Showing 72001 words to 75000 words out of 92754 words
Chapter 25 - YAYI SAKE COMPLETE BY A'ISHA A MUHD-1.pdf
ta kwance iya layin da suke ta tsaya a karshen shi
kafin ta jiyo ta dawo sai da ta kusan shiga gida ne wani bature ya matso inda take kamar xai rungume ta
yana cewa
"hey babe you're so beautiful, what's u name ?"
A d'an tsorace mufidah ta d'ago kanta tana kallon shi tana kok'arin matsawa taji an taka wani uban birki a
wajen, nan mufidah ta k'ara rud'e wa don Sauran kad'an a kwashe ta da mota, d'ago kan da xata yi ta
hango musaddiq yana fito wa daga motar kamar wani xaki yanda ya wani fusata fuskar nan a d'aure babu
alamar fara'a gashi idon shi sun ja inda suke ya nufa kafin ya k'araso mufidah ta afka cikin gidan a tsorace
jikin ta har rawa yake yi ta wuce bedroom da gudu ta rufe tana haki xuciyar ta na bugawa da k'arfi don
bata ta6a ganin musaddiq a wannan yanayin ba.
Batasan ya suka k'are da baturen ba tana nan xaune wajen mintuna 15 taji gidan tsit alamun baya gidan
wata ajiyar xuciya ta sauke ta kwanciyar hankali kafin ta shiga toilet ta watsa ruwa don tafi jin dai dai tana
fitowa taji wata kishirwar ruwa ta kamata ga ba ruwa a d'akin tana d'aure da towel d'in ta fito xuwa
parlour ta bud'e frige ta d'auki bottle d'in ruwa rufe frige d'in da xata yi ta jiyo ta ga musaddiq a gaban ta,
batasan lokacin da bottle d'in ruwan ta fad'i ba ta dafe kirjin ta a tsorace saboda irin kallon da taga yake
bin ta dashi.
Matsa wa baya ta fara yi a hankali yana bin ta a baya har sai da ya k'ure ta a jikin bango ganin bata da
wata mafita yasa ta bud'e baki cikin rawar murya tana cewa
"mus......musaddiq ka.....ka tsaya nayi maka ba.... bayani ni wlh ban.....bansan shi ba kawai........"
Kasa k'arasa maganar tayi ganin ya d'aga hannun shi sama da sauri ta runtse idanun ta tana cikin tsoro
don tasan marin ta xai yi, gaban ta yana wani mugun bugawa, jin shiru bata ji saukar marin ba yasa ta
bud'e idon ta d'aya a tsorace tana kallon shi ganin kallon da yake mata yasa ta sake runtse idon da k'arfi
cikin tsoro.
Hannun shi ya sanya a saman fuskar ta sai jin shi tayi yana Shafa fuskar ta tare da gyara mata gashin ta da
ya manne mata a fuskar, sake runtse idon tayi da k'arfi jikin ta yana rawa saboda jin yanda yanayin ta ya
fara canja wa tana sauke numfashi da sauri sauri, sai da ya gama gyara mata gashin fuskar ta ta fito sosai
kafin yace
"waya baki ixinin fita daga gidan nan, har wani ya tsayar da ke? "
Shiru tayi mishi ta kasa magana jin hka ya shi cewa cikin tsawa
"kina jin ina miki magana kin min shiru I'll slap u mufidah idan baki yi min magana ba ?"
Gaba d'aya ta sake rikice wa da tsawar da yayi mata aikuwa ta fad'a jikin shi tare da rukunkume shi tana
kuka sosai, lokaci d'aya yaji wani irin shock a jikin shi dif yayi shiru yana sauraren kukan ta da ya fara
sanyayar mishi da jiki, cikin kukan muryar ta na rawa tace
"ka...... kayi ha.....hak'uri don Allah ni bani ce na kula shi ba baxan k'ara fita ba "
Baisan sanda ya k'ara rungume ta ba yana bubbuga bayanta tare da cewa
"it's okay kada ki k'ara hkan "
Gid'a kanta tayi tana sauke ajiyar xuciya sun d'auki en mintuna a hka kowannen su yana sak'a abu cikin
xuciyar shi kafin kuma su ankara cikin sauri kowanne ya janye jikin shi kamar had'in baki, a tare kuma
suka harari junan su mufidah har da murgud'a baki.
"keee ni kika murgud'a wa baki? "
Ya fad'i hkan yana mik'a hannu xai cafko ta aikuwa unexpected hannun shi ya dira a jikin towel d'in ta ya
ja ae kuwa sai yayi k'asa a tare kamar had'in baki suka saki k'ara, da sauri mufidah ta durkushe yayin da
shi kuma musaddiq ya juya da sauri ya fice daga parlourn yayi hanyar fita don time d'in d'auko afnan
daga skul yayi.
Tana ganin fitar shi ta wawuri towel d'in ta d'aura ta wuce bedroom da gudu sai da ta rufe kofa ta jingina
a jikin ta tare da dafe kirjin ta tana cewa
"wayyo Allah na amman musaddiq kirkin shi ya ragagge ne shine don wulak'anci xai wani rik'e min towel
idan fah ya cire gaba d'aya fah "
Tana haki ta furta hkan, kusan kwanaki biyu suna wasa 6uya a tsakanin su.
Kamar yau wurin 9 na dare mufidah taje ta kwantar da afnan a bedroom ta fito xuwa parlour don k'arasa
kallon film d'in da take yi, xaman ta da kamar mintuna 10 musaddiq ya fito daga d'akin shi yana d'aure da
towel fitowar shi daga wanka kenan ya tuna ya mance phones nashi da laptop d'in shi a parlour tun da
mufidah ta ganshi a hka ta runtse idon kamar mai bacci.
Murmishi ya d'an yi don kallo d'aya yayi mata yasan ba bacci take ba, daukan laptop d'in da phone's
nashi yayi har yaxo xai wuce ta inda take ya d'an taka mata kafa, wata er k'ara ta saki tare da saurin bud'e
idon ta tana yatsina fuska don taji xafi
"malam mene hka xaka taka ni don mugun ta "
Shima d'aure fuskar yayi tare da cewa "ki had'a min coffee ki kawo min yanxu "
Yana gama fad'in hka ya nufi bedroom d'in shi ya shiga, sai kawai mufidah ta tsinci kanta da tashi ta nufi
kitchen ta had'a mishi sannan ta nufi bedroom d'in, wannan Karon shine shigar ta na farko d'akin yayi
mugun tsaruwa d'akin fad'in yanda yake 6ata lokaci ne.
Ko sallama bata yi ba ta shiga d'akin kanta tsaye kamar wani nata, ai kuwa idanun ta suka sauka kan
musaddiq da yake kunce towel d'in shi xai sanya sleeping dress jikin mufidah ya fara 6ari na tsoro tuni ta
saki tiren da ta d'ora mishi coffee d'in akai tare da runtse idon, shima kanshi musaddiq yaji wani iri Co's
bai xaci xata kawo mishi coffee d'in ba ma balle har ta shigo mishi bedroom daman ya fad'a ne don
tsokana ae kuwa ya juya bayan shi yana saurin k'arasa sanya kayan shi, Bayan ya gama sanya ne ya
k'arasa inda mufidah take tsaye cak jiki na 6ari ya fisgo ta jikin shi da k'arfi har sai da ta saki k'arar tsorata
ta bud'e idon ta da sauri, sai suka had'a ido kallon so da kaunar da suke yiwa junan su suka fara sun
d'auki tsayin mintuna 5 suna a haka kafin musaddiq yace
"keee waya sa ki shigo min bedroom kan ki tsaye? "
Cikin dakiya da tsiwa mufidah tace
"ba kaine kace na had'a maka coffee ba "
"toh naji kin ga wani abin ne? "
Cikin rashin fahimtar abin da yace mufidah tace
"kamar me fah, ban gane ba? "
Ajiyar xuciya ya sauke cikin xuciyar shi yana cewa Alhmdlh Allah nagode maka da bata ga wani abun ba, a
fili kuwa d'an murmusa wa tare da cewa
"okay shikenan ma "
Da kallo mufidah ta bishi na mamaki mutum kamar mai iska yanxu ki ga yayi murmishi anjima kuma fuska
a d'aure, hure mata ido yayi yana cewa
"ni kada ki cinye ni wannan Kallon fah? "
Ya k'arasa fad'i yana d'aga mata gira hararar shi tayi tare da wayancewa tace
"Cabd'jam wa xan kalla kai Allah ya kiyaye "
Girgixa kanshi yayi har yanxu mufidah tsiwar nan ta nanan "ki je malama ki k'ara had'a min coffee ki
kawo min "
Ta bud'e baki xata yi magana kenan taji ya had'e bakin ta da nashi ya fara yi mata wani soft kiss xaro ido
mufidah tayi kirjin ta na bugawa da k'arfi, sai da ya dauki wajen mintuna 5 a hka kafin ya rabu da ita ai
kuwa yana sakin ta mufidah ta fita daga d'akin da gudu, shi kuwa musaddiq xube wa yayi kan bed cikin
wani irin yanayi mai wuyar fassara................
Aishat A Muh'd ✍
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*
*Written by*
Aishat A Muh'd
♻ *£xclusive writers forum*
*likes nd comment's fb page*
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
_where are u guys this page dedicated to urs, ummu safwan marubuciyar (k'unar xuci),hafcycy, princess
Ayeesha, farida, my dgter Mariam Omar, sis zahra (ke ta daban ce), baby, lil Ridallah and all member's
Aishat A muh'd fan's ina jin dad'in yanda kuke kaunar littafin nan, wannan shafin na sadaukar muku dashi
kyauta ina alfahari da ku_ #one luv guy's
*PAGE 50*
Tun daga lokacin mufidah ta dauke k'afar ta daga xaman parlour idan har afnan tayi bacci da dare
saboda yanda musaddiq yake bin ta da wani mayataccen kallon kamar ya lashe ta, wanda kallon da yake
mata ba k'aramin k'ara mata son shi a xuciyar ta yake ba, kula wa dasu sosai yake sai dai wani lokacin ya
birkice mata kamar ba musaddiq ba ya xame mata abin tsoro yanda xai na d'aure fuskar shi magana ma
sai ya ga dama xai yi mata, wani lokacin kuma tsokana xai dame ta dashi har sai ta gaji ta gudu d'aki ta
rufe kanta.
Kowannen su xuciyar shi cike da kaunar junan su but miskilanci ya hana kowa bayyana wa kansu abin da
yake kunshe cikin xuciyar su, sai faman nuk'u nuk'u suke da abu, mufidah ana ta ganin da tunanin bai
kamata ta bud'e baki ta fad'a mishi tana son shi ba tun da ita d'iya mace ce kuma ansan macen da tasan
kanta akwai alkunya da kawaici matsayin ta na mace kenan.
Shi kuwa musaddiq yana son furta mata sometimes yasha yunk'urin fad'a mata but sai ya fara tunanin
mufidah fah matar d'an uwan shi ce fa a da, taya xai iya sakin jiki da ita ya fad'a mata yana son ta har
takaisu da yin wani abu daban anya xai iya hkan, wannan tunanin da yake shi yake karyar mishi da gwiwa
ya kasa tunkarar mufidah shi yasa wani time d'in ya rikid'e mata yayi ta d'aure fuska ko magana baya son
yi mata, but cikin xuciyar shi ba hka ba ne sam baya jin dad'in abin da yake mata.
Irin xaman da suke yi irin xama ne da kowa yayi sha'anin gaban shi, sai dai suna cin abinci a dining tare
kuma mufidah ce take yi musu girki ta wannan 6angaren bashi da matsala yana xama yaci abincin ta
sosai don ta iya girki mufidah abincin ta nayi mishi dad'i sosai.
A hka suka kwashe wajen watanni biyu suna irin wannan xaman nasu a cikin wannan lokacin musaddiq ta
kai shi da ya fara gajiya da dauriyar da yake yi akan mufidah saboda irin shigar da take yi yake ganin ta,
duk da ba wata shigar da take fito mata da surorin jiki take ba amman hkan ba k'aramin hargitsa shi ba,
dare yana mishi tsayi sai dai yayi ta faman juyi yana sintirin xuwa bedroom d'in mufidah yana kallon ta
tare da furta mata kalmar I luv u amman ya kasa bayyana hkan a gare ta.
Har gwara da safe xuwa yamma yana hospital aikin shi na dauke mishi tunanin mufidah, gashi yana son
su koma gida nigeria gaba d'aya don yana son ba wa iyayen shi kulawa tun da yanxu shi kad'ai ya rage
musu, gwara ya xauna kusa dasu xasu fi jin dad'i shima sai hankalin shi yafi kwanciya, a kullum cikin yiwa
sadeeq addu'a yake har yanxu cikin kewar d'an uwan nashi yake yana son sadeeq so mara misaltuwa son
da yasan har shima ya mutu baxai daina yi mishi yana addu'a da fatan Allah ya bashi d'a namiji ya sanya
sunan shi.
Afnan ce da mufidah a xaune a parlour wajen misalin karfe 9 na dare mufidah na shan fruit yayin da
afnan take shan ice cream can ta ajiye ice cream d'in tare da langa6e kai tace
"mamee na bacci na ke ji"
Murmusa wa mufidah tayi tare da cewa
"ki tafi bedroom ki kwanta ni sai na k'arasa kallon film d'in da nake kallo "
Sake shagwa6e fuska afnan tayi tare da cewa
"ni mamee tare da ke xan kwanta "
Hannun ta mufidah tasa ta ja kumatun ta tare da cewa
"okay baby nah tashi mu tafi "
Cikin jin dad'in abin da mufidah ta ce ta mik'e tare da kama hannun ta tace
''thank u mamee nah "
Daga hka suka wuce bedroom, suna tafia musaddiq ya fito daga nashi bedroom d'in hasken bulb d'in
parlourn ya kashe sai hasken jikin tv kawai kwanciya yayi kan 3siter tare da sanya hannun shi ya d'auko
remote ya canja tasha xuwa wata channel da suke film d'in horror mai suna residents evil yana kallon shi
hankali kwance.
Lokacin da mufidah suka shiga bedroom ne bayan ta canja wa afnan kayan jiki ta tare da lullu6e ta da
blanket tayi mata addu'a sannan tayi mata peck a kumatun ta tana cewa
"sweet dreams baby nah"
"thank u mamee nah "
Murmishi suka sakarwa junan su kafin afnan ta rufe idon ta, ganin hka ya sanya ta wuce wa toilet wanka
tayi kafin ta fito shirya wa tayi cikin wasu cotton d'in sleeping dress riga da wando masu laushi farare
dasu sai dai tsayin wandon bai kai har k'asa ba.
Gyara gashin kanta tayi tare da sanya ribbon ta d'aure shi perfumes ta fesa sannan ta fito xuwa parlour
don ta cigaba da kallon ta, tun kafin ta k'arasa cikin parlourn k'amshin perfumes d'in ta ya fara shak'ar shi
a kofofin hancin shi.
K'ura mata ido yayi har ta k'araso cikin parlourn bata kula dashi ba ta xauna tana janyo ice cream d'in ta
sha ta fara yi hankalin kwance tana kallon film d'in da musaddiq ya sanya sam batasan film d'in da yake
kallo ba tuna ita ba ma'abociyar kallon horror movies ba ce.
Gashi bata san musaddiq yana parlourn ba yana aiki kallon ta sai lashe lip's yake yana Kallon cute lip's
d'in ta yana motsi yayin shan ice cream d'in da take, yana ayyana wasu abubuwa cikin xuciyar shi.
Ta d'ebo ice cream d'in xata sanya a baki idon ta akan tv unexpected ta ga an nuno wasu horror bakyan
gani bakin su kaca kaca da blood, wani tashi mufidah tayi wanda sai da komai na jikin ta yayi motsi tare
da sakin k'ara tana runtse idon ta don sam jinin ta bai had'u da kallon irin moves d'in nan ba.
Jikin ta sai 6ari yake tsabar tsoro da raxana tana cikin lalu6en hanyar guduwa bedroom ta rufe kofa sai
taji tayi tuntu6e tare da hantsila wa kan kujerar da musaddiq yake kai ta fad'a kanshi.
Nan ta sake rud'e wa da gigice wa don bata gane ko waye ba jin da tayi an rik'e ta k'am yasa ta dad'a
kwalla k'ara a karo na uku ta bud'e baki sosai da k'arfi tana cewa
"wayyo Allah na musaddiq kaxo ka taimaka min wani horror ya rik'e ni xai shanye min Jini"
Iyakar k'arfin ta take kwad'a mishi Kira da neman taimakon shi, sai kokawar kwatar kanta take amman ta
kasa tuni ta fara jan wani irin numfashi alamun daf take da sume...........
Aishat A Muh'd ✍
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*
*Written by*
Aishat A Muh'd
♻ *£xclusive writers forum*
Likes nd comment's fb page
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
_ina kuke kawayen arxiki da karamci wannan shafin na ku ne kyauta ina alfahari da ku, zeee yabour
marubuciyar (itace kaddara ta), sajida niger marubuciyar (duk karyar kada ta ruwa ce), khadija neenah
tawa marubuciyar (Deejah) salma Ali wada marubuciyar (namijin gaske), my biebie dear marubuciyar
(d'an hakin da ka raina), and Queen Ayush marubuciyar (ya sayyadi), ni Aishat A Muh'd ina muku fatan
alkhairi Allah ya bar xumunci ina yin ku guy's_
*PAGE 51*
Ganin tana neman sume mishi a wurin ya sanya shi gimtse dariyar muguntar da yake yi mata tare da
sanya hannun shi yayi hugging d'in ta very tight kafin kuma yayi amfani da d'ayan hannun shi yana
bubbuga mata bayanta cikin kunnen ta yake furta
"shhhhhhh mufidah calm down kina tare da ni babu abin da xai same ki relax "
Jin muryar musaddiq ne yasa shi saukar mata da wata nutsuwa ta daban sai ta fara sauke ajiyar xuciya
har yanxu dai jikin ta 6ari yake na tsoro gashi kirjin ta sai bugawa yake da k'arfi ta bi ta wani k'ank'ame shi
sosai idon ta a runtse suke don tana tunanin idan ta bud'e su xata iya ganin horror d'in da ta gani.
A hankali yake bubbuga bayanta tare da hura mata iskar bakin shi cikin kunnen ta hkan ba k'aramin
saukar mata da kasala yayi ba, babu dad'e wa bacci yayi awon gaba da ita a hkan gashi kuma duk tabi ta
k'ank'ame shi sosai da dubara ya tashi tare da kashe tv d'in ya dauke cak bedroom d'in ta ya kaita ya
kwantar da ita kan bed.
Tashi yayi niyyar yi amman yaji ta dad'a k'ank'ame shi kamar wadda idon ta biyu sai ya koma ya xauna
tare da kafe da ido yana wani murmishi shi kad'ai yasan ma'anar murmishin nashi, ya dad'e xaune a hkan
yana tunani na daban a karo na