaskia bani da bakin godia gare ku en exclusive saboda kunyi min abin da naji dad'in,a gaskia ku
mutane ne masu hankali da ilimi tare da sanin ya kamata jinjinar ban girma gare ku Allah ya k'ara kare
min ku, Allah ya k'ara had'e kan mu daman can mu tsintsiya mad'aurin ki d'aya ne,ina son ku sosai_ν ½νΈ»

*my Sumayya salees sadeeq (sumynbash)* _bani da kalaman godia a gare ki hak'ik'a ke masoyiya ta ce
Allah ya bar xumunci ameeen_❀



*Page 3*



Da sauri Yah sadeeq ya juyo da kallon shi kan musaddiq ganin abin da yake yake faruwa yasa shi furta
"subhannallah musaddiq

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login