Showing 66001 words to 69000 words out of 92754 words
Chapter 23 - YAYI SAKE COMPLETE BY A'ISHA A MUHD-1.pdf
ganin fuskar shi dab da ta ta, kallon
junan su suke ido cikin ido irin kallon da man da geet suke yi idan soyayyar tasu ta motso. lol
Sun kwashe some minutes suna kallon junan su kafin mufidah ta tsuke fuska tace
"malam ni ka d'aga ni xan tashi ka gani danne ni kana kallo na "
Shima 6ata fuskar yayi tare da cewa "wane xai tsaya kallon ki, kuma ni bani na janyo ki ke kika janyo kan
ki "
Hararar shi tayi tare da cewa "to d'aga ni "
Shima hararar ya rama tare da yatsina fuska kafin yace
"cika min riga ta "
Sai lokacin idanun mufidah ya fad'a kan hannun ta da yake rik'e da rigar shi k'am da sauri ta cika mishi, ya
fara kok'arin tashi.
Yana tashi mufidah idanun ta suka sauka kan jikin ta inda rigar ta gaba d'aya ta nannad'e daga kasa ae
kuwa cikin sauri ta k'arasa haye wa kan gadon ta tuk'unk'une da blanket har kanta, abin sai ya bawa
musaddiq dariyar ma har sai da ya murmusa cikin xuciyar shi ya furta
" har yanxu akwai yarinta a tattare da ke mufidah, ina son komai naki i luv u so much "
A fili kuma yace "ke malama ki tashi mu tafi gida dare nayi "
Tana cikin blanket d'in ta murgud'a baki tare da cewa "tabbb ba inda xan je ina gidan mu "
"ki taso mu tafi idan nayi k'irga 5 baki fito ba I'll slap u "
Tana jin shi ko uhm bata ce mishi ba har ya fara k'irgen, jin har ya kai 4 ne yasa ta mik'e wa xata fad'a
toilet, ae kuwa kamar ya sanya abin da take niyyar yi sai ji tayi carab ya rik'e hannun ta tare da murgud'a
su ya jiyo da ita tana kallon shi ya mayar da hannun ta dukka biyun bayan ta ya rik'e su da hannun shi
d'aya kallon ta yayi tana xubar da hawaye don ba k'aramin rik'o yayi mata, lumshe idanun shi yayi sam
baya kaunar ganin hawayen ta kawai sai ya sanya hannun shi ya janyo hijab d'in ta ya xura mata ganin da
yana kok'arin d'aukar ta yasa magana da sauri tana cewa
"ni ka kyale ni na shiga toilet xan yi fitsari "
Kallo d'aya yayi mata yasan ba wani fitsari da take ji, ya dauke ta cak yana cewa
"idan ki matsu kiyi a hka "
Nan ta fara wutsil wutsil da kafafun ta alamar ya sauke ta amman bai kula ta ba har sai da suka fito
parlour, umma da abba ma basa nan xaune don hka kawai ya fita har xuwa wajen da yayi parking motar
shi ya sanya ta kafin ya shiga shima yayi wa motar key suka bar gidan.
Saboda takaici sai kawai ta rushe da kuka don ta rasa abin yi sai kukan mybe idan tayi ta samu relief a
cikin xuciyar ta, lumshe idanun shi yayi tare da bud'e su lokaci d'aya suka yi ja don baya kaunar ganin
kukan ta xuciyar shi na k'una idan yaga hawayen ta, daure wa yayi har suka k'arasa gida tak'i fito wa daga
motar sai da ya dauke ya kaita har bedroom d'in ta tukunna ya fita.
Sai da ta gaji da kukan ta bacci ya dauke ta, musaddiq sai da ya shigo d'akin ya ga tayi bacci sannan
hankalin shi ya kwanta yayi mata addu'a sannan ya kashe mata hasken ya bar d'akin sai lokacin yaji
xuciyar shi tayi mishi dad'i hankalin shi ya kwanta.
Ko Washe gari ma kulle kofar bedroom d'in ta tayi bata fitowa ba sai da tabbatar ya bar gidan sannan ta
fito, abinci iya cikin ta ta girka ta koma bedroom ta rufe don sosai haushi ya bata ba.
Sosai hankalin musaddiq ya tashi don ya kasa jure rashin ganin ta, amman sai ya daure don baya son ta
fahimci abin da yake cikin xuciyar shi idan ba nesa yayi da ita ba cikin lokaci k'ank'ani xata fahimci abin da
xuciyar shi take ciki, hkan yasa shi fara shirin koma wa Australian.
Ranar dasu mumy xasu dawo a ranar musaddiq ya bar nigeria ko mufidah bai k'ara gani ba, sai daf da
mangarib su mumy jirgin su yayi landing a airport sai ganin su mufidah tayi kawai, nan ta rungume mumy
da afnan tana mai farincikin ganin su, hka ma mumy baki yak'i rufuwa na ganin mufidah afnan sai labarin
kasar london ake yiwa mufidah.
" yau kenan kika dawo 'yata? "
Cewar mumy suna shiga bedroom d'in ta, d'an murmishin yak'e mufidah tayi cikin xuciyar ta tana cewa
wannan masifafen mutumin ne xai bar ni na tafi gidan mu, a fili kuma tace
"ehhh mumy d'axu na dawo "
Murmishi tayi tare da cewa "yayi kyau hkan, ae da ma baki dawo ba anjima kad'an xaki ganni"
Murmishi kawai mufidah tayi mumy tana sonta shi yasa ita ma take son ta sosai, hka lokaci ya cigaba da
tafia suna xaman su cikin kwanciyar hankali ta 6angaren mufidah tana kok'arin yaki ce wani abu da yake
son shiga cikin xuciyar ta tana son karya ta xuciyar ta akan abin shi yasa bata kaunar xama waje d'aya
tana k'e6e wa ita d'aya tunanin shi xai fara addabar xuciyar ta, shi yasa take k'irk'irar abubuwan da xata
hana xuciyar ta tunanin shi don ita a ganin ta sam baxa ta bari son shi yayi tasiri cikin xuciyar ta ba.
*AFTER 3 MONTH'S*
bayan wad'annan watannin da suka shud'e ne shiru musaddiq yak'i dawowa mumy da daddy sun yi
mishi maganar ya xo ya d'auki mufidah su koma Australian d'in amman ya fara yi musu hanya hanya
ganin hka yasa mumy da daddy suka yanke lokaci nan da two weeks mumy xata kai mufidah har
Australian d'in ba tare da sun bi takan musaddiq ba tun da yak'i tsayawa ayi maganar.
Musaddiq kuwa ta 6angaren shi baya son yana ganin mufidah hankalin shi ya tashi yake, ganin ta ba
k'aramin canja mishi tunani yake ba xuwa wani abin daban, taya xai iya tunkarar mufidah da buk'atar shi
sai yake ganin kamar bai yiwa d'an uwan shi adalci ba wannan tunanin nashi shi yake dad'a nisan tashi da
bayyana wa mufidah abin da yake kunshe cikin xuciyar shi shekara da shekaru.
Cikin kwanakin nan aka gama shirya tafiar mufidah da afnan, gyaran jiki na musamman mumy ta d'auko
don gyara mufidah ciki da waje, ae kuwa tasha gyara ba kad'an ba, tayi wani irin kyau sosai na daban,
sam mufidah ba'a son ranta xata tafi ba don kawai tana jin kunyar mumy da daddy ne bata son nuna
rashin son tafiyar da bata yi, Sauran kwana biyar su tafi ne taje yiwa su umma sallama don xata kwana
uku acan.
Sosai umma ta dage ita ma tana gyara d'iyar ta ta duk da ta yaba da gyaran da mumy tayi mata, hka
nabilah ma gudummowar ta daban ta wannan 6angaren, umma ta xaunar da mufidah tayi mata nasiha
sosai tare da bata shawarwari masu amfani, abba da yah Omar ma kowa da tashi nasihar, mak'ale wa
mufidah tayi tak'i dawowa gidan mumy sai ranar da xasu tafi Australian d'in da safe mumy ta xo ta sanya
ta a gaba suka koma gida, da kanta mumy ta shirya mata kayan ta sosai da yake tashin dare xasu yi.
Xuwa mangarib sun gama komai xuwa karfe 9 jirgin su xai tashi don hka 8:30 na dare suna airport, nan
suka yi sallama da daddy da yake har dashi a en rakiyar ga umma, abba, yah Omar, nabilah da muhibbat,
ga Dr muh'd da matar shi nafisat har dasu a en rakiyar don muh'd yana bawa duk wani abin da ya shafi
musaddiq muhimmanci,kowannen su jiki a sanyaye suka yi sallama har jirgin su mufidah ya tashi suna
tsaye kafin kuma su koma gida duk kewar mufidah da afnan ta kama su don mumy kwanaki biyu xata yi
ta dawo.
Acikin jirgin kuwa mufidah hawaye ne yake xuba a idanun ta cikin xuciyar ta baxa ka iya tantance halin da
take ciki ba farinciki ko akasin hka,kwantar da kanta tayi idanun ta a lumshe tana tunanin irin xaman da
xasu yi ita da musaddiq a wannan lokacin............
_to readers ga mufidah a hanyar ta ta xuwa australian wajen musaddiq, ko ya xaman su xai kasan ce ni
kaina na k'agu naji irin xaman da xasu yi, don hka ku jira ni a next page d'ina don jin abin da xai faru,
godia mara adadi gare ku fan's d'in yayi sake! ni Aishat A muh'd ina gaida ku tare da yi muku fatan
alkhairi luv u all my fan's_
Sai kun yi hak'uri da wannan page d'in don ban samu damar editing ba
Aishat A Muh'd ✍
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*
*Written by*
Aishat A Muh'd
♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM
LIKE AND COMMENT'S FB PAGE
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
_Gaisa da fatan alkhairi gare ku masoyan Aishat A muh'd, ina jin dad'in yanda kuke kaunar littafin nan,
don hka na sadaukar da wannan page d'in ga duk masoyin littafin yayi sake!,luv u oll my fan's_❤
*PAGE 47*
A cikin jirgin kuwa mufidah hawaye ne yake xuba a idanun ta cikin xuciyar ta baxa ka iya tantance halin
da take ciki ba farinciki ko akasin hka, kwantar da kanta tayi idanun ta a lumshe tana tunanin irin xaman
da xasu yi ita da musaddiq a wannan lokacin.
Lokacin da jirgin nasu yayi landing a babban fili saukar jirgi na australian, mutane suka fara firfito wa
mufidah tana sanyo kanta xata fito taji wani sanyi ya ratsa mata fuska sosai nan ta k'ank'ame jikin ta, tana
tunanin yanda xata iya xama a wannan uban sanyin garin, a nutse ta sauko daga matattakalar jirgin
mumy da afnan suna bayan ta.
Bayan duk sun gama komai ne suka nufo hanyar da xata kaisu wajen hanyar fita daga airport d'in xuwa
wurin da xasu tari taxi, mumy ce ta tsayar da taxi d'in cikin harshen turanci tayi mishi bayanin inda xai
kaita da sunan unguwar da musaddiq yake xaune, ba wani 6ata lokaci ya amince da hkan kafin ya fito ya
taimaka musu da xuba kayan su cikin boot tukunna suka shiga yaja su.
Mufidah ta ware idanun ta sosai tana kallon yanayin garin na australian sosai k'asar ta birge ta don bata
ta6a xuwa k'asar ba, wani lokacin idan ta tuna wajen wanda xasu je har su xauna tare sai ta ji xuciyar ta
na bugawa.
Tafiyar tsayin mintuna 50 ne ya kaisu anguwar da musaddiq yake har number d'in gidan mumy ta fad'a
wa taxi driver d'in, ai kuwa a dai dai kofar gidan yayi parking, sai da ya sauke musu kayan lokacin da
mumy ta nemi alfarmar hakan a wajen shi, tukunna ta biya shi, knocking d'in kofar gate d'in mumy tayi
gateman ya bud'e da yake ya san mumy basu wani 6ata lokacin shiga gidan ba.
Door bell mumy ta danna sau uku ana hud'un ne suka ji ana kok'arin bud'e kofar, lokacin da musaddiq ya
bud'e kofar sakin baki yayi cikin matuk'ar mamaki yana Kallon mumy wadda ta had'e fuska babu wasa
sam ba hango mufidah ya tsaya kawai yana kallon mumy ko magana ya kasa yi
"bani wuri na shige mun gaji da tsayuwar "
Mumy tayi furucin ganin bashi da niyyar matsa ma, kamar wani yaro ya matsa mata taxo xata shige tace
"musaddiq Allah ya shirye ka, yanxu a hka kake bud'e kofar kasan wane xai shigo maka a lokacin "
Wata irin kunya ta kamshi ya sunkuyar da kanshi yana sosa kai tare da tunanin yanda yake boxer ne a
jikin shi kawai ko riga babu lokacin yana kwance cikin bedroom yana tunanin mufidah yaji knocking d'in
so bai tsaya sanya kaya ba ya fito, ita dai mumy shige wa tayi cikin parlourn.
Jiya yi an rungume kafafun shi ana cewa "Oyoyo daddyna i miss u so much "
D'ago kanshi yayi ya ga afnan ce ae kuwa ya d'aga ta sama yana dariya tare da cewa
"i miss u too dear,ashe mumy da ke ta xo min? "
Tana dariya tace "yes daddy dani taxo har da mamee nah "
Dariya ya sake sanya wa ya d'auka shirmen afnan ne kawai sai ya sanya bakin shi ya bata peck a kumatun
ta, d'aga idanun shi da xai yi suka had'a ido da mufidah tana tsaye tana kallon su cikin sha'awa da birge
wa, sai kawai suka tsaya kallon junan su cikin wani yanayi na shauk'i.
"bani hanya na wuce kada ka cinye min yarinya ka wani xuba mata ido kak'i matsawa ta wuce "
Cewar mumy kenan ganin shiru mufidah bata shigo ba, sai lokacin ya sauke idanun shi akan ta ji yayi
xuciyar shi tayi mishi sanyi da ganin ta yana rik'e da afnan ya wuce ciki, yayin da mumy ta rik'o hannun
mufidah suka wuce su ma cikin parlourn.
Lokacin da suka shiga musaddiq yana xaune kan kujera afnan tana kan kafafun shi tana mishi hira
murmishi kawai ya ke yi, yana son afnan idan yana ganin ta ko yana jin muryar ta jinshi yake tamkar yana
tare da d'an uwan shi sadeeq.
"malam ai sai kaje ka sanya kaya koh oh ni khadija musaddiq ko kunya ta baka ji ka xauna a hka a gaba na
"
"mumy ba hka ba ne just afnan ce ta tsaida ni labari take bani "
Yana gama fad'in hka ya xaunar da afnan tare da cewa "sweet dgter give me five minutes ina xuwa"
Langa6e kai tayi tare da cewa "okay daddy "
Kallon mufidah yayi sai aka ci sa'a ta d'ago kanta suka had'a ido ae kuwa harara ya sakar mata tare da yi
mata kallon xan kama ki ne yarinya ita ma hararar ta watsa mishi girgixa kai yayi kawai ya wuce bedroom
d'in shi.
Cikin mintuna 10 sai gashi ya fito har ya shirya cikin Blue Jeans and black T-shirt mai k'aramin hannu yayi
kyau sosai, gaida mumy yayi ta amsa mishi, mufidah ganin idon mumy ne yasa tayi mishi gaisuwa d'aya
daga ina yini taja bakin ta ta tsuke , to shima lafia kawai ya furta sannan ya kalli mumy yace
"mumy ga bedroom nan ki je kiyi wanka ki huta bari na fita na samo muku takeaway "
"to shikenan "
Abin da mumy tace ta wuce d'ayan bedroom d'in, daman two bedrooms ne a gidan da parlour d'aya sai
kitchen da kuma madaidaiciyar harabar gidan, gida ne mai kyau sosai wanda aka tsara shi da abubuwan
more rayuwa.
Mumy tana shige wa bedroom ne afnan ta bita yayin da musaddiq ya sunkuyo dai dai kan mufidah har
numfashin su na had'u wa yace
"ba dai har kin gaji da xama babu miji a kusa ba yasa ki tak'ura wa mumy ta kawo ki waje na"
Wayyo wani bak'in ciki ne da takaici ya tokare mufidah kamar ta rushe da kuka saboda abin da ya fad'a
mata,kasa magana tayi kawai ta kau da kanta, murmishin mugunta ya saki tare da d'aga kafad'ar shi yace
"anyway duk abin da kike so kin xo inda xa'a share miki hawaye bari naje na dawo 'yammata xan ce ko
second hand "
Kasa jure wa mufidah tayi ta tashi a fusace har ta bud'e baki xata yi mishi magana sai kawai ta fasa ta
wuce bedroom d'in da mumy ta shiga ashe bashi ne nashi ne sai jin muryar shi tayi yana cewa
"haba mameen afnan saurin me kike ki bari na fara gayyatar ki xuwa d'akin kya shiga "
A xuciye ta jiyo tare da cillo mishi phone d'in hannun ta cikin fusata, yana dariyar k'eta ya cafe wayar a
hannun shi, haushi takaici ya k'ume mufidah sai kawai ta rushe da kuka daman kiris take jira, ganin mumy
tana kok'arin fito wa daga bedroom yasa musaddiq fit ya fice da sauri yana mamakin saurin kukan
mufidah daga tsokana sai kuka.
"lafia mufidah me ya faru ?"
Mumy ta tambaye ta tana d'ago ta daga tsugunnawar da tayi, cikin kukan tace
"ba komai mumy "
"haba mufidah hka kawai mutum baxai yi kuka ba sai da dalili tell me me ya faru kike kuka?
"mumy bige wa nayi a kafa ta "
Kawai ta tsince kanta da fad'a wa mumy hkan, cikin tausayi mumy tace
"Ayyah sannu kin ji "
Gid'a kanta tayi nan mumy ta kama hannun ta suka shige bedroom d'in.
Wanka mufidah take a toilet tana tsiyayar da hawayen takaicin abin da musaddiq yayi mata kuma xai ta
rama ita ma, tana tunanin mafitar rama wa har ta gama wanka bata samu mafita ba.
Bayan ta fito ne daga toilet lokacin su mumy da afnan har sun gama shirya wa sun koma parlour, don hka
ta shirya a nutse cikin wani wando maroon colour irin wanda yake kwanciya a jikin mutum da wata black
T-shirt mai k'aramin hannu akwai kwalliyar xanen heart a gaban rigar da silver colour sai ta sanya wata
rigar sanyi wadda tsayin ta iya gwiwa rolling kan ta tayi da black veil kafin ta fesa perfumes ta fito xuwa
parlour.
Yana xaune kan dining table ya hango ta kur6ar coffee yake a time d'in da ta fito but sai ya ajiye cup d'in
ya tsira mata ido yana kallon ta ba wani make up tayi ba but tayi kyau, da yaga tana kok'arin d'ago kanta
yasa shi saurin dauke idon shi