Showing 78001 words to 81000 words out of 92754 words
Chapter 27 - YAYI SAKE COMPLETE BY A'ISHA A MUHD-1.pdf
xuciya.
D'ago kanta yayi yana kallon innocent face d'in ta yace
"Mufidah nasan ba bacci kike ba ki bud'e idon ki ki kalle ni, ki fad'a min matsalar ki please "
Wasu hawayen su suka sake xubo wa cikin xuciyar tana cewa Musaddiq babu abin da yake damuna sai
halin da kake ciki ciwon da sona ya haddasa maka shi ya sanya ni shiga cikin wannan yanayin, a fili kasa
magana tayi saboda yanda bakin ta yayi mata nauyi sosai.
Muryar shi kamar xai fashe da kuka yace
"na rok'e ki Mufidah ki sanar da ni "
"daddy mai ya samu mami na? "
Yaji muryar Afnan cikin tsakar kanshi, wayance wa yayi da k'ak'alo murmishin yak'e yace
"Afnan babu abin da ya sami mamin ki bacci take yi "
"toh daddy I'm hungry "
Ta k'arasa fad'i tana yatsina fuska, ya rasa yanda zai yi Afnan zai je ya bawa abinci ko kula ya tsaya kula
da Mufidah, ganin Afnan zata fara yi mishi kuka ya sanya shi ajiye Mufidah suka fito parlour yana waigen
Mufidah.
Sai da ya zuba wa Afnan abinci a plate tare da drink a cup ya zaunar tare da kunna mata tv channel d'in
cartoon ya ce
"babyn daddy kiyi xaman ki anan idan kin gama cin abincin ki kalli cartoon yanxu xamu fito da mamin ki,
kin ji? "
Afnan wadda take kai spoon na abinci baki ta gid'a mishi kanta tana murmishi, shima murmishin yayi
yana jan kumatun ta na gefen dama kafin kuma ya wuce bedroom d'in Mufidah da sauri.
A yanda take lokacin da ya fita a hka ya same ta da sauri ya k'arasa inda take tare da hawa saman bed
d'in ya yaye blanket d'in da ta rufa tare da d'ago ta gaba d'ayan ta ya zaunar da ita cikin jikin shi yana
tatta6a jikin tare da duba ta don ya fahimci abin da yake damun ta.
Ganin bashi da kayan aiki cikin bedroom d'in ta yasa shi daukan ta ya nufi bedroom d'in shi da ita, yana
bud'e kofar wani sassayan K'amshi mai dad'i ya fara ziyartar hancin kafin ya shimfid'e ta saman bed d'in
shi da yasha gyara.
Jiki na 6ari ya fara duba ta bai ga wani babban ciwo fiye da damuwa tare da kukan da tayi ne ya janyo
mata xaxxa6in da ciwon kai, zuba mata ido yayi yana kallon ta cikin xuciyar shi yana tunanin wacce irin
damuwa ce ta haddasa mata ciwo hka, gashi tak'i magana kuma har yanzu idon ta a rufe suke sai dai
hawayen da yake zubo mata.
Nan ya fara lalla6a ta don ta fad'a mishi abin da yake damun ta amman kamar da dutse yake magana,
ganin baza ta kula shi ba yasa shi tashi bathroom ya nufa ya samu wani bowl mai kyau ya tari ruwa a ciki
sannan ya d'auki towel k'arami ya fito xuwa inda take.
Ajiye bowl d'in yayi saman bedside sannan ya fara kok'arin zame kayan jikin ta, ai kuwa da sauri ta mik'e
zaune tare da bud'e idon ta tana rarraba su kamar wata mara gaskiya hkan da tayi ba k'aramin sanya
Musaddiq dariya yayi ba amman sai ya gimtse ta.
Ya cigaba da cire wa cikin tsoro Mufidah tace
"Musaddiq mene haka kuma? "
D'an murmishi yayi tare da cewa "jikin shi ya d'auki xafi da yawa ina son xan goga miki ruwa ko xafin ya
ragu "
Cikin rawar murya tace
"ni.... ni gas.....gaskiya a'a zai daina "
Wani murmishin gefen kumatu yayi tare da girgixa kanshi yace
"bazai yiwu ba Mufidah idan baki damu da rashin lafiyar ki ba wasu sun damu "
D'ago kanta tayi da sauri ta kalle shi cikin mamaki wato bama xai ce ya damu ba sai wasu da akwai aiki a
gaban ta kuwa wajen tankwara zuciyar Musaddiq ya sakko su gyara zaman auren su.
Gira ya d'aga mata kafin ya fara cire kayan runtse idon ta tayi gam har ya gama cire wa sai iya underwears
kawai ya bar mata, sake runtse idon ta tare da k'ank'ame jikin ta tana jiran saukar ruwa a jikin ta amman
taji shiru har tsayin wasu en mintuna.
A hankali ta fara bud'e idanun ta suka had'a ido kuwa sake rufe su tayi da sauri ganin ashe zuba mata ido
yayi yana kallon ta son ranshi wata irin kunya ce ta gama lullu6e Mufidah.
Musaddiq wanda gaba d'ayan shi ya fara fita hayyacin shi ya kasa dauke idon shi akanta, gaba d'aya idon
shi sun fara canja launi ga wani abu da yake ji yana tsirga mishi daga cikin brain d'in shi xuwa gangar jikin
shi, wani tunani na daban ya fad'a 6angare guda kuma wani mugun son Mufidah ne yake dad'a ratsa
zuciyar shi.
Dakyar ya iya saita kanshi ya fara goge mata jikin nata had'uwar tattausar fatar jikin shi da nashi, shi ya
sake haddasa Musaddiq shiga wani mayuwacin hali wanda ba don yana kok'arin danne abin da yake ji ba
da xa'a yi mai gaba d'aya a yanxu.
Bayan ya gama ne ya mayar mata da kayan sannan ya had'a mata tea a baki ya dunga bata har ta d'an sha
tukunna yayi mata allura wanda yasha fama da ita kafin ta tsaya yayi mata, hka magani ma dakyar ta sha
sannan ya kwantar da ita cikin jikin shi har bacci ya dauke ta mai nauyi tana jikin shi yana aikin kallon ta
lokaci zuwa lokaci yana sakin murmishi shi kad'ai yasan zuciyar shi yanzu ta samu nutsuwa tunda ta sami
abin da take muradin so.............
Aishat A Muh'd ✍
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*
*Written by*
Aishat A Muh'd
♻ *£xclusive Writers Forum*
*Likes nd comment's fb page*
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
Email:Aishataudimuhd.as@gmail.com
*PAGE 54*
Zame ta yayi daga cikin jikin shi ya tare da kwantar da ita kafin ya tashi ya fito xuwa parlour wurin
Afnan sai ya tarar ta 6ingire tana shan baccin ta kan carpet, d'an murmishi yayi tare da daukan ta ya kaita
bedroom d'in Mufidah ya kwantar da ita, sannan ya fito ya koma d'akin shi.
Kwanciya shima yayi kusa da Mufidah ya rungumo ta cikin jikin shi k'am kamar wanda xa'a kwace mishi
ita zuciyar shi fal farinciki wai yau shine rungume da Mufidah wadda ya fitar da ran samun ta har abada
sai gashi Allah yayi ikon shi ya same ta a lokacin da bai ta6a zato ba.
Kallon beautiful face d'in ta yake yana hashashen wasu abubuwa cikin zuciyar shi cikin nishad'i yayi
kissing lip's d'in ta yana nan kwance yana faman tunani har bacci mai dad'i yayi awon gaba da shi.
*After 1 hour*
A hankali Mufidah ta fara bud'e idanun ta har ta gama bud'e su gaba d'aya ba inda idon ta ya sauka sai
kan kyakkyawar face d'in Musaddiq yana baccin shi hankali kwance, tamkar ba bacci yake ba kamar irin
lumshe idanun shi yayi.
Wani smiling tayi kaunar shi tana ratsa ilahirin zuciyar ta da jijiyoyin jikin ta, wani mugun son shi ne yake
shiga cikin zuciyar, hannun ta ta sanya saman fuskar shi tana kyakkyawan sajen face d'in shi mai matuk'ar
kyau da tsari ga laushi har ta kai saman lip's d'in shi tana zagaye su da 'yan yatsun ta, tana murmishi ita
d'aya.
Ba zato taga Musaddiq ya bud'e idon shi ya sauke su kan fuskar ta, suka had'a ido yana mata wani irin
kallo mai tattare da ma'anoni daban daban.
"wayyo Allah nah, Allah yasa bai ga abin da nake mishi ba?"
Cewar Mufidah cikin zuciyar ta ga wata azababbiyar kunyar shi da ta rufe, d'aga mata gira yayi da sauri ta
sunkuyar da kanta tana mai murmishin jin kunya.
'Yar dariya yayi kad'an yana sake hugging d'in ta a kunne ya rad'a mata
"Mamin Afnan ya kika bari ki cigaba kinsan kuwa yanda nake ji kuwa? "
Nok'e kai tayi tana cusa fuskar ta cikin chest d'in shi tana girgixa kai tare da cewa
"ni fa ba abin da nake maka "
Cakulculi ya fara yi mata tana dariya tare da kok'arin kwace kanta daga jikin shi but ta kasa hkan, cikin
shashshak'ar dariya tana jan numfashi tace
"Musaddiq ka bari please".
Yana dariya yace
"ai kuwa sai na rama yarinya tun da kika tashe ni a bacci ko na kirawo Afnan mu had'u mu danne ki kowa
ya za6i inda yake so ya ciza "
"wayyo Allah kayi hak'uri baxan k'ara ba "
Ta fad'i cikin yanayin shagwa6a, nok'e kafad'a yayi tare da cewa
"nak'i wayon yarinya "
Nan ya cigaba da yi mata cakulculin sai da yaga tana kok'arin shid'e mishi ya barta tana mai da numfashi,
ido suka k'ura wa junan su cikin wani irin shauk'in son junan su suke ke kallon junan su kowanne da irin
abin da yake sak'awa cikin zuciyar.
Musaddiq kasa jure wa yayi sai da ya had'a lip's d'in shi da nata ya fara kissing a nutse yana yawo da
hannun shi cikin jikin ta, saukar lip's d'in shi a nata ne yasa ta lumshe idanun ta tare da sakin wata ajiyar
zuciya ya gama saukar mata da kasala.
Sun d'auki wajen tsayin 6 minutes a hka kafin Musaddiq a hankali ya zame jikin shi ya tashi kallon yayi da
idanun shi da suka yi ja yace
"tashi muyi wanka lokacin sallah yayi ".
Mufidah wadda tun da ya tashi suka had'a ta dukunkune kanta cikin kafafun ta tana murmishin jin
kunya, tana jin furucin shi ta yunkura ta sauka daga kan bed d'in kafin ya ankare ta kwasa da gudu ta bar
cikin d'akin.
Ba k'aramin dariya ta bashi ba amman ya danne dariyar yayi murmishi yana girgixa kai yace
"huh... Mufidah yarintar ki tana birge ni ina son ki da yawa Allah yasa ke ma ki soni koda rabin son da
nake miki ne "
Yana gama fad'in hka ya wuce cikin bathroom ya fara wanka.
Mufidah kuwa tana k'arasa wa cikin d'aki ta rufe kofar tare da jingina a jikin kofar tana dafe kirjin ta sai
lokacin gudun da tayi ya bata dariya nan ta shiga yin dariyar.
"Mamee lafia kike dariya ke d'aya? "
Taji saukar muryar Afnan a kusa da ita, hannu ta sanya ta d'aga Afnan tana juyi da ita cikin d'akin suna
dariya cikin farinciki da nishad'i kafin musamman ma Mufidah, ta sauke ta k'asa ta sanya hannun ta taja
kumatun ta cikin dariya tace
"ni da wannan rigimammen daddyn naki Afnan "
Zaro ido Afnan tayi tana kad'a harshen ta tace
"lalala Mamee daddyn nawa ne rigimamme? "
"Ehh mana ya cika rigima kamar wani boy "
Ai kuwa Afnan ta fara tuntsura dariya saboda boy d'in da Mufidah ta kirawo Musaddiq dashi, tana rik'e
ha6a kamar wata babba tace
"Mamee daddyn nawa ne boy ai kuwa xan fad'a mishi "
"ba sai kin fad'a min ba Afnan naji da kunne na "
Da sauri Mufidah ta jiyo suka had'a ido da Musaddiq yana sakar mata murmishi, da gudu ta fad'a toilet
tare da sanya key tana murmishi ita d'aya kafin ta fara wanka.
Bayan ta gama wankan ne ta d'aura alwala ta fito, ganin basa d'akin yasa hankalin Mufidah kwanciya ta
fara gyara jikin ta sai da ta gabatar da sallah tukunna ta d'an yi light make up kafin ta shirya cikin wata
pink gown colour d'in pink d'in mai d'an duhu kad'an bata kai har k'asa ba mai k'aramin hannu akwai
kwalliyar duwatsu bak'ak'e a jikin gown d'in.
Gyara gashin kanta tayi tare da d'aure shi da ribbon irin daga gefen nan tayi parking d'in shi tayi kyau
sosai, different perfumes tayi using dashi har dasu humra masu kamshi sosai, ta kalli kanta a mirror ta
tabbatar tayi yanda take so sannan ta zura bak'in flat shoes ta fito zuwa parlour tana tafiyar ta a nutse.
Tun daga nesa Musaddiq ya hango Mufidah tana taho wa yana zaune kan dining table shi da Afnan suna
cin abinci,sakin baki da hanci yayi yana kallon Mufidah gashi ya cika spoon da abinci ya kai kusa da bakin
shi amman ya kasa k'arasar dashi cikin yana kallon ta.
Har sai da ta k'arasa dining d'in sannan ta rik'e hannun shi da yake dauke da spoon ta k'arasar dashi cikin
bakin shi, sai a time d'in ya dawo hayyacin shi gashi ba bakin magana saboda abincin da yake bakin shi.
Sai Kallon da yake bin ta dashi tare da yi mata alama da hannun kinyi kyau ita ma da ido tayi mishi alamar
nagode suka sakar wa junan su murmishi kafin su mayar da hankalin su kan cin abincin.
Bayan sun gama ne Musaddiq ya kalli Mufidah yace
"ki shirya zamu fita yanxu"
D'an kad'a idon ta tayi tare da harshen ta wanda hakan ya tafiyar da Musaddiq zuwa wani wajen daban
tace
"ni ai na gama shirya wa mayafi kawai zan d'auka"
Cikin salon tsokana tayi mishi maganar, hararar ta yayi kafin yace
"ai ba tallan ki zan je yi ba, idan baki son zuwa sai mu tafi da Afnan "
Cikin sauri ta mik'e tana cewa
"tabd'ijam kama fara ai idan baku tafi da ni kuma ba inda xaku je "
Tana k'arasa fad'in hka ta wuce bedroom Musaddiq ya bita da kallo yana had'iyar yawu sai da ta shige
bedroom kafin ya dauke idon shi ya furzar da d'an huci yana cewa
"huh Mufidah rigima don kinsan bazan jure ba ne shi yasa kika fad'i hkan "
"daddy ita ma Mami rigimar ce da ita naji d'axu ma tace maka rigimamme? "
Hannun shi yasa yaja karan hancin ta yana murmishi yace
"Ohhh Afnan surutu ba na hana ki tambayar komai ba? "
Langa6e kanta tayi gefe guda tare da cewa
"Sorry daddy na dai na "
"Yawwa 'yar albarka "
Cikin shagwa6a tace "ni daddy big teddy bear xaka siyo min wadda tafi ta gidan mumy girma "
"Angama baby na za'a siya miki "
Rungume shi tayi cikin murna tana cewa
"thank u so much daddyna "
Kissing d'in ta yayi a kumatu yana k'ara rungume ta, yana son Afnan sosai jin ta yake tamkar sadeeq,
tunawa da sadeeq da yayi ne ya haifar mishi da kewar d'an uwan nashi addu'a kullum idan yayi sallah sai
yayi mishi wani lokacin ma idan tunanin shi ya fad'o mishi xai yi mishi ko kuma idan ya d'auko picture d'in
su wanda suka dauka a tare yana kallo yana kewar d'an uwan shi duk jikin shi yayi sanyi surutun Afnan
ma sama sama yake jin ta..............
Aishat A Muh'd ✍
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*
*Written by*
Aishat A Muh'd
♻ *£xclusive Writers Forum*
*Likes nd comment's fb page*
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
Email:Aishataudimuhd.as@gmail.com
*PAGE 55*
Mufidah ce ta fito cikin wata gown milk colour da adon flowers bak'i tayi rolling kanta da black veil tayi
kyau, tana k'araso wa parlour inda suke tace
"ai na d'auka kun tafi kun barni? "
D'ago kanshi ya kawar da duk wata damuwa a fuskar shi ya kalle ta tare da cewa
"kinci darajar Afnan da tace mu tsaya ki amman da tuni mun tafi "
Turo bakin ta tayi irin na shagwa6ar nan kafin tace
"ni na fasa fitar ma ku tafi "
Kallon Afnan yayi tare da cewa
"tafi mota ki zauna gani nan "
Cikin murna Afnan ta fice da d'an gudun ta, kallon shi ya mayar kan Mufidah yana cewa
"haba habibty ki taso mu tafi kinsan bazan ji dad'in fitar ba idan ba k.... "
Ganin yanda Mufidah take kallon shi ne yasa shi tuna su6utar bakin da yayi ya wayance da cewa
"ba fah da wata manufa na fad'a ba kada kiyi tunanin wani abin "
Ya k'arasa fad'i yana tashi tsaye, girgixa kai Mufidah tayi tana murmishi cikin zuciyar ta mai cewa
"ina mamakin wannan halin naka Musaddiq, kana barin abu cikin zuciyar ka ni kuwa zan sanya ka ka furta
min sona cikin zuciyar ka a yau ba sai gobe ba insha Allah, tun da na gano ko wace sweet babyn ka "
Tana k'arasa fad'in hka cikin zuciyar ta ta saki murmishin mugunta tare da mik'e wa tsaye, kallon ta yake
yaga tana ta zuba murmishi ita d'aya yace
"lafian ki qlau kike murmishi ke d'aya? "
D'an murgud'a mishi baki tayi tana cewa
"lafiyan kenan "
Tana gama fad'in hka ta fice da sauri zuwa compound d'in bin ta yayi a baya yana murmishi shima cikin
zuciyar shi yana cewa
"yarinya yau zaki yi bayani don sai kin furta min abin da yake kunshe cikin zuciyar ki tukunna zan fallasa
miki sirrin zuciya ta ".
Sun zazzagaya wajen shak'atawa dasu mall sosai sun yi shopping abubuwa da yawa musamman kayan ci
da na sawa abubuwa dai da yawa, tuni Afnan ta gaji har bacci ya kwashe ta a mota tana rungume da
sabuwar teddyn ta.
Daga k'arshe suka wuce wajen wani beach bayan yayi parking d'in motar shi ya sanya mata key suka jera
suna tafiya ba k'aramin kyau da dace wa suka yi da junan su ba, d'an satar kallon Musaddiq tayi