Showing 81001 words to 84000 words out of 92754 words

Chapter 28 - YAYI SAKE COMPLETE BY A'ISHA A MUHD-1.pdf

10 Jul 2025

2463

taga yana
kallon wani gefe guda d'an murmishi tayi tana ayyana me zata yi yanzu wata dabara ce ta fad'o mata.


Ai kuwa take ta aminta da dabarar daman hill shoes ta sanya sai kawai ta gurd'e k'afar ta tana sani ta tafi
zata fad'i har da wani runtse idon ta kamar da gaske da k'arfin tace
"wayyo Allah Musaddiq "
Da sauri ya jiyo da kanshi ganin tana kok'arin kaiwa k'asa cikin sauri ya rik'o ta hannun shi yana tallafe da
hips d'in ta d'ayan kuma da hannun ta, hango tsananin rud'e wa tayi cikin kwayar idon shi.

"wash Allah na kafata"
Ta furta hkan tana yatsina fuska kamar zata fashe da kuka, cikin sauri da damuwa kan fuskar shi yace

"Ohhh mene ya samu k'afar? "
Ya k'arasa fad'i yana kallon ta, cikin shagwa6a tace
"ciwo take min "
"sorry mu k'arasa mu zauna sai na duba miki"

Gid'a kanta tayi sannan ya d'ago ta, sai tak'i take k'afar ya kalle ta yana cewa
"ya dai? "
"ni ciwo take min bazan iya tafiyar ba "

Kamar da gaske take fad'in hka shi yasa bai kawo wani abun cikin zuciyar shi ba ya sanya hannun shi ya
dauke cak suka fara tafiya hannun ta dukka biyun suna rataye a wuyan shi, fuskar tana wurin wuyan shi
duk wani numfashi da take fitar mai d'umi yana dukan wuyan nashi tuni Musaddiq ya fara jin wani canji
yanayi na daban a jikin shi, Mufidah kuwa sai murmishi take abin ta tana kalle kallen mutanen da suke
wurin wajen ya birge ta sosai ba ruwan wani da wani kowa harkar gaban shi yake.


Sun k'arasa inda zasu zauna ya sauke ta a hankali da sauri Mufidah ta canja fuskar ta irin ta damuwa sai
wani yatsina fuska take, zaunar da ita yayi yana cewa
"sannu "

Ya fad'i yana tsugunna wa a gaban ta tare da cire takalmin da yake k'afar ta bayan ya cire ne ya tsaya
kallon kyakkyawar k'afar ta ta kafin kuma ya fara d'an daddannawa kad'an cikin nutsuwa da hankali don
kada yayi mata da k'arfi ta sake jin wani ciwon.

"wash! da zafi ni ka bari zai warke fah "
Ta fad'a tana k'ak'alo hawayen dole.
"kinsan bazan jure ganin ki cikin ciwo ba don hka oya ki tsaya na gani "

D'ago kanshi yayi ya kalle ta sai yaga tana hawaye cikin rud'ewa ya saki k'afar ya zauna tare da janyo ta
jikin shi yana bubbuga bayanta yana cewa
"sorry habibty na bari ki daina kukan nan kin ji? "
Ai kuwa ta 6are baki ta saki kukan shagwa6a gashi tana kiran wayyo k'afar ta, kuma idan ya sanya hannu
zai ta6a ta dad'a k'arfin kukan tana girgixa kai kada ya ta6a da zafi.

Nan Musaddiq ya sake rud'ewa sosai shi yanzu ya zai yi mata ne idan zai ta6a k'afar zafi gashi bai ta6a
k'afar ba tana mishi kukan zafi kuma shi bazai jure jin kukan ta ba, ganin tak'i shiru duk ta d'aga mishi
hankali ne yasa shi had'e bakin shi da nata.


D'an tutture shi ta fara yi ya sake matse ta a jikin shi d'if tayi da ita tana kar6ar sak'onnin Musaddiq
daman ai kukan na k'ak'ale ne, sai da ya tabbatar ta had'iye kukan nata tukunna ya cikata suna had'a ido
ya sanya d'an yatsan shi d'aya ya dungure mata kai yana cewa
"rigimammiya ko Afnan bazata yi rigimar ki ba "

D'an hararar shi tayi tana turo bakin ta tace
"Duk rigima ta dai wani yafi ni "
Kallon ta yayi yana cewa
"dawa kike? "
D'an kad'a idon ta tayi tana cewa
"da wanda ya tsargu "
Nuna ta yayi yana cewa
"lallai yarinyar nan kin rainani da yawa xanyi maganin ki yanzu "

Kafin ya k'arasa fad'i ta mik'e da sauri zata gudu ya kawo hannun shi zai kamata sai ta goce tana mishi
dariya har da gwalo, nan ya biyo ta suka fara gudu tuni su Mufidah an mance ciwon k'afar karyar da aka
yi ta fara gudu tana dariya.

Bata yi wani nisa sosai ba ya cafkota suka zube cikin farin yashin da yake k'asan wajen suna dariya tare da
sauke numfashi da sauri da sauri, kallon junan su suke kafin Musaddiq ya sanya hannun shi ya d'an
lankwasa d'an yatsan ta d'aya har yayi k'ara cikin jin zafi tace
"wash ni me nayi maka ne da zafi fa?"
Yana kallon face d'in ta yace
"tunawa nayi da ciwon da k'afar ki take yi yanzu naga kuma kina gudu "
"bata warke ba na dai na jin zafin "

Ya bud'e bakin shi zai yi magana wayar shi ya fara k'ara alamar kira zaro wayar yayi ganin sunan Muh'd ya
sanya shi picking d'in wayar, d'aya hannun shi kuwa ya janyo Mufidah ya kwantar da ita saman chest d'in
shi don yau jin shi yake cikin wani irin farinciki da nishad'i.


Muryar Muh'd ce ya tsinkayo yana cewa
"Hey lover boy kana ji na?"
Murmishi Musaddiq yayi yana cewa
"ina jin ka mana ya akayi guy? "
"Qlau jin ka nayi wajen 2 day's baka kirawo ni ba na kirawo ka kuma baka yi picking ba "
"sorry guy abubuwa ne suka yi min over "
Cikin zolaya Muh'd yace
"ko kuma an tsaya cin soyayya ba an mance da ni "
Er dariya Musaddiq yayi yana kallon idon Mufidah yace
"kusan hkne fah guy kasan mutum idan yana moment d'in nan sai a slow "

Wata dariya Muh'd ya kwashe da ita yana cewa
"Ohhh sake maimaita min ban ji sosai ba "
"kai fa d'an air ne wani lokacin nasan ka ji abin da na fad'i "
"lallai guy kace kana nan kana fanshe soyayyar ka ta tsayin shekaru, hkan yayi kyau Allah ya kawo mana
baby boy ko girl "

Hannun Musaddiq yana kan Mufidah yana shafawa yace
"Amin aboki tare da kai "
"tabd'ijam an fad'a maka zan jira ka ne ai ni an kusa juye min "
"Ah haba aboki da gaske? "
Musaddiq ya fad'a cikin farinciki, cikin tabbatar wa Muh'd yace
"wallahi aboki da gaske na ke "
"wowww na taya ka murna sosai guy "

Jin d'an hayaniya yasa Muh'd yace
"kana ina ne Musaddiq ?"
Cikin murmishi yace "me ka ji ne? "
"hayaniya na ji kamar ma baka gida "
"ina wurin beach muna hutawa "

Cikin dariya Muh'd yace
"wow lover boy kace kana hutawa, a dai yi a hankali kada ka 6ata mana Afnan don nasan ba hak'uri ne
da kai ba ana barin sai bata nan "

"Allah ya shirya ka Muh'd"
"Amin aboki thank for your du'a"

Kafin kuma ya cigaba da magana in seriously yace "Musaddiq ya kamata ka dawo nigeria fah kaga kai
d'aya su mumy suke dashi a yanzu duk da basu nemi wani abin sun rasa amman nasan basa son zaman
ka a australian, sun fi son zaman ka a tare da su ya kamata ka dawo "

Ajiyar zuciya Musaddiq ya sauke a hankali kafin yace
"nima nayi tunanin hka friend but insha Allah nan da d'an lokaci xamu dawo"

"Yawwa d'an uwa, agaida min da Mufidah nd Afnan, kace wa Mufidah kasa ta mance da ni tun da kuka zo
bamu ta6a yin waya ba ina jin zata kirawo k'awar ta (nafisat matar Muh'd),su sha hira amman ban da ni "

Dariya Musaddiq yayi kafin yace " hkan ne dai dai guy "
Shima Muh'd yana dariya yace "kai koh?, shikenan dai sai anjima "
Yana gama fad'in hka Muh'd ya katse wayar lokaci d'aya Musaddiq ya saki ajiyar zuciya yana sake hugging
d'in Mufidah zuciyar shi tana cikin farinciki.............




Aishat A Muh'd ✍
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*



*Written by*
Aishat A Muh'd

♻ *£xclusive Writers Forum*

*Likes nd comment's fb page*
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
Email:Aishataudimuhd.as@gmail.com




*PAGE 56*




Yana gama fad'in haka Muh'd ya katse wayar, lokaci d'aya Musaddiq ya saki ajiyar zuciya yana sake
hugging d'in ta zuciyar shi tana cikin farinciki, gaba d'aya ya mance ma inda suke ya mance yana tare da
Mufidah a kusa zuciyar shi ta ingiza bakin shi har ya furta kalmar
"i luv u Mufidah "
Ba tare da ya shiryawa hakan ba, sai da ya gama furta maganar sannan ya dawo cikin hayyacin shi ya tuna
su6utar bakin da yayi.

Mufidah kuwa kusan suman zaune tayi saboda jin kalmar da ta fito daga bakin Musaddiq kallon shi take
fuskar ta d'auke da tarin mamaki.

Wayancewa yayi ta hanyar hararar ta kafin yayi magana cikin sautin tsawa yace
"malama d'aga ni zan tashi kin wani danne ni "
Girgiza kanta kawai tayi tana tashi daga jikin shi, bata ko kalle shi ba ta nufi inda suka yi parking motar su
ta tsaya tare da sunkuyar da kanta tana kallon k'asa zuciyar ta sam babu dad'i, don ta tsani ayi mata
tsawa a rayuwar ta.

Bin ta yayi da kallo jikin shi yayi sanyi sosai wani mugun tausayin ta ne ya rufe shi,akan mene zai yi mata
tsawa me tayi mishi, dole yayi yak'i da zuciyar shi don samun zaman lafiyar su, bazai yiwu su cigaba da
irin wannan zaman ba.


Jikin shi a sanyaye ya fara tafiya zuwa inda take, bud'e motar yayi da key d'in hannun shi, cikin sauri
Mufidah ta shiga ta zauna har yanzu still bata kalli inda yake ba, shima shiga yayi ya zauna ya kasa kunna
motar su tafi kallon ta yake yi ko zata d'ago kanta ta kalle shi.


Sun d'auki tsayin mintuna bai ga alamar zata yi mishi magana ba ko zata kalle shi, sai kawai yayi wa motar
key suka bar beach d'in, tafiya suke shiru kowannen su zuciyar shi da abin da take sak'awa, sam dawowar
bata yi musu dad'i ba kamar yanda suka taho ba cikin farinciki da nishad'i ba.


Suna k'arasa wa gida yana gama parking Mufidah ta bud'e murfin motar ta fita tare da bud'e murfin
motar na baya ta d'auki Afnan dakyar ta fito tana tafiya har tana kok'arin fad'uwa.

Da kallo ya bita fuskar shi da zuciyar shi d'auke da damuwa yana son yi mata magana but bakin shi yayi
mishi nauyi sosai ya kasa yi mata magana, yana kallon ta har ta shige ciki tukunna ya fito daga motar tare
da d'ebo shopping d'in da suka yi ya nufi cikin gidan.


Ko da ya shiga bata parlour kayan hannun shi ya zube su tare da zama kan kujera yana dafe da kanshi,
tunanin hanyar da ya kamata ya bi don ya rarrashe ta yake, yasan bai kyauta ba da tsawar da yayi mata.


Mufidah kuwa tana shiga d'aki ta kwantar da Afnan kan bed sannan ta wuce toilet ta d'auki tsayin
mintuna 5 a ciki kafin ta fito, fitowa tayi daga d'akin zuwa kitchen don ta had'a musu abincin dare.

A parlour ta tarar dashi zaune bata kalli inda yake ba ta wuce kitchen abin ta, da kallo ya bita zuciyar ta
gama yanke hukuncin a yau ba gobe ba zai bayyana mata irin tarin son da yake mata.


Lumshe idanun shi yayi sakamakon fara jin k'amshin girkin da take yi ya fara dukan hancin shi, yana nan
zaune Afnan ta tashi daga bacci ta fito zuwa parlour, cikin jikin shi ta shiga tana kwanciya, shafa mata
kanta kawai yake don baya cikin nutsuwar shi.


Bayan ta gama girkin ne ta jera a saman dining table, duk zirga zirgar da take akan idon shi d'in yana nan
zaune a parlourn, bayan ta gama ne ta gyara kitchen sannan ta fito zuwa parlour ta gyara ta fesa air
fresheners masu k'amshi.


Tana gama wa da nan ta nufi d'akin Musaddiq ta gyara mishi tsaf, tare da sanya mishi room freshener, sai
da taga komai yayi mata yanda take so sannan ta bar d'akin, tukunna ta fito ta nufi d'akin ta gyara shi tayi
shima yayi tsaf dashi.


Sannan ta fito zuwa parlour inda Musaddiq yake ta nufa, sai da ta zo gaf dashi sannan ta kalli Afnan tace
"Afnan zo nayi miki wanka "
Tashi Afnan tayi ta nufi inda Mufidah take tsaye, hannun ta ta rik'e suka wuce d'aki, ta bar Musaddiq
zaune anan cikin rashin samin mafita.

Bayan tayi wa Afnan wanka ta gyara mata jikin ta ne cikin kayan bacci, tukunna Mufidah ta d'ebo musu
abincin su ta bar na Musaddiq akan dining table, bayan sun gama ci ne, Mufidah ta kwantar da Afnan kan
ta yana kan cinyar Mufidah tana karanta mata wani english novel's mai dad'i.


Lokacin da Musaddiq ya wuce bedroom d'in shi yaga bata yi fushi ba ta tsaya ta gyara mishi sosai, sai yaji
ya k'ara jin tausayin ta, wanka yayi tare da yin alwala ya fito, jallabiya ya zura ya fara gabatar da sallah
bayan ya idar ne ya d'an jima yana addu'o'i kafin kuma ya tashi.


Cire jallabiyar yayi ya canja da wasu white sleeping dress ya fesa turaren shi masu k'amshi, tukunna ya
fito zuwa parlour dinning table ya nufa, amman wayam ya gani ba Mufidah da Afnan kuma wannan ne
time d'in da suke had'u wa wajen cin abincin dare.


Jikin shi ne ya k'ara yin sanyi a time d'in da ya tabbatar iya nashi abincin ta bari, bai wani iya ci sosai ba ya
d'an ci kad'an ya tashi koma parlour ya zauna, tv ya k'ura wa ido yana kallon film d'in Jack the giant slayer
da suka nuna wa a time d'in but zuciyar shi tana tunanin Mufidah.


Tun Afnan tana sauraren ta har bacci ya d'auke ta, ganin tayi bacci ne yasa Mufidah gyara mata
kwanciyar, ta d'ora kanta saman pillow ta lullu6e ta da blanket tare yi mata addu'a sannan tayi kissing
nata a kumatu, d'ayan hannun ta yana gyara mata gashin kanta ganin ya rufe mata face d'in ta.


Tashi tayi tsaye taga Afnan tana rik'e da hannun ta, murmishi ta saki tare da sunkuya wa ta cire hannun
ta a hankali wanda Afnan ta rik'e, sannan ta rage hasken d'akin ya d'an yi duhu.

Toilet ta wuce ta fara yin wanka, bayan ta gama ne sannan ta fito zuwa gaban dressing mirror ta fara
gyara jikin ta tare da amfani da body sprays a jikin ta da humra.


Sleeping dress d'in ta ta d'auko a cikin wardrobe nata, cire towel tayi tana kok'arin sanya kayan baccin,
sai ji tayi an rungume ta ta baya, a tsorace ta saki er k'ara tare juya wa don ganin wane, jikin ta har rawa
yake don ba k'aramin tsorata tayi.


Saukar sanyayar muryar shi taji cikin kunnen ta yana cewa
"calm down matsoraciya ni ne fah "
Juyo wa tayi tana hararar shi cikin tsiwa tace
"malam baka iya sallama ba ne zaka shigo min d'aki kai tsaye? "

Kallon ta yake fuskar shi d'auke da murmishi cikin zuciyar shi yana cewa ta rama kenan, a fili kuma yace
"ai ba laifi ba ne da na shigo d'akin mata ta koh?"
Cikin mamaki tace "matar ka!"
"Ehhh mana, ko laifi ne ?"
D'an ta6e bakin ta tayi kawai, sam ta mance a yanayin da take, ganin irin kallon da yake bin ta dashi ne
yasa ta kallon jikin ta.


Zaro ido tayi tare da d'ora hannu akan ta tana sakin 'yar k'ara tare da zube wa a k'asa, ta had'e jikin ta
waje d'aya cikin jin kunyar shi sosai.

Dariya ta bashi sosai sai da yayi mai isar shi kafin ya tsugunna a gaban ta yana kallon ta yana cigaba da
dariya.

Cak ya tsaya da dariyar saboda ganin hawaye yana fita a idon ta, hannun shi ya sanya tare da kama
kunnen shi dukka biyun yace
"I'm so sorry Mufidah, nasan nayi miki laifi d'azu na tsawar da nayi miki, bazan k'ara ba fushin da kika yi
dani, bazan iya jure hakan ba, forgive me please "

D'an girgiza kanta tayi kawai bata iya cewa komai ba, langa6e kan shi yayi tare da cewa
"please Mamin Afnan"
Turo bakin ta tayi tare da cewa
"ka fita idan na gama shiryawa ma yi maganar"
Kafin ta ankare har ya sure ta gaba d'ayan ta ya nufi hanyar fita daga d'akin nata, don yau yana son ya
warware matsalar su..........



Aishat A Muh'd ✍
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*



*Written by*
Aishat A Muh'd

♻ *£xclusive Writers Forum*
*Likes nd comment's fb page*
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
Email:Aishataudimuhd.as@gmail.com

*PAGE 57*




Kok'arin sauka take but yak'i sakin ta har ya k'arasa cikin d'akin shi, kan kyakkyawan bed d'in yayi
mata masauki, cikin shagwa6a tace
"ni fah bacci nake ji malam "
D'an zaro ido yayi yana dariyar mugunta kafin yace
"yarinya ai yau ke da bacci sai gobe "
Ya k'arasa fad'a yana kashe mata ido d'aya, duk da kuwa bata ganin shi sosai saboda d'akin babu
wadataccen haske, hararar shi tayi tana kok'arin sauka daga kan bed d'in.

Ai kuwa ya sanya hannun shi ya fisgo ta cikin jikin shi, ta bud'e baki zata yi magana taji ya rufe shi da
nashi, sai da yayi kissing d'in ta son ran shi, kafin ya cika ta suna kallon idanun junan su.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login