Showing 84001 words to 87000 words out of 92754 words
Chapter 29 - YAYI SAKE COMPLETE BY A'ISHA A MUHD-1.pdf
Cikin wani irin shauk'in Mufidah, da wata irin murya da Mufidah batasan yana da irin ta ba yace
"ina son ki Mufidah, i luv u Mufidah "
Jin saukar muryar shi Mufidah tayi kamar a mafarki yana furta mata wannan daddad'an kalmar, ko
kwakwkwaran motsi ta kasa yi, kamo hannun ta yayi tare da had'e su da nashi ya sake cewa
"Ina son ki Mufidah, kina sona ke ma, ina son ki furta min wannan kalmar da na dad'e ina sauraren ta
daga bakin ki ? "
Wasu hawaye ne suka zubo daga idon ta, wanda na kasa tantance su na farinciki ne ko akasin haka,
ganin hawaye suna zuba cikin idon ta yasa Musaddiq rikice, ba dai bata son shi ba, kasa magana tayi sai
kukan da take tana kallon shi.
Idanun Musaddiq sun yi ja saboda tsabar tashin hankali kada Mufidah tace bata son shi, hannun shi ya
sanya dukka biyun ya rik'o kafad'ar ta, cikin sanyin murya yace
"Mufidah kiyi min magana don Allah, ki fad'a min dalilin zubar hawayen ki "
Sam Mufidah tak'i bud'e baki tayi mishi magana sai kukan da take, ba k'aramin rud'e wa yayi ba jikin shi
har rawa yake, ga gumin da yake tsatstsafo mishi na tashin hankali,zuciyar shi bugawa da k'arfi take
kamar zata faso kirjin shi ta fito.
kunna hasken d'akin yayi tare da sakkowa daga kan bed d'in, bud'e locker d'in bedside yayi ya d'auko
diary d'in shi, sake hawa kan bed d'in yayi tare da kamo hannun Mufidah ya damk'a mata diary d'in a
hannun ta, cikin murmishi yak'e yace
"ki bud'e ki karanta abin da yake cikin nan, nasan shi zai tabbatar miki da irin so da kaunar da nake yi miki
"
Ya gama fad'in haka yana kallon ta, idon ta akan diary d'in mene amfanin karanta shi, bayan ta san abin
da yake cikin shi, gani yayi ta ajiye diary d'in a gefen ta, tare da matsowa inda yake, hannun ta ta sanya
tana mai rik'o nashi hannun duk biyun, cikin sanyin murya tace
"Mene amfanin karanta abin da na karanta "
Cikin mamaki yake bin ta da kallo, hannun d'aya ta d'auko ta d'ora shi kan saitin zuciyar shi tace
"Me yasa kake wahalar da kan ka Musaddiq, nasan abin da yake cikin diary d'in, saboda kukan da nayi na
tausayin halin da ka shiga a dalilin sona, shine ya haddasa min xaxxa6i a jiki na, bazan iya butulce wa
zuciyar da take yi min wannan son ba "
D'an jan numfashi tayi tare da yin murmishi ga hawaye suna zuba, ganin yanda Musaddiq ya bud'e baki
da hanci yana kallon ta, muryar ta na d'an rawa ta cigaba da cewa
" Na tausaya maka halin da ka shiga sosai duk adalilin so na, gaskiya kai ba k'aramin masoyi na ba ne,
wanda yake min so na gaskiya, nima ina...... "
Bata k'arasa fad'i ba, sakamakon kukan da kubce mata, rungume ta yayi cikin jikin shi, yana fitar da wani
irin hawaye a idon shi.
"Mufidah ki dai na kukan nan, ya isa haka kukan ki na ta6a min zuciya ta, na baki diary d'in nan don ki
karanta, nasan baki na ba zai iya fahimtar da ke yanda nake son ki ba, ina son ki Mufidah son da ba
kowanne namiji ne yake yiwa matar shi ba, ina son ki son da zan iya mutuwa idan ace ban same ki ba,
Mufidah ina son ki, son da fatar baki na bazata iya fayyace miki ba, ina son ki son da bazan iya........ "
Da sauri Mufidah ta sanya hannu ta toshe mishi bakin shi tana mai sake fashe wa da wani irin kukan
tausayin Musaddiq, shima hawayen ne suke zuba a idanun shi, cikin kukan ta dad'a k'ank'ame shi a jikin
ta, wani son shi na k'ara ratsa zuciyar ta.
D'ago kanta yayi yana kallon cikin kwayar idon ta yace ,
"ki fad'a min kina sona, ina son jin wannan kalmar"
Cikin shashshak'ar kuka tace "ina son ka Musaddiq, i luv u so much irin wanda bakina bazai iya fad'a ba "
Wani sanyin dad'i ne ya kwaranya cikin zuciyar shi, ya dad'a rungume ta cikin jikin shi, suna tona wa
junan su asirin zuciyar su, acikin wannan lokacin ji suke kamar su fi kowa farinciki, jin su suke kamar su
dawwama a hakan, suna masu faranta ran junan su.
Daga nan sai wasa ya fara canja salo na daban, cikin 'yan mintuna Musaddiq ya fara aikawa da Mufidah
xafafan sak'onnin shi, jikin shi har wani rawa yake, gaba d'aya ya gama fita a hayyacin shi ya mance
duniyar da yake ciki ma, zafafan kalamai yake furta mata su cikin wani irin shauk'in son ta.
Soyayya da take kunshe cikin zuciyar shi ta shekaru ya gama fayyace wa Mufidah, ba tare da yasan yana
hakan ba, kukan tausayin shi kawai Mufidah take zuciyar ta na k'ara son shi, iya wahala kam tasha ta a
wannan lokacin, saboda had'uwar ta da jarumin namiji irin Musaddiq, ba ita kad'ai ba ma shi kanshi
Musaddiq d'in ya wahala,har zuwa lokacin da mai afkuwa ta afku, kafin daga baya bacci mai dad'i ya
d'auke su.
*_ASUBA TA GARI MUSFEEDAH_*
Tun a cikin daren gaba d'ayan su, kowanne ya kamu da zazzafan zazza6i a jikin su, har zuwa wayewar gari,
dakyar Musaddiq yayi k'arfin hali ya tashi, wanka yayi tare da alwala sannan ya fito a toilet.
Sallah yayi kafin ya taimaka wa Mufidah ita ma tayi wanka, sai da tayi sallah tana idar wa wani nauyayyen
bacci yayi awon gaba da ita, ga jikin ta zafi har yanzu zazza6in bai sauka ba.
Shima Musaddiq d'in bacci ne ya d'auke shi mai nauyi sosai, don ba'a samu cikakken bacci ba, gashi kuma
an tashi da zazza6i.
Knocking d'in kofar da ake yi ne ya tashi Musaddiq daga baccin da yake yi, dakyar ya iya lalla6a wa ya
tashi tare da bud'e kofar, Afnan ya gani a tsaye tana kuka da alama ta dad'e tana yin knocking d'in, jikin
shi ta fad'a cikin muryar kuka tace
"daddy ina kuka shiga kai da mami? "
Shafa kanta yayi tare da cewa "Afnan bacci muke yi, sannan mamin ki bata jin dad'i, kada ki tashe ta mu
je na shirya ki, akwai skul "
Nan yaja hannun ta zuwa d'akin Mufidah ya shirya ta cikin uniform d'in skul, sannan suka fito ya had'a
mata tea tare da soya mata eggs, tayi breakfast sannan ya wuce kai ta skul, bayan ya ajiye ta ne ya dawo
gida yana addu'a cikin zuciyar shi Allah yasa Mufidah zazza6in jikin ta ya sauka.
Lokacin da ya shiga bedroom d'in shi bai tarar da Mufidah ba a ciki ba, sai ya wuce bathroom yayi wanka,
sannan ya fito ya shirya cikin wani yellow 3quater and white T-shirt mara hannu, ya fesa different
perfumes a jikin shi kafin ya fito zuwa d'akin Mufidah, jin shi yake yau wasai dashi kamar wanda aka
sauke wa wani babban abu a kanshi da cikin zuciyar shi.
Yana tunanin halin da suka kasance shi da Mufidah a tsayin daren jiya,murmishi ne shimfid'e a saman
fuskar shi na farinciki da nishad'i, yana k'arasa shiga cikin d'akin, ya hango ta kwance saman bed har tayi
wanka ta shirya cikin wata doguwar riga har k'asa mai hannun vest, irin mai kwanciya a jikin nan ce,
idanun ta a lumshe suke but ba bacci take ba, tunanin Musaddiq d'in ta take.
Daddad'an k'amshin perfumes d'in shi ne ya ziyarci cikin hancin ta, d'umin jikin shi taji a nata, a nutse ta
bud'e idon ta ai kuwa suka had'a ido, yana wani haske ta da kyakkyawan murmishin shi, d'an hararar
wasa tayi mishi tare kok'arin tashi zaune.
Cikin sauri ya janyo ta zuwa jikin shi yana cewa
"sweet baby nah ya zazza6in naki, dafatan ya sauka ?"
Ya k'arasa fad'i yana tatta6a jikin ta, jin babu d'umi yasa shi sakin ajiyar zuciya yace
"naji jikin naki babu d'umi alamun ya sauka, gashi ni kin shafa min har yanzu ban daina jin shi ba "
Kunyar shi take ji ta kasa yin magana, but fuskar ta d'auke da murmishi, ya gama karantar kunyar shi take
ji,
"Baki tambayi ina Afnan ba ?"
Dakyar ta iya bud'e baki tace
"Hmm nasan ka kaita skul, tun da na tashi ban gan ku ba "
D'an murmishi yayi so yake ta d'ago kanta ya kalli face d'in ta, amman tak'i d'agowa, don haka ya sanya
hannun shi ya dafe saitin zuciyar shi yace
"Wash! Allah nah zuciya ta"
A kid'ime Mufidah ta d'ago kanta tana kallon shi, ganin yanda ya kwanta sai juyi yake yana rik'e zuciyar
shi, yasa Mufidah fara hawaye don duk a tunanin ciwon ne ya tashi, cikin rawar murya take cewa
"wayyo Allah, sannu Musaddiq don Allah ka tashi mu tafi hospital "
Ganin yanda ta rud'e ne yasa shi tuntsire wa da dariya, sakin bakin ta tayi tana kallon shi, ga hawaye na
zuba, kawai sai ta d'auko pillow ta fara dukan shi da shi, Musaddiq yana dariya tare da yi mata gwalo
kuma yana kare dukan.
Gajiya tayi ta zube kan bed tana mayar da numfashi, janyo ta jikin shi yayi yana cewa
"nima na rama abin da kika yi min jiya a wurin beach "
Murmishi kawai take tana girgiza kanta, wato ashe ya gane karyar ciwo tayi.
"ina son ki Mufidah "
Ya furta hakan cikin kunnen ta, " nima ina son ka sosai "
Ta mayar mishi da amsa suna yiwa junan su murmishi.
A haka suka tashi zuwa parlour, kitchen suka shiga tare suka had'a breakfast bayan sun gama ne, suka
sake koma bacci..........
Aishat A Muh'd ✍
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*
*Written by*
Aishat A Muh'd
♻ *£xclusive Writers Forum*
*Likes nd comment's fb page*
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
Email:Aishataudimuhd.as@gmail.com
*PAGE 58*
Baccin su suka sha sosai, basu ankara da tafiyan lokaci ba sai da aka kirawo Musaddiq a waya daga
skul d'in su Afnan kan yazo ya d'auke, don anjima da tashin su, cikin sauri suka shiga wanka tare suka yi,
bayan sun fito ne suka shirya a gurguje don tafiya d'auko Afnan.
Bayan sun gama shirya wa ne, suka tafi school d'in d'auko Afnan, suna d'auko ta ya wuce dasu restaurant
suka ci abinci,sannan suka wuce wayo cikin tsantsar farinciki suke a wannan ranar, sai da dare yayi suka
dawo gida a gajiye.
Wanka Mufidah tayi wa Afnan ta kwantar da ita, sannan ta shiga nata wankan kafin ta fito har Afnan tayi
baccin ta saboda gajiyar da tayi, tana cikin shirya wa Musaddiq ya shigo d'akin yana cewa
"My sweet baby laifi me nayi aka bar ni, ni da a parlour? "
Jiyo wa tayi tana murmishi tace
"ba laifin da kayi my man, wanka na tsaya yi ne "
Shima murmishin yayi tare da cewa
"Yayi kyau hakan habibty, mu tafi d'akin mu koh ya?"
Yayi maganar yana d'aga mata gira, sunkuyar da kanta tayi tana murmishi tace
"okay, yiwa Afnan addu'a kafin na k'arasa shirya wa "
"toh angama ranki ya dad'e"
Cikin sigar tsokana tace "Ohhh har na kai wannan matsayin? "
Yana jan hancin ta yace "kin ma wuce haka baby nah "
Yana gama fad'in haka ne yayi wa Afnan addu'a a jikin ta, sannan yaja ta suka bar d'akin zuwa nashi,
hmmm wannan daren ma an bawa soyayya hakk'in ta sosai, don tsakanin Musaddiq da Mufidah
kowanne yana nuna wa d'an uwan shi irin kalar son da yake mishi, kafin daga k'arshe bacci mai dad'i ya
d'auke su, suna rungume da junan su, zuciyar kowa fal farinciki.
*_ASUBA TA GARI MUSFEEDAH_*
*AFTER 1 WEEK*
(Agurguje)
Cikin 'yan kwanakin nan tsakanin Mufidah da Musaddiq soyayya kawai ake xuba wa, suna bawa junan
su kulawa sosai, hankalin su ya kwanta sun yi fresh abin su, suna waya sosai dasu Mumy, Daddy, Umma,
Abba, Nabila, Yah Omar dasu Muh'd da matar shi Nafisat, ana jin lafiyar juna.
Duk wani shiri Musaddiq ya gama yi na koma nigeria, hospital d'in da yake aiki yayi musu sallama tare da
ajiye musu aikin su, sam basu ji dad'in barin Musaddiq asibitin ba, don ba k'aramin taimaka musu yake
ba babban likita ne da yasan me yake yi, da haka suka rabu cikin tsananin kewar shi.
Sai da Afnan ta samu hutu a school tukunna suka tattara inasu inasu suka bar Australian, suka tafi k'asar
switzerland suka samu hutun tsayin sati uku acan.
Kafin su nufi k'asar Saudi Arabian su yi umarah, sai da suka yi wajen sati hud'u a Saudi Arabian saboda
Musaddiq ya d'an yi fama da mura da zazza6i, kafin daga baya ya warware su fara shirye shiryen dawowa
gida Nigeria, sun yi tsarabar su sosai wadda zasu raba wa 'yan uwa, duk k'asar da suka je sai da suka yi
tsaraba.
Daman tuni an sanar da 'yan uwa dawowar su don haka aka fara shirin tar6ar su, ba irin Mumy da tafi
kowa farinciki saboda Musaddiq da ya fad'a mata ya dawo gida kenan bazai koma Australian ba, ba
k'aramin jin dad'i da farinciki tayi ba.
Jirgin da suka hau saukar yamma yayi sosai daf da mangarib, bayan jirgi yayi landing mutane suka fara
fito wa 'yan uwa sai wara idanu suke su hango ta ina zasu gano su Mufidah.
Babu jima wa suka hango Musaddiq yana rik'e da hannun Mufidah, ga Afnan a kafad'ar shi tana bacci sun
yi matuk'ar yin kyau sosai, fad'ar irin had'uwar da suka yi ma 6ata lokaci ne.
Duk sai aka zubo musu ido ana kallon su, ganin yanda suka yi matuk'ar dace wa da junan su, ga wani
kyau da suka k'ara da ka gansu kaga fulanin asali.
Kunya ce ta rufe Mufidah ganin yanda ake kallon su, zame hannun ta tayi daga na Musaddiq kallon ta yayi
kawai ya girgiza kai, tun kafin su k'arasa su Mumy ma suka taho aka had'u cikin farinciki, kowa bakin shi
yak'i rufuwa saboda murna, nan aka gaggaisa da juna tukunna aka nufi motoci don tafiya gida.
Dr Muh'd wanda ya zuba wa Musaddiq ido ganin yanda yayi k'iba kamar ba shi ba gashi sai murmishi
yake saki yana wani jifan Mufidah da wani irin kallon so, sai ya kasa daure wa yayi ya ta6o Musaddiq yana
cewa
"lover boy adai kula ba mu kad'ai ba ne akwai surukan ka, kada ayi abin kunya a bari sai an ke6e "
Hararar shi Musaddiq yayi tare da cewa
"ke fah na fahimci d'an sa ido ne na k'arshe, ina ruwan ka da mu naga matata ce "
Dariya Muh'd yayi tare da cewa "d'an duniya, naga alama ma mun kusan samin baby da gani baka yi
sassauci ba wajen uhm "
Bai k'arasa ba ya kwashe da dariya sai kawai Musaddiq ya biye mishi suka yi dariyar tare da tafawa, da
haka suka k'arasa gida suna tsokanar junan su, uhm Aminan kwarai kenan, Musaddiq nd Muh'd kullum
son junan su suke tamkar wasu 'yan uwa na jini, (ni kaina amintar su na birgine, don a yanzu kafin a samu
irin aminan sai an tona, saboda son zuciya yayi mana yawa
yanzu, Allah kada ka bamu ikon cin amanar mutumin da ya d'auke ka matsayin aboki, amini kuma d'an
uwa, Amin).
Bayan sun k'arasa gida ne mamaki ya kama Mufidah da Musaddiq ganin yanda gaba d'aya aka canja
fasalin gidan, side d'in da Sadeeq da Mufidah suka fara zama tuni an rushe shi, an sake wani sabon
fasalin mai kyau da tsaruwa, komai an canja na gidan tamkar bashi ba.
A part d'in su Mumy aka zauna bayan anyi sallahr mangarib da ishsha ne, aka zauna yin kwarya kwaryar
walima ta farincikin dawowar su Musaddiq gida lafia, anci ansha anyi musu addu'ar fatan alkhairi, kafin
kuma kowa ya kama gaban shi cikin tsantsar farinciki.
Bayan watanni biyu da dawowar su Mufidah Nigeria Nabilah matar Yah Omar ta haihu an samu baby
girl, ai kuwa sun sha suna yarinya taci sunan Mufidah ba k'aramin jin dad'i Mufidah da Musaddiq suka yi
ba, ai kuwa babyn tasha kaya sosai a wajen su.
Bayan suna da kwana biyu ne Mufidah ta fara zazza6i sosai mai zafi nan Musaddiq ya rud'e sosai babu
6ata lokaci ya duba ta abin ka da matar likita nan ya hango babyn shi d'an wata biyu da sati uku a tare da
ita, ai kuwa ya d'aga ta yana juyi da ita a cikin bedroom d'in cikin mamaki take kallon shi kafin ta bud'e
baki tace
"lafia dear? "
Sakko da ita yayi tare da zaunar da ita kan sofa ya dire gwiwowin shi a k'asa tare da rik'o hannun ta cikin
nashi yace
"my sweet baby ina matuk'ar farinciki yau saboda na kusan xama uba shine baki fad'a min ba sai da na
gano da kaina koh? "
Wani murmishin jin kunya ta saki tana kare fuskar da hannun ta tace
"ni....ni fah bansani ba da gaske "
Tashi yayi ya xauna kusa da ita idanun shi cikin nata yace
"ina son ki Mufidah bazan iya rayuwa babu ke ba kiyi min alkawari na kasance wa dani har abadan ba