Showing 75001 words to 78000 words out of 92754 words
Chapter 26 - YAYI SAKE COMPLETE BY A'ISHA A MUHD-1.pdf
biyu ya sake kok'arin tashi but har yanxu tak'i sakin shi dakyar da dabara
ya kwace jikin shi yayi mata addu'a tare da lullu6e ta da blanket sannan ya tafi bedroom d'in shi .
Yana tsaka da yin wanka yaji kamar ihun mufidah cikin sauri ya d'aura towel ko damuwa da wanke
kumfar jikin shi bai yi ba ya fito da gudu yana kok'arin bud'e kofa ne ita kuma ta turo kofar sai k'um suka
yi gware but mufidah bata damu da jin xafin da taji ba na bugewar ta fad'a jikin shi cikin shashshak'ar
kuka tace
"ni gaskia ka mayar da ni wurin mumy tsoro na ke ji "
Musaddiq wanda yake dafe da goshin shi cikin damuwa yace
"me yafaru kuma yanxu?"
"ni ji nake kamar suna bina Allah tsoro nake ji "
Raba ta da jikin shi yake kok'arin yi saboda ya fara shiga wani hali amman ina mufidah sai dad'a rik'e shi
take tana kuka
"okay okay ya isa hkan "
Shiru tayi tana faman sauke ajiyar xuciya suna tsaye a hka wajen 5 minutes kafin ya fara kok'arin raba ta
da jikin shi nan tak'i yarda, ya rasa yanda xai yi da ita gaba d'aya ta d'aga mishi hankali wata muguwar
kasala ce ta baibaye shi har takai da ya fara jin nauyin jikin shi yana kok'arin xubar dasu a k'asa.
Namijin kok'ari yayi wajen daurewa xuwa jan su saman bed ya kwanta yayin da mufidah ma ya kwantar
da ita gefe amman sai da ta dad'a rik'e shi sosai, girgixa kai musaddiq yayi lokaci d'aya tunanin shi ya fara
sauya salo xuwa wani abin daban.
Kasa daure wa yayi ya lalu6o lips d'in mufidah ya fara kissing d'in su cikin wani yanayi na daban jikin shi
har 6ari yake tsabar birkita mishi lissafi da mufidah tayi.
Tuni mufidah ta wartsake daga baccin da ta fara yi saboda abin da taji musaddiq yana yi mata kasa kwace
kanta tayi saboda rik'on da yayi mata irin na sadaukan maxa ne.
Kukan da ta daina shi ya dawo mata ta fara kokawa saboda jin wannan bak'on al'amarin da yake kok'arin
shiga tsakanin ta da musaddiq, sai da yayi romance da ita son ranshi, mufidah ido ya raina fata tun da
duk kukan da take da kok'arin kwatar kanta da take ta kasa sai kawai tayi luf da ita ta mik'a wuya tun da
duk ragowar k'arfin da yake jikin ta, ta rasa shi ganin hka da musaddiq yayi yasa shi cigaba da abin da
yake yi.
Yana daf da cimma burin shi ne mufidah taji ya tsaya cak kafin taga kuma ya tashi tare da shigewa
bathroom tana jin k'arar yanda ya saki shower ruwa yana xuba a kanshi, da sauri ta mik'e ta gudu
bedroom d'in ta sai da ta sanya key a kofar tukunna hankalin ta ya kwanta duk tsoron da take ji ya kau
abin da ya koro 6era daga rami ya fad'a wuta yafi wutar xafi, kafin ta kwanta ta lullu6a da blanket har
xuwa yanxu gaban ta fad'uwa yake jikin ta ma rawa yake, tana tunanin yau mai juyar da hankalin
musaddiq har yayi kok'arin yin wani abin da ita.
Tun da ta ta6a jin hirar shi a waya da muh'd har yake fad'a mishi shi ya rasa yanda xai yi da yanayin shi
gashi baxai iya tunkarar mufidah da buk'atar shi ba ya bashi shawara yanda xai yi bata ji abin da muh'd ya
ke fad'a mishi ba but taji musaddiq yana cewa wannan ba shawara bace baxan iya ba idan na gaji sai na
sake aure amman dai so shi d'aya nake yiwa sweet baby nah, daga hka hirar tasu ta xo k'arshe sosai
mufidah a lokacin ta fad'a duniyar tunanin wace ce sweet babyn musaddiq, tun kafin ta ganta ta fara
kishi da ita.
Tun da ita tasan auren had'i aka yi musu da musaddiq ba ganin juna suka yi ba suna so, a yanxu bata da
tabbacin ko yana sonta, ita dai tasan ta fara son musaddiq a tun kafin ta auri sadeeq.
Shigowar sadeeq cikin rayuwar ta shi ya hana son yin tasiri cikin xuciyar ta tun da ta riga da tasa a ranta
sadeeq xata aura, amman xuwa yanxu ita kanta har tsoro take ji ganin yanda xuciyar ta take son
musaddiq abin har mamaki ya ke bata, ita yanxu mene ne mafita.
Da wannan tunanin bacci mai k'arfi yayi awon gaba da ita bata kai da ta nemo mafitar ba.
Musaddiq kuwa tun da ya kunna wa kanshi shower ruwa yana xuba a jikin shi idanun shi a rufe suke ruf
kan shi yayi xafi brain nashi tana tunano mishi da irin yanayin da shiga a en mintuna da suka wuce.
Tunanin mafita shima yake ya gaji da wannan abin yana son kawo k'arshen irin wannan xaman a tsakanin
shi da mufidah, ya d'auki tsayin mintuna 20 a hkan kafin ya samu kwarin jikin shi ya kashe shower d'in
tare da d'aura towel ya fito.
Ajiyar xuciya ya saki ganin mufidah bata d'akin kafin kuma ya saki wani murmishi yace
"ashe ma tsoron bai kai xuci ba sai da ta gama hargitsa min tunani ta gudu idan na kama ki sweet
babynah xaki yaba wa aya xak'in ta "
Yana gama fad'in hka ya sake sakin murmishi yana tunanin yanda xai yi wajen fara janyo mufidah a jikin
shi ta saba dashi yana son ta dawo bedroom nashi suna kwana tare ko da wani abin baxai had'a su ba shi
dai yana ganin ta kusa dashi hankalin shi sai yafi kwanciya da hka shima bacci ya dauke shi mai dad'i cike
da mafarkan mufidah...........
Aishat A Muh'd ✍
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*
*Written by*
Aishat A Muh'd
♻ *£xclusive writers forum*
*Likes nd comment's fb page*
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
_ina masoyan my sister *sumayya salees sadeeq*,ina masoyan karanta littattafan ta irin su *rayuwar
ashwema,dangartakar xuci, yareema jawad*kun ji ta shiru na kwana biyu hutu ta tafi amman yanxu ta xo
muku da sabon wani daddad'an labari mai suna *DARIYA BA SO BA*my sister sumy muna biye da ke har
xuwa lokacin da xaki kammala shi, maxa ku garxaya ku nemi shi don kada a bar ku a baya, ni Aishat A
Muh'd ina miki fatan alkhairi tare da addu'ar Allah ya k'ara basirah da xumunci a tsakanin mu_ #ana tare
*PAGE 52*
Washe gari da safe tun da mufidah ta shirya afnan xuwa skul ta had'a mata komai ta dawo bedroom ta
kwanta duk jikin ta ba k'arfi tana nan kwance taji an turo kofar tare da jin muryar musaddiq yana
tambayar afnan
"ina mameen ki afnan? "
"daddy tana bedroom a kwance "
Kafin mufidah ta lullu6e jikin ta da blanket har ya shigo suna had'a ido ya watsa mata wani kallo na daban
wanda ya haddasa wa mufidah sake fad'a wa a kogin son shi gashi ya sake k'ara mata kasalar da take ji,
kasa d'ago kai tayi ta kalle shi wasa kawai take da en yatsun hannun ta, bata ankara ba taga ya xauna a
kusa da ita har suna jin d'umin numfashin junan su.
Mamaki sosai ya sake rufe mufidah bata gama wannan mamakin ba taji ya rik'o hannun ta idanun shi a
saman fuskar ta yana kallon ta yace
"mameen afnan xamu fita ayi mana addu'a kuma muna buk'atar rakiyar ki ko xuwa parlour ne, ko afnan?
"
Cikin dariya afnan tace "Yes! Daddy, mamee ki taso please "
Ta k'arasa fad'i a shagwa6e, shima cikin muryar shagwa6a yace
"please mamee ki taso kada mu yi late fah "
Gaba d'aya mufidah kasa kwakwkwaran motsi tayi saboda tsabar mamaki tana tunanin anya wannan
musaddiq ne kuwa ba irin mafarkan da take yi ba ne, jin yana kok'arin d'aga ta ne yasa ta tabbatar ba a
mafarki take ba idanun ta biyu.
D'ago kanta tayi da sauri ta kalle shi suna had'a ido ya kashe mata ido d'aya da sauri ta kawar da kanta
sam bata da kuxarin tafia tana tsaye cak ganin hka ne yasa musaddiq rik'e d'aya hannun ta yana cewa
"afnan rik'e d'aya hannun mameen na ki mu tafi naga alama tayi suman tsaye sai mun tallafa mata "
Dariya afnan ta sanya kafin ta rik'e hannun mufidah suna janta kamar mutum mutumi har xuwa
compound d'in gidan a wajen motar shi suka tsaya afnan tayi kissing d'in hand d'in mufidah ta shiga mota
ta xauna tana yiwa mameen nata bye bye amman batasan tana yi ba.
Musaddiq ne ya matso kusa da ita sosai kafin ya rik'e hannun ta dukka biyun da nashi kallon ta yake
fuskar shi dauke da murmishi yace
"mameen afnan ina neman alfarmar gyara min d'aki xan dawo da wuri ina son xamu fita tare "
Mufidah sai ta tsinci kanta da gid'a mishi kanta alamar to, wani murmishi ya saki tare da janyo ta jikin shi
ya rungume yana cewa
"thank u mameen afnan "
Sakin ta yayi tare da bata peck a kumatun ta sannan ya shiga cikin mota yaja suka bar gidan yana hango
mufidah ta madubin motar anan tsaye inda ya barta hannun ta d'aya dafe da wurin da yayi mata peck
murmishi ya saki shi kad'ai wani dad'i da nishad'i yana ratsa xuciyar shi har ya sauke afnan a skul sannan
ya k'arasa hospital.
Bayan tafiyar su da mintuna uku sannan mufidah ta dawo daga suman tsayen mamakin da musaddiq ya
gama bata, anya kuwa babu wata a k'asa canjawar shi farat d'aya daga daren jiya xuwa yau.
Dole na tsaya na karance shi naga ne abin da yake cikin xuciyar shi kafin na sake dashi, murmishi tayi
had'e da lumshe idanun ta tana tunanin lokacin da musaddiq ya rungume yarrr taji tsikar jikin ta ya tashi
kamar a time d'in yayi hugging d'in ta.
Da wannan tunanin salon da musaddiq ya fara ne ta nufi cikin gidan, tana xuwa ta fara gyaran gidan tun
daga bedroom d'in ta ta fara xuwa parlour kitchen gyaran bedroom d'in musaddiq ne na k'arshe.
Tana cikin kok'arin canja bed sheet ne taga wani k'aramin diary ya fad'o daga k'ark'arshin pillow daukan
shi tayi tare da ajiye wa saman bedside, cikin lokaci kad'an ta canja fasalin bedroom d'in musaddiq ta
gyara shi tsaf tsaf ko'ina tun daga toilet har xuwa cikin room d'in wani sanyayen k'amshin turaren room
freshener yake yi bayan ta gama gyaran ne har xata fito idanun ta suka sauka kan diary d'in musaddiq da
ta ajiye.
Sai kawai ta tsinci kanta da son bud'e shi ta karanta shi d'auko shi tayi ta nufi bedroom d'in ta dashi har ta
xauna xata bud'e shi ta karanta sai ta dubi agogo taga time yaja sai kawai ta ajiye ta nufi kitchen da niyyar
idan ta gama girki ta dawo ta karanta shi.
Kitchen ta shiga ta fara had'a musu abinci Kala biyu da snacks sai drinks d'in da tayi na xallar fruit salad
tana gama wa ta jera su a dining table kafin ta gyara kitchen d'in tayi wanke wanke Bayan ta gama gyara
ko'ina tsaf ne ta sake fesa air freshener a ko'ina.
D'akin ta wuce ta fad'a toilet tayi wanka da alwala kafin ta fito ta xura jallabia sallah ta gabatar kafin ta
gyara jikin ta cikin wani English wears riga pink colour da siket baki irin mai bud'e war nan daga k'asa belt
d'in siket d'in ita ma pink ce tayi kyau sosai light make up tayi sannan ta fesa different colour's perfumes
a jikin ta da humra kowanne motsi tayi kamshi ne daddad'a yake tashi a jikin ta.
Bayan ta gama shirya wa ne sai ta xauna kan sofa phone nata ta d'auko ta kirawo umma dasu mumy suka
gaisa kafin kuma su yi sallama ta ajiye phone d'in, xama tayi tana tunanin abin da musaddiq yayi mata da
safe ba k'aramin tsaya mata a rai yayi ba.
Sake hango diary d'in shi tayi a karo na biyu taje ta d'auka son karanta shi kawai take gashi book d'in ya
birge ta sosai, hannu tasa tana kok'arin bud'e farkon shafin dai dai lokacin gaban ta yayi wani irin mugun
fad'uwa...............
_tohh fah readers ga mufidah da dairy d'in musaddiq ko xata karanta ko kuma xata bari, gashi kuma
musaddiq ya fito da wani sabon salon ko me yake nufi da hkan, ku jira ni a next page don jin me xata
kasance, ku dad'a hak'uri da ni na kusan gama muku shi gaba d'aya_
Aishat A Muh'd ✍
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*
*Written by*
Aishat A Muh'd
♻ *£xclusive Writers Forum*
*Likes nd comment's fb page
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
Email:Aishataudimuhd.as@gmail.com
*PAGE 53*
Sake hango diary d'in ta yi a karo na biyu taje ta d'auko shi, son karanta shi kawai take gashi book d'in
ya birge ta sosai, hannu tasa tana kok'arin bud'e farkon shafin dai dai lokacin taji gaban ta yayi wani irin
mugun fad'uwa jikin ta ne yayi sanyi dakyar ta iya tattara k'arfin da yake jikin ta wajen bud'e first page
d'in.
Dummm wata muguwar fad'uwar gaba ta sake yi a karo na babu adadi sai dai wannan karon tafi ta
koyaushe sakamakon ganin picture d'in ta wanda idan baxa ta manta ba ranar da suka had'a wa Yah
Omar birthday party ne ta d'auka tana dariya tayi masifar yin kyau sosai a pic d'in.
Tsura wa picture d'in ido tayi brain nata yana dad'a hargitse wa mene had'in pic d'in ta da Musaddiq da
har xai sanya mata shi a cikin diary d'in shi, next page ta bud'e kuma taga ya rubuta Mufidah ina son ki
kece rayuwa ta, na fara son ki tun ranar da na fara had'uwa da ke lokacin da kika shigo hall a time d'in da
na ke lecture har na kore ki waje, nan gaban Mufidah ya cigaba da bugawa da k'arfi duk ta wani rud'e
jikin ta har 6ari yake yi.
Lokaci d'aya hawaye suka fara xuba a idanun ta cigaba da karanta duk wasu sirrikan cikin xuciyar
Musaddiq har da text messages d'in da yake turo mata su duk ta gane su xuwa lokacin da ya fara kamu
wa da ciwon xuciya duk a dalilin sonta!.........
Tun kafin Mufidah ta k'arasa karanta wa take xubar da hawayen tausayin Musaddiq najin irin wahalar da
Musaddiq yasha akan ta wani irin mugun tausayin shi ne ya dad'a kamata ga wani irin son shi da yake
k'ara shiga cikin xuciyar ta.
Ta dad'e xaune anan tana kuka dakyar ta iya jure k'arasa karanta wa, wani irin ciwon kai ne ya dirar mata
lokaci d'aya ga idanun ta sun kumbura sun yi sosai saboda axabar xafin da suke mata ma dakyar take iya
bud'e su.
Dama Musaddiq hka yake son ta hka yayi dakon sonta da kaunar ta wanda daga k'arshe ya kamu da
ciwon xuciya, why why Musaddiq da xaka 6oye min wannan abin kana dad'a cutar da xuciyar ka, daga
yau ta dauki alk'awarin kasance wa da Musaddiq xan na kyauta ta maka tare da yi maka biyayya duk abin
da xai mata ta dauki niyyar kyautata mishi duk mai yi maka irin wannan mugun son baxai ta6a iya jure
wulak'anta wanda yake so ba.
Tunani kala kala Mufidah ta dunga yi akan yanda xata kawo k'arshen wannan irin xaman nasu da
Musaddiq, dakyar ta iya tashi tsaye ta nufi bedroom d'in Musaddiq ta ajiye mishi diary d'in kamar yanda
ta ganshi, d'akin ta ta dawo kwanciya tayi kan bed ta kudundune da blanket sakamakon sanyin da ta fara
ji yana ratsa gangar jikin ta.
Cikin few minutes xaxxa6i sosai ya rufe Mufidah don ba k'aramin kuka tasha ba har ya sanya mata ciwon
kai ga xaxxa6i ya rufe ta idanun ta a lumshe but hawaye suna fito wa daga cikin su ji take kamar tayi
tsuntsuwa ta ganta gaban Musaddiq tana bayyana mishi abin da yake kunshe cikin xuciyar ta.
Jikin ta ya d'auki xafi sosai tana nan kwance taji shigowar motar Musaddiq cikin gidan runtse idon ta tayi
lokaci d'aya kamar mai baccin gaske tayi luf da ita ko kwakwkwaran motsi bata yi.
"Mamin Afnan where are you? "
Taji muryar Musaddiq ta doki cikin kunnen ta wanda ya haddasa mata fad'uwar gaba a karo na babu
adadi.
Musaddiq da Afnan sai da suka duba parlour, kitchen, garden basu ga Mufidah ba tukunna suka yi
tunanin ko tana bedroom don hka suka nufi nan.
Tura kofar bedroom d'in yayi ya hango ta kwance kan bed ta kudundune cikin mamaki yace
"Mamin Afnan lafia? "
Jin tayi shiru bata bashi amsa ba ne yasa shi k'arasa wajen da take da sauri, hannun shi ya sanya tare da
yaye blanket d'in da ta lullu6a da shi, hannun shi ya sanya saman wuyan ta da sauri ya janye saboda xafin
da jikin ta ya d'auka, sake runtse idon ta Mufidah tayi gam ita a dole bacci take batasan hawayen da suke
xuba a idanun ta sun fallasa ta ba.
Cikin gigice wa Musaddiq ya ce
"Mufidah xaxxa6i ne yake damun ki? "
Ya sake tambayar ta a karo na biyu but tayi tsit ta kyale shi, ganin hkan da tayi kuwa ba k'aramin sake
hargitsa Musaddiq yayi ba, baisan lokacin da ya xauna ba ya sanya hannun dukka biyun ya d'ago ta tare
da yi mata maxauni cikin jikin shi lokaci d'aya suka saki wata ajiyar